Showing 3001 words to 6000 words out of 115153 words
muka Gama zagaye muka dawo Wanda yaran Iya basa zuwa ko sunce zasu Zo basa zuwa karya sukeyi basa taimaka Mata da komai sai in taje a bamu Dan abinda ya samu,kowa yasan Aure Auren Iya ba Wanda ke damuwa.
Wace ce Ni Rumaila?
Mu Asalin Fulanin Yola Adamawa ne Amma rayuwa da tashi irin na Fulani Babana Ahmad Wanda aka Fi sani da Amadu dukkan Danginsu kakanni Jigawa state Suka dawo tare da shanunsu da dabbobinsu karkashin Birnin kudu rigar Manu,Babana Ahmad su Uku ne a wajen Iyayensu Ahmad shine Babba sai Sulaimanu sai Kuma Autarsu Rafia,Iyayensu da kakanni basuyi tsawon Rai ba Allah ya karbi rayuwarsu sai Yan Uwansa Sulaimanu da Rafia,Bayan Auren Rafia wurin Haihuwa ta rasu Suka koma daga shi sai kaninsa,Sunyi karatun Addini sosai sannan suna kula da shanunsu na gado shi da kaninsa har sukayi Auren fari tare rana Daya Affa na Ya auri Matarsa ta farko uwar gidansa me hankali da hakuri Maryam Ana ce Mata Mairo,Shi Kuma Sulaimanu Kawu na ya Auri Aisha Ana ce Mata shatu itama ta kirki ce,tunda Affa yayi aure har shekaru Biyar Allah Bai bashi Haihuwa ba shi kuwa Kawu Matarsa har ta Haifi Yara biyu,ganin Haka yasa aka bashi Shawara da ya Kara Aure,Anan Kuma lokacin Iya ta fito Daga Hannun Muzammilu tana zawarci,ganin an tabbatar Hafsatu Iya tana Haihuwa sai Amadu ya Fara sonta ya nemi Aurenta Wanda lokacin ma an gaji da Daurawa Iya aure tana fitowa,mutane Yan tsirari Suka daura Auren Hafsatu da Ahmad,Bayan Shekara da Auren Iya ta samu ciki,Murna wajen Affa ba a magana,ko wata Uku Iya Bata Yi ba Uwargidan Affa Mairo itama ta samu cikinta,Basa kishi suna zamansu lafiya har Iya ta Fara Haihuwar Yarta kyakyawar gaske Fara tas ranar suna taci suna Rumaila,na taso cikin kulawa bulbul Dani wata uku tsakani Mairo itama ta Haifo yan biyu duka Maza ranar suna suka ci Hassan da Hussaini,Daga Nan Kuma sai karayar Arziki ta samu Affa da Kaninsa shanunsu Suka dinga mutuwa Daya Bayan Daya,noma ma idan Suka Yi ba Albarka matayensu Suka Fara Shan wahalar rayuwa ko wata Biyar ba ayi ba Iyata ta tashi masifa ita Bata Zama da talauci Bata gaji tsiya ba.
Babu irin Lallabata da Amadu baiyi ba Amma Iya Taki tace sai an saketa gashi Iyata itama Bata da wasu dangi Wanda zasu fada Mata ta ji,Daga Ita sai Yayanta Malam Haruna sai sauran dangi Yan Uwa dai Wanda Basu Isa komai a wajenta ba,Babu fada da Nasihar da Malam Haruna Bai Mata ba Amma Taki ji,Haka Ina Yar wata shida Iya ta kwantar Dani a tsakar Rana a tsakar gidan ta nuna Amadu da yatsa tace ga yarka Nan kuci talaucinku tayi Tafiyarta,Bayan ta tafi Mairo ta dauke Ni,taci gaba da rikeni Amma na dinga ramewa Ina cuta Dole Amadu ya Kai Iya Kara wajen Yan Sanda,Sai da Yan Sanda Suka ce ta karbe Ni za a biyata kudin shayarwa sannan Iya ta karbi Yarta tana murna baza ta shayar a banza ba,duk halin talaucin da Affa ke ciki Haka duk watan Allah sai ya kawo kudin shayarwa dubu goma,a Haka ma Iya masifa take Masa tana zaginsa Dole ya aika Mata da takardar sakinta har gida yaci gaba da biyan kudi,sabo da kudin da take karba Iya sai Taki yaye Ni a nono har na Kai Shekara kusan Uku Ina Shan nonon Iya taki yaye ni,anyi anyi Amma taki sabo da kudi sai da Yayanta Kawu Haruna ya ci mutuncinta sannan ta yaye ni.
