Showing 90001 words to 93000 words out of 115153 words

Chapter 31 - DANGIN RABI COMPLETE

23 Aug 2025

1578

su,Suna Haka sai ga Momy da Mama tare da Yan matan su harda Yusra suna Yanga,Momy tana yatsina Kamar taga Kashi,Iya a ranta Tace lallai za a yita sai na tabbatar na gyara muku Zama zaku ci Ubanku,a fili kuwa Iya Hijab dinta ta gyara, Abbi tashi yayi ya tafi abinsa, Fu'ad yace Iya yau Zan tafi dake yawo,Tace na gode Dana ai nasan baza ka bani kunya ba,Zama su Momy sukayi Mama ta ja tsaki,Iya tana jinsu Amma ko kallon inda suke Iya Bata Yi ba,Momy Tace barkanku ya Kauye?,Babu Wanda ya amsa bare tasa Rai za a kulata.

Mama Tace ya Ana magana Kuna Jin mutane,Iya ta kalleta shekeke Tace au damu kuke ne?Affa da Kawu Mikewa sukayi Suka koma bangarensu Suma ko kulasu Basu Yi ba, Fu'ad ba karamin farin ciki yaji ba da su Iya Suka Yi Haka,Rukayya da Haleesa Suka Mike tare da cewa Bari mu huta daga ciki Suka Yi bedroom,saura Iya da Yafendo da matar Kawu sai Kuma mu da su Momy,Umma ita kanta su Iya sun birge ta,Tsaki Momy taja,Iya a ranta Tace zanyi maganinki Bari na warware daga bakunta, ta Mike da matar Kawu Suka Yi ciki,Umma ta tafi Itama, Fu'ad Hannu na ya rike Muka Yi waje muma saura su Momy su daya da su Khaleesat,Naila dama tana Kano ita,Momy Tace kan uban Nan Kinga Yan Kauye? Mama Tace kyale su zasu ga wulakanci sun zunguri sama da Kara,Umma Su Iya kaf matan ta tafi dasu bangarenta a can Nene ta same su Suna kallo.
Ni kuwa Fu'ad ja na yayi part dinsa na gidan ba kowa a ciki,kullum Ana gyara part din ko Ina Neat.








Masu Sharhi Ina matukar Godiya.



AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈







NA KUDI NE

WACCE TA FITAR DA SHI ZUWA WASU GROUPS DA WACCE BATA SIYA BA TA KARANTA ALLAH YA ISA.












DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM







86-90










Official








By
AsmaBaffa











Page naku ne

Auta
Mmn Ummee
Aeesha
Dr Zainab Abdullahi
Alhusnah Mrs Idris
Balkisu
Ummu Arfat
Farhat Mrs Mj
BK
Basmam Glam
Muneerah










A palon na tsaya Ina Kare Masa kallo Wani Yadi ne a jikinsa ruwan Zuma me tsada yayi kyau,Saman 3seater Muka zauna,kallona Kawai yakeyi ya zuba min kyawawan idanuwansa,Kunya ce ta kamani na murguda Masa Baki tare da dauke kaina daka Kallonsa Ina murmushi duk na rasa inda Zan sa kaina sabo da kunya Kuma da farin ciki yau Ina kusa da shi,Hancina na Sosa tare da shafawa,Duk Bai dauke idanunsa ba,Mayafina na gyara sabo da rigar wuyanta me wani raga ne naga kuma shatin Albarkatun Kirjina sun Dan Yi Showing,Mene Haka ya Furta tare da bankade Mayafin ya maida shi baya, Dan tashi na gani ya Furta nace Sabo da me? Umarni na bayar yace Yana kashe min Ido daya,a kunyace na Mike tsaye na Danyi Taku biyu na juya na juyo sannan na zauna s kunyace,yace dama Haka kike? Nace me? Da sigar Rada yace kin hadu,Labbansa na karanta Kawai,Hannunsa ya saka cikin Nawa tare da shigar da yatsunsa cikin Nawa saman Cinyarsa ya Daura Ni tare da zame Mayafin Nawa Gashina da yasha gyara ya warware Yana shafawa,Gashin ya tattara tare da hade shi a hannunsa ya maida shi Bagare daya ta saman kafadata ya Shiga bin bayana da kiss,juyo Dani yayi a cinyar tasa Muna facing juna Bakina ya laluba muka fara Kissing kamar zamu kashe kanmu.

