Showing 57001 words to 60000 words out of 115153 words
labarin gidan da Fu'ad ya kera kamar gidan wani Senator yafi ma na wasu Senate din,Har da me kula da Compound Garden da komai na gidan,mace Kuma Guda daya Dattijuwa me kwazo Umma tace za a kawo min Bayan wasu satikai zata dinga tayani aikace aikacen gida sabo da girman gidan,Motocin Fu'ad wajen Guda biyar masu tsada,Ni kaina na Matsu na tashi na zaga na kalli gidan,Amma ance kar na tashi sai ango yazo,a fili nace Ni fa na gaji har yanzu yaki shigowa wallahi Nan da 30mnt idan Bai zo ba kallo na Zan tafi na kyale shi,Duk da Haka shuru Ina ta jira,Har Zan tashi sai naji Ana ta kulle gida nace maybe shi kadai ne sabo da yanzu maza da yawa sun daina Shiga dakin Amarya da abokai,da Sauri na koma na zauna tare da lullube kaina da Mayafi me sharara.
Da Sallama ya shigo na amsa Sabo da Ni ko kuka banyi ba to kukan me zanyi dama ba a gida nake ba na rigada na bar Gaban Iya bare nace zanyi kukan rabuwa da ita,Ta cikin Mayafi na nake ta Kallonsa ya hadu shaddar ta Masa kyau wata ruwan kunun kanwa Inji Yan garinmu,Tsayawa yayi yaki Zama nace ka zauna mana,Ina Kallonsa Yana hararata,Ledar take away dake Hannunsa ya ajiye min,nace Wai baza ka cire min lullubin ba Kai baka koyi yanda akeyi ba,kiyi ta Zama a lullube karki Bude,nace to Dama Kara nayi Dan kar ace nayi rashin kunya Amma Allah na gani lullubin ya dameni nasa hannu na cire tare da ninkewa na ajiye a sip Ina cewa Umma tayi min fadan tattali,Murmushi yayi yace Allah yasa kiyi Aiki da fadan,gashi nayi ma na Adana mayafina da wata ce da tuni a Kan gadon zata jefar da shi,Sai lokacin ya zauna a gefen Bed din ya tsura min ido,ban kulashi ba na jawo akwatunan Lefe na tare da Bude su gaba daya Ina kallon kayan da aka zuba min,Wani lace na dakko na daga shi Sama tare da tambayarsa Yaya kaga wannan ka Iya zabe Dan Birni, Shadda na dakko Tasha dinki nace ka iya zabe ya ka hango Ni a ciki? Fu'ad sai lokacin yayi magana yace Muni zakiyi,kayan bacci na Shiga dubawa nace,sai da yaga wata gantalalliyar Riga Sharara kamar net yace wannan zata Miki kyau,Ido na zaro nace dama Haka kake? Ina ganinka ba ruwanka Ashe Kai kafi kowa ma,ai gwara Kawai kace na kwanta tsirara banga amfanin ta ba,jambaki na dakko pink nace wannan fa a dinga shafa maka? Da Sauri yace ae wannan dai dai lasa ne, Ina Dariya nace tunda aka lashi kunnuwa ma Ina ga lips ai shi a cinye shi kawai.
Kayi Aiki wajen siyen kayan Nan,da Kansa Akwatunan ya rufe ya maida inda suke yace Alwala za muyi Sallah,nace daga ita sai cin kaza na sani,Daga Kazar fa? ya tambayeni,nace Salahu ya Gama Yi maka wajen an wuce Nan wajen sai dai bacci Kawai,Hararar Wasa ya min tare da furta Alwala fa, ba musu na Shiga toilet nayi Alwala na fito shi Kam Yana da Alwalarsa, Sallah ya ja mu Nafeela raka'a biyu tare da adduoi,Muna Idarwa ya tashi ya tafi ya barni,na jira shi har na gaji sai Kawai na jawo kaji na da kayan ci iri iri Dana Sha,naci na koshi na maida sauran kitchen,wanka nayi da brush na fito na shafa body lotion Dina,Kamar yanda Umma ta koya min shafa farin miski a gaba na,banson kamshin me Kalar Ruwa nafi son me Kalar Madara kamshinsa yafi min dadi,kadan nayi amfani da shi sai sauran turaruka na Jan Hankalin me gida,Ni Kawai sawa nayi sabo da Umma Tace na dinga amfani da su ba don miji na saka ba sabo da kuruciya da yarinta da tayi min yawa,ga karancin wayewa duk da na waye Amma har yanzu ban Gama karasa gogewa ba,sai dai a jikina da kwalliya tare da iya sa Kaya, na Gama gogewa anan shima Dan Ina da kyau ne ga jiki na me kyau gani fara sai kaga Kamar a birni na taso duk abinda na saka kyau nake Yi.
