Showing 105001 words to 108000 words out of 115153 words
Sha Tara ta arziki Driver ya maida ta har kauyenmu gidanta,Iya ta Kara kyau tayi kiba sosai.
Iya Bata Dade da komawa ba kawarta Wacce ta kaita gidan Sanata suyi aikin share share ta kawo wa Iya Ziyara,Tace Iyan Rumaila naji abin Alherin Daya sameki Kinga yanda kika Kara haske da kiba kuwa gaskiya kinyi auren yarki da kafar dama,Iya Tace Allah ya nufa,gashi Nan da wata Uku zamu keta Hazo zuwa Saudi Allah ya Kira mu mun amsa,Kawar Iya tace Iyye gaskiya Ina murna,Dama akwai abinda ya kawo Ni wajenki Iya,Iya Tace Ina jinki,Dama Baban Sanatan Nan da muke Aiki a gidansa shine matarsa ta Rasu Kuma ita kadai ce matarsa ita ce Uwar yayansa ciki harda me girma Sanata,To kin San mutuncin mutum Aure,In fada Miki tun watan jiya Sanata ya dinga neman Ina za a ganki,nace ai ke kawata ce shine yace nazo na tambayeki idan Zaki Auri Babansa,Iya Tace Tsohon Zan Aura? Haka Kawai Ina zamana lafiya a jawo min takaba da wuri,Kawar Iya Tace ke fa ba tsoho bane,shi kanshi Sanatan yaro ne kwanan Nan ya cika shekaru 40, Kuma irin auren wuri ne,kin San irin auren da Iyayen da keyi da kadan suke girmar yaransu na farko ke kin sani,Wlh Baban Sanata baifi shekara Hamsim da wasu Yan haya haya ba,idan kika ganshi Zaki Rantse yayan Sanata ne, shi yace Kawai Bai son Zama ba mace,Aure shine cikar mutum,Hakan tana faruwa Sanata ya dinga nemanki ko Zaki Auri Babansa,Kuma wallahi Iya Baban me kudi ne na gaske Attajiri ne gadon kudi ne, shi kanshi Sanatan kudinsu ne yasa aka tsaida shi takara,Kuma Baban Sanatan ko yaushe Yana kasar waje idan kika ci sa'a ma da ke zai dinga keta Hazo,Iya kiyi tunani Alheri ke Kwankwasa Miki kofa,Kuma Baban Sanatan zaiyi sa'an Baban Rumaila shekarunsu zai kusa zuwa Daya,Iya Tace Ahhhh wannan Mijin aure ne,wannan abin a aure shi ne,Ya Gama cika sharudan aure,a Ina zamu zauna idan anyi auren? A cikin Kano GRA,Iya Tace na Amince kawai,Kawar Iya ta rangada Guda Tace nasan baza ki ba Dani ba ta wajena sai dai kiyi shawara da danginki da Kuma yaranki,Kar su Rumaila suce Basu yarda ba,Iya Tace sunci Ubansu gaba Dayan su,ko da Basu hanani ba sai yanzu su din banza,Iya Haruna Danuwanki fa zai yarda? Uba na ne shi? Harunan me, Nan take Iya ta jawo waya ta dinga Kiran yaranta ta fada musu,fatan Alheri Suka Mata sun San ko sun hanata baza ta yarda ba ubansu zata ci.
Rumaila ni ta Kira a karshe,Iya Tace ke Rumaila Kafin na tafi kasa me tsarki Inshaallah zanyi aure na samu Mijin Aure,nace Haba Iya Ni Wallahi ban yarda ba,Iya Tace ke din banza Rumaila ke wacece Dan jakar Ubanki? Karki yarda Din,Kuka na saki Fu'ad Yana kwance a cinyata,sai da na Gama Wayar Ina share Hawaye nace Wai kaji Iya ce zata Kara aure, Fu'ad yace to sai me? Ni gaskiya ka buga waya ka Mata nasiha, Fu'ad yace ba ruwana tsakanina da Iya da kunya,surukata ce mene Nawa ciki idan ba so kike Iya taci Ubana ba,kina ji dai Tace kudinta zata Nema na kanta Kar mu dinga taimaka Mata tana Mana biyayyar dole,ai Kai tana Jin maganarka idan ka Mata zata hakura da auren na furta da Shagwaba, Fu'ad yace Sunnar Ma'aiki Zan Hana? Ba ruwana Iya tayi aurenta Allah ya bada lada sannan Addua zamu Yi mata Allah yasa wannan shine auren Iya na karshe har Abada baza ta fito ba,Kansa Dake saman cinyata na goce ya sauka a saman kujera na tashi Fuuuuu Ina kuka nayi cikin Bedroom,Dariya Fu'ad yayi yace Zaki zo ki sameni,Ni kika jefarwa da Kai ko? Ina daga daki nace ae din an jefar.
