Showing 111001 words to 114000 words out of 115153 words
Nima fuska ta na gyara na yafa Mayafin na dauki Hand bag Dina nace da me Aikina naje Shopping yanzu Zan dawo,pls kafin na dawo ki Kara gyara kasan,sama na gyara komai yanzu,To a dawo lfy Hajiya,Glass Dina me tsada na maka a fuskata na shiga motar Fu'ad Baka katuwa,Ni ke Driving naje na siyo abinda nake bukata sannan na Kira Fu'ad,Nace ka tashi na biyo na daukeka ko na wuce gida? Yanzu sai da kikai Driving bayan na hanaki nace ki Bari sai kin Haihu,Akwai abinda na damu Zan siya ne shi yasa,zo ki dauke Ni to,Office dinsa na Shiga Ina mota ya fito ya sameni sanye yaje cikin kana Nan Kaya na kirki muka wuce gida,Ina Driving Yana tsokana ta Wai me ciki ko kunya bakya ji kowa yasan ta ya aka same shi,ban kulashi ba sabo da na Saba da tsokanarsa kullum,yace Wai yanzu ya zanyi idan kin Haihu sai anyi 40days zanyi wani Abu? Ae na bashi amsa,yace wlh akwai kura a kasa,ke l bazan iya ba babu ruwana jini na daukewa Zan dawo bakin aiki,nace ai Iya Tace a can Wajenta Zan zauna,tab ki daina ma sa Rai wlh bazan yarda ba muna ta surutu har muka je gida.
Tafiya na ja rayuwa na gudu ciki na ya cika wata tara, kullum sa rai nakeyi da Haihuwa, Fu'ad ma Bai fita yayi nisa gudun kar a samu matsala,Yau Kuma Saturday Abbi ya tura Fu'ad Lagos zaiyi wani meeting zai wakilce shi,7am ya bi Flight yace da wuri zai dawo,Sai da ya lallabani sabo da na tashi bana Jin dadi,shi Kuma tunaninsa tunda kullum Haka nake cewa Bai kawo komai ba, kuka na sakar Masa da kyar ya lallasheni ya tafi,Ciwon Baya da Mara ne ya takura min naji abin ba sauki Kawai na Kira Umma na fada Mata a waya ai kuwa sai gata ita da Fadila a mota,Fadila ke Driving na hada kayan Dana tanada na Haihuwa a wata jaka katuwa ta Yan gayu me tsada,kana gani kasan Yan gayu ne kudi Kuma ya zauna,Umma ta kalli jakar Tace Haihuwar fari kenan ba a San Kan Nakuda ba har wani kyale kyale akeyi,nace Umma ayi sauri Kar na Haihu a mota Muna Hira da Fadila,Umma Tace ah ba nakuda kike Yi ba,idan tazo wannan Maganar baza ki Iya yinta ba, private Hospital inda nake zuwa Awo can Muka je,Bayan an duba Ni Tace Haihuwa ce Amma ba Yanzu ba sai yamma gado za a baku,Dakina Ni kadai dake na kudi ne ko Ina sai kamshi,Kamar jira ake a bani daki sai ciwo Gadan gadan ya taso,Marata na rike Ina bubbuga kafafu na,Umma ta kalle Ni,Shuru bana iya magana,Fadila tana gefena Tace ciwon ne ya dawo? Ko kulata banyi ba,Dankwalina na zame na mikawa Umma bana magana,na fara wash wash....Umma Tace Sannu Addua zakiyi Nace wacce Zan karanta? Umma Tace ko Mai ma,zamewa nayi na sakko kasan Tiles na zauna Ina cewa Umma Kira min Iya ciwon Nan bana tashi bane dama na fada Masa,Umma Tace ai Rumaila har yanzu Baki fara komai ba tunda kike Iya magana,Nace Nan duk banyi komai ba? Fadila Tace sosai nace to Kawai mutuwa zanyi,Indai ciwo ya fi wannen ai sai na tafiya Kiyama,Umma ce ta Kira Iya ta Mata bayani,Iya hankalinta ya tashi tace bani Rumailan ko Bata Hayyacinta? Umma ta Mika min waya nace Iyata na fashe da kuka,Iya Tace Rumaila ya jikin ba Kuka Zaki ba Addua akeyi,Nace Iya sai dai Allah ya sada mu a darulsalamu,Iya Allah sarki Uwa sai ta goge hawayenta hankalinta ya tashi tace ko nazo ne Rumaila? Nace ae Iya ki taho na ganki,Iya Tace gani Nan Inshaallah,ai Iya mijinta ta sanarwa Kawai ya Mata booking a jirgi tazo sharp sharp,Asibitin ta wuce Direct a Taxi.
