Showing 48001 words to 51000 words out of 115153 words

Chapter 17 - DANGIN RABI COMPLETE

23 Aug 2025

1581

Rumaila kin cuci kanki,Ana ta Yi ba ke,Ga Iya arzikinta yazo Allah ya Buda min,tunda Iya ta samu wannan kudin shike Nan sai Yanga da gadara kana magana zata ce me nake Nema a wajen wani,Waya ma daina dagawa tayi idan za a Kira ta sau dubu baza ta daga ba Wai Bata da lokaci ta Zama Busy,Lokacin Me Shayi Yana ganin Soyayya sai gasar kyautata Masa sukeyi Iya da kishiyarta.

Yau da cikin dare Zazzabi ne me zafi ya lullubeni da shi na kwana ko Sallar Asuba da kyar nayi ba tare da na iya karanta Azkhar ba,Ina kwance Ina Rawar Sanyi na dukunkune a cikin bargo,Umma taga har 11am Lokacin Fu'ad yazo sunyi Sallama ya wuce Office Amma ban fito ba,Bedroom Dina ta Shiga taji Ina Nishi tare da Rawar sanyi,Umma tazo gefen Bed Dina tare da taba gefen fuskata da Bayan Hannunta taji zafi rau,Tace zazzabi kike Yi Amma baza ki fada min ba? Paracetamol ta bani na Sha tana cewa nasan bazai wuce lalurar ciki ba,idan Kuma Baki warke ba sai Samha tazo ta duba ki,Nace Aunty Samha dama Likita ce? A e mana cewar Umma,Bayan Nasha na kwanta ban samu sauki ba sai wurin Sallar La'asar sannan Zazzabin ya sauka na fara gumi,Wanka da Brush na sakeyi tare da gabatar da Sallar Azhar da La'asar,Shiryawa nayi cikin wani 3qurt Tight legins me Kalar jikin Tyga,Ya dameni sosai Shape Dina ya fito dama gani da fadin mazaunai da tudu sosai nafi kiba a nan gaba daya,Riga me siririn Hannu Iyakacinta kugu na peach color,Gashina na gyara na fito Zan Ebo abinci na dawo dakina, Ina fitowa Fu'ad da wani abokinsa suka shigo su biyu suna tafawa, Fu'ad ne a gaba ban so Suka shigo ba,da sauri na shige kitchen Amma sun Riga da sun ganni,Abokin Fu'ad Mujaheed zaiyi magana a kaina Fu'ad yace shuru tare da daura yatsansa a saman jajajyen lips dinsa,Bana son zubar da aji nasan abinda zaka ce Bari na Kira Umma Ku gaisa ya furta tare da wucewa Dakina irin Umma zai Kira,Hijab Dina ya gani a saman bed

Dakko shi yayi harda linkewa sosai ya Shiga nemo bakar Leda a room din Nawa,ya birkito min kayan sawa ta a sip duk ya zubo da su kasa, Bangaren Inner wears yaje a shirye suke ya Watso su kasa farrr, Pant daya ya dauka ya kalla tare da tabe Baki ya jefar Yana yarfe hannu Wai kyankyami,Haka ya ya sa kafa ya dauke Bra da take kusa da kafarsa yayi chilli da ita ta daki bango ta fada can Haka yayi watsa watsa da kayan,sai a Drawer ya ga ledoji ya dakko ya saka Hijab din a ciki ya fito,Ni kuwa kunya tasa na kasa fitowa daga kitchen, Mujaheed abokinsa ya kalla yace tana zuwa Umman,Kitchen Direct ya leko ta kofa Ina jikin Fridge a tsaye Ina cin abinci na,Ledar da hijab ke ciki ya jefo min a fuska ta ya fice abinsa tare da haurawa sama ya Kira Umma ta fito Suka gaisa da Mujaheed sannan Mujaheed yace Umma na wuce,Dama ka Dade da zuwa Hala? Ae Umma a Garden Muka tsaya mun Dade,Ana ta shirye shiyen bikin? Yace ae Umma Yana Sosa Kai,mashaallah Allah ya kaimu ai gwara Mujaheed kayi aurenka da wuri,yace Umma so nake na bude musu hanya,Suna Dariya Umma Tace ka kyauta,Bayan ya tafi Hijab Dina na saka tare da fitowa,Na ga Fu'ad da Umma suna kallo suna Hira,Sannu kin tashi kenan Rumaila? Nace ae Umma naji sauki sosai ma,Haka ake so Allah ya Karo sauki nace Ameen,Bai kulani ba na wuce da Hijab Dina,Ina shiga naga Barnar da ya min Kamar nayi kuka,Sai Dana Gama cin abinci sannan na gyara kayan da dakin baki daya.