Rigar bacci na zaba Yar karama da kyar ta wuce Mazaunai na,me siririn Hannu jikinta me santsi silk ce me fito da sura gata Yellow me adon flower Maroon,nayi kyau matuka,Powder na Dan shafa sama sama tare da lipgloss,gashi na na taje na gyara shi sosai Yana kamshi sosai, Fu'ad Yana bedroom dinsa hadadde kafin ya shigo sunci abinci tare da friends dinsa shi yasa yayi wanka ya shirya cikin kayan baccin sa Sky blue and white marasa nauyi,wandon 3qtr da Riga me gajeren Hannu,Sai kamshi yake bulbulawa,Hadari ne ya taso aka fara walkiya da tsawa Nan take ruwa ya kece, Fu'ad kofarsa ya Bude zai dawo dakina ko ya kirani na dawo dakinsa Kawai kafin ya fito yaji kafarsa an rike ta Gam,ji yayi Kamar an sa Igiya an daure Masa kafafu,karfi yasa dole sai ya fisge kafarsa Yana fisga ya Fadi a kasa Tim,Ni kuwa jinsa shuru yasa na fito zuwa dakinsa na ganshi a kwance a kasa,da sauri na Shiga dakin lna cewa lafiya ya Fu'ad? Kallo ya bini da shi yanda na Gama tafiya da Imaninsa,Nace Wai lafiya kayi shuru,Hannunsa na rike tare da Mikewa tsaye na jashi sai ya tashi Kuma da Kansa ya koma saman Gadonsa ya kwanta Yana murmushi yace kwanciya Kawai nayi,Nima ban kawo komai ba nace Kuma a Kofar daki?, Kai ya daga min Yana cewa hauro saman bed din,Hannayena biyu na saka a saman gadon sai da Rabin jikina ya hau gadon Kawai naji Suuuuu an janyeni na koma baya tare da fadawa kasa,Mikewa nayi nace kut kaga jiri nakeyi, Fu'ad yasan Kan lamarin ya kama Dariya yace taho mu kwanta,tashi nayi na koma naji an rike min kafafu Kam,Kuka na saki nace wayyo kafafuwana, Fu'ad yace Nima Haka aka Yi min zanje Dakinki,Nace rike Hannu na ka jawo Ni, Fu'ad yace Haka Kawai naje a karya min hannu ba ruwana,Dan Allah ka jawo Ni na furta na hada uban Zufa,Hannu Fu'ad yasa tare da riko Hannu na Yana ja yaji kamar ya jawo katon Dutse,ya jawo da karfi aka dada Masa uban duka a Bayan hannunsa sai da fatar wajen tayi ja,Ya sake Ni da sauri yace saura kadan na karye Salahu yazo ba ruwana sai dai ki kwana a kasa ko ki koma bedroom dinki, Pillow da bargo ya jefo min,Ina shimfidawa na kwanta sai naji an sake min kafa na dawo normal, Fu'ad pillow dinsa ya dakko ya dawo da Kansa saitin kaina Yana sama Ina kasa.
Nace Salahu yana gari, ai idan ya hanani tabaki Bai Isa ya hanani kallonki ba cewar Fu'ad,nace ae kalleni na turo Masa fuskata gaba,yace Ke ba fuskarki nake nufi ba,jikinki nake nufi ki cire rigar na kalla,kunya nake ji Ni gaskiya,shike Nan na daina kulaki ya furta,rigar na cire kafin Fu'ad ya kalleni ba Kaya an tsokane Masa ido,Kara ya saki ya Danne fuskarsa da pillow Yana cewa ki saka rigarki,Nayi sauri na saka Ina ta Masa dariya,Ba Wanda ya sake magana Shuru Mukayi sai Adduar bacci da Mukayi Fu'ad shi ya fara bacci sannan nima ya kwashe Ni,ga gajiyar biki,Da Asuba Fu'ad Bai kulani ba Yana tsoro kar azo ya Kuma shiga masifa a banza,jikin bed ya bubbuga na tashi,Ina tashi ya wuce masallaci,Ni kuwa Dakina na koma,Bayan nayi Sallah da Azkhar tare da Kai kukana zuwa ga Allah,bacci na koma shima Fu'ad Haka.