Umma ta Kira Fu'ad Yana Meeting da mutane Yana ganin Kira ya dauki Excuse ya fita ya Kira Umma,Umma Tace muna asibiti fa Rumaila nakuda sunce Haihuwa sai Nan da Magriba ma,Hankalin Fu'ad idan yayi dubu ya tashi,Ina Rumailan? Umma Tace gata yace Bata Wayar ko baza ta Iya ba? Umma Tace ga Fu'ad,Lokacin ciwon ya Murda tun Ina daurewa Ni dai na kasa na fashe da kuka,Yana ji ta waya Ina cewa Zan mutu,dama Ni akwai kwailo,sai birgima nakeyi a saman gadon,idan na gaji na sakko kasa,Sai da ya Dan lafa Sannan Umma ta Kira Fu'ad ta bashi Ni,Sai Kuma ya jini Ras muka gaisa nace naji sauki karka damu yace to,kafin ya rufe Baki ciwon ya dawo nace Iya ya dawo wallahi wayoo Allah marata...wash......... Fu'ad Wayar ya kashe ya koma Meeting,da kyar yake dannewa yayi sauri ya sallami kowa gashi Return ticket dinsa sai 6pm,Gashi zai canja wani babu na time din duk sai yamma,ai kuwa ya dinga tsinewa Nigeria Yana me za ayi da wannan kasar komai nata babu na arziki sai tsiya,ai har abada wannan kasar idan kaga anci gaba a kasar nan to sai dai idan mutanen ciki za a kwashe gaba Daya a kawo sababbi a zuba,Dan ko jariri ne Indai an haife shi a Nigeria to idan ya girma ya Sha nonon zalunci,shi kadai yake ta masifa sai waya yake bugawa Umma ba ji ba gani,Ko minti biyar bayayi zai sake Kira yace Umma ya jikin nata? Taji sauki?har yanzu Bata Haihu ba? Ina asibiti Ina ta gumurzu har Yamma ban Haihu ba sai wurin 5pm da taimakon likitoci na Haifo Dana Namiji katon gaske kyakyawa ajin farko.
Na Sha wahala,sai bayan na Haihu an gama komai Har jaririn Iya sun Masa wanka Nima nayi na canja kaya,aka hada min tea me kauri Ina Gama shanyewa jini ya Balle min,Hankalin kowa ya tashi jini na tashin hankali ba kadan ba,Nan likitoci Suka fara aikinsu a kaina da kyar aka samu ya tsaya,Wurin Magriba aka Gama min komai na Dan farfado Iya ta sake min wanka na shirya na canja wasu kayan,jiri Yana daukana,dakin Hutu Suka canja min ko Ina Yana kamshi,Bayan sunyi bincike da gwaje gwaje Suka ce dole sai an Kara min jini Leda biyu,Umma ta Yiwa Yan mazan gidan waya duk Suka zo aka dinga gwada su duk babu Wanda yazo Daya da Nawa A+ sai Islam,lafiya Kalau yake Amma Leda Daya Suka ce zasu eba a turo wani shima,lokacin Fu'ad ya dawo dama yasan komai suna waya da Umma,yayi zuru zuru ya fada tunda ya tafi babu abinda ya iya sawa a bakinsa,Direct wurin abinci ya wuce yaci badan Yana so ba sabo da Kawai yaje a gwada shi,Malt ya Sha da Fresh milk, ya wuce wajen aka gwada shi anyi sa'a shima A+ ne irin Nawa Dana Islam,Nan take aka ja nasa,yayi yayi su barshi ya shiga yaga lafiya ta sunki yarda,Zama yayi tare da zuba tagumi,Ya gaji ya koma masallaci yayi Sallah ya zauna Yana ta Addua harda guntun Hawayensa Allah ya bawa Rumailansa lafiya ko ta Jaririn Bai bi