Sanata da kawar Iya da wasu Manyan Dattijai su suka Yi bincike akan Iya,Itama Iya da kanta tayi bincike ta hanyar kawarta,Iya Tace farko a fada min cutar da matarsa tayi ta mutu,akace ciwon zuciya Iya Tace Alhmdllh tunda ba kanjamau bace,a hakan ma Iya sai da tayi Test na aure a asibiti shima Tace sai yayi,Sai da ta tabbatar lafiya sannan Tace wani Mummunan halinsa Bai dameni ba Ni Zan gyara Masa Zama idan na Aure shi,Daga Baya yazo zance wajen Iya,shi dai tunda yaga Iya ya Yaba,halin Iya ya birge shi ga sa Nishadi yayi ta cin Dariya,Sanata ma yazo har gidan Iya,yayi mamakin canjawar Iya ya ganta wannan lokacin a nutse,Iya ta kalli Sanata tace Hausawa na cewa dole ace da Mijin Iya Baba yanzu Sanata ka koma dole kace da Matar Baba Iya,Sanata yayi ta Dariya, Iya sai kyauta take Sha,Dake manya ne sati daya sai Iya ce ta bugo waya Tace an daura Aure,Har Abbi ya Mata Murna da su Umma,Ni kuwa bana son zancen,Ranar da Iya zata tare harda Umma aka raka Iya Kano wani katafaren gida na gaske sai Yan aiki ko Ina,Iya ta dinga mamakin lamarin Allah,Haka Muka Bi Flight washe gari zuwa gidan Iya har Fu'ad,su Aunty Rukayya mun Sha mamakin ganin gidan da Mijin Iya ga kudi sai ka ganshi da kuruciya sabo da Naira ta ratsa shi, Ashe Babban Director ne a maaikatar lafiya ta tarayya, Ya dinga Jan mu da Hira da barkwanci kamar dama ya San mu,tun daga wannan Rana na daina Adawa da Auren Iya,Kuma Yana kiran mu a waya mu gaisa,Haka duk Yaran Iya manya marasa karfi sai da ya Basu jari me tsoka,Sanata Kuma Wai duk zai kaisu kasa me tsarki suma.
Bikin Hajara da yazo munsha wanka da kyar Fu'ad ya Bari nayi kwana daya,Ana Gama biki Iro ya tafi da abarsa Lagos inda yake Aiki,yanzu sai bikin Saude Muka sa a gaba,lokacin Kuma tuni Fu'ad ya maida Ni school Kamar yanda yace Haka, Islamiyyar matan Aure Saturday Sunday,sai ta Boko Kuma kullum,Sannan yanzu Yana ta koya min mota da Kansa,Ita kuwa Rabi an sata Itama a makaranta me hade da Islamiyya idan ta tafi tun safe sai Wurin Magriba take dawowa,Muna zaman mu lafiya hankali kwance cike da so da kaunar juna,Fadila ce dai Taki hakura har yanzu gaba take da mijinta anyi fadan har an gaji an zuba Mata ido Yana ta Amarcinsa da Rabi ko ta kanta baya bi ya gaji da lallashi,Su Khaleesat kuwa sunga Lallai Abbi da gaske auren dole zai musu har Naila dole a cikin masoyansu suka fitar da mazajen aure,Haka mazan ma Islam da Abdulhakeem tare za a hada duk a musu aure dama suna da matansu a Hannu, Fu'ad Kam cikin frnds Dinsa Guda biyu Khaleed da Ahmad sunyi aure ansha Shagali Muna gaisawa da matansu sosai mun Zama kawaye.
Ranar Monday kotu ta Aiko wa da Abbi takadda Akan anyi kararsa kotu yazo kotu da gaggawa Ranar Laraba,Haka Abbi dai ya sanar da Umma da Fu'ad tare da Sauran yaransa Momy da Mama ne suka Kai kararsa kotu,ranar Laraba gaba dayanmu muka Halacci kotu,a can Muka Iske Mama da Momy tare da Baba Jummai tana cikinsu dama abokiyar munafuncinsu ce itama,Baba Jummai Harara ta galla min Dan Kawai tana sha'awar Fu'ad Dina shike Nan ta tsaneni itama sabo da baza ta samu abida take so ba.
