Showing 63001 words to 66000 words out of 115153 words
gyaran jiki,Ina fitowa naga Fu'ad zai shigo wajen Umma,yace Ina Kuma Zaki tafi again? Gyaran jiki,Ni me zanyi da jikinki idan Dan Ni ake gyarawa a daina Babu abinda zanyi da gyaranki,Nace kayiwa kanka,,Kuma kayi ta yangarka bashi kake ci Allah sai na rama Nan gaba,sai na juyaka zaka sani ne,Nafi karfin mace ta juyani,Namiji ne Ni na gaske,nace zamu gani ne wlh sai ka min wanka, Fu'ad ya tintsire da dariya yace ai wannan love ne Sunna ce Guda ki canja wani Abun,nace sai ka dinga kaini Unguwa,kana dauka na, Nan ma duk love ne ya furta,tafiyata nayi Ina fushi.
Gaba daya wani mugun kyau nayi sabo da gyara,bangaren su Momy ko kulamu basa Yi sunce baza su je biki ba,Umma tana Jin shirye shiryen su da suke Yi Akan ranar bikin sai sun tozarta Ni sai sun kunyatani sun kawo Yan Sanda a Gaban mutane sun kamani,Umma ta samu Abbi ta sanar masa kudurinsu,Abbi yace ai baza ayi biki ba Ana daura aure ba abinda za ayi Amarya za a Kai dakinta sabo da Aljanu ne da Rumaila Bai kamata ma Sam ayi Kade Kade ba,munyi Maganar da Fu'ad ma,hakan ma yafi cewar Umma.
Biki ya rage saura sati daya Fu'ad ya bani Kudade masu yawa ko zanyi wani Abu,Lefe kuwa Akwati goma Sha Uku aka hada min,Kauyenmu duk Yan Uwana sai da aka bawa Iya da Affa Iv na biki na Amma Iya ta boye Taki rabawa,Affa kuwa konawa yayi gaba daya, Fu'ad gidansa na gani na fada ya tsaru karshe Bamu da nisa da gidan Abbi,Abbi da Umma sun zuba min kayan daki na gagara komai an shirya ko Ina ba inda ba azuba Kaya na gani na fada ba,an kashe kudi,Gaba daya anyi komai a nutse har kayan Lefe na Dana sawa ta duk an maida su gidan,Haka na Fu'ad ma komai Yana can sai Wanda zamu sa na biki Kawai,duk abinda ya Dace anyi ankonsu Yan Islamiyyar mu da Yan makarantar Boko Wanda muke shiri dasu.
Bangaren Fu'ad ma hakan ya Gama komai abokai sai shiri sukeyi duk da ba Wani Event da za ayi,Ana gobe daurin Aure Nasha gyaran gashi da Lalle me kyau kowa ya ganni yaga Amarya,Kawayena tare da su muka kwana,Baki Yan Uwa da sauransu duk sun zo,Ranar Asabar aka daura Auren Rumaila Ahmad da Fu'ad Suffiyan Jawa kan Sadaki dubu dari,Naila ce ta Dakko Dj,anyi rawa anyi liki anyi Hotuna da duk abinda akeyi na al'ada,Rabi sabo da bakin ciki barin gidan tayi gaba daya sai dare ta dawo,Jin Ana Shirin kaini dakin miji na fara ciwon kan karya harda kuka,Nene Tace karya ne wlh sai Mun kaita yau,Haka aka sani a gaba nayi wanka tare da canja wani shegen material me tsadar gaske Riga da skert aka shiryani,Ina ta kuka Ina tuno Iya da Affa sune Kawai suke fado min a raina,Bayan an kaini a gurguje mutane suka tafi aka maida su gidajensu sabo da Hadari gagarimi da ya gangamo.
AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈
NA KUDI NE
MASU FITAR MIN DA NOVEL BAN YAFE BA,DUK WACCE TA KARANTA BATA BIYA BA BAMU YAFE BA.
DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM.
