Showing 27001 words to 30000 words out of 115153 words
suke wuce a flight,Ko da Suka sauka a Jigawa state Already Motoci Uku masu tsadar gaske Sunyi parking Daya motar Fu'ad ne shi kadai ya shiga sai faman fushi yake Yi an Masa Dole, Umma Tace mota daya ta ishe mu bana son kallon Nan na mutanen Kauye,ai kuwa mota daya suka shiga.
Har cikin kauyen motocinsu Suka gangara a hankali,suna ta kallon kauyen Fu'ad a ransa yace Dole yaran Nan suyi jahilci no wonder dama akwai kauye Haka a kasar Nan Allah sarki na tausaya musu suna rayuwa cikin kunci Allah mun gode maka, Ni kuwa Rumaila yau naje gona nayi ciyawa da yawa na siyar na samo itace da yawa na siyar har dubu Daya da dari biyar na Samu yau bazan je makwafta neman Abinci ba sai farin ciki nakeyi,Wata Kazata Dana ke kiwo Wanda Kawu ne ya bani ita gashi Bata yin Yaya juya ce,sabo da Haka kwadayin me ciki yasa na Samu na yanka kazar katuwa da ita na gyara ta a gidana Ni Daya na soya ta Tasha Maggi tayi Dadi sosai na zuba a kwano na rufe abata a dakina.
Taliya na dafa da miyar jajjage Lallai yau Dadi zanci,sabo da Haka na Kara gyara gidan fes da shi kana gani kasan akwai Tsafta a gidan Nan ko Ina fes Kal Kal,wanka nayi tare da wanke gashin kaina na shafa Dan Vaseline Dina sama Sama sabo da ana zafi,Vest Fara tas na saka tare da jean skert Wanda a gidan Su Fu'ad Khaleesat ta bani,Tabarma na Shimfida a jikin bishiyar tsakar gidan na kunna wayata Ina Jin gidan Radio Kamar yanda na Saba,gefe Kuma ga Guava manya manya a plate guda biyar Ina yankawa da wuka Ina ci,idan Ina cinta bana tashin zuciya bare Amai.
Su kuwa Su Umma kwatancen da aka musu Suka bi aka nuna musu har gidan su Rabi,ai Saude Hajara da Rabi suna Jin labarin mota a kofar gidan su Rabi Yan Abuja sun Zo da gudu Suka dawo gidan su Uku,Hajara Bata San su ba Tace Na Shiga Uku Kunga Bature da Shadda yayi shigar Hausawa,Rabi Tace banza shine Yaya Fu'ad din ai ga Umma ga Nene,Hajara Tace Yasin Nan gaba ko da tsiya sai Baba ya barni na biku Nima ko Dan wannan baturen ai naje inyi ta kallonsa,Rabi tace to shine fa Rumaila take wa karya Tace shine ya Mata ciki,Allah ya tsinewa me karya Kamar wannan me zaiyi da ita cewar Hajara,Saude ta tabe Baki tace Wai Dan taga a Kauyen Nan ana cewa tafi kowa kyau gata Fara shine take hada kanta da wannan,a can fa Baki ga shishigin data dinga Yi ba tana ta cusa Kai Rabi Tace Kuma ba kwar jini ba ita tasan inda ta kwaso cikinta yanzu haka ma Is Ilu me gadi ne yayi Mata.
Sai da Suka Gama zagin Rumaila tas sannan Suka fada gidan Suna washe Baki lokacin tuni su Umma sun shiga gidan,an sauke su ana rawar jiki,bayan sun gaisa da masu gidan sannan su Rabi,Umma Tace Rabi Ina kawar taku fa? Baki Rabi ta tabe tace ai tayi cikin shege mun daina kulata tana Nan da katon cikinta,Salati Umma da Nene Suka saki tare da furta Rumailan? Saude Tace ita fa Dawowar mu da wata uku ta Fara laulayi,Fu'ad Dake zaune gefen Momy ya Bude manyan idanunsa da mamaki Yana ganinta Saliha Amma ta aikata Haka Amma sai yace Jahilci ne yasa Bata San Mene Zina ba shi yasa Bari yayi Mata Uzuri,duk abincin da aka kawo musu Fu'ad Bai ko kalle shi ba,dama Umma tasan bazai ci ba sarkin Iyayi su dai furar su lafiyayya Suka Sha har pure water sun Sha,Nene taci shinkafa da miyar da aka kawo musu,Umma Tace Ga Iv dama Muka kawo na bikin Fadila Kuma bamu taba zuwa ba sai yanzu Abbi yace ya kamata a kawo muku ziyara,Baban Rabi da Mamanta tare da wasu Dangin su biyu Suka dinga godiya da cewa Inshaallah zasu Zo,Fu'ad ya zaro kudi Yan Dubu dubu Yana bawa kowa har su Rabi sun samu Dubu biyar biyar.
