Showing 60001 words to 63000 words out of 115153 words

Chapter 21 - DANGIN RABI COMPLETE

23 Aug 2025

1564

suna kallo,duk takaici ya kamasu sunga yanda aka kashe min dukiya,Rabi ta fito Tace a dai dinga tunawa da tsohuwa a Kauye,Nayi shuru na kyaleta sabo da Fu'ad ya hanani magana.
Fu'ad ne yace to Ku wuce gida ban son tashin hankali karku jawo naci mutuncinku a banza ku tafi tun Muna mu biyu,Binsu muka yi a baya Ni da shi Zan Rufe kofa Safna ta dungureni sukayi waje,Nace sai na rama Fu'ad ya rike Ni Ina ta wutsil wutsil sai na kwace na Rama Amma Fu'ad ya rike Ni tam,Sai da ya tabbatar sun tafi sannan ya sake Ni,fushi nayi gaba daya na koma Dakina na kwanta,Zuwa yayi ya iskeni nayi kwanciyata Kuma naki kulashi.

Palon Hajiya su Iya Suka Shiga,sun Dade a zaune Iya tana cewa me kudi ya huta kalli gida Dan Allah,Hajiya ce ta fito ta Sha wanka,Hajiya Mero ta gaishe ta Amma Iya tace Hajiya Ina bakuwarki nazo gidanki Ni bazan gaishe ki ba a ka'ida kece Zaki gaishe Ni,Iya Tace Iyye....Ke Mero wace wannan? Hajiya Mero cike da kunya tace sabuwar me Aiki ce, Iya Tace Ki gyara lafazinki Mero ba Yar Aiki ba dai me neman na Halali,Yar Aiki ai Kamar me Bauta kenan,Hajiya tace Kai Mero bazan Iya da wannan ba a kawo wata wannan baza a fada Mata taji ba...kafin ta rufe Baki Iya tace yarki ce Ni ko Haifa ta kika Yi da Zaki fada min naji? Da girma na da yarana kice Zaki juya ni,Yarana kin San Nawa ne?,ke kuwa kwata kwata Baki fi shekara 40 ba,Mero ta dinga dungurar Iya Wai tayi shuru,Iya Tace ke Kyaleni ba shurun da zanyi gaskiya ce dole na fada,Mazajen Dana aura ma Basu juyani ba bare wata ke matar Sanata wacce Nima da Zan dage Nan da wata daya sai dai Kiji na Aure Sanatan naki, Zuciyata Bata mutu ba Hajiya.

Fu'ad ganin Ina fushi sai yace zo muje muyi game,Ina son Tv game da sauri na Mike Ina murna muka koma Bedroom dinsa a kasa Muka zauna da Handle Muna fara game Kawai Sai dai Fu'ad yaga Handle din ya kwala Masa duka a goshinsa,Kuma da hannunsa zai ga ya goce ya koma Goshinsa ya kwalawa Kansa da Kansa a Goshi,yace Salahu ya tashi a bacci karki sake zuwa kusa Dani cewar Fu'ad, Ba shiri ya jefar da Handle,Ina ta dariya Yana Jin haushi na Muka bar game dole,Goshinsa na mulmula Masa Ina bashi Hakuri.












AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈






NA KUDI NE

DAN GIRMAN ALLAH FANS KU RIKE AMANA KARKU FITAR DA NOVEL DIN NAN ZUWA WASU GROUPS KYAUTA,WACCE TA FITAR BAZA MU YAFE BA,A RIKE AMANA DAN ALLAH.








DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM.












46-50












Official










By
AsmaBaffa











Page naku ne

Frozen Feast kn
Fatin Hana
Ummun Arfat
Nafee
Yar Baiwa
Maryam Muhammad
Zainab Sabo