56-60
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne
Ummin Hibbah
Khadijamuhammad
Maryam
Ummi Deejat
Momyn twins
Mmn Ummee
Ransa a bace ya kalle Ni kamar nice na kwala masa Handle din,yace tashi ki tafi Dakinki Yana hararata ,Mikewa nayi sum sum na tafi Ina ta tsinewa Salahu,nace Allah wadaran halinka tsohon Dan Iska azzalumi,ya jawo Mijina ya tsaneni,gani nakeyi kamar laifina ne ko da dare ban leko ko Palo ba,washe gari bayan na Gama shirya Karin safe eban nawa nayi Zan koma bedroom dina sai ga Fu'ad ya fito cikin wasu kana Nan Kaya rigar me dogo hannu, ya zuba kyau,kallo daya na Masa tare da dauke idona Zan wuce caraf ya riko Hannu na,Kallonsa nayi kamar zanyi kuka nace kayi Hakuri ba laifi bane,murmushi ya saki tare da furta Haba Amarya bakya laifi I'm sorry,Abincin Dana eba ya karbe tare da ajiyewa saman Dining shi ya ci sannan yayi Amfani da Tissue wajen Goge bakinsa,Kallonsa nake Yi nace Baka ce yayi dadi ba? Dankalin turawan dake gaba na ya sake cin guda daya tare da furta yayi dadi,Zan fita bazan dade ba Zan dawo,Ka dawo da wuri please tsoro nake ji, Inshaallah yace,Ina zaka je ne Wai? Wajen me magani zamu je da Abbi mu dakko shi Gidan Nan ki Sha Rukiyya,Surori masu zafi Zaki Sha yau,Murmushi na saki nace kace Tilawa za a zazzagar a gidan Nan Allah ya Bamu sa'a.
Ameen ya furta tare da juyawa zai tafi sai zuuuuu wandonsa ya fado kasa gaba daya ya rage sai Boxers,ga rigar Bata da tsayi me dogon hannu, ya ka hango Fu'ad Reader, Dariya ce ta kwace min na duka kasa na sake jawo wando Amma sai ya kama Kamar gaske sai ya sake fadowa Kuma ba yawa yayi Masa ba bare ace,wandon ya karasa zarewa daga shi sai Boxers sai rigarsa, Zama yayi yace yaji za a Kira me magani ya hanani tafiya,Yana kwance a Palo a Haka ya kwanta yasan aikin Salahu ne,har na Gama gyara ko yana gidan Bai fita ba,sai da yasa wando sunfi Uku Amma da yayi niyyar fita sai wando ya Fado kasa, tuwon Danyar Shinkafa nayi miyar zogale ta Sha nama nasan Yana sonsa,Da Yamma 5pm Yana Garden Yana karanta Jarida Ina Palo na kunna kida a manyan speakers Dina Sai ga Kawayena Laila,Hafiza da Zabba'atu,Ihu Muka saki tare da rungume juna,Laila Tace kut gaskiya kin Gama hayewa irin wannan gida haka Rumaila kamar baza a mutu ba,nace kafin a mutu na samu rabon ai,Sai ki dage da karatu ki Kara wayewa,musamman turancin Nan Rumaila ya kamata ki goge har yanzu Baki iya ba sai kadan kadan cewar Zabba'atu.
Nace Ni fa yanzu abinda ya dameni yafi karfin wani turanci Bari dai na dakko muku littafina na English Lesson ku Dan tuna min wani waje,jakar Islamiyya ta na dakko tare da dakko littafin English Dina, Laila ta karba ta duba Tace yanzu sabo da Allah Rumaila wannan ne Baki Iya ba? Opposite ne fa gashi Opposite na Good shine Bad,Nayi tunani Bath na wanka take nufi nace yo Ni me zanyi da wannan, wanka ai sai Teku,idan wanka ne ki tafi Teku shine zakiyi Good Bad,Dariya suka dinga Yi,Hafiza Tace ya kamata kije kiga Likitan kwakwalwa Rumaila,Nifa ba turanci ne a gaba na ba,ku yara ne baku San Aure ba,mu masu Aure abubuwan sunyi Mana yawa,Duk cikinsu nasan sun girmeni Amma nace su yara ne, Basu Gama zaucewa ba sai da suka ga hadadde Fu'ad shine mijina,Sai Kallonsa suke Yi nace a daina kalle min miji.