Munyi nisa mun Lula wayarsa tayi Kara Yana ganin Umma yace to fa ya daga kiran Ina Rungume a kirjinsa Wanda da sai da ya saita Muryarsa sabo da tana rawa,Yace Umma Tace turo min Rumaila yanzu akwai abinda zata Yi, Fu'ad dama yasan abinda zata ce kenan,Gani nayi ransa ya baci ya canja lokaci daya,Nace lafiya? Lfy Umma ke neman ki,Hannayena na sakalo ta wuyansa nace shine kake fushi? Shuru yayi,Murmushi nayi nace Kayi Hakuri komai zai wuce soon,Kiss na Shiga manna Masa a jere na gangaro tun daga goshinsa zuwa kumatunsa na sauka a lips dinsa.

Rigata ya gyara min ya gyara shima kamar bamuyi komai ba Sannan Muka fito a tare muna Hira,Yusra ce take leken mu ta saman Momy tare da Farida ko me suke cewa oho, har part din Umma muka Shiga Umma tace zo muje kitchen,Binta nayi Fu'ad ya zauna kusa da Iya, Fu'ad yace Iya yaushe Zaki ga gidana Ni? Iya Tace au Wai ba a Nan gidan sashen Rumaila yake ba Wani gidan ne daban naku? Fu'ad yace ae Baki sani ba? Iya Tace kan Uba lallai Allah ya yarda,Ashe mu muna Kauye Muna karbar Kebur (Cable) Zane mu Kawai akeyi da Kebur,Fu'ad Yana murmushi Ana labarai aka nuna kasar Switzerland Iya Tace wannan wanne gari ne haka? Fu'ad yace Switzerland kenan Iya a Nan ake buga kudade har na Nigeria,Iya Tace na rike sunan,wannan kasa abar zuwa ce Ina son su,shegu sai sun Gama kwashe kudin su Aiko da ragowar kasar mu,ga Inda Yan Kidnapping zasu je can su dinga dauka ba ruwansu da ciniki ko Nawa Suka fada Basu za ayi hankali kwance.

Iya Tace Amma gobe zaka kaini yawon ko? Fu'ad yace Inshaallah,ganin Iya ta kankane Rumailan tasa sai Kawai ya Dan fita compound daga can ya wuce masallaci sai da yayi Sallar Isha sannan ya dawo lokacin naje zanyi Sallar Nima naga na fara period ma gashi Banda pad Kuma kunyar Umma nake ji,Wayata na jawo a saman Mirror na Kira Fu'ad,Yana dagawa nace kana gidan Nan ne? Yace ae Ina part din Abbi,Da Shagwaba nace yanzu naga na fara period Kuma bani da pad ko daya,Wani haushi da bakin ciki ne ya lullube Fu'ad yace Innalillahi Ni Kam na Shiga Uku Kawai a kaini kabari a binne Ni na huta,Wai kwana Nawa ma kike Yi ne? Nace 3days,Yanzu har 3days Ina laifin 1-2 days ma,kice Umma ta baki,Ni kunyar Umma nake ji Kawai kaje ka siyo min,Da Kansa ya fita Kofar gida kusa da gidan akwai wani Chemist katon gaske a Nan ya shiga,Yace pad nake so me kyau,yace ga wacce take hade da Maganin Infection,ita ya siyo me tsadar kana gani ba sai an fada maka ba, a Bedroom din da nake ya shigo ya bani yace muje na gani ko karya kike Yi ban sani ba,Dariya nayi nace akan me Zan maka karya,Toilet na shiga sai Bai iya Bina ba baya son ganin kazanta,na leko nace shugo mana,fuska ya yatsina yayi kwanciyarsa a saman bed din Yana latsa waya har nayi wanka tare da shirya kaina na fito daure da towel Ina goge ruwan jikina da karamin,Mikewa yayi zaune yace kawo na tayaki Yana bin cinyoyina da kallo har na karasa bakin gado inda yake zaune.

