Showing 81001 words to 84000 words out of 115153 words

Chapter 28 - DANGIN RABI COMPLETE

23 Aug 2025

1524

da shawara ta,Kai duniya aji tsoron Allah,yanzu gashi Ina cewa kar tayi aure karatu zata Yi kin yarda da wuri,Da Sanda bani da galibu ne ban isheki kallo ba ma,Rukayya Tace kefa Yar Iska ce duniya ce to ta canja Nima na Kara hankali nasan naka sai naka,nace Hankalin kudi ba anga Yan kudi na,ai zanje wajen su Basiru ne duk sai na muku wankin Babban bargo,Kuma na fada Miki ke Haleesa aure nayi cancel dinsa sai Nan da shekara Hudu zamu duba mu ganni muje ki rakani mota.

Haleesa ta bini rike da jakata har mota ta gaida Fu'ad Nace kinji dai me na fada Miki wallahi idan na Kira Yaya Rukayya naji Kina zance da saurayi Ubanki Zan ci,Ku Yan yaran Nan baku fiye hankali ba,baku San so da ki ba kowa ma so kukeyi sai anyi aure ku damu mutane da complain,Bamu shirya sulhu ba Yanzu daga anyi aure sai Sulhu kullum tsakanin Mata da miji,Haleesa Tace to Umma Rumaila,ke Zan ballaki naga ma kin rainani, Fu'ad Yana Jin Rumaila Wai Ita babba tana ta masifa Dariya kawai take bashi Haleesan ta fini girma sosai sabo da ita lukuta ce ga tsayi,Hand bag Dina na Bude na Bata 5k,Tace na gode Umman mu,ki daina tsofar Dani tam, mota Yaja Muka tafi Ina ta mita Yar wannan Yarinyar har tasan tayi saurayi duniya ta lalace,Dariya Fu'ad yayi yace Sannu babbar Hajjaju an girma,Dariya nayi nace ai masifa nayi ta Yi a gidan nan,Haka muka zaga gidajen Yan Uwana ko Ina naje na Zama Hajiya sai abinda nace Biyayya Kawai ake min, Fu'ad yace sai Mun koma gida zansa a kawo su Gidanmu gaba daya suyi ko sati daya ne, nace Allah ya kaimu Amma yanda za ayi ba duka ba,idan aka kawo wannan group suka Yi sati sai a maida su a kawo wasu.

A besa da gida ya ajiyeni Zan fita yayi sauri ya fisgoni yace Haka zamu rabu babu komai,Rungume shi nayi yace Bayan wannan fa? Kissing nasa nayi a lips sai ya rike bakin gaba daya Muka Shiga tsotsa,Muryarsa ta fara rawa na janye jikina,mayen kallo yake Bina da shi yace ko zamuje Hotel din mu kwana gobe na tafi ai Haka kika ce min jiya,nace Ba kai kace tunda mun Gama da wuri ba Tafiya zakayi Kuma kayi booking Flight fa,yace Flight din banza kudin Nawa ne a kan na rasa kissing naki kadai ba gwara nayi asarar millions ba,Dadi ya Gama kashe Ni Ana so na Kai Fu'ad sai ya siye mace da kalamansa,Nace Kayi Hakuri gwara ka karbo maganin na warke da wuri mu koma Zama waje daya kwana da tashi, yace Haka ne Kuma kin tuna min Amma zanyi missing naki,nace ai Ni har ma na fara missing naka Kamar nayi kuka,Wata Yar Akwati ta sarka ya dakko ya Bude naga sarka da dankunne da zobe na Gold yace ga kyautarki,murna ta kamani nace dama da gaske kakeyi,Kai ya daga min wuyana na Mika Masa ya saka min da Kansa na cire dankunne na na watsa a jaka ya saka min da Kansa na dinga Masa godiya,yace muga jakar Taki akwai kudi? Nace Wanda ka bawa Iya ya ishe mu,duk da Haka sai da ya Kara min wasu nayi godiya.