Sai wurin magriba sannan suka tafi,Tunda nayi auren Nan Fu'ad Bai samu dama ko kiss ya min ba,Kuma yayi Hakuri Bai taba nuna min Yana Jin haushi ba,abin duk ya dameni Babu Wanda muka fadawa har na cika wata Guda da aure,duk abinda ya kama na matar aure ina yi,sai dai muyi Hira Kawai da Fu'ad ba Wani Abu da Muka Yi na aure,Bayan Magriba katsam sai ga Fadila da Mama sun shugo,Lokacin Fu'ad ya fita,a mutunce na tarbe su sai kallon banza suke Bina da shi,Jin nace Baya Nan ai sai suka Mike,Fadila Tace to me muka zauna Yi Wanda Muka zo Wajensa baya Nan,nace ai kuwa dai ya kamata ku Kama Gaban ku tunda Dan Uwan naku ya fita,Girgiza Kai Mama tayi Tace zaki ga abinda zai same ki,Nace Allah na tuba me kika Isa ki min karshe kice Zaki je gidan boka a turo min Aljani to Ina da su me ya rage Kuma Ni da nake da Salahu,kin San waye shi Salahu? To Dagaci ne a kauyensu Yana da yara a karkashinsa su kadai ma sun ishe ku, sai na turo muku shi zaku gane shayi ruwana,Momy taji tsoro tasan dukan data Sha, tafiya sukayi suna zage zage,Bayan sun tafi Zama nayi Ina tunanin Wai Ni me nayi musu ne? Me na tare musu haka.
Bayan wasu lokaci shi kanshi Fu'ad din sai Naga ya canja min ya koma Fu'ad dinsa na asali,ko abincina baya ci,baya kulani ko na Masa magana da kyar yake amsawa,abin ya dameni gaba daya,Na tambaye shi ko na Masa laifi yace ba abinda na Masa,a Bedroom dinsa na same shi ya zauna Yana latsa system dinsa,Me ya kawo ki?ya tambaya nace dama anjima nake son zuwa wajen Umma,ba tare da ya ko kalleni ba yace a dawo lfy,Wai wanne laifi na maka ne? Me.....ki fitar min a daki Ni bana son ganinki Kuma ba abinda kika min kije Kawai,shuru nayi tare da juyawa na tafi,Da Yamma Shiryawa nayi cikin lace me shegen tsada na Lefe na sai da na fito Zan tafi na ganshi a Palo yace na fasa barinki ba inda Zaki je,Kamar zanyi kuka nace Dan Allah kaji, baza ki je ba ya Furta da fada,Haka na hakura da zuwa sai a waya na Kira Umma muka gaisa,Bayan Kwana biyu sai ganinsa nayi kamar zai dakeni,Ina kitchen yace Ke zo ki tafi gidan ku,Ido na zaro nace lafiya? Ki tafi gidanku nace kuma karki sake na ganki a gidanmu can kauyenku Zaki tafi,kayiwa Allah karka Bari abinda Iya tayi ya dawo kaina,Iya ta kashe aure da yawa karka rama a Kan Yar Iya,Ni dai ba inda Zan taf.....Mari ya tsinka min,da sauri na dafe kumatu na,ganin yanda ya koma kamar wani Zaki da sauri na kwashi kayana da abubuwan bukata cikin Akwati katuwa na saka Hijab sai tasha,Kuma ikon Allah ko kuka banyi ba Ni dama bani da saurin kuka.
Nan take Hajiya ta Kori Iya Tace fitar min a gida ko wlh na sa Yan Sanda su kamaki,na Miki Uzuri sabo da naga ke garar Kauye ce,Iya ma Tace kamar yanda Uwarki take ba garar Kauye,Iya ficewa tayi tana masifa tace na fasa ma auren Sanatan,Tasha ta koma ta hau motar Jigawa Wanda a lokacin Nima Ina Tasha.
Iya ta koma gida da minti Goma har ta dora abincin dare Nima sai gani,da kyar na Gane gidanmu Iya ta canja sabon gini,Da kyar Iya ta Gane nice Rumaila,Mikewa tayi tana shafa kayan jikina Tace Rumaila kece kuwa? Kuka na saki nace nice Iya,Ina auren? Ya koreni yace na dawo kauyen mu,Iya tace kin ci Sa'a na yafe Miki na daina fushi da ke da yau sai dai kiyi kwanan Sauro a waje,to Allah ya taimakeki sannan ya kamata ki fara godewa Kudi domin su suka sa na yafe Miki,Kudi na gode muku na Furta,ki sake godewa Kudi,shuru nayi Iya Tace Baki ce komai ba Nace Kudi Na gode a Karo na biyu.