Abbi ne ya kalle kowa yace ku saurara kuji abin Nan naku ya Ishe Ni yayi yawa musamman Bangaren Mama da Momy duk kunbi kun raba min kan Iyali,Baki idan Suka zo gidan Nan sai an raba kansu to wallahi na gaji Nan gaba Zan yanke mummunan hukunci a kanku,Mama Tace dama ai Haka zaka ce tunda mu ba a kaunar mu Amma Rumaila itace gaba daya ke hada fadan ,ita duk abinda sukeyi ita da Fu'ad ba a gani sai mu sabo da Bamu da yanci a wajenka,Fadila Tace ba abinda sukeyi sai iskanci a gidan Nan,ai fadan da na muku daban yanzu Kuma zancen Rumaila kukeyi ita da Fu'ad cewar Abbi,Ai sune suke abin fada Momy ta furta,Nan take Abbi yace to Na hada Rumaila da Fu'ad aure Nan da wata daya ko biyu za ayi biki kowa ya huta, Fu'ad yace Abbi wata dayan dai mu mun shirya,Islam yace Ni Kuma fa Abbi na samu wata me zafi,Abbi yace Zamu je ayi bincike sai a Kai kudi Inshaallah,nasiha Abbi yayiwa kowa Amma su Momy Basu dauka ba,Rabi Tace Ni ba ayi zance na ba ya kamata Nima a kwato min hakki na anyi magana Kawai Akan Yar gwal Rumaila,Sanda kika koma layin Su Momy har suka kaiki gidan Fadila na sani? Abbi ya tambaya,kin zauna Hassada gashi kinga abarki a kanki,ai itama Rumaila barikinta Kawai takeyi a gidan Nan cewar Fadila,Nima Rumaila nace Kamar yanda mijinki yayi Raping Rabi ba,Nayi niyyar rufa Miki asiri Amma na fasa,tunda Ni kadai kuka sawa Ido a gidan nan.

Abbi Bari na baka labari yanda akayi Raping Rabi,Umma ce ta kyafta min Ido Wai kar na fada,nace Abbi kaga Wai kar na fada Inji Umma,Abbi yayi murmushi yace Fadi Rumaila,Zan sake magana Umma ta harareni,Abbi kaga sai Harara ta takeyi Wai bazan fada ba,Abbi yace Fadi Mana ke Umman Naila ba ruwanki,nace tunda aka Kai Fadila gidan miji Abbi dama ko shimfida basa hadawa,ba irin nasihar da mijinta Bai Mata ba Taki ji,shi Kuma da ba Wani tsoron Allah ne da shi ba sai yayiwa Rabi Fyade,Fadila tana ta rufa Masa asiri shi yasa Tace Rabi karya take yiwa mijinta,Rabi tana Jin Haka Tace Kuma har kallon Yan bariki yake min Yana kashe Ido daya,na karbe zance da cewa ita tana can tana hauma haumarta Bata gane Halayen mijinta ba sai dai tayi wanka ta fice yawo da kawayenta,shi kuma yaga Rabi Yar Dagwai Dagwai shi yasa ya samu ya Girgije da Rabi,Abbi yace to a Ina ke kika ji labari? Nace a gabana Fadila tayi waya ta buya tunaninta ba kowa Ashe Ina wajen,Kuma ta rufawa mijinta asiri Wai Bai aikata ba, Abbi yace to a Nan ba abinda zance ke Fadila idan ma kin boye gaskiya Allah Yana kallonku ke da mijinki Kuma Nan gaba sai kinyi Dana sani,Rabi kuwa Halinki ya kaiki fadawa wannan yanayi Ni dai naja kunen ku nayi muku Nasiha Wanda duk yaki ji ba ruwana,Wannan shine na karshe da Zan muku fada ,Indai akan Rumaila ne kuke wannan tashin hankali to zanyi Mata aure ta bar Nan gidan,Mama Baki ta tabe Tace yafi dai ayi can baza asa Allah ya jarabce mu ba da masifu Ana aikin Yan wuta a gidan Nan,aje a hada jini da Aljani cewar Momy,Allah ya ganar da ku Umma ta furta.