Umma tace ku rakamu Inda Rumaila take mu gaisa da ita da Iyayenta,Rabi tace Yasin ko mun raka ku baza mu Dade a wajenta ba Kar ace muma mun Zama Yan iska,Uwaku ku Baku San Kaddara ba cewar Umma.
Har gida na Rumaila suka raka su Rabi suka shiga Suka Iske Ni na tasa goba a gaba Ina ta ci gidana fes Haka Babu alamar ciki a jikina Kuma nayi wani haske nayi kyau,Dariya Suka dinga Yi min ban kulasu ba Suka ce to masu gashi har gadon baya sai a rufe ga Umma da Nene Nan sun Zo zasu ganki,Haka kawai naji wani farin ciki ya lullube Ni na washe Baki nace Dan Allah? Tunda Mata ne ai ba sai na lullube kaina ba zafi ne ya dameni kice kawai su shugo,ai kuwa su Rabi suka juya tare da cewa Umma Ku shugo tace anyi sa'a Bata tafi Gona ba Wai Dan su Bata Ni a wajen su Umma ai kuwa Har Fu'ad aka shigo da Sallama mamakin ganinsa ya kamani yayi wani uban kyau komai fari ya saka Shaddar ta Masa kyau,kwarjininsa yasa naji wani Iri na manta ma ba dankwali a kaina dama bamu Saba daura dankwali ba,gashi na ya zubo har tsakiyar bayana Baki wuluk da shi,Surata ya karewa kallo a boye Kamar waya yake dannawa,tabarmar na gyarawa su Umma shi Kuma na kawo Masa kujera ta zaman gindin Murhu,a Nan yayi magana Yana tsaye yace Miya zanyi ko tuwo da Zaki bani kujerar Mata na zauna,kaji yaro da Iyayi Umma ta furta,na kalle shi ya galla min Harara na dauke kaina cike da kunya nace Nan kauye ne irin wannan gare mu,Su Rabi Suka Fara Dariya harda cewa gare ki dai ai ke da wa? Share su nayi na durkusa na gaida su Umma Ina ta cin goba Dan Kar na tsaya na Fara tofar da yawu ko Amai,shima na juya na gaida shi da kyar yace lfy,su Rabi suna ta gulma ta,Allah ya rufa min asiri na shiga dakina Na ciko wani katon Tire na zubo musu taliya da miyata tana ta kamshi,kazar Nan gaba Daya Na zubo a plate me Dan kyau na kawo na ajiye gabansu,dama watarana indai Ina da kudi pure water nake sha,saura guda hudu na kawo musu shima.
Mamaki ya Kama su Rabi Ina na Samu kayan Dadi Haka? Umma Tace Inye Ashe Yar tawa Dadi kawai take ci,dariya nayi kadan Nace Kawu nane yake bani Ina kiwatawa shine ita Kuma wannan juya ce Bata Haihuwa na gaji da asarar Abinci na na yanka ta na huta,Umma tace baza muci ba Alhmdllh,rokonsu na Fara Dan Allah Umma kuci nasan kunfi karfinta indai Baku ci ba kawai Ni Baku Zo min ba,dariya Suka Yi Suka dauki cokali suka Fara ci Suka ji girki me shegen Dadi dama na gidan su Rabi Babu Dadi shi yasa Suka kasa ci,Fu'ad ya kalli su Umma sun wani zage sai ci suke Yi,Umma ta Mika Masa spoon Tace kaci Mana,Su Rabi suna ta dariya a gefe Wai sun San ma bazai ci ba,Da mamakinsu sai Suka ga ya karbi spoon ya Fara ci shima yaji Dadi sai ma ya wuce su Umma dama ya fisu Jin yunwa,baici komai ba,Nene Tace Ina Iyayin? Sake Bata fuska yayi Yana cin abincinsa,Har Naman kazar yake ci iya cinsa Haka su Umma ma Nene sai Santi take Yi,Tace ke Kam Yar Nan Wanda ya Aure ki yayi dacen me iya girki,a Ina Kika koya ne Haka Kamar wata me dafa Abinci a restaurant ko gidan Sarkin garin Nan?Dariya akayi har Fu'ad sai da ya murmusa,Nace ai Nene dagewa nayi na koya wajen Iyata,kin kyauta cewar Umma,na kalli su Rabi na tabe Baki nace wasu kuwa sai shegen gishiri a Miya.