Tasalluwa tare da Baba Jummai suna kitchen suna Aiki suna Hira,Tasalluwa ta kalli Jummai Tace Oh Jummai Allah ya taimakeki da Yarinyar Rumaila ta kwace ki a hannun Yan fashi da tuni Dan Momy Fu'ad ya sadu da ke,Baba Jummai tayi Dariya Tace ke dai Bari tarko na ya Gama Kama bera,Rabo na da harkar Nan tun Mijina Yawale Yana da Rai,Baba Jummai ta share hawayenta taci gaba da cewa ai Ni lokacin murna nayi a Raina tsinanniyar Yarinyar tazo da siririyar murya Wai Oga na fanshe ta ayi Dani Yar Iska shi yasa na tsaneta,ke Tasalluwa na samu Kamar Fu'ad ya Tara Dani ai na Gama ganin Daren lailatul khadari ai wallahi da Allah yasa ya sadu Dani to Ana gamawa Zan roki Allah ya dauki Raina sabo da me nake Nema a duniya na Gama samu,Ni fa idan Nan gaba Ina da sauran shekara ashirin a duniya to da za bani Fu'ad ya sadu Dani Zan yarda Allah ya karbe sauran shekaruna du, Amma Yar iskar Yarinyar Nan me Kalar Lamsa tazo wani ayi da ita na fanshe ki ita a dole ta CeCe ni ji nake kamar na kashe ta Wallahi,shi Kuma Shuumin tana cewa ta fanshe Ni Baki ga murna ba wallahi,abin ya bani mamaki Bai San ma ya fara murmushi ba Ina kallon Dan mayyar,Dariya Tasalluwa ke Yi Tace gaskiya Ban taba ganin Tsohuwa irinki ba Baba Jummai wajen shekarunki 65 Amma kina son wannan harka Kuma da yaro me tashe Haba,Baba Jummai Tace sirri na na fada Miki Tasalluwa karki min tijara ni ko a da Harija ce daga Ni har Mijina Yawale Haka muke Kuma ke kin San ba a daina son abin Nan sai idan ba yanda za kayi,Tasalluwa da mamaki take kallon Baba Jummai,Tace kalle Ni da kyau Ni fa Dan bakusan wace Ni ba ne kawai kallo na kuke Yi,Tasalluwa Tace Kamar ya? Baba Jummai tace a son maza nake nufi Kuma matasa da ace kudi gareni to kullum a Hotel za'a na kawo min matasa Yan Shila Ina biyansu,Bakya tsoron Allah? Tasalluwa ta tambaya,Hmm Aljanna ta me Rabo ce idan Allah yaso ya bani sai ki Hana cewar Baba Jummai,Tasalluwa share zancen tayi Jin abin yafi karfin ta.

Samha Amaryar Abbi ita Umma ta Nemo ta dinga dubani tana da kirki ba laifi har cewa tayi ya kamata itama naje gidanta na Danyi kwana biyu nace zanje Inshaallah.
Bayan Kwana Uku na warke fes Dani Umma Tace na shirya muje Babban Asibiti a gwada cikin Nan Nawa a gani ko akwai ko da matsala ne, wani katafaren asibiti Muka je da Umma private Hospital ne,Babban Likita muka gani Dr David,Wasu gwaje gwaje ya min na sosai Bayan Umma ta fada Masa labarin cikin da komai, Bayan yayi duk Test dinsa ya tabbatar bani da wani ciki ko daya,mamaki ya hanani magana nace wallahi Umma Asibitin Dana ke zuwa Ana min gwaji Kuma Basu taba cewa bani da shi ba,Umma Tace na fada Mata Asibitin na Bata labari,Tace dama wannan Fu'ad ya kaiki Amma Baki taba fada min ba? Murmushi nayi na kareshi nace No Ni Nace Ina so,Karya kike Yi,Da gaske Umma Dan Allah karki Masa fada baida laifi,Kallo na Umma tayi yanda nake ta faman Bata Hakuri,Tace shike Nan ai kunfi kusa muje gida.

