Showing 84001 words to 87000 words out of 115153 words
magana da juna Kawai sabgar Hajara Suka daina shiga,Ina zaune a kitchen Ina Bitar karatun Alqur'ani Ina girki sai ga Hajara ta shigo da Sallama ita daya sodo sodo da ita,Hajara ma wankan tarwada ce me haske Kuma Fulani me kyau ga Hanci,Allah ya taimaketa Iya Bata gida da taci Ubanta yau,da fara'a nace Hajara Yan Mata,Murmushi tayi Tace uhm ke Wato kin Zama matar Aure,nace ae Mana ai kune Yan Mata yanzu,Kujera na Mika Mata nace zauna,Zama tayi Tace Rumaila dama zuwa nayi ki yafe min abinda nayi Miki,Hankali ya shige Ni gaskiya Bamu kyauta ba Dan Allah kiyi hakuri,Nace ba komai Hajara Ni ba abinda kuka min, bana rike ku da komai wallahi,Ni hakan ma nafi Jin dadin Rayuwata ba Wanda zai Bata min Rai Kuma kun Sanni Ni ba komai ke damun rayuwata ba,Abu daya kuka min idan na tuna Ina Jin haushi bazan boye Miki ba,Na farko Sanda aka ce nayi cikin shege kuka dinga tsokanata a gari Kuna sa Yara suna min Ihu,Haka Kuma Sanda kuka yiwa Affana wulakanci a gabana kuka dinga kiranshi da Yar Shila wannan abin shine Kawai ya Bata min Rai,ai ko ba komai mahaifi mahaifi ne,muyi Wasa tare Amma akan bakwa kaunata kuka yiwa ubana mahaifi haka a gabana a Gaban Baki su Nene duk da cewa Saude da Rabi sun fiki laifi a wuri na,Idona ya ciko da Hawaye nace ba komai na yafe Miki ya wuce,Amma kar kusa Rai Zan koma muna Komai da ku Kamar da can a baya tunda har Iyayenku ba Zagin da Basu Yi min ba gwara naki Innarki har tuwo ta taba bani sau biyu bazan manta ba,wannan ya nuna ba Amana,ba Kauna ta kawaye Wanda suka taso tare Muka Yi Wasan kasa tare,babu kauna ko ta Albarkacin Yan Uwa musulmai,me ya kamata muyi idan kaddara ta fadawa Dan Uwa Musulmi shine Addua,Amma mu yanzu mutane Hassada da cin Amana tayi yawa,ba dama wani ya motsa idan bala'i ya samu mutum har murna mukeyi Ana Allah ya Kara,idan abin farin ciki ya samu wani sai bakin ciki da Hassada sharri kala kala,Allah Kawai ya shirye mu Baki daya,idan Zan taso magana ma bazan Iya yafe muku ba Amma Kawai a bar zancen ya wuce,Naji an kawo kudi Allah Sanya Alkhairi kema ba laifi kinyi sa'a,sai a dage idan anje can a koyi Ilimin Addini Dana Boko,Rabi Tace Dama yace zanyi karatu a can,a Nan ma ya saka Ni a makarantar Boko da Islamiyyar garin Nan shima idan yazo zance Yana koya min wasu abubuwa,Shine su Rabi Suka daina shiga harkata,ko naje wajensu Basu fiye kulani ba,su Rabi....dakatar da ita nayi nace can ta matse muku ai kawayenki ne kunfi kusa,okay shi yasa kika zo min sabo da sun koma kanki Alhmdllh ai daya Bayan daya wallahi sai na ganku a Rana Ina zaune Zan Sha kallo,bana son Munafunci Kun Sanni Ni tun asali ba a gulma Dani,ki dage ki koyi Zaman aure,ki koyi Mene Aure,ki San cewa Aure ma gaba daya Ibada ne ba Wai Dan iya Jin dadi ba,idan kika San Aure Ibada ne kaf to kin hutawa ranki hange hange,ki San ya Zaki zauna da Miji lokacin da yake da kudi ko babu,ki San ya Zaki zauna da surukanki,ya Zaki zauna da Dangin miji kannensa,yayyensa,su Ya gana da su Yafendo,da su Goggo,ya Zaki tattala miji da Nuna kauna da Iya soyayya,ki koyi girke girke,iya kwalliya tsaftar jiki lungu da sako da tsaftar gida idan nace gida Ina nufin ko Ina na cikin gidan,Ya Zaki sa Kaya ki birge me gida,ki koyi Zama da kishiya idan ta Allah ta kasance ko an Kara Miki Nan gaba,Hajara Tace idan an Kara Miki dai sai ki dinga jawo min jaraba jikina,Dariya mukayi,Nace Hajara a kula da tsaftar Baki,Hajara baki,Baki da kasa kin Gane kasa ai