Showing 18001 words to 21000 words out of 115153 words
Dade da farawa ba Hasali ma zafi suke min wasu kuri-kuri da su,shi kuwa yasan me ya taba ya fuske yace Dan Ubanki Ni sa'anki ne? Abokaina Zaki zaga Haka? Are you out of your mind? Baki da tarbiyya dama,Tsoronsa nake ji matuka ga kwar jini yake min,Hakuri na fara bashi Ina lumshe Ido sabo da kamshinsa me dadi da nake Shaka nace dan Allah kayi Hakuri wallahi bazan sake ba ai shine suka min Dariya Ni Kuma na tsani dariya.....kafin na Kai Aya ya yarfa min Mari,Wayar charger ya fisgo ya fara tsula min na Fadi na kwanta a kasa zan fashe da kuka yasa kafarsa me shegen laushi ya take min baki ya shiga zirara min wire gashi ba bakin kuka,ban taba sanin mugu ne Haka ba sai yau,ita kuwa Nene suna palo da su Rabi da abokan Fu'ad Nene tana cewa Dan Momy ya samu mutuniyarsa Rumaila suna ciki suna ta hira,Ni kuwa Yana ta sauke min ruwan bulailai nishin wahala Kawai nakeyi sai da ya tabbata na Sha wahala ya kyaleni,Cikin kasalalliyar muryata na saki wani marayan kuka Wanda sautin kadan ma yake fita ba Wanda zai gane kuka ne,Nene data ji sautin sai ta saki shewa daga Palo tace Alhmdllh yau Allah ya nuna min wacce Fu'ad zai kalla taja ra'ayinsa har su Sha hira,wayyo Rumaila dama kin saki dariyarki da ya fiye Miki Mun Gama Gane ki.
Tana gama furta Haka sai ga Fu'ad ya fito da fara'a Yana wani nishadi,Nene ta kalle shi tace Ja'iri ku abokai sai a fara shirin biki fa mutuminku yayi kasuwa,mugaye su sun San Fu'ad Zane Rumaila yayi,toilet din Nene na shiga na wanke fuskata harda shafa powder yanda baza a gane ba na fito sum sum,gaba daya aka bini da kallo Nene Bata gane ba tace barka da fitowa bakuwar Alkhairi ayiriri ta saki Guda,Ajiyar zuciya na saki da wani haushin Nene Kawai kuka ya kwace min me karfi,kowa ya bini da kallon mamaki da Sauri na shige Bedroom dinmu,Nene tace Kai Fu'ad ko wani abu ka Mata? Kamar ba shi yayi komai ba yace haba Nene wai akan na karbo zobe na a hannunta na kwace nata shine fa take kuka wai sai na Bata abinta na kakanta ne ya Bata Ni Kuma ya birge Ni,Nene ta kyakyace da dariyar murna soyayya ta kullu tace kunfi kusa aka canja zance Ni kuwa wanka nayi tare da gasa jikina,abinka da wacce ta saba da wahala sai gani kamar ma hakan Bai faru ba, Allah yasa ba dukan fasa fata ya min ba.
Atamfa nasa Riga da skert cikin kwancen kayan Naila dake nafi Naila kiba da shape sai gashi Kayan sun kamani daf,Mayafin data bani na yafa Kalar atamfar black and Dark Blue na fito da dari biyar a hannu na,Su Rabi naga sai hararata sukeyi akan ance Fu'ad Yana so na sabo da basu San gaskiya ba.
Saude kuzo muje yawon da muka ce Mana,Rabi tace na fasa zuwa tana wani fushi,Saude ma tace Ni na fasa yamma tayi sosai biyar ta wuce, to Ni dai na tafi nayiwa Nene Sallama nayi waje,na taka kofar fita na tsinci muryar Fu'ad Yana cewa duk wacce taje gantali to yau 6pm za a rufe gida ba shiga ba fita mutum sai dai ya kwana a waje,a Raina nace kaji mugu na fice abina ba Wanda na kula sai masu gadi Wanda nace su bude min zan fita.