Tana yaye Ni taci gaba da karbar kayan Abinci da kudin cefane a wajen Amadu na ciyar da Ni yarsa, ita kuwa Mairo lokacin ta Haifo Yarta mace ta Uku,ita Kuma Iya ta hango Darihu da mota kurkura tunaninta me kudi ne ta aure shi,sai da ta shiga gidan ta gano Ashe motar ma da bashi ya siye ta sannan tokar Wani company da suke tarawa a wani katon Rami ita yake satowa Yana siyarwa masu Gona suna Taki da ita,Company Yana ganowa suka kulle shi a prison lokacin Yana Prison Iya taje ta ci Masa mutunci tare da karbo takardar sakinta ta dawo,lokacin tunda tana morar Affa na shine ta rikeni a wajenta tana samun kayan Abinci Dana cefane.
Dalilin bacin ran da Iya ta jefa Affana ya tsane Ni baya kaunata tsakani na dashi sai Harara,idan naje gaida shi sai ya kore Ni da zagi tun bani da hankali har nayi hankali na daina zuwa wajensa sai Idan mun hadu a Hanya ko bazai amsa ba ina gaida shi,Bayan na cika Shekara biyar Arzikin Affa Dana kaninsa ya dawo,ganin Yana Wasa da Naira Iya ta koma zawarcinsa tana bin danginsa akan ya maida ta gidansa Affa yaki yarda karshe ma ya ci Mata mutunci,Daga Nan ta Hadu da Dauda me kantin Hatsi,shi Kuma a waje zai kashe ma kudi kana shiga Sabulun wanki sai ya gagareka,Ganin Haka Iya ta Fara tsiya sabo da ya sake ta Amma yaki sakinta har ta Haifi Jamila da Kubra tana yaye Kubra ta zube Masa yaransa ta dauke Ni,Nima a Dole take rike Ni sabo da tayi tayi Amadu ya karbe Ni yarsa yaki yarda shi yasa ta hakura duk Aurenta Dani take tafiya,gashi tana Dora min Talla ba ilimin Addini bare boko.
Shekarata goma sha Daya Buhari Wanda ke zuwa Lagos Cirani ta Aure shi tunaninta kudi zata ci,Ai kuwa ta tafi Dani,Idan Ina dakinta Ina Bacci sai Buhari ya dinga galla min mintsini sai dai taji na fashe da kuka an Rasa dalili Ashe Buhari baya son rike Dan wani Haka gashi da son Mata,Iya dai da son kudi gata da saurin samun ciki,Nan ma ta Haifi Yarta Sakina,Bayan Shekara Uku ta Haifi kabir, Da dare ta shiga Makwafta barka daga Ni sai Buhari Dattijon ya kulle Ni a dakinsa Yana Shirin Yi min Fyade Allah ya kawo Iyata ta dawo a Daren taci kwalarsa ta dinga durawa Uwarsa zagi Nan take ya sake ta,ta dauke Ni,Yaranta su Sakina suna kuka Iya ta zubar Masa da su a tsakar gida ta Kara gaba Dani,Iya Sam Allah Bai Sa Mata Wani damuwa da yaranta ba ta kanta kawai take Yi gashi halinta ya jawo min Mahaifina baya kula Ni bare ya siya min Abu ko na kwandala,ko wani abin idan aka bani nasan Mairo ce ta saka Shi yayi min.
Ko dinkin Sallah ba ko wacce Sallah ake min ba,Sam Iya Bata damu Dani ba kowa Yana damuwa da yaransa Amma Iya Bata iya dinka min Kaya sai Talla da aikin gida ba makaranta a jahilce nake,shi yasa watarana Sam bani da wayo bani da wani hankali idan nayi wani abin gwara tinkiya da Ni.