An saka ranar bikinmu Amma Fu'ad baya fara'a bare murna ganin Haka Nima sai na daidai ta sahu na bana nuna Ina son Auren,Bayan Kwana biyu Abbi har kauyen mu yaje ya sanar musu Affa yace shi fa ba ruwansa,Dole duk wani Abu na Al'ada Abbi ne wakili na Yan Uwansa Kuma suke wakiltar Fu'ad, Umma tuni take ta gyarani,Ina dawowa daga makaranta sai gidan gyaran jiki,Haka Umma da Nene Suka shirya har kauyenmu wajen Iya Suka Nema aka ce ai tayi yaji tana gidanta.
Gidan aka rakasu da fara'a ta tarbesu tare da shimfida musu tabarma Bayan sun gaisa,Iya taga kudi sai kallonsu take faman Yi tana zare Ido a ranta tana cewa Ina ma nice wannan Hajiyar,Umma Tace nasan Baki sanmu ba mune wacce Rumaila yarki ke wajenmu,Umma ta hangame Baki Tace Yan Uwan su Rabi ko? Nene Tace ae Haka ne,Iya taga kudi ta manta ma da laifin Rumaila sai Tace Allah sarki Ina kuka bar Rumaila ta? Umma Tace ai Rumaila tana Nan lafiya ta samu Miji ma,Me kudi ta samu? Iya tayi saurin furtawa? Umma Tace Dana ne ai,Tace Ashe Adduar tawa Allah Rumaila ya bawa,Allah me girma duk laifin da Rumaila tayi Masa sai ya Bata kudin Ni Kuma da nake ta Adduar sai ban samu ba,Umma Tace ai ke da Rumaila duk daya ne,karki Yi sabo dai ikon Allah ne,Iya Tace duk dadin Inuwar gemu ai Bata Kai ya makogwaro ba,Umma Tace dama zuwa Mukayi mu fada Miki bikin Rumaila Kuma mu baki labarin cikinta ki yafe Mata,dake masu kudi ne sai Iya Tace Ina jinku,Umma ta Bata labarin komai,Amma sai Iya Tace ban yarda ba Amma sabo da kudin da kuke dashi kun birgeni sabo da kudin na yafe Mata ayi aure lfy Ni dai bada Ni ba,kudin aure da aka Kai Kuma a kawo min Ni uwar 'ya nice Nasha wahala na haife ta,sabo da tunda na samu cikin Rumaila nake cikin bala'i da cuta,tunda na haife ta sai da ta kwana tana kuka ban runtsa ba ranar da tazo duniya,ga shegen tsotson Nono kwana takeyi tsotson duk abincin da na ci ita ke shanye shi a nono,na rame na kekashe,ta fara hakori tana kashin hakori idan ta feso Kashi tun daga bangon daki sai ya Dire da daya bangon,Ni kenan a wanki da ruwa na zama agwagwar dole,Hakori ya fito idan tana Shan nono ta cijeni yafi a Irga,sannan yanzu zata Yi aure Kuma ace kudin aurenta ma ban gani ba sai dai labari,a kawo min kudi kuje kuyi bikinku lfy.

Umma ta girgiza Kai ta Bude Jakarta Tace gashi dubu dari ne kudin auren dama kawo muku Mukayi sai a bawa babanta shima,Umma Tace Sanda Nasha wahalarta ko kwayar gero Bai Aiko min da shi ba,duk wani Abu daya Kama Banda sadaki su Umma sun bawa Iyaye na,Bayan su Umma sun tafi Iya murna ta dingayi tana Jin dadi ta boye kudinta,Tana zaune tana gyara kayan Miya sai ga Me shayi mijinta ya shigo gidan Direct da Sallama,Iya tana ganinsa Tace me ya kawo ka gidan matar wani kana kallon tsaraicina? To ai ban sakeki ba har yanzu kina matata ki tashi mu koma gida biko nazo Iya Tace kazo a banza ai Ni yanzu nafi karfinka sai dai matar Chairman,da kasan irin kudin da nake da su da baka zo wajena Biko ba,nafi karfinka,Me shayi ya zaro dubu biyar yace ga wannan? Iya ta tabe Baki Amma ta faki ido ta fisge kudin me shayi Tace naci banza Kuma bazan koma gidanka ba,Me shayi yace tunda Baki da mutunci bani kudi na,bana son Wasa bani kudi na ko wallahi yanzu na Mori kudi na,Iya dama an kwana biyu ba a hadu ba,tayi wayo Tace bazan bayarba idan ka Isa ka Mori kudin naka mu gani,Me shayi yayi sama da Iya tare da shigewa dakinta gaba daya,Iya Bata so aji a makwafta sai ta koma rada rada, Wanda ko Me shayi da kyar yake Jin me take cewa....ka Bari....ba a wannan Wasan Dani...idan an girma asan an girma.....Me shayi shima da rada yace Dama Abinda ya kawo Ni kenan gwara kiyi shuru,da Rada ta sake Furta shike Nan tunda taurin Kai gareka zanyi maganinka wani satin me zuwa Allah ya kaimu nasan zaka zo ne.