ba,Yana masallaci aka Kara min Leda daya,aikuwa Ina Jin jini a jikina naji wani karfi naji ma gaba Daya na warke,Da kaina nayi wanka Amma da ruwa me Dan dumi,sai gashi Dana Yi da towel shima ba duka jiki ba,Har gashi na na wanke sabo da duk kyankyamin kaina nakeyi,Sai Dana Gama na fito na dakko sabon Brush da toothpaste zanyi,Umma Tace Ikon Allah Rumaila da Iya shiri Haka Kamar kin San Haka zata faru komai kinzo da abinki,murmushi nayi nace ai dama dole ka dinga tunani iri iri,Bayan na fito,Suna kallo harda Dan shafa man jariri a kafafunsa da Hannayena,Na dakko turaruka na Ina shafawa sama sama,Har kayan da zansa,Su Iya sai kallon Ikon Allah suke Yi,Iya Tace Dan Ubanki Wai wa kike yiwa kwalliyar ne kina jego,Ni dai banyi magana ba,na saka Bra ta tana kamshi na zura doguwar rigar Atamfa ta sabuwa dal black me digon maroon,Dake akwai ac Nan take gashi na ya Bude na taje sama sama na Dan gyara abina tare da shafa Masa Dan Mai na tufke,na koma saman gadon Hutu na,Umma sai da suka wanke kayan Dana Bata suka tafi dasu gida,ta sake zuba su a washin machine ta wanke ta shanya,Fadila kuwa lafiyayyen farfesun kaji ta kawo min,su Khaleesat su Rabi duk sun zo,Rabi Tuwon Danyar shinkafa ta kawo Miyar kubewa danya ta Sha kifi Ni Nace shi nake so, nace ta hado da yajin jego,Rabi Tace a jiki yayi kyau Rumaila Harda wannan wanka Haka daga Haihuwa,a kunne ta rada min Karfa ki jawo mutumin ya zauce,Murmushi nayi Kawai na Matsu Naga Fu'ad,Kuma sabo da shi na gyara ban so Mijina yaji wani Abu ba me Dadi ba,ban son ya shaki wani Abu marar Dadi shi yasa na daure,Me wankin toilet tuni ta shigo ta wanke ta sake goge Room din wani kamshi ke tashi,Jariri Yana ta baccinsa cikin kayan sanyi farare masu Matukar kyau da tsada, Fu'ad ne ya siyo tun cikina Yana 7mnths.
Sai wurin 9pm Kamar yanda Likita Tace zata Bari ya Shiga ya ganni kowa ma zai shiga,Amma Dake Mata ne Basu Hana ba,Daga Ni sai Iya sai Khaleesat,sune zasu kwana tare Dani,Ai Likita Fu'ad ta Kira ya dinga Hararar Likita Yana Tsaki Yana bala'i Kamar zai kashe ta yace Kuma wlh daga wannan bazai sake kawo matarsa wannan Asibitin ba,aka dinga bashi Hakuri,yace ko Asibitin Gomnati ne Idan na nemi Alfarma za a barni ko ta window Naga matata, har Shugaban Asibitin sai da ya bashi Hakuri sannan ya hakura ya ja tsaki ya shiga,shi kuwa me Asibitin ya jawa maaikatansa kunne sosai,Fu'ad kofa ya bude ya shigo da Sallama Yana fargabar halin da zai sameni sai ya ganni a zaune sosai Ina cewa Iya Miko min shi na shafa Masa turare,Iya tace Iyye Rumaila ba kunya,Baki na turo nace Iya ko da ganin kirki ban Masa ba,Iya ta Miko min nayi Bismillah na karbi abina na Bude turare ina shafa Masa a kayansa, Fu'ad yayi Sallama Bamu ji ba ya tsaya Kawai Yana ta kallona da jariri Yana wani murmushi.