Murmushinsa me tsada ya saki tare da furta kin Zama Yar Lukuta wannan cinyoyi sun Tara tsoka me Iya ke Baki Haka? Dariya nayi kadan na Mika Masa karamin towel din ya karba Yana goge min gashi na Yace Bari a dakko Handrier Umma,Me Aiki ya leka ya fada Mata inda zata dakko tana kawo wa tayi knocking ya Bude kofa ya karba ya rufe ya dawo ya jona tare da kunnawa da hannunsa yake barbaza Gashina Yana busar da shi,cikin kankanin lokaci ya bushe yayi Amfani da cumb ya taje harda shafa min mayukan gashi iri iri karshe ya fesa min Hairspray kaina Yana saman cinyoyinsa,nice na Kama gashin da Ribbom ya wanke hannunsa a toilet,Yana fitowa yace kawo lotion din a shafa Miki Baki da sauri ke kin fiye Nawa,Ni dai na Mika masa,yace Ina face Cream din? Nace ai duka shi nake shafawa yace Haka aka ce kiyi? Baki gansu ba set Guda kowanne bangaren akwai nasa shine Zaki na shafa kowanne a fuska idan kuraje Suka fito fa Bai karbe ki a fuska ba,karki lalata fuskar Nan tam,Ni dai Shuru na Masa nasan tsurfar masifa ce da shi,Harda sawa kofa key Yana shafawa sai faman lailaya min wuya yakeyi wani Dadi naji kamar ana min massage,na wani lumshe Ido shi kuwa wani dalla dalla yake bin ko wacce gaba Yana murzawa,kirji na ya gangaro Ina ji nace a tsalle nan,Harara ya watsa min nayi Shuru Ina ji Ina gani ya janye Towel din ya barshi a Hips Dina,zan Kare kirji na da hannu yace Don't...Fasawa nayi ya haye saman Bed din tare da wani sani a tsakiyar kafafunsa Kamar wata Yar yarinya,Albarkatun Kirana ya Shiga shafawa lotion da Hannu biyunsa,Ido na sake lumshewa tare da zaro Harshena na lasi labbana,Maitar ta motsa kenan? Naji ya tambaya,Dariya nayi ba shiri Ni ban ma San nayi ba,Mai Kawai nake shafa Miki ba abinda nake yi,Yana magana Yana Sarrafa Albarkatun Kirjina yanda ya ga dama,sai da yaga dama sannan a gangara cikina zuwa bayana,Mike tsaye ya Furta na sauka na Mike yazo ya shafe cinyoyina tare da lailaya su har ya Gama sannan yace na Gama,da sauri na Daura Towel dina, Zan fita Ni na manta ma nayi hanyar toilet zato na kofa na bi,Dariya ya dinga min,Hankali na ya tashi,yace baza ki sa Kaya ba Haka Zaki tafi? Sai lokacin na tuna,Dawowa nayi na duba jakata na Dauki wata doguwar Riga me Hannun bra maroon me adon fari digo digo,yace ajiye rigar Nan sai Mun koma gida,doguwar Rigar lace na saka Brown,Shiryawa nayi shi Kuma ya Mike yace Zan tafi gida Sarkin santi daga shafa Mai kin wani rikice,Fuska na kwabe yace bacci nake ji,Nace tun yanzu ko goma Bata Yi ba,Me Zaki bani? Nace ba komai,to Good Night yace tare da kissing Dina a lips sannan Muka fito tare ya wuce Ni koma na koma part din su Iya sunyi Shirin bacci,Nima dakin da Iya take na Shiga ita daya ce zata kwana,Nima Shirin bacci nayi na kwanta kusa da ita,Iya Tace Wannan matan Haka Umma take zaune da su?nace Ae,Iya Tace yo kishi hauka ne?

Baki na tabe nace Iya ki rabu da su duniya ce ai Allah Yana kallo,Shuru ma magana ce kana zamanka Zaki ga allonsu ba Rubutu Allah da Kansa zai Yi maganinsu,Ni Wannan Yusran Kawai na tsana Yar Kawar Momy jira kawai nake ta kulani inci ubanta,Dariya Iya tayi Tace sabo da kar ta aurar Miki miji? Mu Wato mu kyale su Momy da Allah ke Kuma kici Uban Yusra ko? Ni ba kishi nake da ita ba,sai dai ki gayawa wani Rumaila Amma Ni Iya ban iya jurar wulakanci ba,anyi Daya biyu to na Uku bazan Iya Shuru ba.....wayata ce tayi Kara Iya Tace Tashi ki fita baza ki Hani bacci ba da Baby Baby Abu yaki karewa ki koma dakin Haleesa ita kadai ce dama sa'arki ce sai kiyi a can,Wayar na daga tare da Mikewa na koma dakin Halisa ita daya ce Bata Yi bacci ba kallo ma takeyi,kwanciya nayi a gefenta Ina waya kasa kasa, Ina ta fadan kalaman soyayya Wanda suke susuta me gida,Haleesa tana ji Tace wlh ba Wanda ya Isa ya hanani soyayya da saurayina Kuma aure kamar nayi,na samu Dan mijina za a hanani,Ina jinta bace Dan Uwarki Ni ba Mamanki bace kike ce min ba Wanda ya Isa?Shuru ta min,Nima na share zancen.