Zaune nake a palon Nene Muna Hira kaina ba dankwali sai ga Baba Jummai tayi Sallama tare da shigewa kitchen, Fu'ad ne ya shugo tunda aka sa bikin mu baya min fara'a,Baba Jummai ta kitchen ta rabe a jikin Kofa tare da leko da kanta tana kallon mu,Nene ta Mike ta Shiga bedroom,Daga Ni sai Fu'ad,Littafi na dakko da biro na zauna dirshan Ina Rubutu Wai Ni a dole karatu nakeyi Ina cewa,Malam Idrisa.....da Budurwarsa....Idrisa bashi da Aiki Sai fushi.......ita kuwa Budurwar Malam Idrisa Tace sai dai Idrisa ya kashe Kansa Amma sai anyi aure,sai dai Idrisa yayi ta fafatawa da Aljanin matarsa, Fu'ad yanaji yayi Dariya yace to ya sunan ita matar Idrisan? Mayafin Abayata peach color ya dakko a saman kujera da Kansa ya fara yafa min Yana gyara min lullubin,Baba Jummai a ranta Tace Kwarata Ina kallonku,Kinyi Sallah? Fu'ad ya tambayeni,nace bana Yi period nakeyi,Baba Jummai ta Bude Baki tana boye Tace kinji ba kunya duniya tazo karshe,Kwana Nawa kikeyi? Nace kwana biyar,yace Kai na Shiga Uku Ashe auren Mata biyu ya kamani,Fuska na Bata nace wallahi za ayi bala'i,ka siyi masifa da kudinka,Haba Baba Jummai ta rike Tace kaga lusari Wai ta hanashi yin Mata biyu Ina ma Ni zai aura a matarsa ta biyu ai da kinci Ubanki a hannu na,Da kallo nake bin Ya Fu'ad yayi mugun kyau a wannan yardin Milk color,jikinsa ya birgeni nace goyani kafin Nene ta fito,Tsugunawa yayi Zan hau bayansa Baba Jummai ta yo waje da sauri Wai Dan mu gani ta kure mu,Sai taga bamuji komai ba sai ma Fu'ad da yace Baba Jummai taimaka Mana da Aron zanin atamfarki Zan goyata,Takaici ya zowa Baba Jummai har wuya Amma ba yanda ta Iya taje ta kawo zaninta me Dirty data cire, Fu'ad ya toshe Hanci yace sabo fa nace wankakke Haka Zan Goya Me dakina da wannan local zanin Shiga ki dakko min na Nene.

Baba Jummai Tace Wai me dakinsa a wankakkun kayan Nene ta kawo zani yasha guga Yana kamshi, Har zata tafi yace ungo wayata Baba Jummai kiyi Mana Hotuna masu kyau,wallahi idan basuyi kyau ba sai na dakatar dake daga aiki,nace Jummai Kawai Babu wata Baba Jummai tunda Bata ja mutuncinta na,Baba Jummai Tace ba kyau...ba kyau,Haram...Haram,ko kallonta bamuyi ba sabo da ita dama nace a goyani Dan taji haushi,Har Zan hau bayansa sai ga Nene ta fito,da Sauri na zauna tare da Fuskewa, Fu'ad yayi waje abinsa Yana takama,Baba Jummai tana ta murna a ranta tace shegu Allah Kara.

Zanin Nene na dauka na mayar da sauri,Nene Tace naga Kamar zanin farar atamfa ta,nace ae Zikirin Wazifa zanyi kin San jiya na koma darikar Tijjaniya,A Ina kika ga Yan kungiyar a garin Nan Rumaila? Baba Jummai ce ta rakani sabo da tayi sabon bazawari a cikinsu,Karya kike Min Baba Jummai ta hayayyako da masifarta tana cewa Ni Yar Izala ce to.

