Showing 69001 words to 72000 words out of 115153 words

Chapter 24 - DANGIN RABI COMPLETE

23 Aug 2025

1572

Sallah da salatin Annabi ko ma Dace a can,Amma a Nan Kam kudi yafi karfin mu,Kawai muci gaba da Sallah yafi Mana mutunci,babu asara ace talakan Nigeria ya mutu anyi Jahannama da shi,Bai ci a Nan ba a lahira yana wuta to gwara Kawai mubi Allah,Muna daki tare da Fu'ad Dariya yake ta Yi kasa kasa Jin Iya abinda take cewa,Nima Dariya nayi ta window na leko tare da furta Sannu da zuwa Iya,Iya tace wani kuturin Munafunci ne wannan lekowa ta window ki fito Mana,Kunyar Iya naji kar ta ganni da Namiji,Iya Tace ke Nifa ban Gane ba ko kwarto kika wo ne? Nace Iya Mijina ne fa shine da wannan motar,Iya ta kalle Ni ta window Tace karya kike,wallahi Iya da gaske na fada miki,shine nace ya kwana yaki yard.... Fu'ad ne ya rufe min Baki da hannu,Iya tace Kai fito Algungumi harda Shiryawa sai Dana tafi Unguwa duk yanda akayi baka zo da gaskiya ba fito na ganka, Fu'ad ma ta window ya leko yace Iya....da sauri Iya ta rufe idanuwanta Tace bature nake gani,ke Rumaila wannan ai sai Naga fuskata a jikinsa kin gani kuwa jikinsa kamar mudubi,Dariya Fu'ad ya dingayi ya Bude kofa muka fito, Iya tace Dan Nan Kaine Mijin Rumailan da gaske ko gizo idona ke min? Fu'ad yace ae Iya,Me kike so ayi Miki a duniya Iya? Mene burinki idan kin samu kudi? Iya Tace yaro Abinda yake bani haushi in Shiga birni naga masu kudi Ana binsu da jiniya da matakan tsaro motoci suna wiwiwiwi....an sa mutum a tsakiya Ana take Masa baya,Ni Buri na Kawai a daukar min Hayar matakan tsaro a sani a dalleliyar mota Ina tsakiya matakan tsaro gaba da baya Ana min jiniya wiwiwiwi....shine Buri na Kawai Ni bukatata kenan abinda nake ta so kenan na Tara kudi ayi min jiniya sau daya a duniya Ni na Gama cika Buri na,Dariya Fu'ad ya dinga Yi yace an Gama Iya za a Miki ta sati Guda ma Bata kwana daya ba,Iya ta dafe kirji Tace Allah Kai Dan Aljanna? Nace da gaske Iya,Iya Tace Kayi zamanka ka kwana Ni sai na bar muku ma gidan na koma gidan Dan Uwa na,Kai idan sati daya ma zaka Yi kayi abinka baka da matsala,Kuma Allah ya tsinewa Salahu ya saka muku,ya Hana masoya zaman aure, Fu'ad Yana ta Dariya Iya taji kudi ta zauce,Wajen Iya naje naja Hannunta na nuna Mata irin kayan abincin da Fu'ad ya Siya Mana,Iya Tace na batawa kaina lokaci Dana dinga aure aure Ina Shan azaba a gidan mazaje daban daban, Ni da aure munyi hannun Riga yayi Gabas nayi arewa,Iya tace karka ji kunya ta ai ka Zama da na,kayi abinda kake so, Fu'ad a ransa yace yawwa naga wajen Zama sai jibi Zan tafi,Hannu na Iya ta ja dakinta cikin rada Tace ice ko kin dama Masa kunu? Nace a'a Iya,Kaji banza ko baku iya kula da Miji ba abinci da nama ai sai mu talakawa mune bakinsa,abinci na sha'awa ake musu,Su Dan zogale,danwake,Dan tubani Haka,Nace to ai Bai fiye cin wannan da kika lissafa ba,Iya Tace wannan kwai banzan yaro sakarai to su wainar fulawa da Awara fa? Nace Yana ci,Iya Tace gobe da ita zai karya wannan zai Sha tattali da gata Rumaila,Zan fita Iya ta sake fisgo Hannu na Tace kin shafa turaren Nan kuwa? Nace a'a Iya, Zan hambareki wlh shashasha ta furta tana hararata,Iya Tace tafi ki bani waje,na juya Zan tafi Tace idan kikayi Wasa da Shagwaba sai kinci Ubanki wallahi,irin wannan mazajen kauna ake nuna musu sai da Shagwaba lamura suke tafiya dai dai,Kunya Iya take ta bani na fice da sauri,Magriba tana Yi Iya ta nuna min da hannu Wai na bashi buta yayi Alwala, Fu'ad yaga Sanda Iya take min Inkiya da hannu,Dariya ta kamashi ya Danne abarsa,Bayan yayi Sallar Isha ya dawo Iya Tace daki da zafi kuyi kwanciyarku a tsakar gida ba sauro a Nan, Fu'ad yayi shuru Iya da kanta ta soya Masa wainar fulawa ta shige dakinta, Fu'ad shima kunyar Iya tasa Muna Gama cin abinci ya shige bedroom Yana ce min kije wajen Iya ki kwanta kar taga Bamu da kunya.