Nace sai yaushe? Yace ko yaushe Zaki iya ganina,Idona ya ciko da kwalla kamar mun rabu kenan sai da ya sake lallashi na tare da manna min kiss a goshi na fita Ina cewa Dan Allah ka dawo da wuri,Kuma kana zuwa gida ka kirani nasan kaje lafiya,karka manta da Addua,Yace Inshaallah ki kular min da kanki Banda fita na fada miki,nace to kaima karka Bari wata ta kalleka Kuma ko wace ta kalleka bazan taba yafe Mata ba,Dariya yayi yace I love you,Ban Saba fada ba naji kunya ta kamani,nace me too na tafi da sauri dake nesa da gidanmu ya ajiye Ni,Sai da naje Kofar gidanmu sannan na juya na kalle shi Bai tafi ba,Hannu na daga masa shima ya dago min,Muna ta bye bye Amma yaki tafiya,Iya ce ta fito taga Ina ta murmushi Muna Bye bye Iya Tace maza ci gaba Sanda hannunki ya sage Kya hakura ai,Ya hango Iya itama,Iya ta Masa Ambolar Zaki ta ware yatsunta Tace uwariyonka tafi Haka,ta janye Ni gida,Lokacin Fu'ad Yana ta dariyar Iya ya tafi,tunda ya tafi yake tunani na,har ya Kira wani Driver dinsa ya bashi motar a airport yace a siyar da motar Nan ta samu matsala Wife Dina ta daki katanga da ita a siyi sabuwa Zan tura maka kudin da Kalar motar,yace ba matsala Oga,a Nan Zan siyar da ita a can sai a siyi sabuwa yace no a Nan zaka siya ka ajiyeta a gidanka idan nazo Zan kiraka ka kawo min,sai na maka waya,Alright cewar Driver, Fu'ad Kam ya bi flight zuwa Abuja.

Ni kuwa Ina tsakar gida a zaune na Nunawa Iya Sarkar daya bani Ina fada Mata Alherin da yayiwa Yan Uwana,Iya Tace madalla ke Kam kinyi Dace,tunaninsa na Lula Ina kewarsa,kayansa daya saka kaf a garin nace ya barsu Zan wanke na goge,su na ebo Zan wanke,Iya Tace mayar da kayan Nan Tattabara Sarkin Aure Yamma tayi idan kika wanke akayi ruwa fa, ki Bari gobe da safe Kya yi Haba wannan wacce kalatar Miji ce haka Wato kina wanke Masa Kaya kina tuna abinki ko,Wai Rumaila kece haka kika Yi zurfi a soyayya? Dariya nayi tare da Rufe fuskata da tafukan Hannayena,nace Kai Iya,Iya tace Kyaji da shi mu Mene Bamu sani ba me za a boye Mana,Iya Tace Rumaila me tallan Awara 'yata itace ta samo Miji na gari ga kudi ga kyau ga soyayya,Ni Kam sai na godewa Allah Yar gidan Dan Daudu an rufta soyayya,Dariya na dinga Yi Ina rufe fuska na tashi na gudu dakina na kwanta Ina shakar kamshinsa daya makale a dakina.

Yana sauka a Airport ya kirani yace gashi a airport,Haka Yana karasa wa gida wajen Umma yace gashi a gida,nace Alhmdllh,Zuwa dare Zan kiraki,da dare kuwa Mun Dade muna zuba love a waya,na tashi na koma dakin Iya na kwanta a gadonta bayanta Mukayi bacci tare,Cikin dare na manta Iya ce ba Fu'ad ba cikin magagin bacci na Rungume Iya ta baya,na dauki kafa na Daura Mata a ruwan cikinta,na tugewa Iya dankwali Ina shafa gashin Iya Nace Baby Uhmmmmm.....Firgit Iya ta farka....


















AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈







NA KUDI NE

NA KUDI NE WACCE DUK TA FITAR DASHI ALLAH YA ISA,WACCE TA KARANTA BATA BIYA BAN BAN YAFE BA.













DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM










76-80













Official













By
AsmaBaffa











Page naki ne

Ummu Deejat






















Iya tana Farkawa kunne ta kasa sai da taji Ina Kiran Baby,Kunnen Iya na samu leben kunnen Wanda na Iya an kwana biyu a duniya wajen ya saki sabo da saka dankunne Na mulmula wajen,Iya Hannu na ta janye ta jawo dankwalinta Dana tuge ta dinga nannade shi sai da ya koma kamar Igiya sannan ta kunna Tochlight ta dage Iya karfinta ta dinga tsula min,Dake cikin magagi nake na bacci a tsorace na farka tare da direwa a kasa na Fadi a kasa,Iya Tace Ni Zaki gayawa Kwana da Miji,Ni Zaki gayawa soyayyar miji,kin San Haka zakiyi kika ki binsa ku tafi,Fitsararriyar banza,Harda mulmula min kunne Yar Iska saura kadan ki hada da Dankunne na ki firde min kunne ya tsarge gida biyu da kin tsinke min kunne sai kin kaini Asibiti an dinke min,Sai lokacin na tuna ma Ni tare muke da Iya,Wayata ce tayi Kara alamar Kira ne na San ma Fu'ad ne,Iya Tace ga babban Fitsararren Nan ya Kira sai ki dauki wayarki ki bar min daki,nasan Abinda zai ce Miki Iya ta gwada Maganar Fu'ad da Gadara da Iyayi zai ce na kasa Bacci,shi yace Miki Baby ke kice Masa Baby to Dan Ubanku Wai me kuke nufi ne? Ya abin yake ne? Wa za a barwa Baby din ne a zabi mutum daya Mana ko shi ya karbi Baby ko ke sai Kuma ku samo wani Sunan a bawa wani Amma ke kince Baby shi yace Baby Ni fa ban Gane muku ba 'yan Babyn Bantan Uba tashi ki tafi Iya ta fatalo min wayata,Dariya nayi nace Iya Can dakin Ni daya kamar mayya,Iya Tace ai mayyar ce dama Ae mayyar Mijinta ba, Allah idan Baki fita ba gobe Tuwon masara zanyi a gidan Nan tun safe har dare shi Zaki ci Kuma,Iya tasan bana cin Tuwon masara sai dole,kofa na Bude na fice ta rufe kofarta na koma Daya Bedroom din sannan na Kira Fu'ad,Muka Sha Soyayya har labarin Iya na bashi abinda ya faru ya dinga dariya.

Washe gari da safe bayan Mun karya Wankin Fu'ad na kwaso da Nawa Zan wanke,Iya tana zaune tana gyara wake Tace Ina ganin banbanci,In haifi mutum Amma wani bare ya fini,nace to Iya kema kawo naki,kiyi naku bana so wanki na kala daya ne Zan wanke abina,Ni Ina da matsayin da za a hada wanki na Dana miji ne? Baki na Bude nace Kai Iya,Dariya tayi Tace Ke Ni tsokanarki nake Yi wanke abinki Amma anjima da Yamma ya kamata ki shiga gidan Kawu ki duba matarsa jiya ruwan Miya ya zubo Mata a Hannu ta kone da yawa kin San kawun naki Sarkin korafi ne,To Amma Bari na tambayi Fu'ad din Idan ya barni to,Iya Tace Yau baza ace Baby dinba? Ko kunyar ta motsa ne yau?in dai Dan nice kice Baby dinki ba ruwana ai Ana so a dinga Dan boyewa Miji suna,Nace Iya ai kece idan ance kice a'a idan ba a ce Nan kiyi ta fada,Wanki na fara Ina ta faman Yi Iya Tace kayan Dan gwal sai an karar da Sabulan gida da Omo duk Akan kayansa,tun dazu kike bulbula musu kumfa kinyi Sabi yafi biyar ayi da Sabulu ga Kuma Omo,Murmushi Kawai nayi Ina Jin Iya har na Gama na shanya,nace Iya Zaki Yi amfani da itace? Iya Tace ae nace to bazan shanya a Nan ba sabo da kar hayaki ya kamasu,Iya dama tana sani Tace ae Dan taji me zance,Kai Kawai ta jinjina Tace Wai Ni Kam Rumaila ko a birnin makarantar kula da Miji kika Shiga ne Nima na siyo Littafi nazo daukan Darasi,Dariya Iya ta bani nace Iya a wajenki na koya,a'a ai Ni duk inda naje Allah ya gani banyi Biyayya ba,Ina so nayi Amma na kasa tursasa kaina shi yasa na Dan fasa yin wani auren sai zuciyata ta Dan shakata na gaji da kaunar mazaje daban daban karshe Kuma bazan zauna ba,Kauna ta mutane maza da yawa tasa zuciyata ta cunkushe da Goslow, ta wannan ta Shiga ta fita,ta wannan ta Shiga ta fita yanzu sai nayi shara a zuciyata,tas Zan shareta na saka mutum daya na karshe sai na rufe ta ruf,Iya waye na karshen yanzu Nan gaba kina sa Rai Zaki sake aure? Iya Tace kwarai kuwa Inshaallah da Aure Zan koma ga Allah,nace waye to Iya? Me tsautsayi Wanda Allah ya kawo zai Sha wahalar Iya cewar Iya,nace Dan Allah Iya mu tafi dake Birni ki hakura da auren nan,Iya Tace ai birni Kam zanje Inshaallah Amma bazan zauna ba sai dai nazo da yawo naga dakin mijinki da danginsa na dawo,In Allah ya yarda ba Wanda zai ce Yana sonki ma,Allah ya bani farin jini sai ki Hana na gani Iya ta furta, Fushi nayi ban sake magana ba,Har Suka bushe na goge Masa kayan da Nawa na killace su sannan na Kira shi a waya.