Sai Bayan 11am Naji Door bell,lokacin na tashi nayi wanka na cakare cikin atamfa ta ruwan Toka da Baki,Riga da skert dinkin ya kamani daf,nayi dauri na zamani Ina kamshi na fito tare da sakkowa daga matakalar bene,Ina budewa naga Naila da kwandon Abinci daga Umma,Hararata tayi da Gadara Tace Ina Dan Uwana? Nima da Gadara Ina yatsina fuska kamar naga kashi Nace Baki Iya gaisuwa ba? Kamar ba Tarbiyyar Umma ba,Nifa yanzu na zama yayarki ki taka a Sannu,Bangajeni tayi ta wuce Karaf a Kan Idon Fu'ad daya fito yasha wanka cikin wani Danyen yadi, ya kalli Kanwarsa Naila yace Baki da kunya Ashe Zaki iya Bangajeni tunda kika bangaje Rumaila,Ai Rumaila ba Kai bace Yaya Kuma Ni na tsaneta ya zata min rashin kunya Bayan na girme ta,in banda ma kaddara ta Isa ta Hada ko hanya da Kai tana Yar matsiya.......Tasssss kake ji Fu'ad ya gasawa Naila Mari,wani Marin ya kawo Mata ta taka da gudu tare da Bude kofa tana kuka,Na jefa Mata gyalenta nace ki taka a Sannu yayarki ce Ni yanzu,karki ganni yarinya kice Zaki dinga kawo min Raini,Kofar na rufe na juyo cike da murmushi na kalli Fu'ad Nace ka birgeni daka kwadawa Naila Mari Kamar Ni ta zageni Ina matar yayansu,Basket din ya karba a Hannu na tare da ajiyewa a saman Dining, Fu'ad Ya min kyau da yawa,juyowa yayi da Niyyar min magana,ba zato na Rungume Shi a jikina,yace tab lallai Salahunki yayi tafiya,Dariya Mukayi gaba daya na dago da kaina Muna kallon juna nace ko ya tafi China ko India Oho,Fu'ad yace bacci yake Yi Bai tashi ba,Yana can yayi nauyin bacci,nace wani shegen yace kar yayi bacci da wuri ya tsaya takura Mana ai gashi Nan ya kasa tashi da wuri,Kamar daga Sama muka ji ance kyaleku nayi,Bamu ga Wanda ya fada ba,Kallon juna Mukayi, Fu'ad yace Ni dai gaskiya na fara tsoronki Kuma
A hankali ya rankwafo da kansa Muna facing juna Muna sakarwa juna murmushi,Saman tsinin Hancina yasa Harshensa ya Dan lasa tare da manna Masa Kiss,Nace Kai Kuma da Hanci ka fara? Ganin kamar Ina so yayi kissing Dina sai ya fasa da tsokana yace ban Iya abinda kike so ba,Ina a jikinsa na fara shagwaba Ina juya idanuna nace ka Iya mana,ke ai kin taba Yi da Salahu Ni kuwa saurayi nake Virgin ban San komai ba,Wanda ka sani Allah ya toshe maka Basira ka manta gaba daya ka yarda? Dariya yayi yace a'a bance ba,idan na manta ai kece a ruwa,Ina da Salahu,Fuska ya Bata sosai kishi ya kamashi,ganin ransa ya baci nace I'm so Sorry,Karya Salahu yakeyi ba abinda yayi,ta ya kika San ba abinda yayi dake? Bayan kince har Jini kin gani da kyar kika iya tafiya zakice baiyi komai ba,ganin da gaske yakeyin kishin nasa nace Zobon Aljanu ne fa ya zuba a gadon ba jini bane, murmushi yayi kadan,kankame shi na sake Yi,Saman kujerar Dining ya daura Ni,cike da Shagwaba nace Ni a cinyarka zan zauna,Yace a'a akwai matsala,wacce matsala Kai da ba ruwanka da mata Me zaka ji gani Yar yarinya,Damunsa nayi sai na zauna a cinyarsa yace leko to ki gani,Cinyarsa na leka na gani Hajiya Babba ta Mike,Kunya naji nace gaf take da yin Amai tayi fushi Wallahi Allah ya Bata Hakuri,plate da cups na kawo da sauran kayan bukata da kaina nayi Serving nasa sai kallo yake Bina da shi,Idonsa duk ya canja, Ni kuwa nasan na birge har wani Kara Iyayi nake yi,Tea cups dinsa na dauka na Dan kurba nace Uhm naka yafi dadi na janye nasa na tura Masa Nawa ,Slize Bread na Bude tare da saka Masa tsokar Naman kaza a ciki na rufe na bashi a Baki da kaina Yana ci Nima Ina ci,Kazar na yago na sa Masa a Baki ya fara ci na Mike tare da hayewa Saman Table din kumatunsa na rike da Hannaye Biyu nace to bani naci Ina magana da wani salo,mamaki ya Gama kashe Fu'ad ta ya nasan wannan soyayyar, shi yasa ya kasa komai Yana kallona Ina abinda naga dama Ina bashi mamaki,a ransa yace tun ba a yi nisa ba kenan Nan gaba abin sai ya fi Haka,yarinya sai nuna min take yi ta fini wayewa,zanyi maganinta,Bari fada na ya Kare da Aljaninta.