Cikin rashin sa'a Dana fita Ina ta shiga street street sai Kawai na bace nayi nisa da yawa na kasa gane hanyar gida,Ina ta yawon bulayi na gama tsurewa ga magriba ta wuce sai na fashe da kuka Ina ta tafiya da chinchin dina a hannu Wanda na siya,wani bawan Allah ne ya tambayeni da turanci what Happened?Ina shesheka nace Ni bana Jin turanci,baki ya tabe yayi tafiyarsa ya barni tun daga shi ba Wanda ya kulani,ga ba waya a hannu na,gashi har 8pm ta wuce har na gaji da bulayi na samu gefen titi jikin bishiya na zauna ko zan hadu da na Annabi ya taimakeni.
Ina zaune sai ga wani Igbo yazo inda nake Yana Jin hausa kadan kadan,yace Kai wannan yarinyar meke faru? Nace na Bata, bana gane ba ka Bata Kamar wannan kudi talk to me Ko Ina iya ganewa,Nan nace dama Ni bakuwa ce na fito yawo na manta gidan mu to shine nake Neman na Annabi ya agaza,Igbo Bai gane wata hausar ba yace Ke Yarinyar Ni Emmanuel bana Annabi bane na Jesus ne sabo da Haka bazan iya ba,waye Jesus na tambaya,yace Kai baka school ne to Yesu me Bayyana Nan gaba? Yace yes,Ohhhh na furta ai shima Annabi ne,Igbo yace karya kake yaro so kake na taimakeka shine kace is the same,I can't Help you at all coz Ni bana Annabinka ne ba,nace ai duk Annabawa ne Amma nawa shine Yafi daraja,tafiyarsa yayi ya barni Nan.
Gidan kuwa basu damu da rayuwar kowa ba Babu Wanda yasan ban dawo ba sai su Rabi ko Nene tayi baccinta,Hawaye Yana bin kumatuna na tsaya a gefen titi sabo da haushi chin chin dinma na jefar da shi,motoci sun zaci karuwar dare ce sai tsayawa sukeyi Babu Wanda nake kulawa har na gaji na Mike titi Ina tafiya a hankali 9:32pm wata mota baka kamar na San me motar Amma na share Ina tafiya aka Sha gabana glass ya sauke a hankali na ga Fu'ad ne Yana ta sheka Dariya,da gudu na karasa jikin motar da niyyar shiga naje zan shiga ya ja motarsa ya tafi,sai da yayi uban nisa sannan ya sake tsayawa tare da Danna min horn Nan gane ni yake jira a fili nace zalimu anyi niyya da gudu na kwashe naje zan sake Shiga ina karasawa jikin motarsa na sakeyi da Niyyar shiga ya sake fisgar motarsa yayi gaba sai da ya sake yin nisa ya tsaya,lokacin har na hakura nasan ba zai taba taimako na ba Amma rashin zuciya Haka na sake zuwa da gudu ta window Muka hada Ido Kawai na kalle shi na fashe da kuka
,Kofar gaba ya bude min na afka ciki da Sauri na rufe da karfi abinka da ba a saba ba,wani sanyi da kamshi ya ratsa ni,a Raina na furta mu dai Bamu da Rabo a duniya sai dai Allah yasa Mu cika da Imani mu samu a gobe kiyama,Ashe yaji Ni zancen zucin ya fito fili.
Tsintar muryarsa nayi yace can dinma kuka Yi wasa baza ku samu ba,shuru nayi sabo da kwarjininsa ban iya cewa komai ba har muka je gida,da gudu na fice na wuce part din Nene Allah yasa kowa ya kwanta,Saude suna jina na shigo suka Mike zaune ke kuwa Ina kika tsaya kwashe labari nayi na fada musu suka dinga sheka min Dariya.