Gashi Kuma Allah yayi Ni da kyau da kyan sura ka rantse Ni nayi kaina,Fara ce Ni sosai da gashi na na Fulani ya wuce kafaduna Baki wuluk,Bakina pink Dan Karami ga kyawawan hakora na farare kanana masu kyau,Gira ta me yawa da cika,gashin Ido na Zara Zara ga Idon manya masu kyau,Fuska ta ba me tsayi ba ba Kuma me Fadi ba Yar cakwas,gashi kwantacce a gaban goshi na har Dan saje gareni yabi ta Bayan kunne na,idan Ina magana sosai ba sai nayi dariya ba Dimple Dina yake lobawa gwanin birgewa,kowa ya kalleni ko mace ce sai ya Kara kallo na bare Namiji,asararru kuwa yan madigo idan suka kalle ni sai yawunsu ya dalalo Amma baza su samu ba Allah ya shirye su, Kirar jikina me kyau Doguwa Dani da Hips Dina sosai,Ina da Dan jiki na Kuma ba me kiba ba baza a kirani da ramammiya ba,ko ta Ina na hadu cif cif sai rashin Ilimin da Rashin wayewa ga kauyancin masifa da gabanci Dan ma Allah yasa mu Fulani ba sanmu da Hi da Hya ba,Hausar ma tamu Bata fita sabo da fillanci ya Mana yawa,an San Fulani da kunya Amma mu sabo da jahilci tsagerun Fulani ne mu sabo da Talla idonmu ya bushe,Ina da kirki na sannan gani da tsoro ban fiye tsokana ba Ina Kuma da ladabi Ina girmama na gaba dani ba a fada Dani,Gani da fuska biyu idan Naga dama sai na Zama me kyan Hali na koma Ustaziya idan baka sanni ba sai na cuceka.
Kadan kenan gaba zaku ci gaba da Gane Rumaila.
Cigaban labari
Bayan mun Gama yawon gaida Yayyena da Kanne sai gidan Kawu Haruna Nan ya dinga Yiwa Iya Nasiha Kan ta zauna karta sake Fitowa daga gidan miji,Kawu yace wallahi kinji Hafsatu na rantse wannan shine aure na karshe da zan tsaya Miki idan Kika sake Fitowa Aradu sai dai kije Yan Hisba ko liman ya wuce Miki gaba Babu ruwana,Iya tace idan naji Dadi me zai sa na fito Amma idan wahala tasa ai Dole na yo waje,Sabo da kina Gadara kin gaji gidan Zama ko? Kina da gidan Zama ke da yarki ko? Kije kiyi duniya ce,Iyata ta girma sosai Amma Bata Jin magana Haka muka dawo gidanmu,Ko Zama bamu Yi ba sai ga Rabi,Saude da Hajara.
Rabi Tace yawwa dama zuwa nayi na fada Miki gobe ne tafiya Birni Inna ta Tace baza su je ba sai bikin Yan Matan gidan yazo an kusa bikin Anty Fadila da Anty Sakna,yanzu da Ni da ke da Saude zamu tafi,Nace Wai a wanne garin suke ne? Rabi Tace Habuja (Abuja) garin Shugaban kasa,Ita Kuma Maman Kano a Kano state state take tare da Yan aiki da Yara Mata su Hudu,Yanzu Ina zamu Fara zuwa? Rabi tace Habuja Mana idan biki yazo Kuma a watakil a Kano akeyi gidan Maman Kano sai mu je Kano mu Sha kallo ko?
Saude tace ai Dole na biku Yasin,Hajara tace Ina son zuwa Nima Amma Baffana yace sai Idan biki yazo sai na biku,Iya tace kuje ku yo mana kallo idan da Hali Rumailata ta samo Mana me kudi ko ta samu Aikin wanke wanke a can,kudin mota nawa? Rabi Tace a bata dubu biyu ma ta Isa idan zamu dawo zasu bamu kudin dawowa,Hajara Tace idan Basu Baku ba fa? Taya ake tafiya ba kudin zuwa da dawowa? Kuma zuwa Habuja za a kaiku a dubu biyu kamar zaku je Kaduna? Nace Motar Shanu zamu bi Tasha zamu je ga Yan cirani Nan ana loda su a motar Shanu trailer a Araha ake Kai su fa,Iya tace kwarai ai Rayuwa maleji akeyi yanzu.