Ina matukar Baku Hakuri fans na rashin posting kwana biyu,Abu ne ya taso ba shiri.
Masu Sharhi da nemana don suji ko lafiya Ina godiya Allah ya bar kauna.
AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈
NA KUDI NE
DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM
106-110
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne
Hajja Maryam
Aisha
Zainab Sabo
Nafee
Alkali ne ya karanto Kara,Momy da Mama sune Wanda suka shigar da Kara cewa Kai Mijinsu ka ci zarafinsu ka musu dukan kawo wuka a Gaban yayansu,Alkali ya karanci ma Family Issue ne sai yace Kawai wannan karar a barta ku sameni a Office,Abbi,Momy da Mama da ni, Fu'ad da Fadila mune muka Shiga Office,Alkali yace su Mama kuji tsoran Allah ku Fadi gaskiya,Momy tace ai wallahi a Gaban yaranmu yayi Mana dukan tsiya ko Qur'ani aka kawo Zan dafa,Abbi yayi mamakin karyarsu Wato su babu nadama ma har da tozartashi su kaishi Kara Bayan shi suka yiwa laifi, Alkali ya kalli Abbi yace Alhaji ka dubu Girman Allah ka fada Mana gaskiya,wannan matsalar ba matsala ce wacce za ayi tozarci ba shi yasa nace Kawai kuzo muyi masalaha a Office,Abbi duk abinda ya faru ya kwashe tare da sanarwa Alkali Kuma Alkali ya gamsu,ya kalli Momy yace Amma ku dai mutanen banza ne,maimakon kuyi nadama ku bada Hakuri ku gyara halinku shine ma kuka kawo Kara kotu wannan kauna ce? Ya nuna Mijin naku ma baida daraja a idonku tunda har kuka kasa Hakuri har ya maida ku dakinku shine ma kuka kawo Kara,Wannan har ya Kai a kawo Kara kotu,Nan Alkali ya bude wuta ya dinga cin Uban su Momy karshe ya koma ja musu Aya da Hadisi Yana musu Nasiha,Amma ko a jikinsu sai Ma Momy cewa tayi mu fa Hakkin mu muka zo a bi Mana idan Kuma baza a bi Mana hakkin mu ba zamu daukaka Kara daga Nan har kotun koli.
Alkali yace ke ki Iya bakinki ba a ja da hukuma,Ko dai Yawu ne a kwalkwalwarki ba a sani ba? Sai da Alkali ya Bamu Dariya Wai Yawu ne a kwakwalwar Momy,Baba Jummai tana kusa ta Kwankwasa kofa akace waye? Baba Jummai Tace sheda Zan bayar Nima,Alkali yace shugo ke wace? Tace me Aiki ce a gidan Alhaji,Baba Jummai ta nutsu a Gaban Alkali tace maganar Allah na gaji dama Ni badan Allah nake Aiki a gidan ba,da farkon kawo Ni Aiki gidan dama Muna duba gidan masu kudi ne sai muzo a matsayin Yan aiki,sai Mun kafu mun San sirrin komai na gidan sai muyi cunen Yan fashi suzo su kwashi dukiya a Bamu rabon mu,Kuma dalilin da ya kawo Ni gidan Alhaji kenan, Alhmdllh munyi Nasara Kuma Yan fashi sunzo mun samu sama da milliyan goma a ciki an bani Milliyan Daya,Momy da Mama da su Muka Yi shawarar komai.
