Showing 6001 words to 9000 words out of 115153 words

Chapter 3 - DANGIN RABI COMPLETE

23 Aug 2025

1528

sallama muka Yi musu suna ta dariya mace Daya ce ta amsa Mana wata Dattijuwa Fara kyakyawa Tace Rabi kune a garin yau? Ya Yan Uwa da mutan gida? Muka Ce lafiya Lau,Wata cikin Yan Matan ta kalle Ni tace Amma fa wankan Nan yayi zanzo aron Glass,Ni nayi tunanin da gaske ne nace Na gode sai na bar Miki ma kyauta,dariya suka sake saki ta wulakanci,wani matashi dogo Kyakyawa yace Bari na muku pics yau na Samu na status,bamu San ma'anar status ba Munga ya Fara daukan mu hoto da makekiyar wayarsa.

Nace Hoto zaka Mana Bari na gyara to ai suka sake sakin dariya,Ni kuwa ba ruwana na sa Hannu biyu bisa kugu na na dafe irin Yan Matan Nan na cuno Baki nace Bismillah dauki ai kuwa Suka sake sakin dariya matashin Nan Yana ta Daukan mu Hoto,Saude kuwa fuska ta Bata domin tasan wulakanci ake Mana,Ni kuwa ko a jikina Ni ba komai ke Bata min Rai ba,sai da ya Gama daukan Hotonsa sannan yace na Gama Ni kuwa nace Na gode na tsaya a gefe tare da cogewa.

Cikin takunsa na mazaje masu ji da kansu cike da Izza da takama irin ta mazan kwarai ya tako Yana kamshi Yana zuwa muka ga yan aiki suna ta kwasar gaisuwa Yana daga musu Hannu da kyar,Yana karasowa gaban Yan Uwansa sai muka ga Yana ta Rungume su Daya Bayan Daya suna Masa magana cikin turanci Barka da Zuwa, Yan Matan suna cewa sannu da zuwa Abban Momy, Mazajen Kuma Sannu da dawowa Bro Fu'ad muka ji suna cewa Duk da bama Jin turanci mun Gane sannu da zuwa ake Masa,Iyayen Mata Kuma cewa suke Yi barka da dawowa Yaya UK? Tsabar yanga ko amsa baya Basu bare muji muryarsa kamar wani Ubansu.

Ganin Haka yasa Nima na matsa layin masu gida da sauri,sai da ya Gama Rungume su tsaf sannan Nima na wara Hannayena kamar yanda Naga suna Yi nace Ayi mini Nima,ai kuwa har su Rabi suka kwashe da dariya,Yan gidan harda rike ciki,shi kuwa gogan ko kallo ban ishe shi ba ya wani Bata Rai kamar zai Masge Ni yaja uban tsaki ya juya da niyyar wucewa,ban Hakura ba nace mu fa? Baza kayi Mana ba? bakuwar Alkhairi ce fa,Rabi ce ta Fisgo Hannu na tana cewa Rumaila mene Haka Wai so kike ya mareki,Baki na cuno tare da furta to mu me Muka Yi Maza? Kamar Wanda muka Masa kashi a gado ai ya kamata muma ayi Mana rungumar Kara.
Ko kallo na baiyi ba yaci gaba da tafiya cikin Izzarsa da Gadara abin sai Wanda ya gani,Yan gidan ma rufa Masa baya sukayi,Dattijuwar da ake Kira da Nenen kauye ita ce tace Rabi kune kuka Zo? Da sauri Rabi ta karasa wajen tsohuwar Tace ku taho muje sashena kawayenki ne suka Zo gaishe mu?Rabi Tace ae Nene,kin San Yan gidan Nan ba wani kulaku zasu Yi ba me yasa Baki taho bangare na ba? Kuzo muje,Haka Muka bi tsohuwar wato Nenen kauye.

Part dinta daban a gidan muka wuce tafiya me Dan nisa sai kallo mukeyi gidan ya Gama kashe mu da kyau,part dinta gwanin birgewa Palo kasa da sama ga dakuna kasa da sama,bangaren Dining daban ga kitchen da store ba abinda Babu na girki a ciki itama Yan aiki suna ta Mata Hidima,Nenen kauye Ta nuna Mana wani daki Tace gashi Nan dakin da zaku zauna ta Furta tana kallon Saude tace ke kinyi Shuru ko gajiya ce? Murmushi Saude tayi har ga Allah Yan gidan Basu Yi Mata ba sun musu wulakanci da Raina Dan Adam,kamar ba mutane ba Haka Suka dauke su badan Nene ba kenan Haka zasu barsu a waje can compound.