ko? Hajara Tace kasa Kuma? Nace farfajiyar me gida Hajara,Mahutar me gida to Ina nufin inda a Daren farko ake gashin Kuma a ciki,Hajara harda shewa,nace Jauro ya waye Hajara a kula,Kinga baki? Tace ae nace to wayayyu sai sun kusa cinye shi Jauro kuwa daga ganinsa ba kanwallasa bane,Hajara Tace ae wallahi Rannan Daya zo zance ya Rungumeni da kyar na gudu gida,Kuma In zai tafi Wai Ko nayi Masa me ma yake fada Ni dai da turanci yake fadar zancen nasa Wai ko Uhmmm.....Hajara ta daga Kai sama tana tunani Tace yawwa na tuna ko kus ko kis, nayi Dariya nace Kiss ai shine nake fada Miki idan kinyi auren Kya fada min a waya kinji Yar Hajaralle ta Jauro,Hajara Tace Kai Rumaila kina birgeni daga aure kin Zama me Maganar manya,har yaushe kika Yi auren Amma ka Rantse kin shekara Tamanin da aure,nace Ilimi,Birni akwai Ilimi da cudanya da mutane ga Kawayena suna fahimtar Dani kin San Kuma kwakwalwata komai taji ta dauke sabo da akwai kuruciya Bamu da matsala,Hajara Tace Zan na zuwa kina koya min wasu Abun da karatu ma Sai dai Ina tsoron Iyanki karta ci Ubana,Haba Zan lallaba ta Babu abinda zata Miki.
Haka na fadawa Iya yanda Mukayi da Hajara Bayan ta dawo da dare,Iya Tace ta Dan fi sauran Hankali ai Kuma Iyayenta ma wallahi sai da suka min jaje Kuma da Suka ji labarin kinyi aure sun zo min murna ita ai Iyayenta a tsaye suke Baki gani ba ai Basu barta ta biku birni ba,Nima da hankali na rabon mijinki ne ya kaiki shi yasa na barki ma kika tafi,kaji Iya harda wani Kare kanta itama.
Kullum Hajara tana zuwa Ina koya Mata karatun Islamiyya da Boko duk da Nima ba Wani kwarewa nayi ba Amma na sani daidai gwargwado,Itama Hajara tana girki a gidansu sosai wannan ta Iya sai dai Nan gaba idan ta Iya karatu zata koya ko a waya ne, tunda duk wani girki da akeci a kasar Hausa ta Iya dai dai gwargwado.
Kewar Fu'ad Duk ta kamani har yanzu Ina zuba Ido yace zaizo Amma kullum Muna waya a Rana sau Uku sau hudu,Bangarensa kuwa tunda yayi waya Dani ya Gama kwance zaninsa a kasuwa, Umma Bayan Samha ta tafi yazo cin abincin dare Umma Tace Sannu Sarkin karya Ashe can ka tafi ba kunya ko dai a can ma ka Kare kwanakinka ne kace Meeting kaje Kano?Ya guntsi ruwa abakinsa zai Sha da sauri ya feso shi waje Jin abinda Umma Tace zata kure shi,kame kame ya fara yace No...no....Umma...y..Taya zanyi Haka a Ina zanje na kwana ai ba wajen kwana na a garin Nan,to Taya kasan wani Majalisar wani ko Jauro ko Iro kace ne,sannan kace tabi ta Bishiyar da kuka zauna da dare, me zai sa kayi dare a garin nan? Kuma kana cewa ta zuba kayan data wanke a Jakarta pink,duk Ina ka San wannan? Shuru Fu'ad yayi,Umma Tace Dama na Dade Ina zarginka har Abbi sai da muka tattauna da shi,Kai da Nan Kaduna idan aka turaka Meeting baka zuwa sai an Kai ruwa Rana Kuma komai dare baka kwana,Kuma sau Nawa kaje Aiki Kano Abbi yayi yayi ka kwana kaki yarda sai Islam aka tura can, Fu'ad yace Umma baza ki Gane ba,Umma ta make Masa Hannayen da yake wani misali dasu Tace Dama bazan Gane ba mana,Yace Haba Umma Mana....ba Haka bane....Ohhhh...no....Umma Tace gaskiya Mana ake kirana da Iya,Ai Zan tambayi Rumailan nasan yanda Zan Mata ko in tambayi Iya,Kuma idan naji gaskiya sai na Saba maka Umma ta dungure goshin Fu'ad Kamar yaro ta haura sama,tana tafiya ya maza ya dauki waya ya kirani,Yace duk yanda Umma zata bigi cikinki karki fada na kwana ko daya,nace to ai dama bazan fada ba na sani ai,ka manta ai na gama sanin halin Umma,Yace Good,tafiyar Umma yaji ya kashe wayarsa ya fuske.