Zama Iya tayi na Bata labarin komai tun daga tafiyata Birni har yanzu Dana dawo,Iya Tace cab ke me ya kaiki Zama gidan wasu? Baki gajeni ba Rumaila,ai ko duniya za a bani akan a wulakantani gwara a barta,Bayan nayi wanka tare da Sallah tuwon dawa Miyar kuka Iya ta kwaso min a kwano, Tuwon na gutsira da miyar na saka a Baki,Kuka na saki nace Dawa fa? Dawa fa Iya yaushe rabon Dana ganta ma bare na ci Ni wlh ba Dadi,Iya ta kalleni Tace sun cuceki Rumaila Yan Birni sun Gama kashe Miki zuciya kar kici ki zauna da Yunwa,Iya Baki ga dadin bane Dan Baki sani bane Iya,Wannan tuwon ai yafi na semo Dadi cewar Iya,nace wannan sunansa tuwon Somun bata ba tuwon semovita ba,Allah dai yasa Bai Koro min ke da ciki ba? Nace Iya ai duk matsalar akan a samu cikin ne,na Gane Kan zancen cewar Iya,ai komai Hakuri akeyi da zaman aure, ke Dan yace ki taho sai ki kamo kafa ki tafi ai yanzu an daina yaji,Iya gaskiya wannan fadan naki Bai samu karbuwa ba,kema ai ba Zama kike Yi ba,aurenki Nawa sabo da Allah sai Ni yanzu Dan Kawai yace na taho,Gaskiya bazan ji wannan fadan ba sabo da ban taso naga kina hakurin ba,gashi yanzu an rama a kaina abinda kikewa wasu maza hakkinsu ya shafe Ni,Shuru Iya tayi Tace Kuma Haka ne fa.
Muna Zaune Muna Hira Iya Tace saura kadan na Zama matar Sanata Allah baiyi ba,nace to fa Ya akayi Bai tabbata ba?Iya Tace jiya Allah ya hadamu sai dai Uwar gidansa Bata da mutunci na fasa,Dariya nayi nace Iya a jiya kika ganshi Amma har aka kusa aure? Idan auren yazo sai ki Hana na gani Kuma wallahi Watarana sai na koma gidan Sanata ko matar tasa da Hajiya mero baza su san Sanda zanje ba,mijinki ya koroki Zaki dawo ki hanani Rawar Gaban Hantsi ,Allah ya Baki Hakuri Iya Nima ba Haka na so ba kaddara ce Kuma nasan zai zo ya neme Ni,Allah yasa naga kafarsa a gidan Nan wallahi sai na kwashe Masa Albarka,zai ci Ubansa Bari Allah ya kawo shi yace yazo biko sai na wanke shi tas da soso.
Baki Bude nace Haba Iya Ni dai wallahi karki ko Harare shi Haka kawai Aljani na ne ya jawo Bai da laifi,Iya yatsa ta ciza Tace Ina ma Allah zai sa Ana ganin Aljanu da har gidan su Salahu Zan je da tabarya na rotse Masa Kai,Nace Iya ko Ana ganinsu Salahu yafi karfin mu gidansa matakan tsaro ne ko Ina,Sarki ne ko Gomna a garin su? Iya ta tambaya,nace Dagaci ne,Tsaki Iya taja Tace dagacin banza Ashe shi Dan Kauye ne ma,Iya kibi a Sannu wlh Fu'ad Baki gani ba da safe ranannan akan yace zai je Nemo me magani Kawai wandonsa ya dinga fadowa,yin duniya wandonsa yaki Zama sai Boxers Dole sai fasa fita yayi,Tsaki Iya ta ja Tace wannan ne abin tausayi Dan wandonsa ya Fadi babu Wani laifin Aljani tazuge ne tela Bai Masa me kyau ba, ki bashi shawara yanzu Roba ake sawa an daina Tazuge,Iya kin San kuwa waye Mijina? Ga kudi ga kyau ga wayewa ga aji Amma ace a gaba na Salahu ya sutale Masa wando kasa,Iya Tace yo sai me? Ke ba matarsa bace ba sai ki Sha kallo ba.