Bedroom din muka Shiga Rabi ce ta nuna Mana yanda ake amfanni da toilet sabo da ita tana zuwa ta koyi komai,Wanka na farayi da Brush na fito,Suma su Rabi sukayi,Wata jemammiyar doguwar Riga nasa ta wani Yadi Baki ta tsingile min kauri na gaba Daya a waje yake ganin a cikin gida nake ai sai kawai na tufke jelar gashi na Tana yawo a tsakiyar bayana sannan na rataya radio ta Kamar jaka Amma ban kunna ba na fito Haka Palon Nenen kauye, itama dake gidan Yan Boko ne Bata min fada ba,sai ma washe min Baki da takeyi tana cewa sannu Bakuwa Wai ya sunanki ne? Rumaila na Bata amsa tace masha'allah suna me Dadi,Saude CE itama cikin Atamfarta Riga da zani sabuwa, Saude su dama iyayenta suna musu sutura tana da masu kyau dai dai talakan kauye,Rabi ma Haka ta fito cikin Doguwar Riga baka ta Makka da babansu yaje ya siya musu,Abinci Nene tasa Yar aiki Tace Tasalluwa kawo musu Abinci,Tasalluwa Yar aiki da sauri ta cika Mana gabanmu da kayan Abinci.

Wani kamshi Muka ji ya daki hancinmu sai Kuma muka ji sallamar Namiji da wata murya me Dadin gaske,Uhmm kaji Muryar Yan birni to Ana Shan shayi kullum Haka na furta a zuciyata,Nene ce Tace barka da shigowa Abban Momy ayiwa bakinmu afwa Abinci zasu ci ba sai sun Fita ba,Bai ko kalli Inda muke ba mune muka bi shi da kallo kamar mayu,Plate Daya na Bude na abinci Naga katuwar kaza guda an Mata Wani irin gashi kamshi ya buge Ni a hanci,cikin razana da rudewa na kalli kajin nace Alqur'an kaza,Rabi Billahillazi Rahmanu kaza ce,Saude ma ta sake leka kanta ta bugi cinya tace kwarai kuwa Yasin itace irin wacce ke turo Murfi gaba,irin wannan kalarta Bata rufuwa sabo da girma,Rabi tace na Rantse Saude,Saude tace Da Uwata Rabi kaza ce guda,Nace da a Garinmu ne yaushe zanci wannan ai sai dai na kiwatata ta dinga kyankyashe min 'ya'ya Amma Yan Habuja Basu da wayo wallahi.

Fuskarsa kamar zata fashe sabo da bacin rai,Nenen kauye tace Abban Momy me zaka iya ci? Ko magana Bai Yi ba ya mike ya bar Palon Yana zuba uban tsaki,Nene tace oh Kai Muna Dama da Fu'adu a gidan Nan magana ma Sai ya yini Amma bazai ce kala ga kowa ba sai Dole,Nene na kalla nace to sabo da me? Rabi Tace Haka yake ai ko surutu Kika cika Yi Masa sai kansa ya Fara ciwo,wani matashi ne wankan tarwada ya Fado Palon Nene Yana masifa,Nene Tace lfy Kai Kuma Islam? Haba Nene wanne irin yawa ake Mana ne,Kina Jin Abbi Wai bazai min Auren yanzu ba,shike Nan Ni haka Zan Zauna a banza Ina kallon Mata suna juya duwaiwuka,Kwarewa nayi da Abinci Jin kalaman Islam,kunya ta kamamu Muka Yi tsilli tsilli,ci gaba yayi da cewa Ina ji Ina gani waccen ta wuce tana murguda Duwaiwai,waccen ta Mulluka shi can idan ba so ake na Mutu ba Ina da Yarinya ta a barni Mana nayi auren Ni bance kowa ya taimaka min da sisi ba,to wallahi kiwa Abbi Magana tun kafin na zuciya na Fara abin kunya Kuma wlh ta Kan Matan yan gida Zan Fara ta Mata yaran Yan Uwa Zan Fara Wanda ake rikewa, da Sauri nace mu Baki ne wallahi,Harara ya watsa min, Nene Tace To uban rashin kunya Ni kake fadawa Maganar banza? Ko Abban Momy baiyi Aure ba Sai Kai,to layi ake so na bi kina gani Fu'ad baya kallon ko wacce mace da mutunci sai na tsaya jiransa,gaba daya layi yaki ja ya cunkushe, ai wallahi layi ya bar kansa Fuuuu yayi waje abinsa,Fu'ad ne ya sake shigowa da Gadara ganin Muna Nan ya sake Jan tsaki ganin Haka sai Nene Tace Rabi kuje Bedroom kuci zamuyi magana da Yayanku.

