Showing 51001 words to 54000 words out of 115153 words
Nan babu me suna me dadin naka kafi kowa, Fu'ad yace Zaki dawo ne sai na ballaki Kuma daga can ki wuce wajen Momy ki koma wajenta.
Muna tafiya ya zauna yana fesar da iskar bakinsa Yana ta faman yamutsa lallausan gashin Kansa me yawa,Yana ta Tsaki,Umma tana Masa magana Amma Ina Bai San ma me take cewa ba hankalinsa ya Lula wani wajen,Wai uban me kake tunani? Mikewa yayi zumbur tsaye ya koma ya zauna sai Kuma ya tashi yace Umma sai da safe,Karfa ka sake naji ka kula Yaran Nan wlh,yace to Umma ya tafi,Garden ya wuce Direct ya hango Rumaila da Islam suna ta sheka dariya,takaici ya kama Fu'ad ya juya ya Kira Tasalluwa,Tasal yake fada Mata Wai shi bazai iya cewa Tasalluwa ba yayi Masa Kauyenci,da sauri ta zo yace Jeki Garden kice Rumaila taje Inji Umma zancen ya Isa Haka a hakura a tashi dare yayi,Islam yace Anya Umma ce ba Fu'ad ba? Tasalluwa Tace Umma ce gaskiya.
Yanda ya fada Haka Tasalluwa tazo ta fada Mana Tace Kuma Inji Umma,Dole na koma nayi tunanin gaske ne,tunda Fu'ad yaga Mun fara shiri da Islam sai ya Hana Kansa sakewa ya daina fita ya matse min lamba ko ya yaga Zan fita sai ya Koro Ni gida,Umma ta Masa fada yaki ji.
Can Barin Islam Kuma Momy Tace wallahi bazai aure Ni ba,Su Fadila sai zuga Islam sukeyi za a bashi me cikin shege farkar Fu'ad,tun Islam Bai yarda ba har ya fara Yadda yace zai sa Ido idan ya ganmu tare da Fu'ad zai fadawa Abbi ya fasa.
Yau Sunday Ina kwance sai ga Suhailat da gudu Yar gidan Anty Samha tazo da Kaya a Jakarta ta fado jiki na,dake mun Saba tana so na Tace Anty Wai kije Inji Mummy dinmu tana Kofar gida a cikin motarta sako zata Baki,Umma tana ji Tace Jeki kiji maybe yau Bata son shuguwa sauri takeyi,Dama nayi wanka naci kwalliyata cikin Riga da skert na lace ya min kyau matuka Dark green ne da pink,Dan siririn Mayafi na yafa na fita,na hango wata arniyar mota nasan dama tana hawa motoci,Ina zuwa na Balle murfin motar na Shiga nace Salamu'alaykum Anty Samha,Kofar naji an kulle garam ansa luck da sauri na kalli Driver sai Naga Ya Fu'ad ne,Sai da gabana ya fadi,Ya Fu'ad lafiya? Murmushinsa me tsada ya sakar min,wani yarrrr naji tsigar jikina ta tashi, nace lfy Ya? Shawara Zan Baki,Nace ta me Kuma? Karki auri Islam yaro ne bazai iya rike ki ba,Nace Ni Haka nake sonsa,Zan fasa Miki Baki ke Baki da kunya Zaki ce kina son wani a gaba na? Na Isa ne na Balaga na furta Ina murguda Masa Baki, Muna Haka Karaf sai ga Islam har ya wuce mu a tasa motar ta Gaban Glass ya hango tabbas mune,Islam ransa ya baci Yaja kwafa yace ko Dan na kuntawawa Fu'ad sai na auri Yarinyar Nan karshe Kuma Nima sai na wulakantata tunda Yar Iska ce,a ransa ya kulle irin wahalar da Zan Sha a hannunsa idan na Aure shi,da Kuma yanda zai kuntatawa Fu'ad.
