Showing 54001 words to 57000 words out of 115153 words
ya fasa,Da Sauri nace dan Allah da gaske ya fadawa Abbi ya fasa? Fu'ad yace da gaske,Dariyar farin ciki ce ta kwace min nace siyo Mana Lemuka muyi partyn Murna yanzu,Gasu Nan Abbi ya kawo kala kala,To a jera su,Empty Bed din da yayi bacci a Kai ya jawo Gaban mu ya shirya Lemuka da ruwa kusan kala goma,yace saura abin ci,Waya ya Kira tare da yin Order Abinci na Yan gayu,15mnt sai gashi an kawo abinci kala Uku masu shegen dadi na turawa Nan ma na jera su Muka zauna a gefen bed daya gadon Yana Gabanmu da kayan ci da Sha.
Abbi ne ya turo kofa yaga abinda Muka shirya Mun saka a Gabanmu,da sauri Fu'ad ya shiga cewa Happy Birthday to you,ku Kuma lafiya wannan tarkacen fa? Ina Ina na fara uhm....B... Birthday na ne yau,Allah ya kyauta ya jikin? Abbi ya tambaya,da sauki Alhmdllh,Ina wayancewa Ina kwashe Lemuka da sauran kayan ci,kwana biyu nayi a Hospital aka sallamemu,Duk abinda ya faru lokacin da Aljanuna suka tashi akwai a Wayar Khaleesat ta dauka a waya har dukan da nayiwa Momy,a garden suna Zaune da Safna sai Momy,Khaleesat Tace Momy kinga komai na Yarinyar Nan akwai a wayata da shi zamuyi amfani mu Kira Mata Yan Sanda,Kamowa tayi ta nu na musu,Momy tace kinga yanda tayi cilli Dani kamar Buhun auduga lallai Yarinyar sai ta ci malafar Ubanta har yanzu kugu na ciwo yake Yi saura kadan Lakata ta tsinke,Suna zancen Fu'ad yazo ta wajen Yana jinsu,Sai ya share tare da kwalawa Khaleesat Kira,Da Sauri ta nufi Inda yake,muga wayarki Zan dauki number Fadila,Bata kawo komai ba ta Mika Masa,Yana karba ya lalubo video din data dauka Ina Aljanu ya tura a wayarsa sannan ya goge na Wayarta gaba daya tare da Mika Mata Wayarta,harda tambaya kaga number din? Ae Kawai ya furta ya wuce abinsa,Ina zaune a Palo Ina kallo sannan ga littafin English a gaba na na Gama Assignment Dina,Yana shigowa saman 2seater ya zauna tare da yin wani Zama kana kallo kasan kudi ya ratsa shi,Muryarsa na tsinta yace zo ki ga wani Abu, Carbin dake Hannuna na ajiye naje inda yake zaune ,zauna ya furta,gefensa na zauna ya danno min video din da na daki Momy,Ina kallo na zaro Ido har Adduar da Malam yayi min da Maganar Aljanin,Ina kallon Dukan da nayiwa Momy na kyalkyale da Dariya tare da tafawa kaina nace Wow Wallahi na godewa kaina,Weldone Rumaila Weldone ,Sabo da murna ban San Sanda na sakalo hannu na a wuyan Fu'ad Rabin jikina gaba daya a jikinsa,na shako shi sosai tare da lankwaso wuyansa Ina ta dariyar dukan Momy da nayi.