Bayan mun tafi lokacin yayi ya dawo wajen Nene fuskar nan murtuk,Saude Tace Kan Uba mu leka mu kalli kyau,har Rabi Muka dan tura kofar Room din da muke ciki kadan muka leko da kanmu Muna kallonsa,Saude ta dafe kirji tace wayyo sonsa zai kamani,a hankali na rada musu kunji Maganar sa me Dadin tsiya, magana yayiwa Nene Abinci can Yan aiki ne Suka dafa kin San Kuma ban cin abincin Yan aiki,Rabi tace shegen Iyayi ne da shi ita Kuma Nene ta mike da kanta ta Shiga kitchen Yana faman latsa waya sanye cikin wani danyen Yadi fari Kal yayi kyau matuka,Muna kallo Nene ta kawo Masa abinci iri iri harda zuba masa da kanta,nace Rabi Wai me yasa ake sonsa ne kowa a gidan sai abinda yace akeyi? Rabi Tace yo ina Zan sani Nima Haka muke gani har Abbinsu Haka yake ji da shi,Ku dai kiyaye idan Kika shiga gonarsa wallahi Mari Zaki Sha bashi da mutunci ko digo, watarana kallonsa kawai nayi ya Mare Ni.

Har ya Gama cin abin cin nan muna aikin kallonsa har ya fita Bai sani ba,Da wuri muka Yi bacci da dare sabo da gajiyar hanya,bamu iya baccin safe ba da wuri muka farka,bayan na Idar da Sallar Asuba fitowa nayi Rabi Tace Ina Zaki da Sassafe Nan gidan ba a tashi da wuri,Ni dai kin San tun daga kallon wani film din India Naga suna Iksasayin (Exercise) Nima na koya nake Yi kullum da safe gashi har abin ya Zama idan banyi ba bana Jin Dadi,Saude tace ayi lafiya wanke wanke da shara ma ya ishe mu motsa jiki, Ficewa nayi da tsangalalliyar Riga ta Da gudun tsiya na fito Kamar guguwa, Yan mazan gidan na gani suna ta motsa jiki suna tsalle da Dan gudu a cikin katon gidan,Girman gida ya Isa ba sai an fita ba,Wani na hango cikin fafaren Kaya Riga da wando Kaya na motsa jiki yana Dan gudu kadan,Ni kuwa na shararo da uban gudu na wuce shi Kamar Iska,Mamaki ya Kama mazan Dan sun San kaf Matan gidan su ba wacce take motsa jiki,Ni kuwa ban kulasu ba idan na kwashe da gudu sai na Kai karshen gidan Zan dawo na Kai na dawo,Daga Nan na dawo cikin Mazan Nan na Fara tsalle tsalle.

tsabar Jin kansu Babu ma Wanda ya ko kalle Ni kowa harkar gabansa yakeyi,su irgawa suke Yi suna one, two, three,four etc Ni kuwa Dan suce ta Gari ce sai bana irgawa sai dai na Fara cewa Subhannallah Daya Subhannah biyu Subhannallah uku da sauran su,Wani cikin Mazan ya galla min Harara yace Wai wannan daga Ina Haka? Ko a Dangin dangarere ban santa ba,sauran suka ce nima Haka Yar kauye ce ko aiki tazo Yi, Fu'ad ne yaja tsaki tare da komawa Part dinsa irin na dame shi din Nan,sai da na gaji sannan na koma cikin part din Nene.