Sai da muka Gama cin abincin na kwashe komai tare da gyara gidan a Nan Nasha kallon gidan kamar Zan Suma sabo da murna, Fu'ad Yana Palo Yana kallon News ya kwanta ga waya Yana latsawa na sake karewa Palon kallon nace Karya kakeyi Yahuza Kafinta wane Kai,Allah ya tsallakar Dani hawa gadonka, Fu'ad yace kin takurawa Yahuza ki kyale bawan Allah tunda Bai Miki Kayan dakin ba, Murmushi nayi Bayan na Gama Aiki na ko Ina ya sake daukan sheki da kamshi ga Ac tana kada Raba,Kitchen na shiga Ina duba kayan Abinci,bangaren Curry na duba Naga Babu wata kala da nake gani Umma tana yawan Amfani da shi,wayata na Shiga latsawa na Kira Wayar Umma Ina fitowa daga Kitchen,Gaisawa Mukayi da Umma nace Umma Babu Curry din Nan me Kan Zakara,Girkin Rana zanyi karki kawo Mana abinci,Dariya Umma tayi Tace yanzu Rumaila akan Curry daya shine sai an kawo Zaki iya girki,Kuma ba me Kan Zakara ake cewa ba Wannan bokon kuwa Ana ganewa,da sauri nace Umma Chicken fragrance ko? Ba Umma ba har Fu'ad Dariya yayi,yace ance Miki turare ne?Zan Aiko Miki da shi,To Umma mun gode na Furta tare da nanatawa Umma me Kan Dan Zakara na kashe Wayar.
Iya an samu kudi sai ga Iya Tace Allah ya Mana Arziki ta kirawo masu ginin Bulon Siminti aka rushe ginin kasa aka Gina Daki biyu manya tare da katanga me tsayi ta zagaye gidan sai kitchen da Toilet ta sumulmule ko Ina na gidan harda paint Milk color,duk kudin da Iya ke samu Tarawa takeyi gashi tayi gida me kyau harda Dan siyo kayan kitchen masu Dan Araha,Daki daya ta sa Masa carpet Maroon da katifa katuwa,daya dakinta Kuma aka zuba Furniture na talaka dai dai kauye.
Ko da Me shayi yazo Biko na Uku cewa tayi duk me so na sai dai ya dinga zuwa gidana idan na gaji da mutum na sake shi ma'ana na koreshi tare da jefo Masa jakar kayansa,Shi Kuma me shayi Yana son Iya Amma Haka yace shi Kuma bazan Iya Zama a gidan mace ba ya rubuta Mata takardar saki,Iya harda murna Tace ka taimakeni wallahi dama ji nake wani kababa Igiyoyinka duk sun daureni sun hanani walawa yanzu ka kwance ni Alhmdllh.