Washe gari da Yamma Umma ta Kai su Iya gidana Suka Sha kallo,Iya Tace yanzu nanne gida yata Rumaila? Umma Tace ae,Ai Iya sai ta fashe da kuka Tace na tuna Sanda nace bazan shayar da Yar Nan ba sai da Ubanta ya biya kudin shayarwa oh Ashe matar manya ce ban sani ba,da nasan Haka ne Iya ta sake fashewa da kuka Tace Allah ya daidaitaka Salahu,Baki Affa ya tabe yace daga baya kenan,ba ruwan wani Aljani dama Haka Halinki yake Uwar son kudi to gashi Nan ai yanzu kinfi kowa morarta kafin na Mori Rumaila dubu daya kin Mori dubu goma komai gidanki ake kaiwa Bayan Baki Mata rainon kirki ba,Haihuwar ma cewa kikayi ke Baki da karfin zuciyar haihuwarta a gida sai da na kashe kudi a asibiti,ko wacce mace tana jarumta wajen Haihuwa Amma ke duk Asibitin Nan sai da kika cika shi da kuka kina Amadu Allah ya tsine mak,Allah ya kwashe maka Albarka Amadu, ranar kin tsine min tafi cikin Container,Kawu Haruna yace yo Iya ai sai Hakuri na tausayawa Wanda suka aure ta,Affa ya gallawa Kawu Haruna Harara yace Amma munafuki ka wuce gaba aka daura Aure na da Iyan harda cewa nayi Dace,Kasan Haka take ka rufe min,Kawu yace Hannunka baya rubewa ka yanke ka Yar ya Zan Bata Yar Uwata Kai din Affan Rumaila wani na kirki ne Naga sanda aka yanke sadakin Iya dubu daya a zamanin baya cewa kayi ko Dari biyar Albarka,da kyar ka biya, Iya ta karbe zancen Tace turmin daka na siya kacal da kudin,suna ta tone Tone Umma sai Dariya suke Bata sun cika gidan da Hayaniya kamar ana fada.

Washe gari Fu'ad Motocin Securities sun Kai goma yace Iya ta shirya yau zata Sha Jiniya sai an zage birnin Tarayya da Ita,Iya ta shirya harda sa lace din Dana Bata a kayan Lefe na ta Dinka,Gogoro ta sha,Tace Haleesa ta shirya ta rakata,Haleesa ma aka Sha gayu,su Momy suna ta sa Ido suga Wai waye Haka zai fita da wannan zabga zabgan motoci ga securities,tunaninsu Fu'ad ne sabo da Watarana idan zaiyi fitar girma Yana hakan, Iya kuwa cewa tayi Wai Ni a gidan Nan baku da sandar girma ta kudi wacce masu kudi suke rikewa,nace Babu Iya ,aikin banza Baku Iya gayun kudi ba Ina ma da ita da kunga Yanda akeyi,su Momy Al'ajabi da takaici ya kamasu Ashe Wai Babar Rumaila itace zata Unguwa a wannan Motocin na Alfarma,Mama Tace Allah ya yarda lallai tsafin Fulani ya Kama Fu'ad,ko Uwarshi Bai sa Ana mata tsaro Haka ba sai suruka,wannan tsohuwar,Su Momy harda fitowa suga kwaf,Iya zata wuce ta gefen su Tace da Allah Zan tsaya a Gidan Gomnati Ina da Dan Uzuri da Babar Shugaban kasa, Fu'ad da kyar ya Danne Dariyarsa Iya da yarinya ce da anyi Yar karya yace a ransa, Momy ta Bude Baki,Iya Tace rufe bakin Kar kuda ya fada da wata fuskarki kamar Daben Siminti, Security ya budewa Iya rantsatsiyar motar Fu'ad ta Shiga,jikarta Haleesa Yar Rakiya ta Shiga itama,Mama ta tafa Hannu Tace an tsafe Fu'ad,Umma da Abbi shike Nan,Wai ko masu kudi ne ba a sani ba? To me zai Kai wannan tsohuwar gidan Gomnati Wai tana da Uzuri da Babar Shugaban kasa,Nene wacce zata wuce Tace ku dai kunyi asara da Halinku na Munafunci ko kunya bakwa ji.