Duf nayi ganin yanda Malam yake min Ruqiyya suna magana da Aljanin dake jikina naji tsaf duk Abinda Aljanin ke furtawa,Tashi nayi da sauri Raina a bace na dauki carbi na tare da Zama na kalli gabas na Shiga Jan carbi Ina cewa Allah ya Isa Aljani Salahu,Allah ya Isa Salahu,Allah ya Isa Salahu Haka nake ta fada Ina Jan carbi, Fu'ad Dariya ce ta kamashi yace karki damu Yan Mata zanyi manage da ragowar Salahu,Duk da ya rigani Jin dadin wajen ya za ayi,Ashe Dan Iskan Nan ne ya fito Miki a suffata ya cuceni duk ya Bata min suna a wajen mutane,Kai Nima nace Allah ya Isa Aljani Salahu,Dariya nakeyi nace munafuki harda laulayi na dinga sheka amai da yawu,To Kira Iya a fada Mata ko ta hakura ta yafe miki cewar Fu'ad,Nace tsaya na Gama jawa Aljani Allah Isa ko cikin carbi ce,Ki lallaba shi kina ji yace duk Wanda ya aure ki ya auri masifa,Ni kuwa Haka zanyi ta maza a daura Dani mu Kara Dani da shi,Wayata na dakko na lalubo number Iya tare da kiranta,naci sa'a naji ta daga sabo da kar ta kashe idan taji muryata,ban Mata bayani yanda zata Gane ba kawai nace Iya Salahu
Ne ya min ciki,Kya fito ma ki Fadi gaskiya ai sai kije wajen Salahun ya aureki,ba mutum bane Iya Aljani ne,Karyarki tayi yawa Ni Zaki dinga rainawa hankali kince babu ciki yanzu kin dawo kince Salahu ne,Tsaki Iya ta ja tare da kashe Wayarta Ina cewa Iya ki tsaya kiji Amma Ina.
Baba Jummai ce ta shigo tana Galla min Harara ta ganni kusa da Fu'ad Tace Ashe kin dawo Baki mutu ba,ai nayi tunanin wannan dukan da kika Sha sai dai ki farka a lahira,Nace to kwana na Bai Kare ba sai ki kashe Ni da kanki,kar dai ki min rashin kunya dama Sannu nazo na Dan Miki Kuma tunda ke fitsararriya ce na fasa tayi tafiyarta,Nace Lallai tsohuwar Nan duk mutuncin da na Mata Bata gani ba Ina kallon take takenta tun da dadewa haushi na take ji, Fu'ad yace kyaleta Watarana korarta zanyi da kaina daga aiki,yawwa kayi Mata sanadi abincinta ya Kare.
Bayan Sallar Isha Ina kitchen Fu'ad ya shugo sanye cikin Riga Armless sky da wandonsa dogo yayi kyau sosai,Kamshinsa yasa nasan yazo Amma ban juyo ba,Hannayensa ya ware Kamar zai rungume Ni harda tsayawa daf da Ni kamar zai rungumeni ta baya,A hankali yace kamar na rungumeta a haka,da sauri na juyo naji kamar Yana magana kafin na Kai ga juyowa cikin zafin nama ya juya tuni ya kalli kofa kamar Bai San Dani ba,Aiki na naci gaba da Yi,Jelar gashi na ya taba da yatsansa Guda daya yanda bazan ji ba, Hips Dina ya kalla tare da cije lebensa na kasa,kafin na juyo sai Naga ya juya Yana latsa waya kamar Bai ganni ba.
Sake matsowa yayi daf Dani nayi sauri na juyo Dan na kamashi Amma sai na hade da jikina da nashi, da sauri ya matsa gefe harda masifa tun dazu kike so sai kin rungume Ni na matsa kin matso na matsa kin matso Haba dole sai kin Sa na dauki zunubi me yasa kike so nane da yawa Haka? Ance ki fadi gaskiya kinki,Baki na saki Ina Jin sharrin da ya Yi min, Palo ya koma ya kwanta Kamar Wasa bacci yayi gaba da shi dama sarkin bacci ne,Fitowa nayi dauke da plate din Fruits,a gefe na ajiye plate din a hankali Ina Sanda na karaso gabansa tare da tsugunawa a saitin fuskarsa Ina Kare Masa kallo Ina wani murmushi,Gashinsa na taba kadan a Raina na furta laushi,wuyansa na karewa kallo wani lumi lumi a hankali na shafa wajen,a hankali ya bude idonsa Wanda cike yake da bacci,na kalle shi da kunya nace tururuwa ce take maka yawo a wuya shine na cire maka,Idanuwansa ya maida ya rufe yace maida min da tururuwata dadin yawonta nake ji a wuyana,ya Riga ya ganeni,naci gaba da Masa tafiyar tsutsa Ina cewa tururuwa ki sauka idan ta maka Kashi a wuya ba ruwana,Umma ce ta shigo da Sauri na koma cewa ka tashi na yanka Fruits din tun dazu nake ta tashinka,Umma ta harareni Tace kya Gama gulmarki marar zuciya, shi kuwa harda yin shuru Wai yaci gaba da baccinsa.