Hand bag dinta me tsada ta Bude ta Mika min IV tace gashi bikin Fadila kizo Mana fa,nace to Allah ya kaimu,kazar Nan duk Fu'ad ya kusa cinyewa ko Ni banci ko dandane ba,Ina ta kallo Ina hadiyar yawu Ina sa Rai ko zai rage min Amma ganin Kamar Ina yawan kallon ragowar kazar Dan mugunta sai yace Umma Miko min ledar nan,Bata kawo komai ba ta zaro Leda baka sabuwa ta bashi ya juye kazar tas a ledar ya mike tsaye yace muje mu gaisa da Iyayenta sauri muke,Umma Tace wannan wanne Iskanci ne Dan Momy? Kamar Bai ji ba,Ni kuwa hankali na ya tashi sabo da Iya Tace idan na sake zuwa inda take sai ta Tsine min,ga Affa na ya Zama Dan Daudu yanzu a kasuwa ma yake soya kaji da Doya da kwai harda waina Masa da Miya.
Ya zanyi Dole na shiga daki na zura katon Hijab na fito Muka tafi Su Rabi suna binmu a baya sai gulma ta sukeyi suna dariya,Gidan Affa Muka je munci sa'a kuwa dawowarsa daga kasuwa kenan Yana tafe yana karairaya Kugunsa daure da zanin Shadda ga Kuma singlet ya saka,Yana tafiya Yana wulwula ludayin Miya Kamar mace harda Rike kugu,Nace to gashi Affa na Kira shi,ganina da Baki Bai koreni ba ko ya zageni Wanda nayi mamakin hakan,Kallon bakin yayi yace Marabanku dai bayin Allah kune tafe Haka cikin Rana tafatsar fatsar,Habarsa ya rike Yace ikon Allah Ashe tare kuke da Yan maza ke Rumaila shigo da su,Su Umma suka tsaya suna kallon ikon Allah,kunya ta lullube Ni Raina ya baci idona ya cika da kwalla ta da kyar nake dannewa,Su Rabi kuwa sabo da Rashin mutunci sai ma cewa sukayi 'yar Shila ya doyar da wainar?yace Tana can na barwa yarana kafin anjima na koma garin Rana zamanin Nan wa zai Bari Rana ta dinga dukan fatar mutum tana Masa Illa wannan sai maza.
Umma tace Rabi Baku da kirki wlh Rumaila kawarku Amma kuke Mata Haka?Mahaifinta ne fa,Mahaifi ai Mahaifi ne wlh Sam Baku birge ba Kun Bata wayonku,Ana Haka sai ga Baban Rabi Dana Hajara zasu je wani wajen Ni kuwa dama Ina mutunta su na dauke su Kamar su Suka Haife Ni sabo da kawayena,Har kasa na Duka na gaida su,karshe Nima Direct nace Zubairu Shugaban kwarata a dawo lafiya,dake Baban Rabi an Sha kamashi a dakin Mata Yana kwartanci,mugun kwarto ne shi yasa Nima na rama tunda kowa Yana da abin fada, Nene Tace Kun gani Rumaila ta fiku hankali da komai wlh,Amma gaskiya ku gyara ku daina Zagin iyayenku,ke Rumaila ko sun Miki ki barsu da Halinsu Allah Yana gani karki sake fada wani kwarto karki Kara,Hawaye ya shiga sintiri a kumatuna nace Ni na gaji da abinda suke min ko abinda Yan gari ke min ban damu ba Amma ace su kawaye na ai da ciwo,Ni Dan sun min ban damu ba Amma wallahi duk Wanda ya zagi Iyayena sai na zagi nasa, Fu'ad ya kalleni sau daya daya ji tausayi na a duniya yace kizo mu tafi dake can is Better,Na makale kafada Ina shesheka nace Ya...yasin....Ni bazan bi ku ba...sauran Yan gidanku su min wulakanci,Nene Tace da wulakancin Kauye gwara na birni,nace Yan birnin da sukayi Degree a iya wulakanci.