Sai wurin Isha ya Bude min mota na fice abina,Ina fita Muka hadu da Islam ya kalleni shekeke a ransa yace karuwar gida,a fili yace yaushe Zan turo? Nace ko yaushe,hararata yayi a boye yace kin Amince? Nace ae ka turo,wata zuciyar tasa tana gargadinsa kar ya kuntata min Yana so na ba karya,Yana ta tunani har ya manta yace zai aureni ya rikeni tsakani da Allah,Allah sarki Islam mantawa yayi da komai yaci gaba da Nuna min soyayya Yana Yi min dinkuna ba karamin kashe min kudi yake Yi ba,Ni Kuma Sam bana sonsa da aure, Fu'ad shine kullum a Raina shine burina,Amma Ina kallo Abbi da Kansa tare da Yan Uwansa suka min wakilci tare da zuwa har kauyenmu wajen Affa,Affa yace kwandala bazai kashe ba suje ya bar musu Ni gaba daya,Abbi Haka Suka dawo aka saka ranar Aure na da Islam Nan da wata biyu,Islam sai murna yake yi,Ni kuwa kullum a bakin ciki nake,da dare nayi kuka na koshi,sai Shirye shirye akeyi tsakanin Umma da su Nene da Abbi,sai Islam dake doki Yana Murna,Momy Kam Tace wallahi tana Nan akan bakanta Babu Wanda ya Isa yasa Danta ya auri karuwar yayansa.
Fu'ad kuwa an daina ganinsa ma a gidan sai jefi jefi gaba daya baya hayyacinsa,Umma ta tambayeshi yace ba komai,Su Rabi suna Jin Labari Rabi ta kwala Ihu ta Dira tsalle tare da cewa karya ne Ina Raye Rumaila ta auri Dan gayu dangina karya ne,Ni ba a aureni ba a auri Rumaila karya ne,Kawai sai ganin Rabi nayi da Saude sunzo gidan da Ledar kayansu da yawa,Ga biki ya taho,Umma ta sa kullum sai naje gidan gyaran jiki,Ni ba son abin nakeyi ba.
Kullum Momy da su Khaleesat a Zagina suke ga su Rabi sun Karu,ga Son Fu'ad ya min yawa,ga matsalar dake tsakanina da Iyaye na,Naje makaranta na dawo karfe biyu,Momy a Compound ta tare Ni tare da cin kwala ta tana girgizani tana masifa da bala'i,Can Garden Kuma Abbi ya kawo masu karatun Qur'ani suna tayi zasu Yi sauka Wai Allah yasa ayi biki lafiya a Gama lafiya,Karatun da nake juyowa shi yasa naji kaina ya Sara Nan take na Kurma Ihu Aljanun da bani da su suka tashi,Ina girgiza na yage Hijab Dina na jefar na suri Momy Kamar tsinke nayi jifa da ita kanta ya daki jikin mota ta zube kasa sumammiya,idona yayi jajir Ina Ihu jikina Yana rawa,matan gida da Yan aiki Suka dauki ihu,Mazan gidan Suka yo kaina,Umma ta fito da Sauri, Fu'ad kuwa cikin Malam masu karatu ya taho da babban malamin,Islam ya fito da gudu,Ina ganin Malamin na Fadi kasa Ina birgima Ina wani irin Nishi,yatsan kafata ya rike babba ya shiga rero karatun Qur'ani,Wani Ihun nakeyi Ina birgima,Daga can malamin yace Kai waye?
Aljanin dake jikina ya fara magana Yana cewa sunana Salahu,Laifi tayi Mana me girma,Dan me zata kwara Mana ruwan zafi muna kwance muna Hutawa a makwararar gidansu,nazo Bara gidansu ta kwala min kwano tare da korata shi yasa Ni Kuma na shigeta na rigada na aureta Kuma wallahi sai Naga karshenta bazan taba fita ba.