Iya a zaune take saman kujera a tsakar gidansu sai fushi takeyi Taki kula kowa ko Baki ne suka shigo Bata musu magana,Ali Shagali ne ya shigo Iya ta bishi daki Tace Ni fa na fada maka ko Tv ko saki,Nima kayan kallo nake so ka siyo min,bani da kudi bani da inda zan samo su,idan na siya Miki Kayan kallo ita abokiyar zamanki Kuma tayi ya?dole sai na siya muku tare,to ba kayi kudi ba Ni Kawai ba ruwana Malam TV Kawai,Me shayi bakin cikin Halayen Iya sun dame shi yace Jeki gida sai neme ki kin dame Ni na gaji,naji Kuma Zan tafi gidanka din banza mene ciki Banda talauci, me kake da shi,Naji kije sai na nemeki,Zaka zo neman Nawa ne wlh baza ka ganni ba,Iya kayanta ta kwasa da yawa kishiyarta tana kallo tana ta Mata Dariya,Iya Tace kin wa Uwarki Dariya,Uwarki me Dambu ita kika yiwa Dariya ba Ni ba,me Shayi Iya ta gallawa Harara ta fisge dubu daya a hannunsa wacce ya fito da ita zai Aiki yaro ya siyo musu kifi soyayye zasu ci abinci Amma Iya ta fisge kudin tace sai dai ka dakko wata tayi tafiyarta gidanta ko gidan yayanta Malam Haruna bata nufa ba,gidanta Wanda ya kusa ruftowa Nan Iya ta koma da kayanta.
Baba Jummai ce ta fito kitchen dinsu na masu Aiki tana cewa Tasalluwa kije bangaren Umma kiga Yan Wutar Sakata suna can suna ta bariki a bainar mutane Rumaila da Fu'ad,ai gwara su da ke tunda ke ma cewa kika Yi Hotel Zaki Kama idan kina da kudi Daki permanent ki samu Ana kawo Miki gayu kina biyansu kudi,ba gwara su dake ba cewar Tasalluwa Baba Jummai Tace ke dama Tasalluwa ai munafuka ce Wai ke ta Allah ko? Zaki gani,Ana Haka sai ga Fadila Niki Niki da Kaya tare da Rabi,Ni na manta ma Rabi tana Abuja Ashe gidan Fadila aka tura Rabi ta tayata aikace aikace,sai ga Fadila ta rike Rabi tam ta shigo tana rusa kuka,Itama Rabi tana kuka ko me ya faru oho,Momy dasu Safna sune Suka fara damkar Rabi tare da rufe Rabi da duka Tim Tim Rabi tana Ihun kuka tana bada Hakuri,Momy Tace kin kashewa 'yata Aure shegiya bakar jaraba,gashi Nan kin jawo ya saketa biki ko shekara ba a ayi ba har an sako ta ji kake tas...tas Ana ta kashe Rabi da Mari,sai da suka yiwa Rabi dukan kawo wuka sannan suka fatalo ta tsakar gida tare da kayanta, Bangaren Nene tayi tana rusa kuka,Nene Tace lafiya me ya faru? Rabi tayi mukus tambayar duniya Rabi Taki fada sai Momy ce tazo Tace ai baza ta fada ba munafukar banza Wai Haka Kawai ta fashe da kuka Tace Mijin Fadila ya mata fyade,shi kuma ransa ya baci yace ta kawo wata tayi masa sharri sabo da Haka ya saki Fadila su tattara su bar masa gida,Nene Tace Subhannallahi ke Rabi ya Haka? Rabi tana shesheka Tace na Rantse da Allah Fyade ya min lokacin ta tafi unguwa gidan biki ya bani lemo na Sha shike Nan nayi bacci sai Farkawa nayi na ganni a dakinsa ya min Fyade,kwana Uku Ina fada Mata ta bincika sai tayi son zuciya Tace Zanwa mijinta sharri......Rabi ta sake rushewa da kuka,Sanda taga kullum sai nayi kuka shine ta tambaye shi ko da gaske ne shine yace ya sake ta anyi masa Sharri.