Zan saki a makaranta Fu'ad ya furta,nace Ni bazan biku ba,kyale Ni suka Yi Muka shiga dakin Affa a tsaitsaye Suka gaisa da Affa na da Matarsa Suka Basu kudi,Gidan da Iyata ke Aure Muka nufa,tunawa nayi na fada Mata Fu'ad ya min ciki yanzu idan ta ganshi ya kenan,Allah yasa su Rabi sunyi fushi sun tafi, sabo da Haka na canja Shawara nace na tuna Iya Bata Nan yau tana Can Kano taje wani biki,Umma Tace eyya to idan ta dawo ki gaishe ta nace to Muka juya na tafi rakasu.
Sauri nayi na koma kusa da Fu'ad ledar Kazata ragowa da take hannunsa na rike kadan da sauri ya juyo Dan bai san nazo ba,a hankali nace Dan Allah kawo na rike maka Bako Bai kamata a barshi da Kaya ba,Dariya ce ta kwace Masa ya Gama gano wayo na Dama ya gane son Naman nake Yi shi yasa ya min Haka,ai kuwa yace bana Jin nauyi bar min abata Zan rike na gode,a boye na Harare shi Ashe ya gani sai ya Bata Rai,nace Ni bana so na bar bakinmu da wahala Dan Allah ka kawo har mota Zan saka maka,Kafada kawai ya makale Kamar yaron yaye sai ya bani dariya na manta ma da cikin Dake jiki na Sam,Gaf da motar su ya bani ledar yace ga abinki nan,da sauri na karba tare da cewa na gode Na Gode.
Dari biyar na dakko wacce ita ce gareni kacal na mikawa Umma nace gashi Umma idan Allah ya sauke ku lafiya ki Bawa Abbi gudunmuwa ayi hakuri ba yawa,Mamaki da alajabi ya daurewa su Umma Kai ganin ko a dangi idan suna biki ba Wanda ya taba Basu gudunmuwa sabo da ana ganin suna da kudi me zasu Yi da ita Amma sai ga Rumaila ta bada dari biyar iya karfinta abin Nan har Fu'ad ya Basu mamaki,Umma Tace Haba baza mu karba ba,kawai na saki kuka nace Ni ba ku na bawa ba Abbi zaku bawa gudun muwa da Ina da abinda yafi Haka shi Zan bayar.
Shuru sukayi daga Bisani suka bani kudi naki karba,har Fu'ad ya bani da yawa naki karba Dole suka kyaleni Nene tana ta rokata nazo fa bikin Nan Lallai nace indai Ina da Lafiya zanzo.
Har zasu tafi Umma Tace Rumaila Wai da gaske ne ciki gareki na shege? Ba musu nace a ae,waye ya Miki? Nace Nima ban sani ba, Fu'ad yace tanan kin Bata wayonki wlh ,Shuru nayi na tsaya Kamar gunki Hawaye na sharara Kamar ruwa ganin shi Fu'ad ma Kamar da gaske Bai San komai ba Akan cikin dake jikina,cikin Maganar Kurame na nuna wa Fu'ad da Hannu irin cikin ka ne,Bai Gane ba sai Baki ma ya tabe sai Sallama suka min Suka tafi abinsu.
Jikina a sanyaye na koma gida na kwanta Hawaye Yana zubo min Ina tambaya Ina uban Dana yake ne? Nifa na kasa Gane wannan lamari Amma ai Uban sa ba kowa bane face Fu'ad,a fili nace Zan haufo me Kama da Kai wlh har gida Zan Kai maka danka.
Waye Fu'ad?
AsmaBaffa.
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈
FREE PAGE
DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM.