mun Dade Muna Hira a Daren na tattara tsumman kayana gaba Daya sabo da kusan wata Daya zamuyi a can kayan nawa Basu wuce kala bakwai ba na shiryasu a cikin dankwali Dan kanti na kulle abina ,na saka Brush Dina da Toothpaste Dina Mymy Karami da Dan Vaseline Dina,akwai radio ta me Hannu Kamar jaka irin tamu ta Yan fulani Muna ratayawa Muna tafiya Muna Jin kida ko kunna gidajen radio ita na dauka da cassette Dina na kidan Yan fulani iri iri tare da Kidan su me bango,Garba sufa,ta Barmani choge da Dankwairo na zuba a cikin kayana na Bude gidan cassette me zare na tsohon yayi tun duniya na kwance itama Radio din taji jiki Tasha gwagwar Maya da kaina ma idan ta samu matsala gyarata nakeyi na San ta Kan abata,ta Kawu Haruna ce ya bani ita yace mune Yara matasa,sabo da Haka Duk labaran gidan radio baya wuce Ni nasan meke tafiya a duniyar,duk inda zanje Radio ta tana kafadata a rataye kamar jaka Ina tafiya Ina ji,a Haka nake zuwa Talla da ko Ina, labarin wasanni ma Ina jin komai na sani,da karatun Novels Ina saurara.
Washe Gari Ina murna da Sassafe nayi wanka na shirya cikin wata atamfata sharara da ita Goggo sha'u a ganina na hadu Riga da zani,Hannun rigar irin Na vest me Fadi kamar Yar rataya damatsana a waje ga Wuyan ya shake Ni,Na daura zani na tsangalalle kamar Zan Haura ruwa na daura dankwali na Dan kanti yasha guga da wanki na zamge kaina,Yau wankan Abuja ne na dambara jambaki paint pink ne yayi min Kamar Akuya taci dusa,Glass Dina Baki Dana siyo a kasuwa Dan glass din nawa me kana Nan gurbin Ido na saka abina irin shegun Nan ban yarda ba na Gama da Yan Abuja harda Glass wani Baki irin ba mutunci,Na tabbata da zaku ganni da Cikinku ya Gama kullewa Dan dariya.Kayana Dana kulle a Hannu na rike gayu zanyi bazan Dora a kaina ba,Radio ta na rataya sannan dama na Haddace number wayar Iyata nace Zan nemi waya a can na kiraki Iyata Ni na tafi Allah kaddara saduwar mu,aci Indomie lafiya Kuma Dan Ubansa Ali me Shayi ya soya Miki kwai uku kullum kinji Iyata,Iya Tace ja'ira Allah ya kaiku lafiya sai na jiki,Radio ta na rataya na kunna gidan radio Ina Jin shirye shirye na fice a gidan,Yan Gari sai kallo na akeyi suna Sha'awa su a ganinsu na Gama kure gayu,Wasu har Yar iska suke kirana Akan na saka glass Baki,Ni kuwa nace kunyi a banza na nufi gidan su Rabi.
Sharhi fans
AsmaBaffa.
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM
NA KUDI NE
Dari biyu 200 ne
Accnt number
0175487861 Asmau Garba Muhammad Gtbank.
Masu Tura katin MTN ko VTU ga Number
08033933642
'YAN NIGER ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39
Novels Dina na kudi ko wanne complt Dari Uku 300 ne.
RASHIN SA'A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDU'AR KAWA
GIDAN GWAURO/DAN NAZIA.