Dakin Iya na koma tare da kwanciya a bayanta,Dundu Iya ta durma min sai da na saki Kara,Iya Tace Albasa batayi halin Ruwa ba,munafuka Ni Zaki rainawa hankali kun Gama shargallewarku bana Nan shine yanzu Zaki dawo ki kwanta min a baya Dan munafuka ce ke,yaro Dan kirki Yana dawainiya da mu Yaron kirki baza ki kula da shi ba mun samu wajen hutu Zaki barar Mana da dama,wallahi Indai ya sakeki sai dai ki koma agolanci Dan bazan fasa aure ba Matukar ya koreki,ko ya Miki kishiya kici ubanki kuma ko tausayinki bazan ji ba ,Sum sum na tashi Iya Tace Haka kije tafiya a gabansa Kamar Namiji wani gatsar ba kyan fasali? Idan Zaki dage ki dage aure bana Ragwaye bane,Indai nice yanzu Zan tafi gidan kawunki Haruna Zan tafi sai wurin 12pm gobe Zan dawo,Ina kallo Iya ta dauki kayanta a jaka karama tare da saka Hijab ta tafi,Tace rufe gidan sosai sabo da Yan Iskan barayin dare,Haka na kulle gidan,a Raina sai murna nake Yi Iya ta tafi ba kunya, Fu'ad ma tsakar gidan ya fito yace Iya ta tafi? Nace ae ta tafi gidan Kawu,Tun a wajen Fu'ad ya dauke Ni cak tare da shilla Ni sama Muna dariya,Nace mu Kara Addua kar Salahu yazo,yace to yau dai sai nayi na gaske hakki na Zan karba,tsoro naji Zan Masa wayo nace Salahu zai cinnawa Sarauniyarka Wuta, mu Bari iya Romance Yafiye Mana,idan anyi magani na warke sai kayi, Fu'ad yace nasan sai Nan da shekara Nawa Zaki warke ya bar jikinki? Ni bazan yarda ba sai na gwada.
Fuska na kwabe zanyi kuka ta wani fannin Kuma Ina murna Dan nasan dole Salahu zai Hana hakan.















AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈







NA KUDI NE

DAN ALLAH KARKU FITAR DA NOVEL DIN NAN








DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM















66-70














Official










By
AsmaBaffa













Page naku ne

Aeesha
Saadatu Tijjani
Beauty Boss
BestynBeelat











Iya tana tafiya nace dare baiyi ba 9pm kazo muje yawo zamu Fi Shan iska,Baki ya turo Yana Shagwaba Wai No mu gaskiya kwanciya zamu Yi baza muje ko Ina ba mu turawa ne rayuwar turawa za Muna yi,Dariya nayi nasan shima wayo zai min,harda cewa Ni matata baza tana yin Abun Kauye ba,nace Ni kuwa Mijina Ina so yasan Yan garinmu kowa yasan Aure nayi da gaske a daina min kallon banza,Okay naji zamu fita Amma sai dai na fara koya Miki mota a garin Nan Kawai,Farin ciki da murna nace to let's go,tashi yayi Yana tafiyar Nan tasa cike da Izza,Ina mamakin wannan Izzar tasa da baya Iya daina ta,Kawai Kallonsa nakeyi yanda yake Taku ko shugaban kasa Albarka, Bayan motarsa ya Bude Nan naga Kaya kana na a wanke a goge cikin wata Yar Akwati karama,nace dama kasan zaka Iya kwana? Yes nayi tunanin Zan tsaya a hotel cikin garin na kwana gobe na bi flight Amma sai gashi Iya Tace ta daure min Sarauniyar tawa,Dariya na dinga Yi nace cewa akeyi ta daure maka gin......Ido ya lumshe yace wannan batsa ce kunyar Maganar Nan nake ji idan Zaki fada Kawai ki fada da sunan da kika saka Mata,muna tsaye ya canja 3qtr da Riga Armless wasu farare yayi kyau matuka,Mota na shiga mazaunin Driver Yana gaba Yana nuna min yanda Zan tuka mota, yana nuna min Ina tukawa a hankali tunda nasan garin Hanyar inda mutane ke taruwa da dare na nufa,Affa na fara hangowa daure da zanin atamfa,Harda daura dankwali jikinsa Kuma jallabiya ce ta maza ya daura zanin a samanta,Yana suya doya Yana buga tsalle tare da komawa gefe Wai Mai ya tsallo Masa,a wurin nayi parking yaga nice na fito dama ya Gane Fu'ad,Da Fu'ad Muka karasa gabansa tare da rusunawa Muka gaishe shi Yana yarfe Hannu Kamar mace, yace Affa aikin kake Yi ne haka? Fu'ad ya tambaya,yace yo mene amfanin Zama tunda min buga ta hanyar sana'ar Yan mazan Taki yuwa sai muka koma daura zani Muna Yin ta mata,mu Mata sana'ar mu tafi tafiya,Dariya ya bawa Fu'ad yanda yake karairaya ga Maganar Mata sai idan yayi wani abin sai yaga Kamar Rumailansa, Fu'ad yace Affa ka daina wannan sana'ar ka koma Namiji Zan baka Aiki babba,Affa ya Tafa Hannu Yana cewa lalala kyale Ni a Nan rabani da aikin maza , Fu'ad yayi Dariya Yana kallon ikon Allah, nace Affa baza ka Bamu Girkin naka ba? Daya taci kyauta daya ya biya kudi, Fu'ad yasan Wai daya taci kyauta Wato Ni Yarsa, Daya Kuma ya biya kudi ba Kara ba Mutunci,Kai yaro karka ji haushi duniya ce ta canja ta koma daga kauri sai gwiwa,nace Allah bazai Biya kudi ba Affa Mijina ne fa,Mijin yarka surikinka fa Haba Haba Affa,Affa yace inye kaji Yar Gandal Uba Nasiha kike min ko ya kamata Zaki fada min? Nace to mu wallahi kifin kogi zamu ci Tarwadar can muke so,ka godewa Allah ma da Kamar wannan zai ci girkinka,a duniya kyankyami Girkin Dandaudu akeyi,Allah Affa ka daina shigar Nan duk ranar da Yan Hisba Suka kamaka mu dai baza muyi Bailing naka ba,Idan an kulle Ni Dan Allah ki fada musu su jefa mukullin a tsohuwar rijiya har abada kar a sake Ni,na fada Miki dai daya taci kyauta daya ya biya kudi, Fu'ad yace Affa Zan siye abincin naka duka,Affa yace yanzu kazo da magana,jarin dubu ashirin ne a Nan,Nan take Fu'ad ya bashi dubu talatin yace a rabawa mutanen wajen duka,Haka muka tafi Bamu dauki komai ba Naja mota a hankali Ina koya,tuki yayi Dadi ban sani ba naje na daki katangar Kawu Haruna da mota,Ai kuwa katanga kadan ta rushe,sai ga Kawu ya fito a Tamanin,Fitowa Mukayi Ina bashi Hakuri Ina cewa Kawu nice Rumaila,Kawu kamar zai yage bakinsa gida biyu ya fara masifa Rumailan banza Billahillazi sai kin biya da kyar na samu Ni da yaro na Talle muka Gina katangar Nan Dan Iyayi ke a dole kina auren me kudi kinzo kin rushe min katanga Ni dama can Allah Bai hada jini na da naki ba sabo da Sam Baki da Imani ba tausayi,tunda kika je birni ke kadai kike Jin dadin ki sai da mijinki yazo Dan Albarka ya Mana kyauta Amma Dan bakin Halinki kaf dangi ba Wanda kika gayyata,Sanda aka ce nayi ciki kasa rikeni kayi Kawu In Shiga duniya ba ruwanka ka koreni,ko abinci naje karba baka Bari a bani a gidanka karshe bare suke taimako na