NA KUDI NE
GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE
ACCOUNT NUMBER
0175487861,ASMAU GARBA MUHAMMAD, GTBANK.
MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER DA ZAKU TURA
08033933642
'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39
16-20
Official
By
AsmaBaffa
PAGE NAKU NE
BESTIN BEELAT
HAFSATOU
KHADIJA A HAMZA
MATAR MALAM
MUM NAWAZ
SARAUNIYA
Fu'ad Suffiyan Jawa
Alhaji Suffiyan Jawa Dan Asalin Adamawa State ne Fulanin Asali ne,asalinsu dama su Sunyi gadon Dukiya masu Arziki ne, family dinsu Gasu kyawawan gaske farare Kamar larabawa shi yasa ake Kiran Family dinsu da Jawa means Jajaye,Alhaji Suffiyan Dane ga Alhaji Sulaiman da Hajiya Fanna,Su Biyu Suka Haifa a duniya,Alhaji Suffiyan sai Hajiya Rahina har Alhaji Sulaiman Yana da kani Alhaji Sunusi Wanda shima me kudi ne sosai yaransa takwas,Sai Alhaji Usman shima me kudi ne a Germany yake zaune da yayansa biyar, har Allah yayi wa Sulaiman rasuwa Basu sake Haihuwa ba,Fanna kuwa tana raye ta tsufa sosai Basu fiye barinta a Nigeria ba sai dai tazo da yawo tana Germany tare dasu Alhaji Sunusi Ana duba lafiyarta, ta Bangaren Fanna uwa kuwa tana da kanne itace Hajiya Saratu Wato Nenen kauye,Sai Hajiya Hauwau itace a Kano tana auren wani Babban Alkali da Yaransu biyar, sai sauran dangi sosai suna da su talakawa da masu kudi Amma talakawan ba wani zumunci ake yi da su ba.
Alhaji Suffiyan Shi yayi gadon Dukiya ta gaske Kuma Allah yayi Mata albarka yaci gaba da kula da komai Tunda ya Fara Business komai yaci gaba da bunkusa sabo da Yana da nasibi,Yana yawon fita kasashe har Allah ya kaishi Sudan can yankin North a anan ya Hadu da Hajiya Maryam kyakyawar gaske Yana dawowa aka shirya biki da komai a can Sudan aka Daura Aure ya dakko Matarsa Suka dawo Nigeria Birnin tarayya Abuja.
Tunda ya Auri Hajiya Maryam wato Umma Bata Haihu ba ko Bari Bata taba Yi ba,ganin Haka Su Fanna Suka Nemo Masa Hajiya Amina Wato Momy Yar Zamfara ce ya Aure ta,Yana Aurenta cikin Ikon Allah Shekara Daya ta Haifo Danta Kyakyawa wankan tarwada sabo da ita ba Fara ba ce,Ranar suna yaro yaci sunan Baban Suffiyan wato Sulaiman Ana ce Masa Karamin Alhaji, Sai Kuma bayan Shekara Uku Hajiya Amina wacce ake cewa Momy ta sake Haifo Yarta mace taci suna Haneefa,Lokacin Kuma Maryam itama Allah ya Bata ciki sai Murna takeyi,Momy ma ta tayata murna suna zaman lafiya abinsu,Maryam wato Umma ta haifo danta Namiji Kyakyawa fari tas Kamar Bature ranar suna yaci suna Fu'ad Sunan Baban Umma kenan a can Sudan Wanda shima ya rasu tuni sai Mamanta ta rage da Yan Uwa,Bayan Shekara biyu Hajiya Amina da Hajiya Maryam Suka sake haifuwa kusan a tare tsiransu kwana Uku Amina ta Haifo Namiji Umma ta haifo mace Kyakyawa itama Rana Daya aka musu suna Islam,macen Kuma Naila,Tunda Fu'ad ya taso a wajen Momy ya girma Kamar ita ta Haife shi shi yasa ake ce Masa Dan Momy wasu suce Abban Momy tunda Sunan Baban kishiyar ta ne suna zaman lafiya suna yiwa junansu Kara,Bayan wani lokaci Abba ya Nemo wata Matar ya aura Hajiya Rakiya Yar Kano, itama tazo ta Fara haifo mazanta