2
Page naku ne
AUNTY UMMAH
BEAUTY BOSS
NAFEESAT UMAR MUHAMMAD
MUMMY
REAL MAMAN WALEEDA
Rabi na Iske a gidan su tana fesa turare ta Sha lace dinta na Sallah itama duk ya wani jeme mu a wajen mu na gayu ne,Riga ce Doguwa me gajeren Hannu a makale Jikinta harda Aljihu a gaban rigar irin na Yan Talla masu zuba kudi a ciki,Rabi chocolate ce me haske kuma tana da kyau ba laifi,Itama Rabi kayanta a leda Viva ta zuba,Saude kuwa Atamfa tasa itama Amma Tata sabuwa ce ba laifi Saude Kam farin Glass ta kafta itama a Fuskarta idan ka kalle mu ba a magana Haka muka Yi sallama da Iyayenmu sai Tasha Koda Muka je Tasha motar Shanu muka Shiga cikin wahala ga mutane a cike Dam wani Kan wani Haka muka Shiga muma in Banda wari ba abinda motar keyi Amma Haka muka daure dake motar Bata sauri sai 5pm muka Isa Abuja,Taxi muka Shiga Rabi tasan gidan wata Unguwa aka Shiga me azabar kyau ta masu kudin ko a can ta daban ce unguwar,Wani katafaren gida Wanda za a iya kiransa da Gari guda shi muka tsaya muka biya kudin Taxi a Nan na sake gyara Glass Dina Ina ta kalle kalle kamar idona zai Fado,Wani wuri naga Rabi ta Danna a jikin gate din Nan take sai ga masu tsaro sunfi mutum biyar sun leko,Cikinsu wani ya gane Rabi Amma kafin ya Bude Mana sai da suka dinga sheka dariya Akan kallon da suka mana,Bana son dariya a duniya,Saude tace kwayi kwa Gama kanku ake ji,Daya cikinsu yace Rabi kune Haka ku shugo ya Furta tare da Bude Mana kofa, tun daga shigar mu na tsure da kyan gidan motoci ne na gagara a ko Ina,ga fulawoyi a ko Ina,gidan ya Hadu karshe part part ne ko Ina Yan aiki ne ke faman sintiri,mun saki Baki da Hanci Muna ta kallo,Muna tsaye mun kasa gaba mun kasa baya sai kallo mukeyi har Rabi Dake zuwan gidan,Yan aiki Muka hango maza da Mata duk sun firgita ko wacce tana tafiya suna dai daita Sahunsa suna cewa ga Abban Momy Nan ya dawo ku nutsu,Nan take Muka ga sun Nutsu sun jere a layi Kamar Wanda za a rabawa kudi.
Wasu Yan Mata da samari Yan gayu masu kyau Wasu farare wasu wankan Tarwada sunfi su goma Sha biyu Suka fito ta wasu part part daban,Can sai gani Muka Yi Manyan Dattijai Mata sun fito su uku,Daga Baya sai wata tsohuwa ta fito itama sun dauki wanka na Alfarma,Muna tsaye mun kame a wajen Tsabar Raina kanmu da mukayi da kallon Haduwa iya Haduwa,Kaya masu kyau da uban tsada ne a jikinsu,Samarin wasu da shaddo ji na gaske wasu yard masu tsada,Matan kuwa daga masu Ready-made sai masu lace da shadda masu mugun Tsada Dukkansu sun tsaya suna latsa waya Babu Wanda ya ko kalli inda muke duk kuwa da gayun da Muka Sha na kauye,Muna tsaye muka ji an wangale mamaken gate din gidan,Da sauri muka juya Kamar Zan karya wuyana sabo da kallon wasu Laba Laban motoci na gaske masu Arnen kyau,sai sheki da walwali sukeyi,Guda biyar ne Suka shigo gidan Bayan anyi parking securities ne suka fito a sauran Motocin,motar ta tsakiya wacce tafi ko wacce kyau da sheki ba a fito ba Sai da aka dauki Dan lokaci me tsawo sannan muka ga wata kyakyawar kafa Fara sanye cikin wani takalmi na ubansu ta fito sannan mutumin ya fito gaba Daya,Wani mugun kyau na gani Wanda sai da na Raina kaina Nan take,kyan sura da cikar zati da haiba,ga kwar jini marar misaltuwa,wani kamshi ne ya mamaye gidan me Dadin Shaka,Ido na lumshe jikina ya dauki rawa sabo da ban taba ganin Halitta irin Haka ba ko a kasar larabawa ko turawa sai an Tona kafin a samu me kyau Haka komai cif,Rabi ma jikinsu rawa ya dauka tace kuzo mu Karasa wajen masu gidan,da sauri muka Fara tafiya matashin Nan Yana Jikin mota Bai tako ba,Wajen mutanen gida Muka Karasa tun daga nesa da suka hango mu suke zuba uban dariya ganin yanda Muka Yi kwalliya har da Glass.
Sun Gane Rabi