Fadila tunda mijinta yace zaizo ya tafi da ita shuru kake ji ba shi ba labarinsa duk tabi ta damu ta rame,2pm na dawo daga makaranta na hango ta tayi tagumi a jikin mota tana tunani,Wajenta na karasa nace Anty Fadila tunanin Mijin ne Haka? Tace uhm ke dai Bari wallahi kullum Haka yake min Wasa da hankali yace zaizo anjima yace jibi yace gobe abin ya ishe Ni,nace Kuma yanzu Haka kina so ya Dan watsake da ke? Dama ai ance idan aka Saba da maza ba a iya Hakuri shi yasa zawarawa Suka Zama fitinannu a duniya an Saba da watsakewa,Allah yasa ya dawo ya tafi dake,idan kika je ke Kuma shawara Zan Baki wallahi idan kika damki kunnuwansa har hakora ki kafa musu sai sunyi jajir dan ubansa sannan ki kyale su,Harara Fadila ta watsa min Tace wlh Zan mareki kema ai kin kusa auren Zaki ji,Kuma Yaya Fu'ad wlh bazai daga Miki kafa ba,kina ganin sa haka Zaki ji a jikinki,nace ba komai abin kaunata ne,Fadila tafiyarta tayi tare da galla min Harara,Tana tafiya sai ga Mijin nata yayi parking motarsa a gidan,Da hannu ya yafito Ni,nace a Haka kamar na kirki,Ina zuwa Wajensa Fu'ad ya shigo da motarsa Yana ganina da wani ya Bata Rai duk da yasan Mijin kanwarsa ne,Mijin Fadila yace je ki Kira min Fadila kice tazo mu tafi,Da Sauri na juya na tafi na hango Fu'ad Yana muzurai,Da gudu na Shiga Ina kwalawa Fadila Kira Anty Fadila kizo lasar kunne yazo Yana kiranki a parking space,ai Fadila ko Gama ji batayi ba ta fada bedroom ta kwaso kayanta Tace Idan Momy ta dawo Safna kice na tafi gida.

Ke kuwa Ko Dan Jan ajin Nan Babu daga zuwa baza ki Bari Iyaye suyi Masa fada ba sai ki bishi na Furta Ina kallon Fadila tana saka takalminta,Tace ba komai Yana da hankalinsa ba sai an Masa wata nasiha ba wanne hankali zaiyi Kuma tsohuwar munafuka Allah yasa naji labarin kince wa mutane yace Zan na lasar Masa kunnuwa sai naci Uwarki,Dariya nayi nace yau za ayi kwanan lashe lashe a lashe da kyau,duk kurar Nan daya dakko ta kamfanin Audugar su ki lashe ta.

Ina fitowa Muka hadu da Fu'ad Nace ango na Sannu da zuwa,Wannan Hijab din na School yayi Karami ko gwiwa Bai Kai ba duk Ana kallon jikinki ya furta,Dariya nayi na tari gabansa Yana tafiya nace kishi kakeyi? Baki ya tabe yace Allah ya kiyaye,Allah kishi kakeyi zaka ce wani ba Haka ba,Haka ne mana kishi na kakeyi ko? Tsaki Yaja Yana murmushi yace ki matsa min a hanya kin tare min gaba,Da baya nake tafiya Ina magana nace Nima kwanan Nan sai dai kaji Ana cewa Bari muje gidan Rumaila,wacce Rumailan? Ace Rumailan Fu'ad,gidan Rumaila,duk kudin Nan da ka kashe sai dai ace gidana,Umma Tace kayan Dubai za a zuba min,Allah sarki da a garinmu ne Affa kayan Yahuza kafinta za a sa yayi min gado irin na Yan makarantar kwana Boarding school,gashi Sallah babba ta kusa kayan lefen kasa a Dinka da yawa kaga da Sallah na huta Kai dinki ko? Fu'ad dai Yana ta Dariya Jin buri na,Nace ka saka min abin goge kaushi a ciki bani da kaushi Amma Zan dinga wanke dattin dake makalewa a kafa kana ganinta fes tunda Anty Fadila Tace har kunne ake lashewa kaga kafa ma baza a barta a baya ba,da gishiri Zan dinga wanke maka ita sabo da karka lashi Bacteria a cikinka ko Virus.

Dariya ta kama Fu'ad yace kinki girma har yanzu ke Kam,poul wire kake so na koma? kalli fa girman da nayi kace bana girma,Idan kazo Hada lefen ka saka min harda Vaseline sabo da Watarana idan wasu bakin sunzo sun Nema sai a Basu,Ni da zaka hada min da set na kayan me ciki yafi ai,Sabo da Ana yin aure ake samun ciki kafin shekara an Haihu duk da naga alama Kai salihi ne ba ruwanka rayuwarka kakeyi Mata Basu dameka ba shi yasa baka soyayya,Damko Ni yayi a gabansa ya janye Ni baya yaci gaba da tafiyarsa yana murmushi, Ina komawa abinci naci nayi wanka na shirya Zan tafi gidan

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login