Ba'a cin arziki ke kika je kika ci arzikin Rabi ta kaiki gashi kin samu dama aikin banza,Nace to Kai Kawu da kake tada jijiyar wuya a dalilin wa yazo ya gaisheka har ya baka kudin,akan wannan rubabbiyar katangar taka zaka ce wani waye waye kayi kudinta a biyaka,Yanzu idan naga dama gidan me gari zanje nabi takansa Kuma a biya kudin ginin ba Wanda ya Isa ya min ko kwarzane,Iya ce taji Hayaniya ta fito tare da matar Kawu Haruna,Tace Rumaila katanga kika Rusa Masa? Iya Wai Dan tsautsayi yasa na Rusa ta shine yake Zagina idan yayi Hakuri ma ai me motar zai biya kudin ginin harda riba,Iya Tace Haruna Kai yayana ne Amma Kayi Hakuri gaskiya baka da mutunci, Nifa ka takura min Ni da 'yata wulakanci a Gaban suriki na,Ke Rumaila ja mota ku tafi Ni na siyi fadan,Mota muka Shiga na sake tukawa muna tafiya,Kofar gidan me gari na taho inda munafukan tsofaffi suke Zama,Sanda akace nayi ciki sunfi kowa zagi na, Fu'ad yace ki kula fa ga mutane gabanki,Horn na Danne da karfin masifa sai da na tashi Hankalin kowa na leko da kaina ta window nace a tashi Zan wuce,Me gari yace Dan Iskanci duk ga hanya Nan baza ki wuce ba sai ta inda muke Zaune,barikin kika zo nuna Mana an haife shege? Nace ae karku tashi ku gani idan da rabon Zan diddige kafar dattijo to, Kamar da gaske sunga fa lalle zanbi ta kansu Basu San tsokana nayi ba,da gudu Suka tashi na wuce,sai 11pm Muka dawo gida Gaban motar ya Dan fashe sabo da dukan katangar kawu da nayi,Wanka Muka Yi tare da cin tsiren da muka siyo a garin.

Iya kuwa Akan Dan Uwanta yace surikin banza,Iya Kamar zata tashi Aljanu ta dinga masifa Tace wlh akan ka taba Fu'ad gwara na bar garin Nan gaba daya,Kai gwara ma a koreni daga Nigeria gaba daya na haura wata kasar,Akan katanga wallahi badan Iyayenmu sun mutu ba da sai na ambato naka rabon a jikin Iyayen namu na zagi bangaren naka,Kawu Haruna ya Bude Baki yace ai ke sai Addua bazan tsaya magana Ina Bata Baki na da mahaukaciya irinki ba,Kinga kudi ai nasan ko mene Zaki iya Yi akan kudi,Dan Rashin kunya a Kansa kika bar musu gida suci duniya da tsinke ke kin Basu waje,ai Kai baka waye ba Haruna Ka Bari idan Suka dauke Ni na koma birni Zan biya maka kudin makarantar yaki da jahilci,mace da mijinta an daura aure sai a Kama wani boye boye,Yanzu kaima Kana shiga dakin matarka Haka zaka haukace Mata ,Haruna yace na lura bakya ganina da mutunci,yo Ina kake da shi? Ai Sanda akayi rabon Mutunci lokacin Inna ta kaika karatun Allo kana Almajiranta a Zaria,Haruna yace karya kike Wlh na tabbata na fiki mutunci,Iya Tace Kai ka sani Kuma gidan Nan naka ma ai na gado ne ya Shiga gadonmu na rufa maka asiri nace ka zauna a ciki tunda Ni na samu wani gidan daban , Kuma gonaki sunfi yawa a naka kason, to ka sani Idan ban kirawo Alkali ya Raba gidan Nan an bani kaso na ba Allah ya tsine min,Kuma dakunan naka daka ke zaune ciki Kai da Iyalanka Nan zance Ina so,To ai ba mahaukata bane Alkalan,a gado Namiji ke fara zabe,Iya Tace naji gonakina da nabaka kake nomawa kudin haya kake biya na? Shuru Haruna yayi yasan Iya ta fishi gaskiya sabo da gonakinsa da yawa Duk ya siyar biyu suka rage Masa Iya Tace duk ta bar Masa yayi ta noma shine Namiji,sannan ya samu filaye ya siyar,gidan da yake ciki ma da rabon Iya a ciki Amma tunda ta samu wani daban sai ta kyale shi Tace Nan ma ta hakura,har yaranta ta Tara kaf Tace Bata da gado ita su sheda ko ta mutu duk ta bawa Dan Uwanta,gidanta da take ciki shine Kawai mallakarta karma su sa Rai ko idan ta mutu Yara su tayar da fitina,Sabo da gudun matsala Bayan ba ransu,A Nan nake Jan Hankalin mutanenmu idan Iyaye sun mutu to a Raba gado da wuri,sannan idan wani ya barwa Dan Uwansa ya Tara yaransa da shedu ya sanar musu kowa ya sheda sabo da Ana mutuwa Ana barin Rigimar gado,Yara da jikoki sai kaga sun taso da tsiya azo a Bata zumunci Ana kulla gaba a zuriya har karshe.
Iya Dakinta ta koma ta kwanta tana Jin zafin yanda Haruna Dan Uwanta ya ci mutuncin yarta Kuma Yarsa shima Rumaila a Gaban bako Kuma suriki,Iya tana ganin Rumaila ai Yarsa ce,Wato idan Bata Raye bazai Iya rike Mata yayanta ba,ai wannan abin kunya ne Kuma Fu'ad yaje har kyauta ya Masa Amma ya dinga masifa Haka a gabansa,Babu ko Kara Abu na lokaci kankani,kowa yayi fushi da bako zaiji kunya.