Fu'ad Duk da cewar bana gidansa a can yake kwana sai da safe Yake zuwa gida wajen Umma a can yake cin abinci Kuma Ko Office Umma ke Kai Masa abinci,5pm ya dawo Direct gidansu Driver ya maida shi,yaci Uwar wanka cikin suit Silver color yasha kyau,kayan dai dai shi kamar a jikinsa aka Dinka ta zamani,rigar ta sama ya cireta tare da ratayata a kafadarsa Yana tafiya Yana latsa waya,masu Aiki Sai gaisuwa suke kwasa Yana Gadararsa,Naila ce ta fito zata fita a motarta Sannu da zuwa Yaya ta furta,Hannu Kawai ya daga Mata ya wuce sashen Momy ya gaida ta,munafukar da fara'a ta amsa tana tarairayarsa,Harda kawo Masa abinci,Yana ci a Dining Tace Ni kuwa Fu'ad Wai Ina matar taka ne? Fu'ad ya fadada fara'arsa yace taje ganin gida jibi ma nake so naje na dakko ta,Momy Tace Kayi Mata waya Mana ta dawo ai ba yarinya bace da zata bace ko, No da kaina zanje bana so tana hanya Hankalina ya rabu gida biyu zata dawo lfy ko a'a yafi idan Ina kusa da ita,Momy Baki ta tabe Tace Tunda ita Bata da cikakkiyar lafiya Aljanu sun shafe ta ga wata Yar kawata Yusra ka Kara aure Mana yanda kake matashi a Haka kana bukatar kulawa,matarka Kalar lalura ce kullum a mashashara take daga wannan sai wannan,Mika Fu'ad yayi yace Ni Yar matata ta ishe Ni,dayar ma daya na samu nayi,Momy Tace Fu'ad nice na raineka kasan bazan cutar da Kai ba,Kalli hoton Yusra yarinya ce wayayya a turai tayi rayuwa irinsu ne kalarka, Fu'ad ya karbi Wayar Momy ya kalli Yusra fara ce kar Amma ko kafar Rumaila Bata Kama ba a kyau da kyan sura, ya santa ma a Uk Bata da tarbiyya ko kadan gaba daya a turai ta girma sai yanzu ta dawo Nigeria,Iyayenta ma Basu Iya bada tarbiyya ba suna da son Shiga malamai,Wayar ya mikawa Momy yace tayi Momy Amma a Bawa wani a gidan Nan ba Ni ba,na Santa ma Yarinyar Yan Kano ne,Momy Tace Haka Tace min itama Kun San juna,Zata zo min Nan ai zatayi wata daya a gidan Nan idan Allah yayi Kun saba shike Nan ai, Fu'ad yace Uhm Kawai ya Mike ya bar Mata sashenta Baki daya,Mama ma yaje sun gaisa,a wajen Umma ya Iske Aunty Samha Suka gaisa,Kwanciya yayi a doguwar kujera Yana latsa waya kirana Ya shigo wayarsa,kashewa yayi tare da kirana back.