Washe gari da Yamma yan matan gidan su Fadila suna bangaren Nene suna ta hira mu kuwa muna gefe a takure Bamu da ikon Yi musu magana,har mazan duk sun shigo har Fu'ad,kwarjininsa yasa na Mike tsam zan tafi sai kuwa Fadila cikin Izza da Gadara tace munafuka duk yanda akayi baki da gaskiya,wanka fa zanje nayi na furta,Naila Uwar Iyayi tace au ke Nan wanka Zaki Yi kenan? Juyowa nayi na kalleta na fada Mata bakar magana nace a'a wasa zanje nayi da ruwa na basar,Fadila tace iyyee kaji iya bakar magana wajen Yar Kauye,Khaleesat tace sai naci uwarki nace Iya ce tana Kauye ba dadi namanta zaiyi ba wahalar duniya tasa namanta yayi tauri,Baki suka sake budewa,Sakna zaram tasa Baki tace ke dauke plate din da kika ci aninci uban waye zai dauke Miki? ita Yar aikin kanwar uwarki ce? Da Sauri nace ai ko kama da Iya basu Yi ba bare ta zama kanwarta,mazan Nan Banda Fu'ad suka dinga dariyar iya magana ta nan take ba tare da Bata lokaci ba,Islam yace kin birgeni yarinya,Fadila zata sake magana Fu'ad ya daka Mata tsawa da Sauri suka Mike tare da barin waje Nima nayi tafiya ta abina.
Mun cika sati uku a gidan ranar itama yan gidan sai shirye shirye akeyi ga Baki maza da Mata yan gayu masu ji da kansu,Rabi tace naji ance yau Ball za ayi a gidan Nan Mata zasu Yi maza ma zasu Yi kawayensu ne ke zuwa da abokan mazan gidan,Baki na tabe tare da cewa duk kudi ne ya musu yawa suke wannan kirkire kirkire,mu Talaucin Ina zai barmu sai wasan buya Muka iya da tafa tafa tafiyar Nan da zamu tare Wanda har yanzu tafiyar Nan da zamu tare Mun kasa Gane gidan da zamu tafi,Saude ta gyara daurinta tace ai daga ji a kauyen ma wacce ta kirkiri wakokin Nan jahila ce ta gaske,da Yamma sun cika bangaren filin ball din da aka tsara a gidan har da grass carpet,su Rabi duk suna can kallo Ni kuwa ball Bata Dame Ni ba Hasali ma bana ganewa,Yan matan sai wani Yanga suke Ana kwarkwasa.
Wata dalleliyar mota ce ta gaske tayi parking a gidan lokacin na fito zanje na siyo Alawa a waje ai da kallo na bi motar Nan,Bude motar a kayi wata budurwa kyakyawa Chocolate color ta fito tana zuba kamshi,Yar gayu ce ta karshe, sanye take cikin kayan ball dinta ko kunya Babu da gajeren wando cinyoyinta a waje,hannunta dauke da ruwan roba tana Sha da gani kaga babbar yarinya,Khaleesat ce ta fito itama cikin Jersey dinta irin ta bakuwar tana murna tace Lubna kinzo barka da zuwa suka wani rungume juna,Wacce aka Kira da Lubna tace Ina masoyina Fu'ad? Hmm kin San Bai son wannan shirmen baya son hayaniya yanzu ma naga ya shirya zai fita Amma friends dinsa suna Kofar gida tare da shi,Lubna tace Oh na ganshi ma..
kin San fa sabo da shi nazo,sai lokacin Khaleesat ta ganni na kafe su da Ido Ina kallon haduwa,hararata tayi tace daina kallo na,Lubna sai lokacin ta kalleni a wulakance tace sabuwar Yar Aiki kuka Yi ne? Khaleesat tace wai kawar dangi ce,Hmm Kaleesa na furta,Lubna cikin Iyayinta tace kinji tana lalata Miki suna wai Kaleesa,Khaleesat ta kalle ni ranta a bace tace Khaleesat nake karki sake Bata min sanu,Habata na rike nace to shayi nake Sha kullum?idan Haka kike so to ki fara dafa min shayi kullum na tsawon shekara Guda sannan bakina da makogaro na su washe na fara kalkala,Amma bana Shan shayi kice sai nayi Maganar larabawa,Lubna tace Iyye wonder shall never End, Tsaki suka ja tare da tafiya suka nufi inda filin yake Ni kuwa na fice abina daga gidan Baki daya.