Dakinmu na shiga nace Saude Rana tayi kuzo muje mu gaida masu gidan mu Taya su aiki Kar aga bamu da Tarbiyya,Rabi tace akwai masu Aiki ba abinda za a ce muyi,nace ba Tarbiyya bace kazo gidan mutane ka kwanta ko basa so ya kamata mu danyi wani Abu,Saude tace wlh tsinke bazan dauka duk wulakanta mu da suke Yi,Rabi ma Tace ba aiki ne ya kawo Ni ba,Ni kuwa nace zanyi Ni dai,ai Baki da zuciya ke Saude ta furta nace ae Ni ba abinda ya Dame Ni,Fitowa Muka Yi Nene Muka Fara gaisarwa ta amsa da Fara'a Tace Rabi kin San ko Ina Abbi ma Yana Gari kuje ku gaida su,to Muka ce Muka fito,Rabi Tace wannan gidan ko an gaishe su ba ruwansu Basu da mutunci Ni bazan Bata lokaci na ba,Itama Saude tace Nima Haka wlh,Nikam nace ki raka Ni Rabi sai ki dinga tsayawa a waje Ina gamawa sai mu tafi.

Haka kuwa aka Yi muka tafi,Part din Abbi Muka Fara zuwa Rabi ta buya daga waje Ni Kuma na shiga ciki a hankali,Sa'a naci Yana zaune a Palo shi da wani Abokinsa Babban mutum suna magana akan siyasa,a hankali nayi sallama cike da nutsuwa,Dake maza ne a mutunce Suka amsa min Abbi fari tas me Kama da Fu'ad yace karaso Mana,a gabansu na durkusa tare da gaishe su,Suka Amsa Abbi yace Nene Tace munyi Baki su Rabi ko? Ae na furta,Ina su Rabin? Ya tambaya na ce tana cikin gida Bacci sukeyi zasu Zo su ma,Godiya ya min na mike na fita,Ina Fitowa muka shiga part din wata matar da suke Kira da Umma,Umma Fara ce tas Kamar Balarabiya suna mugun Kama da Fu'ad,Ina shiga da fara'a sai na ganta a Dining tana Hada tea,Fu'ad na gani kwance a wata arniyar kujera 3seater Yana kwance ya mike.

Tsoron sa ya kamani akwai Kwarjini wani uban kamshi yake zubawa sanye cikin 3qutr da t-shirt Maroon yayi kyau Yana uban sheki,Umma ce ta kalle Ni da fara'a Tace shigo Mana Bakuwa,a nutse na Karasa gabanta tare da Durkusawa har kasa nace Ina kwana? Lafiya Alhmdllh,ya gajiya? Ina Su Rabi fa? Karya nayi Mata nace Basu tashi a bacci ba idan sun tashi zasu Zo su ma su gaida ki,To na Gode Dattijuwar ta furta,a tsorace na koma Gaban Uban Yanga da takama Fu'ad Yana latsa waya,Shima Dukawa nayi nace Ina kwana? Shuru ba amsa,na sake cewa ka tashi lafiya? Nan ma Shuru? Nace Allah yasa ka yini cikin koshin lafiya,Allah ya rabaka da duniya lafiya,Allah yasa ka mutu kana musulmi,Allah yasa Idan ka mutu ka kwanta lafiya cikin kabarinka yasa a kabarinka ba Kunama ko miciji Wanda zasu dinga galla maka cizo,Allah ya rabaka da kiyashin lahira da tururuwa tare da Sauron lahira me malaria ta lahira,kasan Sauron lahira shi ba Malaria yake zubawa ba Cancer ce take Kama mutum a kabari sabo da Gubar jikinsa,Fu'ad Yana jinta dariya ta Kama shi Amma ya danne abarsa da kyar,ita kuwa Umma cewa tayi tashi ki kyale wannan ba kulaki zaiyi ba an gode.
Mikewa nayi na fita Rabi tace kin gani na fada Miki wlh gidan Nan Basu damu da gaisuwa ba kina batawa kanki lokaci a banza,Umma kuwa Fu'ad ta lullube da fada Haba Abban Momy yanzu ka kyauta kenan? Ni wlh bana son wannan halin naka Sam,ayiwa mutum shedar kirki ai arziki ne,ko mutuwa kayi zaka samu yabo wajen mutane Amma kowa yazo gidan Nan sai ya tafi da sunanka a Baki bana son Iskanci wlh,Mikewa yayi zaune yace Umma I'm sorry idan Ranki ya baci Ni bana son magana ne Haka Allah yayi Ni,ka dorawa kanka dai gaskiya ka gyara, Alright Zan gyara kiyi hakuri ya furta tare da Mikewa ya Isa Dining.