Nace Umma a shawara mu sake zuwa wasu Asibitin kamar biyu a sake Test a gani,Umma Tace kinyi magana a Nan muje,da kanta tayi Driving Runtumemiyar motarta Ruwan Toka Muka je wani me tsada shima an gwada babu komai,Haka Wani ma sun gwada babu,Umma Tace dama Asibitin Kauye me Suka iya babu Good Doctors ba kayan Aiki,Sai murna mukeyi,Umma tun kafin mu koma gida ta sanarwa Abbi da Fu'ad tare da su Nene,Ni Kuma Nan take na Kira Iya ta yafi sau goma Bata daga ba tunda taga New number gashi tayi kudi Bata da lokacin waya da kowa,Affa na kira,bugu daya ya daga na gaishe shi Ina ji Yana ta Maganar matansa nace Affa? Yace Ina jinki sai akayi Yaya? Ko bariki ce tayi dadi anyi kudi mu taho da kawaye na mu hada party? ai kuwa da kinga chashewa,Nace a'a Affa Allah ya tsare Ni da bariki,dama fada maka zanyi an min gwaji a birni bani da ciki,Nan take ya tintsire da dariya yace Ke Ni fa na tsuguna na haife ki,kin zubar da ciki Zaki Raina min hankali kafin nayi magana ya kashe wayarsa,Kiran duniya kin dagawa yayi dole na hakura.

Cikin Dare naci sa'a Iya ta daga Wayar tana Jin muryata Tace Zan daga Miki nono ba nace kar in sake Jin muryarki ba ko ganinki bana kauna,Hawaye ya zubo min nace Iya wallahi anyi gwaji a Nan birni asibiti me tsada ance bani da wani ciki,Iya Tace cab Amma kin iya rainin Wayo kiyi laulayin a gaba na ayi gwaji karki manta asibiti uku na kaiki har birni akace kina da ciki yanzu kin zubar da ciki zaki dawo ki Sharo min karya,Wallahi kika sake kirana ban yafe ba yawwa kije can kiyi barikinki inda kika saba,Wayarta ta kashe ta barni Ina kallon Wayar,Haka dukkan Yan gidan Yan matan da su Momy da Yan aiki cewa sukayi karya ne Umma ce tasa aka zubar min da cikin shi yasa ma na dinga cuta Amma yanzu anzo Ana musu karya sai Dariya sukeyi suna cewa daga ciki an koma kisan Kai.