Iya Tace Fu'ad Ashe ka shigo,yace Iya Ina ta Sallama Baku ji ba,Dukawa yayi ya Gaida Iya, Khaleesat ta Gaida shi,suka Mike tare da Iya Suka fita,a gefe na ya zauna tare da daura Kansa a kafada ta,a Raina nace da na zauna banyi gyara sosai ba ai sai kaga me gida Yana gudunka,Gashinsa na shafa nace Sannu da Zuwa Daddy, Dariya yayi yace Yawwa Mummy,ya aiki? Alhmdllh,ya bani labarin aikin da zuwansa da hanashi ganina da aka Yi,Yace kinsha wahala ga idonki Nan duk sun kumbura,nace kuka naci,na Sha wahala mutuwa ce Kawai banyi ba,dama Haka Haihuwa take? Kai Allah ya rabamu da Ita, Fu'ad yayi Dariya yace to ai Next year za a Karo Mana mace,da sauri nace wa? Nace wallahi bazan Iya ba,to Bari kaji Likita ma Tace sai nayi shekara bakwai sannan Zan sake Haihuwa mahaifata tana bukatar hutu,Sannu Sarkin karya ance Miki duk abinda ake ciki Likita Bata gaya min ba Tace Kalau kike lafiya sumul,Nace to na Rantse da Allah bazan sake Haihuwa da wuri ba ko kana so ko baka so dole a zabga min Allurar Family planing na Gama magana da Likita, Fu'ad yace Ni ban yarda ba ai sai da amincewar miji,ba sai an Miki ba Ni Zan nayi idan Zan kawo sai zare na kawo a waje na zubar sperm din ba shike Nan ba,nace da wa zaka Yi wannan tangal tangal din? Ni baza ka min Wasa da rayuwa ba Wani Iyawa zaka Yi tun yaushe Dadi zai kwashe ka kayi abinka a ciki Bazai yuwu ba,Nifa baza ka takura min da Haihuwa ba Akan Haka sai nayi yaji wannan Uwar wahala Haka,da nasan Haka abin yake ai da na dauki mataki a kanka tuni, Fu'ad Yana ta kallona Ina ta masifa Ina bala'i,yace Ni dai gaskiya Nan da 2years ki Karo min yarinya,Kuka na saki sosai,yace ke Mene Haka Kuma? Na dago Ina kuka nace ba kace sai na sake Haihuwa ba na karasa da kuka....Fuskata ya leka Dariya na bashi yace to Yi Shuru sai Sanda kike so Zaki Haihu Wasa nake Miki,Lokacin na goge Hawayena na Mika Masa jaririn,Ya karba ya Masa Addua sosai,yace kin Masa Addua? Nace ae,Abinci fa kinci? Nace na Sha Fresh milk,tea ga tuwo na ga Farfesu Fadila ta kawo zanci,sai me kike son ci? Nace Fruits Salat,nace ance na dinga cin gasashiyar Hanta, da Fruits sosai da bargon kifi,Dariya Fu'ad yayi yace kinfi karfin wannan Baby ba sai kin Kara da karya ba a Ina kika taba ganin wani bargon kifi? Jaririn Yana hannunsa na Daura kaina a kafadarsa na lumshe Ido zanyi bacci,Iya da Khaleesat Suka shigo,Iya Tace dare yayi ka tafi gida Kai sarakan Soyayya jegon ma tare zaku Yi,munafuka shi yasa Duk halin da kike ciki sai da kika wani Sha gayu Ni dama na Gama gano ki, Fu'ad yayi Dariya yace Iya ai yau a Nan Zan kwana,Tashi yayi yace zaije ya dawo,Jaririn ya mikawa Khaleesat ya fita Bai Dade ba ya jibgo Mana kayan ci Dana Sha abin ma yayi yawa,Iya ta dinga Masa fada,Gida ya tafi yayi wanka ya kwanta ya huta bacci yayi gaba dashi.
Nima tunda ya tafi bacci nakeyi ban tashi ba sai da Iya ta matsa min na Bawa jariri nono sannan na koma bacci na,sai 11am na tashi,Iya tana ta min fada ban tashi da wuri ba,to ba Sallah zanyi ba,Brush nayi nayi wanka Iya da kanta taje ta min gashin mugunta da towel,Umma ta taho min da wasu kayan Nawa Wanda muka cire da jaririn ta tafi gida ta wanke a washing machine, idan ya bushe masu Aiko su goge su Adana min,Bayan naci na koshi aka sa min Ledar jini na biyu,Yana karewa aka zare,Yan makarantar mu suna ta zuwa dubani da ganin jariri,abokan arzuka,lokacin da Fu'ad yazo Ana Kara min jini ya fita,abokansa Haka Suka dinga cika asibiti suna dubani da ganin jariri na Sha kyautar kudade,Abbi da mazan gidan suna ta zuwa musamman Islam,Yayan su Fu'ad da matarsa tare da Babar Abbi Duk sun duba Ni a waya.