Malamin yace yaushe ta zuba muku ruwan zafin? Aljanin yace tana shekara goma sun dafa taliya sun Tace Bata Bari ruwan ya huce ba ta zubo Mana Muna kwance dama Yan Adam Mata da yawa suna Mana Haka Basu San wajen hutawarmu bane sai Kawai su dinga sheko ruwan zafi Basu Bari ya huce,Nazo Ina Bara a gidansu na fito a siffar mutum yaro ta karbi kwanon ta kwala min a kaina shi yasa nace sai Naga karshenta Kuma wallahi bazan barta ba,duk Wanda ya aure ta ya auri masifa har danginsa ta Zama tawa,Nine na Sadu da ita,Islam najin Haka ransa ya baci kishi ya taso Masa yace Malam yanzu ko an daki Rumaila wa aka duka? Malam yace Aljani ka daka,Zumbur na Mike da Muryar Aljani nace au fada zakayi da Ifritu to Bismillah,Islam kishin Aljani ya sadu da matar da zai aura Fu'ad Yana rike shi Yana Karfa ka dake ta Islam,Malam Yana Kai Islam saurara Amma Islam Iya karfinsa ya samu ya zage ya Kai min Uban naushi sai da na tashi sama Zan fado kasa Fu'ad yayi sauri Allah yasa kusa da shi na taho Zan Fadi ya cafeni a jikinsa,Lokacin da Islam ya Kai min duk tunaninsa Aljani ya daka lokacin Kuma Aljani tuni yayi tafiyarsa ya barni aci ubana,Ina faduwa Aljanin ya dawo jikina ya shige abinsa yayi luf yasan Wanda ya aureni ya aurarwa Kansa masifa,Ni kuwa Suma nayi jini ta Hanci ta Baki,Dan rashin Imani su Khaleesat murna sukeyi,Suka kwashi mamansu sukayi asibiti,Islam ko ta kaina baibi ba yayi tafiyarsa wajen Momy dinsa Yana Bata Hakuri Yana cewa na fasa aurenta Momy bazan auri Aljana ba,Momy data Suma Nan take ta wartsake tana Jin dadi.
Abbi Yana dawowa Islam yaje yace ya fasa aurena,Abbi ya kada ya Raya Amma yace Sam baya so na yanzu,Ni kuwa Ina can Tuni Fu'ad yayi Hospital Dani Yana ta shara gudu,agajin gaggawa aka bani,Abbi ya bimu Asibiti daga baya shi da Umma,ba abinda likitoci Basu Yi ba akan na farfado Amma babu alama,Umma tana kuka Tace Kaine duk ka jawo wannan abin Fu'ad da ka amince da tashin hankali Bai samu Rumaila har aljanunta sun tashi ba, Fu'ad Hawaye ya zubo Masa karon farko yace Umma wallahi Ina sonta,Abbi ya kalle shi yace shashan banza,na fasa aurawa kowa Rumaila ko ta warke ta samo wani Mijin da kanta ta kawo, Fu'ad yace Please Abbi Zan haukace,Abbi yace ka Dade baka hauka ce ba ka dage ka nemi soyayayyarta,tana sona Abbi,Inji uban wa? Sai ka Bari na gani da Ido na, Fu'ad yace to zaka gani Abbi, Umma Tace Dan Allah karku damemu da wata Soyayya Rumaila tana wani Hali kana ji Doctor yace sai tayi kwana biyu ko Uku Bata farfado ba Kuma zata iya wucewa Kiyama, Fu'ad yace Wlh idan ta mutu sai na daure Islam har abada ya dakar min Mata
Abbi Yana takaici yace rufe min Baki.
Karshen Free page.
AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈
NA KUDI NE
DUK WACCE TA FITAR MIN DA NOVEL DINA ZUWA WASU GROUPS ALLAH YA ISA BAN YAFE BA, A MADADINA DA DUK WACCE TA SIYA TSAKANI DA ALLAH AKA CI AMANAR FANS DA WRITER NI ASMABAFFA AKA FITAR MIN TO
ALLAH YA ISA
KUMA DUK WACCE TA GANSHI TA KARA TURA SHI ZUWA WASU GROUPS DA WANDA TA GANI BATA SIYA BA TA KARANTA KUMA TASAN NA KUDI NE AMANA AKA CI BAN YAFE BA,
SABO DA DUK WACCE TA SIYA BA IYA KUDI BANE SAI DA AKA AJIYE YARJEJENIYA KAN BAZA TA FITAR BA,TASAN DOKA TA KARYA,KO ADMINS MASU SON BIRGE MEMBERS NA GROUPS NASU SAI SU SIYA SU DINGA TURA MUSU,KU SANI AKWAI CIWO DA HAUSHI KUMA BAMU YAFE BA WALLAHI.
DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM.