Ni kuwa Iya na fadawa itama kar ta tonawa Fu'ad asiri,Iya Tace to Ni Yarinya ce? Da sai kin fada min kar na fada Kawai sai nace yazo ya kwana a Ina to,kune Yara Baku San yau ba,mu munga jiya munga yau,mu da Muka zo a zamanin da ba a Maggi ma,sai dai musha Mangul,da Mangul muke Miya a da babu Maggi,kune Yaran yanzu,nace sai Iya Ina Dariya.
Malamin ne ya Kira Abbi yace lallai Rumaila maganin Nan a gidan Iya zata Yi ta Gama,kar ta bar kauyen a garin za ayi maganin Kuma kar a Bari Fu'ad yaje,Umma Hana Fu'ad tayi ya kawo maganin bamu San Dokar malamin bace, Fu'ad ba irin rokon da baiyi ba Tace wallahi ita zata Kai da kanta Kuma idan yaje garin Nan sai ya hadu da fushinta,Yana gani ya hakura Kamar yayi Ihu,kasa Daurewa yayi ya tafi wurin Abbi Yana Dakinsa ya sameshi,Abbi yace lafiya dai Fu'ad? Fu'ad yace Abbi kaji Umma Wai bazan Kai maganin Rumaila ba ita zata je da kanta Kuma Tace ko ba magani Wai kar na sake zuwa garin sai Sanda aka ga dama aka dawo da Rumaila,Dariya Abbi yayi yace Kai da kace ba Wani sonta kakeyi ba mene Kuma ka damu ka kyale Umma taje, Fu'ad yace Wai Ni me yasa ake min katsalandan ne a cikin rayuwata?Baki Abbi ya Bude yace Iyye? Nine ko Umman taka Muke maka katsalandan? Fu'ad yace to kunce kun bani mace na hakura na karba,yanzu Kuma an hanani ganinta sabo da Allah Ni Wai Ni da me zanji ne,Abbi ya hangame baki yace ba Kai ka koreta ba,Dana koreta ai da dalili Kuma Ni mun shirya gaskiya cewar Fu'ad,Abbi ya jinjina Kai yace Fu'ad duk biyayyarka Amma Akan mace kake wannan Fadi in fada da Ni? Kayi hakuri Abbi na samu matsi daga wajen Umma gaskiya kayi Mata fada Kawai Ni,Abbi yace ba fadan da Zan Mata duk abinda tace Kamar Ni Nace, Fu'ad ya girgiza Kai yace shi yasa su Momy suke Mata gori ai ta mallakeka ai ga irinta nan Ni bana ganin laifin ma su Momy da gaskiyarsu,Abbi yace Kai ka kiyayeni fita ka bani waje baza kaje ka ganta ba Allah yasa naji labarin kaje garin, Fu'ad fuska ba Rahma,zuciyarsa ta kumbura ya fita Kamar zai tashi sama Haka ya finciki motarsa Yana ta mita shi daya har ya koma gidansa,me Gadi ya ganshi fuuuuuu....da ya gaida shi ko Kallonsa baiyi ba yayi ciki,bedroom dinsa ya Shiga ko kofarsa Bai rufe ba ya fada saman Gadonsa faf da karfi,ya daki katifa yayi ruf da ciki tare da Danne fuskarsa a katifa Yana Kiran Babyna Rumaila,shi kadai sai bori da birgima yake Yi a saman katon Gadonsa Yana ta Kiran Babyna I need you Kamar yaro.