Part din wacce ake Kira da Mama na Shiga itama part dinta sai Wanda ya gani ya tsaru,Yan Mata su Hudu na Iske a bangaren sun Sha gayu Suna ta faman Danna waya maka maka,Suna ganina suka Fara tuntsura dariya irin Yar kauye,Suna kus kus,ko a jikina Ni ba komai ke bani haushi ba,Mama ce ta fito Tasha Shadda tana wani taku dai dai,tunda ta ganni take wani Bata Rai tana min kallon wulakanci da kaskanci,Har kasa na duka tare da gaisar da ita Amma sai ta daka min tsawa tashi ke bana son gaishe gashen ku na mutanen kauye,ba abinda kuka sani Sai gaisuwa Jahilan banza,idan na sake ganin ki a part dina sai na sa an Zane ki shegun yara,in Banda rashin mafadi mu fa bamu San ku ba Amma kun biyo wata kawa kunzo wajen Dangin Rabi,to kawar taku ma bamu da wata dangantar kirki da ita,daga anga masu kudi sai a Fara kakalen dangi,Yan Matan Suka sheke da dariya Suna Tafawa,Rabi tana daga waje Bakin kofa tana Jin komai to tana Allah ya Kara,Mikewa nayi na fito Rabi ta dinga min dariya Amma ban kulata ba Kuma ko a jiki na.

Part din Babbar su Muka shiga Uwar gida Momy itama wasu Yan Matan da maza biyu a sashenta suna karyawa a Dining,sallama nayi Suka amsa ko kallo na Basu Yi ba na durkusa na gaishe su Amma da kyar Momy ta amsa tana wani Bata Rai sum sum na mike na fito Muka koma Part din Nenen kauye,Abinda muke so shi Muka karya da shi Muka goge bakinmu da tsokar nama,Bayan munyi wanka munci kwalliyar mu ta mutanen kauye na Samu Nene nace Dan Allah Dan Ara min Wayarki Zan Kira Iya ta na fada Mata mun Isa lafiya,Nene Tace wuu rufa min asiri Baki ji sunana ba Nenen kauye ai Ni tsoron waya nakeyi ban taba siye ba,an siya min ma naki karba Haka kawai Ni tsironta nake ji,Dariya mukayi Nene Tace je ki bangaren Umma itace kadai me mutunci a gidan Nan ita zata Kira Miki babarki,To na Furta Muka tafi tare da Rabi da Saude.









AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈







FREE PAGE





DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM







NA KUDI NE

SHIGA GROUP DARI BIYU 200


ACCOUNT NUMBER
0175487861 ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK.


MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39






3












Official







By
AsmaBaffa












PAGE NAKU NE

FLOWER
ZAINAB GARBA BUTALAWA
ZAINAB SABO











Shigar mu part din ke da wuya muka Iske Umma Tasha Wata Arabian Gown ta manyan Mata masu ji da kansu sai sheki takeyi,Fu'ad ne ya shigo cikin wani Danyen Yadi Brown ba karamin kyau yayi ba,agogonsa Apple,Takalminsa Kam irin Half cover ne me Arnen kyau da Alama Unguwa zasu fita,idanuwansa masu mugun kyau ya zuba su cikin Nawa Nan take wani tsoronsa ya sake kamani da sauri na janye Ido na tare da Furta Sannu Oga,duk na rude sai na kasa tambayar abinda ya kawoni kawai nace Sai anjiman ku muka Yi waje a tsorace,Fu'ad ne ya kalli Ummansa yace Umma wannan ba Yan uwan Abbi bane? Rabi ce Yar Uwa kawayenta ne su biyun cewar Umma,Amma Ana kallonsu suna yawo a gida da kazaman Kaya?ni wlh idan na

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login