Ina fita na hango Fu'ad da abokansa a jikin motar Khaleed suna ta tafawa suna hira da Dariya Su Uku,dauke kaina nayi na Shiga wani karamin shago na siyo madarar gari Yar Hamsim da alawoyi kala uku,a hanyar na bude ledar madarar Ina zazzagawa a tafin hannun na Ina lashewa dadi ya kwashe Ni ban San ma na wuce ta Gaban su Fu'ad ba,Hankali na Yana kan Madara sai ji nayi gaf na bige goshina da Gate,Khaleed yace sannu yarinya, Fu'ad ya Harare shi bana son irin zubar Mana da aji da kuke Yi,Dariya Khaleed yayi ya furta mene abin zubar da aji wannan yarinya me kyau Haka first class,Ni ai zan fara soyayya da ita ta tafi da Imani na, Fu'ad ya hade girar sama data kasa Yana masifa za a zubar Masa da mutunci abokinsa zai so wata kazamar Yar kauye Tsaki Yaja ya shiga gida tare da barin Khaleed,Baki Khaleed ya tabe yasan halin abokinsa dama tsokanarsa yayi,motarsa Yaja ya Kara gaba tare da abokinsa Saif.
Umma na samu akan ta bani Aron waya na Kira Iyata Babu kudi a wayata,Number na Mika Mata a jikin takarda a rubuce da kyar ta iya gane me aka rubuta ta saka a wayarta me tsada bugu daya ta Shiga Iya ta dauka da karfi abinka da Yan Kauye ba a magana a hankali naji tace Alo..Alo Ina ji Iya ce Ina ji Alo duk ta cika Wayar,Umma ta bani na karba Nima da karfin gaske Wanda sai da Umma ta toshe kunnuwanta da yatsunta nace shalo....Shalo....dai dai lokacin Fu'ad ya shigo yana wata Gadara kamashinsa me dadi na Shaka sai na kasa magana,Iya tace Alo ke ya naji kamar Rumaila kiyi magana Mana,Lokacin na dawo hayyaci na nace da karfi Shalo Iya Dan Gidan ne ya shigo Iya wallahi Baki ji ba kamshinsa ne na tsaya shakewa shi yasa kika ji shuru,Iya tace Oh Rumaila da shiririta yanzu tunda kuka je Baki sake kirana ba sai yau? Kiyi Hakuri Iya dadin gidan ne yake dauke Mana hankali,Ke Iya Albishirinki? Goro Iya ta furta nace Kullum fa muna Nan akan kaza Muke karyawa Allah Baki gani ba manyan kaji a Nan na tabbata a kasuwa sai an siyar da irinsu dubu uku uku,Iya tace ya Ilahi wannan wanne irin kudi ne da su? Nace Iya Kuma basu San Koko ba da tuwo ba a ci idan kika ce a Baki Koko ma Iya marinki za ayi a gidan,Dariya ta kwacewa Umma,Lokacin na juya na kalli Umma na hango Fu'ad ya kwanta a cinyarta Yana ta latsa waya,Nan take nace Iya Kuma kinga Babban Dan Gidan can akan cinyar Babarsa ke kuwa Iya ko hannunki na rike sai ki dukeni kice na rainaki su kuwa gashi can kullum sai ya more cinyar Babarsa, Fu'ad ya kama Dariya Yana latsa waya,Suna ji Iya tace yo su Yan Birni Ina ruwansu Haka suke ai,Nace Iya kin gani fa Dan Allah Iya jira yake Kawai ta Kara shayar da shi yanzu da zata bashi nono Yasin zuka zaiyi,Umma tace Rumaila gidanku wannan ce gaisuwar? Zan kwace wayata,a gidan uban wa za a bawa wannan Saurayin Nono?