Ni Wallahi da na sani bazan taba zuwa birnin Nan ba gaba daya tsinannu ne na cuci kaina,dama zuwa nayi Nima na samu wani Saurayin a gidan Nan ya aure Ni kamar yanda Rumaila ta samu Ina bakin ciki ace ba Ni bace za a aura tunda nice ma Yar Uwar gidan Nan Momy tace naje na dinga Taya Fadila Aiki,dama tunda naje mijinta sai yayi ta kallon duwawuna Yana mintsina min Ido daya,ko idan tana daki sai ya fito inda nake yayi ta shafa min kafata,dama wallahi kwarto yarki ta aura Kuma ba Dan Allah ya aure ta ba Dan ya biya bukatarsa ne gashi Nan idan da Dan Allah ne ai bazai saketa ba,Kuma wallahi Alo tsiya Alo Danja wallahi sai kin biya Diyyar fyaden da aka min ai kece kika jawo,Rabi ta furta tana nuna Momy da yatsa.
Momy Tace kashe ki akayi da Zan Biya Diyya,Diyyar Ubanki Zan Biya?kwadayi da bakincin Rumaila shi ya kawoki ga shi kin jawa kanki Hassadarki ta jawo Miki,Rabi ranta ya baci dama Rabi Bata da kunya ko digo ga masifa,kirji ta turo gaba ta hade kirkinta Dana Momy sabo da Momy ba tsayi Rabi akwai tsayi shi yasa ta jijjiga kirjin Momy da nata Tace Sanda kika moreni Harda turani nayiwa yarki bauta Ubanki kika bani?ko kin taba min kyauta? To wallahi bazan koma Kauye ba ko ciki na samu sai na haife muku a Nan matsiyata,Momy Baki Bude take kallon Rabi,Mama ta shigo da Iyayinta Tace to mutan Kauye ga kwadayi wa ya kawo ki? Rabi Tace Uwarki ta Zamfara ta kawo Ni,Mama ta zaro Ido ta tuno Rumaila duk abinda suke Mata Bata taba zaginsu ba,Amma Rabi zagi Kamar ta samu yara kanana Haka take zura musu son Ranta,yarinya Karama ta zazzage su ko sun rama Basu fanshe ba,Shigowa nayi na iske su a Haka Rabi tana ta zaginsu,Wani Bowl na roba da cokali na dakko a kitchen na fito Ina kadawa Ina Waka ku chasu arna ku chasu ku chasu ba Mai Raba ku Ina ta dariya,Su Momy Suka ja jiki Suka koma bangarensu da mamakin yanda Rabi ta zage su,Nene Kuwa Kora ta tayi tana Baki da kunya ko Rumaila,Kiran Abbi Nene tayi ta sanar masa a waya,Wani yaronsa ya turo da wuri ya dauki Rabi zuwa Asibiti akayi bincike Allah yasa ba komai a tare da ita sannan Likitan ya samu dai ya Mata Allurai Wanda zasu wanke mahaifarta koma mene zaiyi waje gudun kar a samu matsala,sai lokacin Hankalin Rabi ya kwanta,Amma duk da Haka Bata kulani Kuma duk gidan Nan Bata kula kowa sai Nene sai Abbi.
Shi Kam Abbi Mijin Fadila yake ta Kira a waya Amma yaki dagawa ma bare ayi wata magana.