Ni kaina banji dadin abinda Kawu ya min a Gaban Fu'ad, bai san tsautsayi ba,Kwanciya nayi tare da yin shuru Ina tunani, Fu'ad kuwa wayarsa da yake latsawa ya kashe tare da birkito Ni na kwantar da kaina a kirjinsa Yana shafa min gashi,Yace tunanin fa? Kamar zanyi kuka nace ka tafi Dani gobe,kana Jin abinda Kawu ya min gashi har yanzu wasu suna ce min karuwa, Murmushi Fu'ad ya saki tare da mannawa Gashina me kamshi kiss kana yace kinyi laifi fa Rumaila kema,Surutun tsiyarki ke jawo Miki wani abin,Kuma kin San mutanen Kauye dole sai Hakuri ko me zakiyi a Iskanci da Rashin kunya yake, Kuma ko me za a Miki karki ce sai kin rama,To be Sincere Baki kyautawa Dattijan Nan ba su Me gari,ki barsu da halinsu,Kinga abinda kika musu dole su zage ki,a dinga takawa a Sannu,ko ba komai manya ne,Nace ai Sanda aka ce Ina da ciki sunfi kowa Zagina,to ai ya wuce tunda Ni mijinki nasan ke ba Haka kike ba,Iya ta Gane,Affa ya San gaskiya to ai shike Nan,yatsana nasa Ina masa Zane a saman kirjinsa nace kenan kaima idan Kai nayiwa Haka da mota haushi na zaka ji?Dariya yayi yace ai idan nine duka zaki ci,sai na farfasa Miki Baki ma sai dai idan Salahu ne zai kwace ki,Dariya nayi tare da Dan bugar kirjinsa kadan da sigar Wasa,ke yarinya ce 17yrs shi yasa idan kika Yi wani abin nake kyaleki nasan kina girma Zaki daina ku dama Yara Haka kuke,Mikewa nayi na zauna a saman katifar nace ai nufinka yarinya ce Ni? Yeah ya furta,Wallahi Ni ba yarinya bace Amma jiya kaji dadinka a jikina zaka ce Ni yarinya ce, Fu'ad yaga da gaske nake Yi fushi nakeyi yace min yarinya,Yace ai Baki girma ba har yanzu yarinya ce karama tunda har yanzu Baki San Dadi ba,Nace nasan Dadi Mana ai girkina Yana Dadi har Santi kakeyi,ganin ban Gane nufinsa ba yace ai ba Wannan Girkin ba ke Baki San Ana Miki shi ba kin girma an Gama,Nace Dan Allah? Yace Da gaske,Nace to Yaya akeyi wa zai min na girma? Tunda kana son Babbar mace to ya kamata na Zama babbar Nima ka daina min gori, Fu'ad yace hmm ai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login