Dariya da kunya Iya ta bani,nace Iya tsakaninmu akwai kunya fa,Kunyar me tsakanin Mata da Miji ?ke kika jawo ma ya Kore ki Baki gajeni ba,Baki gani ba Ni Namiji Yana so na Yana kuka Haka yake saki na dole,Amma ke banza kin Bari an Kore ki,Ni sai dai na Kori kaina ba dai a koreni ba,Ina Jin Iya tana ta kuri,washe gari tuni zance ya watsu Rumaila ta zo,abinka da Kauye har kallo na ake zuwa Yi,Mutane kullum cika gidan suke Yi,Yau ma da sassafe Ina hada Mana shayi Mata Suka shigo su shida,kafin su karaso Iya Tace ku dakata a Nan Hanne,duk mutum daya Naira ashirin,kudin kallon Rumaila duk mutum daya Naira ashirin kudin shiga,Kullum sai dai ku cika Mana gida Kuna kallon Rumaila a kyauta daga yau ba Mutunci Naira ashiri maza kuma Naira Dari dari,tunda Iya ta saka Harajin kallo na sai ta rufe gida,duk wacce tazo ko ba kallo na tazo ba Naira ashirin,Ba wacce ta biya sisi sai suka daina zuwa ko Kare baya shigowa inda muke sabo da sai ya biya kudi,Su Saude da Hajara an taho gulma Iya Tace Ashirin ashirin,Amma da son Gulma sai suka biya Naira Arba'in sannan Iya ta Bude musu suka shugo.
Ina zaune a tsakar gida sai gasu,Baki na Bude da Niyyar yin magana tunda kawaye na ne a da,Nan take Iya Tace marar zuciya rufe min Baki iya kudin kallo Suka biya Basu biya na magana ba,shuru nayi suna kallo na Ina kallon su,sun zura min Ido suna wani tabe Baki,Iya taji labarin abinda Suka min da akace nayi cikin shege,ko minti daya basuyi suna kallo na ba Iya Tace Ashirin dinku ta Kare kun kalli iya kudinku kuzo ku fita munafukan banza,Saude ta harari Iya Tace ai wallahi Bamu kalli iya na kudin mu ba,Dan wannan kallon ne ashirin? Iya Tace zaku fita ko sai na karya ku ta Furta tare da Dakko tabarya,da gudu Suka fice,Iya ta harareni Tace marar zuciya ke Kuma har wata magana Zaki musu aikin banza,Iya a tura musu aniyarsu Mana,Bada Ni ba bana turawa mutum Aniya Ni kowa ya min sai na masa,Nace Iya naje wajen Affa jiya,Iya Tace ke da Mahaifinki ku karanta can bana son labarinsa.
Tunda Fu'ad ya Kore Ni hankalinsa ya tashi ya kasa zaune ya kasa tsaye ko bacci Bai Iyawa,Abin duniya ya Masa zafi,kwana daya tsakani ya shirya yaje gida wajen Ummansa,Lokacin tana shirya Dining taji ya shugo ta amsa Masa sallamarsa,Hannun Umma ya rike ya janyeta zuwa Upstairs ba tare da yace Mata komai ba,Zama suka Yi a gefen gadonta, Fu'ad ya kalli Ummansa hankalinsa a tashe Yace Umma Rumaila ta tafi gida kauyensu,Gaban Umma ya yanke ya Fadi Tace sabo da me? Ni dai ban sani ba Kawai naji Ina Jin haushinta Kawai nace ta bar min gida,Umma ta shiga tafa Hannu tana sallallami Tace ka koreta Amma baka sanar min ba? Fu'ad cikin jimami yace Kuma Umma korar Kare na Mata Baki gani ba abin tausayi na mareta Kuma,Hannu Umma taci gaba da tafawa,shi Kuma yaci gaba da cewa tana ta bani Hakuri tana cewa me na maka Dan Momy me nayi maka Amma Umma sai da na koreta,Kuma fa nace kar ta sake tazo Nan ta tafi kauyensu,Dan Allah daina fada min abin haushi cewar Umma,ai gwara ma da ka turata kauyen Amma idan Yan gidan Nan suka ji labarin Nan ai mun Shiga Uku da dariya da gulma,Kuma kasan Abbi yaji wallahi sai ya ci mutuncinka, Fu'ad yace