Kira na yayi cikin dare Ina daga Wayar naji Muryarsa wani Iri,can kasa yace kinyi bacci ne? Nace ae,Yace to tashi babu lafiya,gabana ne ya yanke ya Fadi nace lafiya me ya faru? Yace Umma da Abbi sunce bazanzo ba sune zasu so su kawo Miki magani,Salati na saki na Mike Zaune a saman katifata nace Innalillahi wa'Innailayhurrajun, Subhannallahi,wa Iyazubillahi yanzu Baby ya kenan Muna cikin wani Hali,na Gama shirye shiryen tarbarka abubuwa sun Karu naci na sha,Na cika fam, Fu'ad Yaja Ajiyar zuciya yace daina fada min kayan takaici please kar ki jawo na sabawa Umma da Abbi,Nace ai bazan yarda ba ka Saba musu ba Ina Sam,muyi Hakuri akwai lokaci,Amma gaskiya da ka fada min da wuri bazan iya cin abincin Rana ba Haka Zan yini kawai,rayuwa babu Kai.... Fu'ad ya karasa da ai Bata Yi ba sam,Hhhhh Kai Ana Shan love a Nan,Haka muka raba dare Muna jimami kafin bacci ya kwashe mu.
Washe gari 11am Fu'ad yace Min Umma da Abbi sun taho suna Hanya,girki Mukayi da shiryar tarbarsu Ina ta murna magani yazo,kudi na kashe sosai wajen tarbarsu,Iya harda saka sabuwar Atamfarta Nima Shadda ta na sa Maroon na Sha kyau,Iya Tace Dan Ubanki yafa Mayafi surukai ne Tarbiyya da Da'a ake Nunawa,Kuma ladabi kamar me Haka nake so Naga kinyi,Ki zauna a gabansu ki lankwashe wuya da kunya,na gwada lankwashe wuya na dawo Kalar tausayi nace Iya Haka?Iya tace sai kace Almajira ai sai su rainaki Kuma Haka nace kiyi Iya ta fara gwada min yanda zanyi gaisuwar surukai........😅😅😅
Sharhi Dan Allah fans
AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈
NA KUDI NE
DUK WACCE TA FITAR DA SHI DA WACCE BATA SIYA BA TA KARANTA BAN YAFE BA.
DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM
81-85
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne
Maman Deedy
Kubcyn Auwal
Sadiya AliyuSafiya89
Fatimamusasamaru
Ummeen Sadeeq
Zainab Sabo
Umarasmau339
Maman Fadeel
Hairat
Maryam Muhammad
Maman Mufeedah
Iya Tana koya min tace Durkusawa zakiyi sosai kallo wuyana Haka Dan kasa kadan ki Danyi wani doro ki kobare,Iya tana gwada min sannan Tace Yi na gani,gwadawa nayi Iya Tace Shu'umar ta dauke a kwakwalwarta Haka zakiyi yawwa, Wayar Fu'ad na gani ya Kira na daga yace Driver ya dauke su Umma a Ariport sun taho Garinku Wai bazai ce ma Kauye ba ya daina fadar Kauye Kar ya ci min fuska Allah sarki Dan mijina.
Basu Dade ba sai naji tsaiwar mota,Iya Tace gasu nan yanzu zamu ji kamshi ya turare gidan Nan,Umma ce tayi Sallama Tasha wani Arnen lace fari tas komai fari ta sa gata fara wannan wanka na Umma yayi,Iya Tace yaron Nan Fu'ad Ashe kyawun nasa ba a banza ba, shigar ma da yakeyi gado yayi Dan na Gada,Iya an nutsu aka amsa Sallama tare da shimfidawa Umma katuwar Tabarma Babba,fitowa nayi da mayafina na durkusa har kasa na gaisar da Umma Ina Mata Sannu da zuwa,Umma Tace leka kice Abbi ya shigo tare muke,Na fita Ina Masa Sannu da zuwa na shigo da shi,Kai Ina Jin dadi da Iya tayi zuciya tayi Mana Dan gidanmu me kyau baza muji kunya ba,Iya Tace sannunku Kun Sha Hanya,bayan an gaisa Iya Tace Oh bayin Allah ya birni ya mutan birni? Umma Tace lafiya wani bangaren wani bangaren Kuma to sai godiyar Allah,Iya Tace Haka rayuwa take dama Alhmdllh Muna ta godiya,Haka Uban Yarinyar Nan Rumaila yace ayi Muku godiya Kuna ta dawainiya Kai Allah ya saka da Alkhairi,Abbi yace Ameen ai ba komai Rumaila ai Yarinyar arziki ce Allah ya musu Albarka Baki daya,Iya Tace Tunda mun Dan hadu Salati goma ga Annabi (S.A.W) aka Kwarara Addua sannan na shiga jere musu kayan ci da Sha,Umma Tace Rumaila wannan girke girke Haka Ina zamu kaisu haka murmushi nayi nace ai Abbi zai ci,yace sosai ma Rumaila,Iya ta nutsu cif kace ba ita ba,Hira ta nutsuwa sukeyi,Iya ta fita Tace Bari a Kira manyan Yan Uwa ku San juna,Kawu Haruna,da wata Dattijuwa Yafendo itama Yar Uwa,da wani shima Dan Uwa,sai a bangaren Dangin Affa na ta kirawo mutum hudu mata biyu maza biyu aka hadu,Iya ta gabatar da kowa aka gaisa a mutunce aka Yi Hira sosai sannan suka tafi.