Bayan Iya ta gama Idda, wata kawarta Dake Aiki gidan masu kudi a Kano itace ta bawa Iya Shawara tazo gidan da take Aiki suna Neman Dattijuwa mace,Iya Tace dakata Hajiya Mero Nawa suke biya a wata? Mero Tace dubu Uku,Iya Tace cab ai gwara na zauna a Nan naci gaba da kiwon kajin Hausa ko na fara surfe da daka,Hajiya Mero Tace to akwai Wanda ake biyan dubu Biyar duk wata? Iya Tace Dama dama,Amma kin San Banda Hakuri duk wacce ta takani ba kyaleta zanyi ba,Hajiya Mero Tace Babu ma Wanda zai shiga gonarki ai su masu kudi basa shiga safgar wani,Iya ta Bude Baki Tace to Kuma kinji wata sabuwa Kuma kice wulakanta mu za ayi,ace baza a Shiga harkar mutum ba ai wulakanci ya tabbata,Hajiya Mero ta kalli Iya Tace gobe Zan tafi idan kinga Zaki je to,Iya Tace Zan gwada idan ba dadi na dawo kauyen mu.
Washe gari Haka Iya tabi kawarta Hajiya Mero Birnin Kano gidan wani sanata zata Yi Aiki a can,Tunda Suka shiga Gidan Iya Tace Ashshahadu'allailahaillahu,Hajiya Mero Kudi Kudi,Billahillazi bani ba Kauye naga wajen Zama,Me gidan ne ya fito Yana takama motoci sun jere zai Shiga ya fita Iya Tace Mero Ina sonsa,Hajiya Mero Tace Iya ki Raba kanki wallahi ko Kallonsa kika Yi sai Hajiya matarsa ta koreki,Iya Tace ita din Banza wallahi sai na gwada sa'a ta,Ta karkashin kasa zanbi Mero,ki fara murna Mero daga yau ki Zama kawar matar Alhaji Sanata,Mero ta Bude baki Tace na Shiga Uku Iya Zaki kawo karshen abinci na a gidan nan,Wallahi sai dai abincinki ya Kare Mero Amma kin kawo Iya matar Sanata ta biyu.
Momy zaune take Tasha wanka ta kalli Safna tace ku shirya kuje ku gano Mana gidan shegiyar kauyen Nan mu gani duk Kaunar da ake Mata me aka zuba Mata,Rabi dake zaune Tace harda Ni za a je Dan Allah na gano lungu da sako,Khaleesat,Safna,Rabi da Farida wacce ta dawo daga Sudan ta gama karatu,Shiri sukayi tare da shiga mota Driver ya ja su,munafuncin Rabi yasa taci gaba a wajen su Mama.
5pm Nasha wata Shadda dinkin manyan Mata na kasar Senegal Dark Brown, Fu'ad cikin kana Nan Kaya marasa nauyi farare ya zuba kyau sai sheki yakeyi har Yanzu Salahu Bai zo ba tunda tun safe Ina Rike Fu'ad Kuma lfy.
A zaune yake yayi zaman manyan yara masu tashen kudi da ji da Kai,A gefensa na zauna ganin Yana Sha min kamshi sai na share shi ban kula shi ba,Kallona yayi ganin ban Masa magana ba duk surutu na sai yace kinyi kyau,na gode na Furta,Kwantar Dani yayi a jikinsa nayi matashi da cinyarsa kaina Yana samanta,Karar Bell Muka ji Kofar a Bude take nace Yes come In,Rabi Tace turawa anyi Boko,Kofar Suka Bude da wani Gadara Suka shigo Sallama sukayi ganin Fu'ad Yana wajen sun San ba Wasa,Yanda nake a kwance nayi matashi da cinyarsa ban ko motsa ba ganin sune nasan wulakanci ya kawo su.
Ku zauna na Furta tare da Mikewa na kawo musu abin sha Dana ci Fu'ad Suka gaisar Ni kuwa Basu gaishe Ni ba Nima ban ce Muka komai ba sai Hararata sukeyi,nace ga ruwa Nan Kainuwa dashen Allah ta kawo musu ku Sha,Khaleesat tayi Tsaki, na sake cewa ya dai kamata kuci Girkin Antynku guda, Fu'ad yace bana son tsokana fa,nace to baka gani har gidana Suka zo suna hararata,Ke wallahi watch your tongue munyi kanwa ta biyu dake cewar Khaleesat,Zanyi magana Fu'ad ya min tsawa ban son hayaniya ke ma biye musu zakiyi kina Babba Zaki zubar da girman na ki ai Aunty Bata fada,Farida Tace ai da ka kyaleta mun zaneta,Tashi sukayi ba Izni ba komai Suka dinga Shiga lungu da sako