Iya Ina Affa na? Kina Jin labarinsa, Yana can ance ya fara zama Dan daudu zani yake daurawa,ban yarda da zancen Iya ba tunanina Kawai wasa takeyi Kawai na share zancen nace Iya Ina Angon naki fa ice ko dai Yana kawo Miki shayi da Indomie kullum? Iya tace Bari ke dai Rumaila shegen Kansa kwalele kamar Fanteka Ashe shima duk a waje yake karya da na Shiga sau daya ya taba kawo min washe garin Dana tare a gidansa,Iya mu kuwa an Dinka Mana Kaya masu kyau an Bamu kwancen wasu abin Alheri Iri Iri da Dan Megidan yayi Mana da Umma gasu Iya Ku sake gaisawa na mikawa Umma waya,a mutunce suka gaisa da Iya ta dinga Yi musu godiya,Umma ta mikawa Fu'ad da kyar ya karba suka gaisa sannan na karbo Wayar,Iya Bata San Hands free Wayar take ba suna ji tace Kai wannan Dan me gidan tatacce ne kinji yanda yake Gadara wannan ku kiyaye shi,Kunya ta kamani nace Iya yafi kowa kirki Service ne ya canja Masa murya,Nan Muka Yi sallama na bawa Umma Wayarta Ina ta godiya.
Tun daga ranar Nan Bamu sake zuwa lesson ba sai da Umma da kanta tazo ta Kira mu tana ta Mana fada,duk abinda ya kamata musulmi ya sani Yana koya Mana Amma wani abin ko saurara bama Yi sabo da mu Sallah ce bama so ace sai munyi gwara kar mu saurari wa'azi kar ma zuciyar mu tayi rauni Amma duk da Haka sai da muka Karu sosai.
Washe gari Nene ce tace inyi fura Abbi zaiyi Baki za a Kai musu,Haka na zage nayi furar daka su Rabi sun tayani sosai sai Yamma bakin dattijai suka zo part din Abbi Yan aiki suka Kai, Fu'ad Bai ko kalle ta ba dake shi furar ba ko yaushe yake so ba.
Yau gaba dayan mu Saude,Rabi da Ni Muna bangaren Umman Fu'ad sabo da kirkinta a can Muka ci ma abincin Rana dake ko wacce part dinta akwai masu aikinta,Umma Kuwa duk ranar girkinta ita take Shiga kitchen tayiwa Abbi da kanta haka Fu'ad ke shagwaba shima kullum sai tayi Masa nasa abinda yake son ci,Momy da Mama Suma Indai Fu'ad yace a Masa girki da kansu suke Masa shi yasa yake abinda yaga dama, Umma tana sama mu Muna kasa, Fu'ad ne ya Mata waya kan ta zo ta bashi abinci Muna hira Bamu sani ba sai Umma Muka gani ta sakko da gayunta dama gata fara tas,Tana shiga kitchen Fu'ad ya shigo ya Sha wanka cikin 3qtr da t-shirt farare tas ya hadu.
Kallo Muka bishi da shi Amma ko tashar data kawo mu Bai kalla ba,Muka ce Sannu da zuwa ko amsawa baiyi ba Yana ta latsa waya ya wuce dining kusa da inda muke zaune, Umma tana serving dinsa tana cewa da Allah zai sa Dan Momy ka Auri Lubna ai da na huta,Yarinyar Nan da iyayenta suna mugun sonka gata da hankali,da kana da aure ai da na huta wlh da girkin ka ko tausayi na baka Yi sabo da Allah shekaru suna ta tafiya kaki aure Next year fa zaka cika shekara talatin cif, babu irin macen da ba ace ka Nema ba kaki,Banda matan da suke kawo kansu suna layin sonka,ga kudi,ga lafiya,gaka Handsome Amma ace ka kasa samo min suruka Dan Allah ka yiwa kanka fada,Nawa ne ma basu da ko aikin Yi Amma suna kwadago a haka suke rike iyalai.
Fu'ad Yana ta yiwa Umma inkiya da hannu Wai tayi shuru su Rabi suna Jinsa,Umma tace gaskiya Ni Lubna ta kwanta min kaje ku daidai a hankali zaka fada sonta,Ransa ne ya baci an Masa fada a Gaban mu ya fasa cin abincin.
Umma na kalla Kamar da Ni ake zancen nace Umma wannan Lubnan kawar su Khaleesat ce me hankali? Umma tace ae Mana,nace Umma wallahi Bata da wani hankali Bata Yi Kalar kamilar mace ba,matar data taho daga wata Uwa Duniya da gajeren wando ba dankwali Wai ita wayayya,Umma tace to Ku Fulani wa ya kaiku