Baba Jummai tana kusa da Fu'ad tana ta goge goge tana satar kallon Fu'ad a hankali Kamar me kunkuni Tace a duniya Yaron Nan Yana birge ni,Kuma Ni da soyayya nake sonsa Amma wannan tsinanniyar ta kanainaye shi Hala ita ke Kira,Umma Tace Baba Jummai zancen zuci kike Yi Haka ne? Haba Dan Allah mene damuwarki a duniya an muku albashi da wuri ga komai Ana muku Zaki ci Zaki Sha,ba duka ba zagi Mene na zancen zuci har zamu fara Jin matsalarki a fili,Samha Tace ke rabu da tsofaffin Nan ba godiyar Allah suka fiye Yi ba,tunda ba a tauye musu hakki ai shike Nan Allah ya gani,idan kika sake Ciwon zuciya ne zai kamaki a banza yanda tsufa ya kamaki Haka,Baba Jummai tayi mukus Allah yasa ba a ji me Tace ba sum sum ta tashi da mopper dinta tayi waje.
Shi kuwa Fu'ad hankalinsa ma ya tafi Kan Wayar Daya Kira,Bayan na gaisar da shi Nace ka dawo daga Office ne? Yace Yeah Ina palon Umma nace ka gaida ta,zata ji,kinci abinci? Nace ae,da yawa? Nace ae,to me kika ci? Nace wake da shinkafa da Salat da tumatur na barbada Maggi star na da Mai da yaji Dan kadan,ke kika dafa? Iya ce tayi, That's really nice,hope dai Baki ci Albasa ba nasan Mata da kwadayi,nace ai kasan Ni bana sonta ma Sai in za a sa a iya girki a dafa yace Correct, Umma tana ta ji da Aunty Samha sun daina Hirar tasu sun tsaya suna sauraron Fu'ad,Umma tana ta mamaki yanzu yaushe ya fara Soyayya da matar tasa,shi da yake nuna aji baya magana sai yaga dama yanzu gashi shine yake ta tambayoyi,wayarsa yake Yi Yana ce min kinyi wankin? Har ma na goge su,ki zuba Kawai a wannan jakar Taki pink idan na zo Zan tafi da su,matar Kawu Haruna ta kone a Hannu,Subhannallah ya furta,Na wani narke murya da Shagwaba nace Wai Iya Tace naje dubiya nace Bari na fada maka,Uhmmmmm......ya Furta sannan yace kije tunda dubiya ce Amma da dare Kuma Hijab har kasa Zaki saka,Nace to ai dama,karki bi ta Hanyar majalisar su Jauro kibi ta can bayan farin masallaci ta wajen Bishiyar Nan wacce ranar Nan da dare muka tsaya a wajen,nace na Gane,Kuma Minti biyar zakiyi a gidan ki koma gida.

Shagwaba na fara Masa Ina bubbuga kafafu Kamar Yana kallo na nace Ni...Ni...Allah...yayi kadan.... Alright 15mnt to,zai Fadi wata Maganar sai ya tuna su Umma suna wajen Kuma yaji palon tsit, Mikewa yayi Yana dariya Yana waya ya haura sama.
Bed din Umma ya kwanta Muka ci gaba da waya harda cewa sai na Masa kiss Haka na dinga Muahhhh....Muahhhh...a waya shima Haka,Iya Ashe ta fito daga daki Tace cinye Wayar ki huta Nasara ya kera muku Kun Zama Shashashu,Bature ya Mai da ku wasu bi ta Nan,Nima tashi nayi na kule daki na kwanta muna ta waya wajen 2hrs sannan muka hakura lokacin Sallar magrib tayi,Bayan nayi Sallar Isha sannan naje dubiya gidan Kawu Duk yanda Fu'ad yace nayi ban karya dokar ba Haka nayi na dawo gida.

Hajara da Jauro soyayya ta barke a tsakaninsu Wanda har ta Amince ya Kai kudin Aure ,Manya sunyi magana Dana ji labarin na Mata murna Jauro ba laifi Kuma Lagos zai tafi da ita tunda a can yake aikinsa na Dan Sanda,ko ba komai Hajara tafi su Saude da Rabi kyan hali,ganin Hajara Itama ta samu Miji na kirki sai Saude da Rabi Suka hade Kai Suka daina kula Hajara sosai sai sunga Dama,Amma suna

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login