Iya dai an hakimce a baya ac ta ko ina,Rawar sanyi Iya ta fara sabo da sanyin Ac, Tace Driver kashe sanyin nan abinci me kyau Bai Gama ratsa ni ba Wannan sai ta zuba min zazzabi akwai ragowar yunwa a jikina,yanda Fu'ad yace Haka aka zage Abj da Iya,Ba inda Bata kalla ba a mota,duk inda Suka wuce sai an kalle su wasu ma zatonsu wani babban soja ne,wasu Kuma Shugaban kasa etc,Driver dake tuka Iya sai da suka tsaya a wani Eatery yayiwa su Iya take away na kayan makulashe Iri iri duk Umarnin Fu'ad ne,Iya ta Sha kallo,Iya Tace Driver ku bi dani ta Majalisar Tarayya Naga majalasa gidan kudi,aka bi da iya ta wajen,Tace gidan Shugaban kasa Villa aka je Nan ma aka wuce,Tace babban masallaci sentri yake ko me? Oh ko Centeral mosque driver ya karasa mata Tace yawwa,Kaini Wajen birnin can Kauye Kauye Nyanya,aka je,Tace babbar kasuwa,aka kaita wuse market, Harda sawa a siyo Mata Ugu leaf zata Yi Miya Wai da shi idan ta koma gida,Iya duk abinda ta nuna sai da aka siya mata,Haleesa Tasha kallo itama da siyayyarta,mamaki ya Kama su Momy ganin su Iya da Kaya Niki Niki masu Aiki sun shigar musu da shi,Momy Tace abin Nan fa nayi ne,harkar Nan da gaske akeyinta,Yusra Tace kaga yarinya Karama ta mallake Fu'ad gaba Daya wallahi Nan da sati Daya idan Bai so ni ba gida Zan koma na fadawa mamata ko zata samo min mafita tunda Harkar ta asiri ce ai muma Muna da malaman.
Iya farin cikin duniya ya isheta ita an Gama cika Mata burinta,Abbi yace ya biya musu Makka gaba dayansu da Suka zo gidan,Iya Tace sharudan Jin dadi sun Gama cikar min na Zama Hajiya,Abbi yasha Addua,Su Affa kwanan su Hudu Suka ce zasu tafi da Rukayya da Haleesa,Driver aka tasa ya kwashe su, Iya Kawai ita ce Fu'ad ya hanata tafiya Amma su duk an maida su gida,Iya kuwa ta koma sashen Umma,a kwana na biyar Umma tasa a Kara gyara Mana gidan mu Tace na shirya Fu'ad yau ya tafi Dani gida.

Bai zaton za a bashi Ni yanzu ba gashi farin cikinsa na Gama period,Iya miyar Agushi tayi da ganyen Ugu dinta tayi Sakwara,Nasan Fu'ad Yana so Bayan nayi wanka na shirya cikin tsaleliyar atamfa ta,kayana da aka wanke a goge na shirya tsaf, Sakwarar a flask na zuba komai,Yana zuwa gidan Umma Tace dama kai Rumaila take jira ku tafi gida, Fu'ad Murna ji yake kamar ya suma,Umma ta bashi mamaki Bai taba zato ba,Umma tana Kallonsa Yana fadada murmushinta Kai Kawai ta girgiza,Shi ya dauki akwatin kayana Ina rike da basket na abinci Muka fito zamu tafi,Kicib Muka hadu da Yusra, fuska na Bata,Tana so ta min rashin Mutunci Amma tana tsoron Fu'ad sai Tsaki ta ja Nima na kalle ta Up and Down nace looser na wuce,Kwafa ta ja Tace Zaki ci ubanki Ina Nan gidan,Gaba ya zaga ya Bude min na Shiga ya Rufe,kayan Kuma ya sa a bayan mota Muka wuce,sai da ya tsaya ya Mana take away na abubuwan ci da Sha iri iri,Da me Gadi muka gaisa Yana min Sannu da zuwa, Fu'ad ta window ya Mika Masa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login