41-45
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne
Maman Dee
Fatimamusasamaru
Balkisu
Mmn Saddeeq
Dr Zainab Abdullahi
Maryam Yamai Aliyu
A zaune Fu'ad yake gefen gadon da nake kwance ya tsura min Ido Kamar zai Hadiye Ni,sai yau ya taba min kallon tsaf a Nan ya gano lallai ba karamin kyau ne Dani ba, Allah yayi baiwa a Nan haka ya furta a ransa,a hankali ya furta Allah ya tashi kafadu Yar gidan Iyanta,Umma Tace me kake cewa? Istigifari nayi ya furta Kawai,Sallah ma da kyar ake tashin Fu'ad yaje yayi,har dare Yayi Umma Tace to ya kamata ka hakura Haka kaje gida sai gobe ka dawo,abinci Kuma su Tasalluwa zasu kawo da komai munyi waya, Fu'ad yace kije dai Gida ke Umma ai Ni ke nake Shirin fadawa ki tafi gida Har na Kira Driver zai maida ki gida,Kaga ban son shirme Ina ka taba ganin Namiji yayi jinyar mace? Gashi Zaki fara gani Umma,Abbi ne ya shigo da kayan shaye shaye na Lemuka da Fruits yace Kai Fu'ad taho mu tafi,Zaiyi magana Abbi ya daka Masa tsawa tashi nace baka da kunya ko? Kabi ka Raina mutane,Mikewa yayi Yana turo jajayen labbansa Yana tafiya Yana kallon inda nake a kwance Haka yabi Abbi dole Suka fita,Key din mota Abbi ya Mika Masa gashi ka tuka, Fu'ad ya kalli Abbi yace Ashe Allah yaji kan mu Allah Zan Shiga cikin Trailer Abbi gwara ka tuka Kawai idan Kuma kana so mu tashi gobe a kabari to na tuka mota,Abbi Baki Bude yace Bani mukulli tunda Kai ka haukace ma naga alama.
Tunda Abbi yake tuki Yana ta yiwa Fu'ad hirar business da zai tafi Italy,Uhm... Kawai Fu'ad yake Iya bada amsa har ga Allah hankalinsa baya jikinsa,Yana wajen Rumaila har Suka koma gida Haka ya fita ya manta ko motar Bai rufe murfin ba yayi gaba abinsa sai Abbi ne ya Rufe Masa,Islam ne ya tari Fu'ad yace Yaya Fu'ad ya jikin Rumaila? Harara Fu'ad ya watsa Masa ba tare da ya bashi amsa ba ya shige part dinsa, Baba Jummai ce ta taho da gudu tana Murna a ranta Dan munafunci tana cewa shike Nan nasan ma Rumaila ta mutu ko Dan Momy Fu'ad?,ai nasan dukan da Tasha da kyar zata tashi baza ma ta tashi ba,Allah sarki gobe Muna da babbar janaza, Fu'ad ya kalle ta yace kece dai Zaki mutu tsohuwar banza ya banko kofarsa ya Rufe ya bar Baba Jummai tsaye a bakin kofa tana jinjina rashin mutuncin Fu'ad.
Tunda Fu'ad ya shige part dinsa Wanka yayi tare da dauro Alwala yazo ya gabatar da Sallar Isha tare da nafilfili Yana ta min Addua Allah ya bani lafiya sai wurin 1am ya samu ya kwanta a saman gadonsa cike da tunanin halin da nake ciki da Kuma rayuwa ta a gidansu ta Shiga dawo Masa tun farkon ganina a gidansu,tunowa yayi ranar da ya fara gani munzo daga Kauye yana rungume Yan Uwansa na wara Hannaye Ina cewa muma ayi Mana,Dariya ce ta kwace Masa ya murmusa Yana cewa Allah sarki da na sani nayi mata,part dinsa Dana gyara Masa yace sai na maida Masa kurarsa ya tuno,Juyi yayi a saman lallausan bed dinsa yace Ban kyauta ba,Haka ya dinga tunano Rayuwata a gidansu wani wajen yayi Dariya wani wajen ya tausaya min har yazo lokacin Dana fadawa Abbi na amince Ina sonsa,shi Kuma yace Bai shirya ba,Nan take yasa Hannayensa biyu ya Shiga yamutsa gashin Kansa me santsi yaja tsaki Yana Jin haushin Kansa,ranar da kyar ya samu bacci ya dauke shi.