Ina zaune a Garden Ina karatu sai ga Fadila ta taho da sauri ta buya tana waya da mijinta tana rokonsa tana cewa Dan Allah kayi Hakuri Honey,kasan Ina sonka wallahi Zan gyara Zan dinga baka kulawa na daina abinda nake yi,kaga makiya suna ta min Dariya yanda ka sake Ni da wuri sabo da Allah ace ko shekara banyi ba ka sake Ni,Mijin yace Ina ruwa na wanne irin fada ne ban Miki ba sai da kika jefa Ni a masifa na murkushe Yar mutane nayi Mata Fyade a banza kin cuceni,Fadila Tace Honey ka dubi girman Allah na rufa maka asiri har yanzu naki yarda na Fadi cewar Kaine kayi Mata Fyade,Yarinyar ma an kaita asibiti anyi Mata wankin Mahaifa Bata da komai naka,yanzu Ni Zan gyara, sau Nawa kake so kullum ka dinga Sex Dani? Mijin yace Sau biyar sau hudu sannan idan zanyi baccin Rana dole ki kwanta kusa Dani ko baza kiyi bacci ba dole sai kin kwanta a jikina,Sannan kafin nayi bacci ki dinga lashe min kunnuwa na, Ina Jin komai ina ta boye dariyata ban San Sanda na saketa ba,Ashe duk Wayar da Fadila takeyi tayi shuka a idon makwarwa Ina ji ita tunaninta sirri takeyi,da sauri ta kalli inda nake daf da ita ga waya a Hands Free,nace ke Fadila Ashe maye kika aura harda lasar kunne? Duk a jikin nasa a rasa inda Zaki dinga lasa sai kunnuwa,Zanci Uwarki wallahi Ashe kina Nan munafuka,to Ni na kawo ki kece Baki ganni ba hankalinki Yana can kina ta zubar da ajikinki kina bin Namiji ya dawo da ke,dama laifin da kikeyi kenan? Bakya bashi kayan Aiki kin jawo yayiwa Rabi Fyade Ashe Hariji ne,Oh kalle shi a Riga Kamar salihi Ashe Terror ne,Kai na cikin waya kayi Hakuri har Bayan keyarka duk zata dinga You turn daga kunne zuwa keya tana lashe maka, Allah yasa ba kurajen aski ko Almajiran keya a kasan keyar taka,Fadila kaina ta yo zata dukeni na Mike da Littafi na nayi ciki,Lokacin akace Abbi Yana Kiran kowa na gidan a palon da ake Family meeting,Ina Jin Haka nace na kusa Zama Amaryar Fu'ad shike Nan Aure na ya taho ai taron Abbi baya wuce hada Aure,har kwalliya nayi nasa Kaya masu kyau Wani material doguwar riga dark Brown nayi kyau karshe,tare da Umma muka Shiga palon,Ina ta washe Baki na kalli Islam na daga masa Hannu nace baka da Rabo a gidan duniya sai dai ka Tara a lahira,ba Wanda ya Gane me nake nufi,Tsallake kowa nayi na koma kusa da Fu'ad na zauna nace yawwa a Nan zanfi iya bada amsa.
Rabi ta harareni da su Momy,Fadila Tace wallahi sai na Kai kararki bari Abbi ya shugo,Rabi Tace Ni Kuma zanyi tonon silili ba,nace Ni Kuma Zan tona Miki asiri ba kin San halina,Umma ce ta harareni nayi shuru idan na kalli Rabi sai na kyalkyale da Dariya kasa kasa,Kamar abin arziki nace Rabi Ashe Sharing kukayi Kuma? Rabi Tace ke kika San wani Shiyare(Sharing)Ni Zaki Nunawa Boko yaushe kika daina cin zogale da Rama har Zaki Raina min wayo,Abbi ne ya shigo da Sallama muryata tafi ta kowa fitowa wajen amsa Sallama,nace ko watan gobe ne ko watan jibi ne bikin nawa oho,Allah yasa asa bikin watan daf da babbar Sallah naje nayi ta suya a dakin Mijina,nasan ma Sa ko Raguna Biyar zai yanka min tunda da kudi, Fu'ad Yana ji Ina magana Kamar kunkuni nakeyi Bai Jin me nake cewa,Ai kuwa da Sa ne Za'a fi samun nama me yawa,Umma a Bata Cinya daya,Na aika da Cinya biyu wajen Affa can Kauye,Iyata na Bata hakarkarin sa,Sauran Kuma ya ishe mu sai Wanda za a bawa talakawa su tsotsa Suma,nace Kai Sa daya yayi kadan Ina lna laifin Sa da Rago biyu,Abbi ne yace wace ne take ta kunkuni sai humhumhum...Kawai muke ji ayi shuru zanyi magana,Shuru nayi tare da nutsuwa sosai.
Sharhi fans Dan Allah
AsmaBaffa.
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈
NA KUDI NE
DAN DARAJAR ALLAH FANS KARKU FITAR DA NOVEL DIN NAN DAN ALLAH.
DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM.
51-55
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne
Maman Saddeeq
Ilham
Mrs Chief Ban
Ina zaune bakin Bed Ina tuna halin Rabi data canja kamar ba ita b Rabi itama tabi layin su Momy Dan Rashin zuciya Bata saurari bikin ba musamman data ji Ana