Abbi kuwa yafi kowa murna sabo da Haka Yan Uwansa ya Tara Mata da maza tare da Yan gidan Muna Zaune yace yanzu zai saka ranar Auren Rumaila da Fu'ad,Murna nakeyi sosai a Raina a fili ban nuna ba,Abbi yace Fu'ad bazan muku auren dole ba kana son Rumaila? Sai yace a fara tambayarta tukun,Abbi yace Rumaila kin amince da Fu'ad Kai na daga alamar ae,To Kai Fu'ad fa? Nan take yace ban amince ba,Ni Abbi ban shirya Aure ba yanzu a kyale Ni Zan kawo da kaina,Umma,Abbi da duk me kaunar Rumaila sai da gwiwar kowa tayi sanyi Umma ranta ya baci tayi tunanin son Rumaila tuni ya Shiga zuciyar Danta Fu'ad Ashe ba Haka bane sam,Da Sauri Islam yace Ni Ina sonta wallahi Abbi,Abbi yace kinji Rumaila kina sonsa? Nan take nace Abbi Ni bance bana sonsa ba Amma ka Dan bani lokaci mu fahimci juna Yana zuwa zance wajena Muna Hira kamar kowanne saurayi da budurwa idan har komai ya min Zan bashi dama ya turo magatansa,Abbi yayi Dariya har Nene yace to Rumaila Allah ya zaba Mafi alkhairi...Momy ce Tace wallahi ban yarda ba,ba a Isa ba,sai da aka zubar Mata da ciki za ayi wa Dana Wayo,Danta ya Mata ciki yace Baya so an zubar ance ta auri Dana to ko sama da kasa zata hade bazan yarda ba,Ya zaka Yi da maganarka da kace shi zai aure ta tunda ya amsa da Kansa shi ya Mata ciki,ya zaka dawo da magana baya ko su yarana ba mutane bane?sabo da ga Dan mowa ko,Mama Tace karki yarda wlh,Samha kuwa Tace ai ba cewa akayi zata Aure shi ba an bashi dama ya nemeta ya dinga zuwa zance, Kuma kun San gaskiya wlh Fu'ad bazai iya yiwa wata ciki ba Haba Dan Allah,Yi Mana shuru munafuka,Abbi ne ya daka musu tsawa yace Islam shi yace Yana sonta Kuma Indai sun daidai ta aure ba fashi sai idan Islam ne da Kansa yace baya so ya fasa ko ita Rumaila Ni Kuma bazan wa kowa auren dole ba Alkawari nane shi yasa na bawa kowa zabi,ai shi Fu'ad ciki ya Mata sai ya aure ta shine gaskiya,Abbi yace bazan musu dole ba suzo Ana ta zargin juna Abu ya lalace na sake shawara ne tare da Yan Uwana da yardarsu nayi Haka,Umma Tace ai Fu'ad shi ya amsa da Kansa yayi Mata ciki sai a bashi ita dole shine gaskiya idan anyi Haka an zalunci Rumaila anyi son Kai, Fu'ad yace na Rantse da Allah Umma bani nayi Mata ciki ba ko Qur'ani Zan dafa ban San zance ba,Islam Dan a bashi Ni Rumaila sai yace Abbi Boye muku nayi gaskiya Ni nayi cikin,aka dauki Salati gaba daya,Ni Kuma nace na Rantse da Allah ba Islam bane Ya Fu'ad shine Abbi,Abbi Kansa ya kulle yace to magana ta Kare Kawai Islam zai na zuwa zance wajenki idan yayi Miki kice a turo magabata Rumaila,Nace to Abbi,Kin amince ko Fu'ad din kike so? Nace Abbi dama Ni ba son Fu'ad nakeyi ba Dan Umma nace Ina sonsa Amma ko kadan ban taba jin kaunarsa ba Kuma har abada bana Jin Zan iya sonsa ko da wasa gwara dai Islam din dama can tamu yazo daya,Aniyarki ta biki shegiya annamimiya cewar Momy, Fu'ad yace Abbi karka bawa Islam Yarinyar Nan Ina bada shawara yaro ne bazai iya rike aure ba,ga shi da son matan masifa kowa ya gani sonta yake Yi,kar yazo ya cutar musu da yarinya a barta tayi karatu Nan da wasu shekaru,Kanin Abbi Muhammadu yace Bama son Shishigi da Iyayi,kace baka so Ina ruwanka da duk Wanda ma za a bawa? Haka Abbi ya sallami kowa Dama nasan yanda ake son Fu'ad fiye da kowa baza a iya Masa dole ba,mutumin da sai abinda yace sai abinda yaga dama yakeyi,Umma ce Kawai ta daina kula shi tayi fushi da shi,ko yazo gaishe ta Bata amsawa,ni kuwa ko a fuska ban taba nuna Masa naji haushi ko wani Abu ba,sabo da Ni ba komai ke tsaya min a Rai ba,Kuma nasan maza Nawa ne suke amfani da Yaran mutane suna lalatasu Kuma baza su aure su ba,bare Ni da yace karya ne Kuma yanzu an gani ba ciki.