Washe gari aka sallame mu Muka tafi Iya ta nace sai dai a maida Ni gidan Umma,nace Iya Fu'ad yace Bai so shi Bai yarda ba,Iya Tace Ubanki Baku Isa ba a barku ku Daya Haihuwar fari kuyi ta shirme,Umma ma Tace Iya tayi gaskiya,Haka Suka tafi Dani,Nace to a kaini na ebo Kaya,Umma Tace mijinki ya kawo Miki muje Driver,Driver ya tuka Muka tafi Part din Umma muka je dakin Dana taba Zama tun kafin aurena da Fu'ad Nan Umma ta shigar Dani ya Sha gyara Bamu dawo da Kaya masu Dirty ba duk an wanke an goge min an shirya a dakin Dama Ashe Umma da Iya sun Gama shawararsu,Sai Fu'ad Kawai Umma ta Kira ta fada Masa,ba yanda zaiyi yace da Ummansa a'a hakura yayi yace ba damuwa,Umma Tace kuyi magana da Rumaila abinda take bukata ka kawo Mata,Okay yace Kawai ransa ya baci kamar yayi kuka,yace Wai mutum da matarsa wannan Hali na Hausawa baza su canja ba.
Haka ya kirani na karanta Masa duk kayan da zai ebo Amma Wanda yake so sai yaki kwasowa da su ya kwaso Wanda yaga dama,ya biya ya siyo min Abubuwan bukata na amfani,masu Aiki Kawai Naga suna ta shigowa da Kaya,sai da suka Gama ya shigo a karshe,Kayan nake dubawa naji ya kulle kofa ya sa key,Ta baya ya Rungume Ni a jikinsa Yana shakar kamshi na, juyowa nayi nace Su Umma sunce sai dai na zauna a Nan,yace ae ta fada min ya zanyi su ita da Iya,Nace ya Naga banga English Gown din Nan ba? Yace kin San yanda take Miki kyau kuwa? Kika saka ta nazo na ganki ai sai kisa nayi aika aika,Shagwaba na fara nace Ni gaskiya ita nake so tana min dadin sawa,wani kallo ya watsa min nayi Shuru,Jaririn ya dauka Yana ta Kallonsa Yana Jin wani irin Dadi yayi da,Flasks din ya Shiga budaya,Ni Kuma na Bude Kofar daya da key gudun kar ace wani Abun mukeyi,yace Wai kullum sai kinci tuwo ne?nace Iya ce Tace Wai sai na dinga ci anfi karfi ya na Iya,Daya ya Bude yaga faten wake da doya yasha Hanta,yayi Murmushi ya rufe ya Bude wani yaga Farfesun Naman rago yace Iyye kina goge duniya me jego,ya sake Bude daya yaga gasashen nama yace Allah 'yar Nan,Dariya ya bani na dinga kyalkyalewa,yace Ni yanzu an daina kulani,naci abinci ko ban ci ba babu abinda ya dameki sai dai kici ki koshi ki bawa danki Nono Ni ko oho,kirana ma bakya Yi a waya sabo da kin samu da,to ya Zan maka tayi na sani ko kana kyankyanmin me jego,Hararata yayi yace Zan mareki da sigar wasa,Zama nayi na dauki jaririn na juya Masa baya na Bude Zan bashi nono, Fu'ad zai leko na fasa,Yayi Dariya yace kinzo da rainin hankali,mene ban sani ba Ni Zaki boyewa nono? Na fasa bada nonon na jawo flask na zuba Tuwon shinkafa ta miyar Egusi,na sa cokali Ina ci,Spoon ya dauka shima ya fara ci tare Muka ci sai da muka kusa gamawa sannan Umma da Iya Suka shigo Wai za a yiwa jariri wanka,Iya tace yunwa yake ji,Rumaila ba Kya kula da jaririn nan, Dan Rashin Imani Kun wancakalal dashi a Kan gadon can gefe Kuna cika cikin ku shi Kuma ko Oho,Umma Tace ai laifin Fu'ad ne,Iya Tace bashi ya Sha da Allah mu sauri muke Yi,Nace to na sake juya bayana sannan na fara bashi nonon, Fu'ad Yana son ya kalla ga su Umma dole yaci gaba da cin tuwonsa,na bashi Iya ta karba ta tafi Umma kuwa dama kayan ta eba ta tafi,Suna fita yace San min na Sha kinji? Nace bada Ni ba na gyara Rigata daf,a gadon ya kwanta dama ya gaji sai bacci ya tafi da shi.
Ba wani suna da za ayi sakamakon Babar Abbi tana asibiti Rai a hannun Allah ciwon sugar ya tashi