Da sassafe Yana Idar da Sallar Asuba tare da Azhkar wanka yayi ya shirya tsaf cikin jallabiya Brown Yana bulbula kamshi tun da sauran duhu duhu a gari ya shiga mota ya bar gidan sai asibiti,lokacin Umma ta Idar da Sallah tana Azhar Kawai sai Sallamarsa taji ya shigo,da mamaki Tace Fu'ad kaine? Ae Umma Ina kwana ya me jiki? Lfy Alhmdllh ta amsa tana cewa Wai Kai Fu'ad meke damunka ne?ko gari Bai Gama wayewa ba,Shuru yayi ya nemi waje a gefen gadon da nake kwance ya zauna,sai da ya tabbatar Ina numfashi sannan ya samu bacci ya fara daukansa sai gyangyadi yakeyi a zaune Umma Tace karka fadawa maralafiya a kanta ka karasata kana gyangyadi tashi ga Empty Bed can kayi baccinka a can,Bedsheet Umma ta shimfida masa a gadon da ba kowa dake private Hospital ne Kamar wani Hotel sabo da kyau ko Ina Yan kamshi da sheki,Kwanciya yayi kamar marar lafiya sai bacci ya kwasheshi,Likita ne ya shigo Yana shigowa yayi tunanin Fu'ad wani patient aka kawo yace ya akayi aka hada patient biyu a room daya Hajiya kina kallo baza kiyi magana ba,ki sanarwa masu kula da su,Umma Tace Dana ne fa tare muke Doctor Bai Jima da zuwa ba bacci ne ya dauke shi baka kula sosai ba Fu'ad ne fa, lokacin Doctor ya lura yayi Dariya sannan yace ai ban sani ba Ashe Oga ne,Murmushi Umma tayi,Doctor ya Isa kaina ya dubani tare da zare min Drip ya min wata Allura ya fita.
Bacci Fu'ad yake Yi sosai wanda sai da ya gaji Dan Kansa wurin 12pm sannan ya tashi lokacin an kawo abinci iri iri,Masallacin dake Hospital din yaje yayi Sallah sannan ya dawo Umma ce ta takura Masa sai yaci,Haka ya zabi abinda zai Iya ci yaci,Basu Dade da Gama ci ba Na fara motsi a hankali na motsa tare da Bude idanuwa na a hankali Ina bin dakin da kallo,Basu san na farka ba sai da suka ji Nace Salamu'alaykum Umma sannan suka juyo da sauri tare da rige rigen zuwa ida nake,ban San me ya faru da Ni ba Ina iya tuna Lokacin da Islam ya Naushe Ni sabo da lokacin hankali na Yana jikina,Kafin nayi tunanin komai Umma ta Kama Ni na tashi toilet ta raka Ni Brush nayi sosai tare da yin wanka na fito Fu'ad ya tafi Kiran Doctor,Har Umma ta bani wata doguwar Riga me siririn Hannu Yar kanti Bata da nauyi,Bayan na saka nace Yunwa Umma,Abincin ta zuba min tuwon danyar shinkafa miyar Egusi ga farfesun kaji a gefe,Ina Ci ya Fu'ad suka shigo tare da Likita,Doctor yace lallai jiki yayi kyau,Ya tambayeni Ina ke min ciwo nace Babu lafiya nake jina,Kawai wajen makoshi na Inda Islam ya nausa ke min ciwo, Wasu magungunan ya ru buta Mana, Fu'ad ya karba yaje ya siyo ya dawo lokacin na Gama cin abincina na wanke Baki na,Umma Tace to Alhmdllh Rumaila Bari naje gida nayi abinda zanyi ga Fu'ad Nan zuwa Yamma Zan dawo,To Umma na furta Ina Wasa da yatsu na gaba daya kunyar Fu'ad ce ta hanani sakewa,mugun kwarjini yake min ga kamshi ya gama tafiya da Imani na,a hankali nace Islam Allah bazan yafe Masa ba,ace Mijin da mace zata aura tun Ina budurwa Yana dukana Haka Ina ga anyi aure sai kace a film din China,wani kongfu ya min sai kace ya samu Jettly,Umma tana hada Kaya Tace kiyi hakuri shima bada saninsa yayi ba.
Kayan Dana cire Dana abinci Umma ta tattara ta kwashe Driver ya dauketa Suka tafi,daga Ni sai Fu'ad,ko kallon inda nake baya Yi sai latsa wayarsa yakeyi Yana murmushi shi kadai Ni Kam Kallonsa nake Yi kamar Zan cinye shi Haka nake ji,Uwar kallo Daina kallo na Haka,naji ya furta ba tare da ya kalle Ni ba,da sauri na dauke kaina gefe Amma ban San Sanda na sake dawowa da kaina dai dai ba Ina ta Kallonsa,Ki Fadi soyayyarki ki daina Bata lokacinki,Murmushi nayi nace ai Ni sai Islam,da Alama Baki San meke faruwa ba ai tuni Islam