Farko naji sun hada Kai suna so su saci kudin Alhaji Wato Abbi su mallaki kadarori da yawa yanda ko ya mutu baza suyi talauci ba,duk da sunfi kowa yawan Yara maza da Mata Amma rashin godiyar Allah tasu ta jawo, Hakan Dana ji yasa na Basu shawara nace Ina da Yan fashi a Hannu idan suna so mu hada Kai zasu samu kudi,Haka Kuma su Momy dukkansu Milliyan Uku Uku Suka samu da aka zo fashi gidan Abbi,Sai Mama Tace a danginsu Kanin babanta me kudin gaske ne a Zamfara Nan ma munyi cunen Yan fashi,na samu Milliyan biyu,Momy da Mama Milliyan biyar biyar Suka sake samu,sai Momy ita Kuma itama Mijin Yayarta me kudi ne a Adamawa Nan mun samu kudi milliyoyi,a kankanin lokaci mun samu kudi kowa sunfi Milliyan ashirin ashirin,Baba Jummai Tace na manta gidan Alhaji Na Allah makwaftan Abbi da aka je Masa fashi sati uku da Suka wuce Momy da Mama da sa Hannunsu Kuma sun samu kudi Nima wacce nake da Yan fashi a Hannu na samu Rabo na,Dama yanzu Abinda akeyi kenan masu Aiki Ana hada Baki da su a cutar da masu gida,ko a turo mace a matsayin Yar Aiki ta sace Yaron gida a samu kudi Kuma a rasa Wanda yayi,a takaice Alkali Ni Baba Jummai a matsayin da naje Aiki kenan Kuma na je gidan masu kudi kala kala a matsayin Yar Aiki na tura musu Yan fashi da Yan kidnapping,gidajen da nayiwa Haka baza su Irgu ba,Kuma Ni tun da kuruciya ta na Sha zaman kurkuku Amma duk hukuncin da aka yanke min bana cikakken sati biyu mutanenmu zasu fitar Dani,Ni yanzu ba tsoron gidan yari nake Yi ba,Kuma wallahi Haka Kawai Shekaran jiya Ina kwance Allah ya saka min Nadama da Dana sanin abinda na aikata da cin Amana,Tausayin Abbi da Kaunar Fu'ad Dansa ita tasa naji Nadama ta kamani,na rasa ta yanda Zan tonawa su Momy Asiri shi yasa nayi amfani da korar da Abbi ya musu na Basu shawara Kan su kaishi Kara kotu.
Su kuma ta bakinka Alkali kwakwalwarsu Yawu ne a cikinta ba hankali ba tunani Suka yarda,har abinda zasu ce Ni na karanta musu tunaninsu Zan goya musu baya Basu San tona musu asiri zanyi ba,sabo da Haka Ni nayi nadama na Mika wuya ga kotu sannan a shirye nake na nuna duk Yan fashi da sauran Yan ta'adda Dana sani,Ai Momy Faduwa tayi kasa ta sume,Mama kuwa Baba Jummai ta nuna tana Allah ya tsine Miki Azzaluma maciya Amana kinci Amanar yarjejeniyar da Muka kulla munafuka,Baba Jummai Tace Ni dama shekaru na sun ja Nawa Zan Kara Nan gaba ai Kawai a kaini kurkuku na karasa rayuwa ta a can,bani da yaro ko daya bare jika,Mutuwar tsaye Muka Yi Ni da Fu'ad har Alkali,Baba Jummai ta kalleni Tace Rumaila lokacin idan Zaki tuna da yan fashi suka kawo ki part din Fu'ad,me yasa Duk Yan aikin Gidan ba a dakko ko Daya ba sai Ni,Sannan da sukace Fu'ad sai ya Sadu Dani ba Niyyar su bace nice na karanta musu Sabo da a duniya Ina sha'awar Fu'ad, Fu'ad Baki ya bude da sauri tare da rufe fuskarsa da tafin hannunsa Dan wannan abin kunya ne,Baba Jummai taci gaba,Ke Kuma Rumaila sai kika ce kin fanshe Ni kika tausaya min,a lokacin idan na dage sai da Ni za ayi to zaku Iya harbo jirgina musamman idan Yan Sanda Suka zo bincike shi yasa na kyaftawa Dan fashin Ido,nace na nemi afwa a barku kuyi a sirri ko tantama bana Yi Indai an barku Kun lulluba to baza ku aikata komai ba,dalili na shine bakin ciki na Miki tunda ban samu Fu'ad ya sadu Dani ba to kema bazai sadu da ke ba,sabo da nasan Fu'ad akwai tsoron Allah duk Ihun da kikeyi nasan wallahi karya ku keyi,shi yasa na biyewa kowa na dinga Nunawa ban san komai ba,sai gashi cikin hukuncin Allah kin auri Fu'ad,Baba Jummai ta tafa min a Gaban Alkali Tace na yaba Miki kinyi dace Rumaila,Amma su Momy wallahi da su muke komai Muna cutar mutane.