Ya Shiga damuwa Umma Bata kulashi,a Palo Ni kadai ya samu Ina karatun Haddar Alqur'ani,Bayan Na amsa sallamarsa Sannu da zuwa na Masa ya amsa da fara'a tare da Zama a kujera Ina kasa,yace Ina Umma? Tana sama na bashi amsa,yace kinga a kanki take fushi Dani ko? Nace ka Bata hakuri,na Bata Taki hakura kije Dan Allah ki rokar min ita,Nace Nawa za biya Ni? Sai ma na Baki kudi? Nace ae Mana Zan ma Aiki a banza Ka haife Ni ne ko sassaka Ni kayi? Kallo na yayi yanda na kalle shi na iya fada Masa Haka,yace Zan siya Miki waya sabuwa ta zamani,nace wacce Iri? Yace Tecno,nace lebra ce Ni ai nafi karfin Tecno,Infnix fa? Nace ruwan dare kenan,Okay Samsung? A Samsung din Yar Nawa? na tambaya,yace Yar dubu dari,nace Kara sama dai Malam baka ganni bane yanzu yanda na koma First class,yace Dubu dari da Hamsim tayi? Nace cike Hamsin din Mana,yace ki dinga Jin tausayi na yarinya nace Allah sai dai ta dari biyu cif yace to Yana turo Baki yace Kamar wata budurwa ta,nace me kace Zan fasa gaba daya?murmushi yayi yace Zan siyo kije ki fara aikin tana kulani Zan Baki Wayar,Ai kuwa naje na iske Umma a Bedroom,Nace Umma Sannu da Hutawa Tace Yawwa Rumaila,Nace Umma ga Ya Fu'ad can yazo,Bata Rai Umma tayi Tace wlh Baki da zuciya Rumaila mutum yace baya sonki Amma har kiyi maganarsa? Nace to Umma Wai ba ya wuce ba,Dan Allah kiyi Hakuri ki dinga Masa magana komai ya wuce Umma ko so kike Yi sabo da fushinki Allah ya jefa Masa wata masifar Kuma? Addua zakiyi Masa,matar mutun kabarinsa idan Mijina ne Zaki gani Umma bazan auri kowa ba sai shi,Hmm ke Kam Rumaila Allah ya Baki wata irin zuciya,Dariya nayi nace Dan Allah Umma kiyi hakuri,na Dade Ina rokon Umma sannan ta yarda,da gudu na fita Ina murna naci sabuwar waya,wata me Aiki na tura part dinsa nace kice Fu'ad yazo inji Ummansa,Ai kuwa tana fada Masa yasan nayi aikin da sauri ya zura jallabiyya ya taho,Yana shigowa Ina murna na nuna Masa sama da yatsa,Murmushi yayi tare da kashe min Ido daya ya wuce da sauri,Kamar barawo Haka ya shigo sakadaf sakadaf,A Gaban Umma ya tsuguna Tace tashi ma Malam nasan Baki kuka hada da Rumaila,zaiyi magana Tace wallahi karma ka fara karya na sani da Rumaila kuka hada Baki.

Dariya yayi tare da daura Kansa a saman cinyar Umma yace Umma na Dan Allah kiyi hakuri,ai ka Bata min sabo da Allah Yarinyar kirki zaka Bari ta subuce maka,Umma wallahi Ni cikin ne Kawai idan na tuna take bani haushi Kiyi Hakuri,naji tashi to ka tafi na hakura Amma ka sani Dan Rumaila na hakura,na gode Umma Bari nayi wanka na dawo mu Sha Hira,Umma Tace uhm naji jeka.

Da murna ya sauko ya fita,Zuwa dare sai gashi a palon Umma Hannunsa dauke da waya Sabuwa dal Samsung ta dubu Dari da Tamanin,A Gaban Umma ya bani,na washe Baki tare da sa Hannu Biyu na karba Ina zuba godiya,Umma Tace mene hadinka da Rumaila zaka siya Mata waya? Yace sabo da kin yafe min sabo da ita,Ai Islam ya dace ya Siya Mata ba Kai ba, ke Rumaila bashi wayarsa na siya Miki,Kallon Umma nayi na marairaice nace Dan Allah Umma na karba Dan Allah Umma,Umma Tace ki bashi wayarsa nace, Fu'ad yace Please Umma,Umma Tace Dalla rufe min Baki bashi wayarsa marar zuciya,Mikewa nayi kamar zanyi kuka nace Dan Allah Umma....ki bashi nace ta daka min tsawa,wayarsa na Mika Masa yace bazan karba ba Ni bana kyauta na karba Kuma,Umma Tace sai ka karbi abarka,nace Umma ki kyale shi bazai karba ba kinji ya fada da bakinsa ba a maida hannnun kyauta baya Umma a duba abin nan,Muna Haka sai ga Islam yaji abinda ke faruwa yace Dan Samsung Zan siya Miki ko ta Nawa ce, Fu'ad ya kalle shi da sauri ya Bata Rai yace Kai baka da kunya ko? To ka siya Mata ka gani idan ta Isa ta rike wayarka,wlh zaka Yi asara sai na farfasa ta gwara ma ka Kama kanka,Islam yace Dama wajenki nazo taso muje Garden,Baza ta zo ba Fu'ad ya furta da bala'i,nace sai naje gani Nan,Da Wayar na tafi na ajiye a dakina na saka Hijab na bishi zamu fita, Fu'ad yace Ke na juyo yace na daina kulaki daga yau kije ki gani din,Kafa na daga tare da buga skert Dina nace Sawa....Muje Islam me sunan dadi,duk gidan

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login