Bayan sun tafi daga Abbi sai Umma,Iya da Ni,Nace Umma Baku ci komai ba,Sai lokacin Umma ta dauki Samosar Dana Yi da spring rolls,Abbi kuwa Tuwon Danyar shinkafar yace zai ci miyar Danyar kubewa ga man shanu.
Umma ma taci har Tuwon nama sunci na ci sai da suka koshi sosai sannan Umma ta fito da magani tayi bayanin yanda zanyi amfani da shi da komai na karba da godiya,Abbi ya min Karin Bayi yace a dinga lasa kullum sau Uku Ana shafe jiki idan zaki kwanta bacci har ya Kare,a kula Dan Allah 'yata kar ayi Wasa,to Abbi Nace,Iya Tace Ina Nan ma Ina Zan Bari ayi Wasa,Umma Tace yace zata ji canji zata danyi wahala da su mutanen boyen Amma a daure,Iya Tace yo Dama magani ai dole sai ya nuna an Shashi,ko Maganin malaria ka Sha sai kaji canji a jikinka marar Dadi bare maganin Jinnu,sai da su Umma sukayi Sallar La'asar sannan suka tashi zasu tafi,Har mota muka raka su da kwan zabi a katon botiki fari me murfi,a mota na saka musu,Umma Tace Rumaila Sarkin kyauta,ta window din Umma na zaga da Bakar Leda katuwa tsarabar Fu'ad Nace Umma ki Kai Masa,Umma ta Gane Fu'ad za a kaiwa duk da ban Fadi sunansa ba Tace Fu'ad ko? Nace ae,Tace yazo Nan ne Rannan? Nace ae,Umma Tace kwana yayi? Nace a'a sai dare ya tafi cikin gari ya kwana a Hotel,Umma tayi Dariya kawai tasan karya na fada,Sun tafi dai bata yarda ba,Abbi yace Ina ruwanki da tambaya tunda Abu ya wuce ma ko kwana yayi me za ayi,Umma Bata Bude Ledar ba Haka Suka Isa gida lafiya da wuri.
Fu'ad ta Iske Yana kallon ball da Alama su yake jira yace Umma Sannu da zuwa,Tace yawwa,Ledarsa ta bashi Tace gashi Inji matarka,da sauri ya karba Yana Murna,Umma ta Haura sama zata Yi wanka,Ledar ya Bude yaga manyan Robobi Guda uku,Daya dambun Naman kaza,Daya soyayyen Naman Rago,Daya Kuma Samosar Dana Yi Sai Yar takarda karama a ciki,ya dakko tare da budewa ya karanta kamar haka
My eyes r hurting coz i cant c u, My arms r empty coz i cant hold u, My lips r cold coz i cant kiss u, And My heart is breaking coz im NOT with u...miss u so Much Baby, Nima a love Sms na gani ya min na rubuta.
Murmushin farin ciki yayi tare da Furta I miss you too Baby,Dambun Naman ya fara ci yace Uhmmm yayi Dadi tattarawa yayi Yana Rufewa Umma ta sakko ya dauki Ledarsa yace Umma na tafi sai gobe,Ko Zaki ci? Munci namu a can tace,ya Mike ya Kara gaba abinsa.
Su Umma Bayan sun tafi Ni da Iya muka ci na ci abinda nayi banyi da yawa ba dama,Har Hajara sai da taci wasu Abun,Iya tana ta Yabon su Umma irin kirkinsu,suna tafiya Iya Tace sai na fara amfani da maganin,na Bude gwangwanin Zaitun nayi Bismillah tare da lasa a yatsa na shanye,can Anjima na Kuma lasa sai