Abbi da dukkan mu mun rasa bakin magana,Momy tayi sumanta ta gaji ta farfado ba Wanda ya kula ta,Alkali yace yanzu za ayi shari'a Kuma wallahi tunda Kun amsa laifinku da kanku Zama daya zuwa biyu Zan yanke Hukunci,ko cikinku akwai me karyata Maganar Jummai? Momy tana Hawaye tace duk abinda ta fada gaskiya ne,Mama ma karya ta kare,Alkali yace ranar Monday a dawo zaman kotu babu Wani zaman sirri a Gaban kowa za ayi,Momy, Mama da Baba Jummai Yan Sanda ne suka tafi dasu za a ci gaba da tsare su har a Gama Kara.
Da Mamaki Muka dawo gida, jikinmu yayi sanyi,tuni labari ya watsu a dangi,su kansu su Fadila da su Islam kuka Wiwi Suka dinga Yi Basu taba zaton rashin Imanin Iyayensu ya Kai Haka ba,Sai ga Fadila Ana komawa gida ta wuce part din Rabi,Rabi Mamaki ya kamata dama taji komai da ya faru,Rabi da fara'a Tace Sannu da Zuwa Aunty,Fadila da murmushi Tace yawwa Kinga wallahi kwadayin danwake nakeyi Dan Allah kiyi min na ci,Idan nayi da kaina bazan iya ci ba,Rabi Tace Aunty ko dai juna biyu ne?Fadila Tace ban son Iskanci Kawai Ni ki min Ina jira,Rabi ta shiga kitchen sharp sharp tayi Mata,tana ci Saddeeq ya shigo dama kwanan Rabi ne yayi mamaki Amma Kuma yayi farin ciki matuka ganin Matansa suna ta Hira lallai Fadila anji jiki,Zama yayi a cikinsu,su Rabi an samu kishiya harda share Angonta suka ci gaba da hirarsu da Fadila,yace ikon Allah yau baza a kula Ni ba?Fadila Tace Dan Allah Malam tunda ka dawo ka tafi kayi wankanka mu Hirar zumunci mukeyi,Kai Saddeeq ya jinjina yace au abinda zaku Yi min kenan shike Nan sai na rabaku,Fadila ta kalli Rabi Tace je ki kula da mijinki,Rabi ta Mike suka Shiga ciki,Fadila sai da ta cika cikinta sannan ta koma sashenta,Rabi da Saddeeq Kuma da dare a banfaren Fadila Suka raba dare suna Hira.
Ni kuwa da Fu'ad da muka dawo wanka Mukayi Kawai tare da kwanciya Muna tattauna abinda ya faru,Abbi kuwa Bai Yi saurin yanke Hukunci ya saki matansa ba sabo da shi a duniya baya son saki,ace ya auri mace Kuma ya saketa,sai Ranar Laraba da Muka koma kotu,ko da aka zo Shari'a Baba Jummai a waya ta Kira Ogan Yan fashin nasu Tace su hadu a Salama Hotel Dake maitama wata sabuwar harka ta samu,yace sai gobe zai zo,Duk wasu mugaye sai da Baba Jummai ta Basu Venue na wajen haduwa,da Yan Sanda aka kamasu a Hannu Daya Bayan Daya,Ranar Monday aka sake Shiga kotu babu Bata lokaci kowa ya amsa laifinsa,sai lokacin Abbi ya saki Momy da Mama saki dai dai aka yanke musu hukunci,Mama da Momy daurin shekara talatin a gidan Yari Baba Jummai kuwa sabo da ta Dade tana Yi gashi a cikin yan fanshin sun tabbatar da sunyi kisan Kai Alkali ya musu daurin Rai da Rai a gidan Yari har Baba Jummai,Baba Jummai da Yan fashi ko damuwa basuyi sosai ba sabo da dama sun Saba,wannan ne Kawai aka yanke musu Rai da Rai,Momy da Mama su suke ta barka kuka tare da Yaran da suka Haifa,Dukkanmu dasu Umma jikinmu yayi sanyi Kuma mun tausaya musu,Abbi matansa sun koma Biyu Umma ita kadai a gidan Nan sai Yara duk sun koma karkashinta ta Zama Uwar kowa,Aunty Samha da yaranta ita dama gidanta daban Haka Muka ci gaba da Zama cikin kwanciyar hankali da Jin dadi,Har Saude mun Sha biki tana Kano gidan mijinta Haka su Naila Abbi ko Shagali ba ayi ba sabo da abinda ya faru Aure kawai aka daura tare da Kai Amare,Gaba Daya sun