Showing 96001 words to 99000 words out of 115153 words
Toka,Kamshin turarensa ne da yake Fesawa ya tashe Ni a bacci,Ido na na rufe Ina kallo ya gabatar da Sallah tare Azkhar dinsa ya Dade kafin ya Idar yasan bani da lafiya shi yasa Bai tashe Ni ba,Wayarsa ya dauka tare da Kiran Umma Bayan sun gaisa yace Umma a kawo Mana Breakfast,Umma Bata tsaya wani Jin kwaf ba Tace to,lska ya Shiga hura min a kunne na bude idanuwa na Yi a hankali,kin makara da yawa Baby,a hankali na tashi zaune naji sauki sosai maganin yayi min Aiki matuka,da kaina na Shiga Toilet tare da gasa jikina sosai,wanka nayi da Brush Nima na Daura Alwala na fito,Sallah na fara Yi tare da Azkhar.
Lotion na shafa me kamshi,baya Room din ko Ina ya fita oho,Pant da bra na saka sai T-shirt din sa me dogon Hannu na zaro black me adon Orange a gaba,tamin girma sosai tsayinta har wajen Rabin Cinyata Amma nayi kyau sosai,Powder na shafa da Maroon jambaki,Gashina na gyara sosai na Kama da katon Ribbom Orange gashi na ya sakko har bayana me tsayi sosai nayi kyau gwanin Sha'awa Ina Shafa turaruka ya shigo a bakin Kofar yaja ya tsaya tare da Harde Hannayensa a kirji Yana kallona kamar zai lashe ni,Ina kallonsa ta mudubi Fuska na Bata gabana Yana Faduwa Tsoronsa nake ji gaskiya,Allahumma ajirni fi musibati waklibini khari min ha.... nake furtawa a hankali sabo da Fu'ad Ni yanzu Tsoronsa ya kamani baya tausaya min,a hankali Naga Yana takowa inda nake,mudubi na kafe da kallo nasan wajena zai zo ma,tun kafin ya karaso na fashe da kuka,Dariya na bashi sosai,da Kalar tausayi Yana wani lakwansa magana yace Allah sarki ba Wani abin Zan sake Yi Miki ba Breakfast zamu ci Umma ta Aiko da shi,Yanzu Baby abin har ya Kai Haka?sai kace Kinga zaki,Hawayena na goge Ina shesheka nace gwara wallahi ace Zaki ne ko Kura ko damusa Suka shigo dakin Nan nasan Zan iya guduwa ko ta window ko na shige Toilet nasa key Amma Kai fa? Dariya Fu'ad yake ta Yi yace Haba akwai Amana da Imani tawan ba abinda Zan sake Miki,Kinga kin Bata kwalliyar Taki da Hawaye ya furta Yana goge min da Hannunsa,Kinyi kyau ko na bar Miki rigar Nan ne? Kai na girgiza nace bana so ka rike abarka tunda ba Mutunci ne da Kai ba Sam ba ruwana da kayanka,Dariya yake yace Zagina fa kika Yi Miji Guda ki kalli idona kice bani da Mutunci? Nace to kana da shi ne? Ba Kai ka fada da bakinka ba jiya,Ni Fu'ad Bani da mutunci ko? Tsoro naji sabo Kar ya dawo yace zai nuna min rashin mutuncin shi yasa da sauri nace ba Haka nake nufi ba Kayi Hakuri kana da mutunci sosai,Daukana yayi cak a kafadarsa ya nufi Bed Dani sabo da tsokana,Wata Kara na tsala sai da me Gadi dake Gate a saman bench ya Mike tsaye zumbur yace Wai me akeyi ne a ciki Haka tun jiya? Babu me bashi amsa yace Ina ruwana to Nan ya bawa Kansa amsa tare da komawa ya zauna Yana me ci gaba da Jin Radio dinsa,Tsokanarki nake Yi cewar Fu'ad ya ajiye Ni a kasa tare da rike Hannuna yace muje,tare Muka fito,nace bana son Dining a Palo saman Sofa ya ajiyeni ya kawo abinci da komai na bukata,Chips da ketchup naci sosai Ina Shan tea abina,Ga Farfesu nace bani farfesun kajin nayi tashin komada ko na murmure da wuri,Sai da na Dame ciki na da girki naji wani karfi karfi,na Dan Jima a zaune kafin na Mike na kwanta sosai Bacci ya kwashe Ni, Fu'ad da Kansa ya gyara bedroom dinmu har wanke wanke yayi Ina ta bacci na.
Iya ce tayi mafarkin bani da lafiya,ta tashi ba kuzari a jikinta,Umma Tace Iya lafiya yau ko kallon baza kiyi ba? Iya Tace ke dai Bari a jikina naji Rumailata kamar Bata da lafiya,Murmushi Umma tayi Tace lafiya take Iya Bari na kirata a waya,Iya Tace kyale zancen waya zancen karya Indai Rumaila ce ko Bata da lafiya baza ta fada min ba cewa zata Yi Kalau take,Anya kuwa Aljanin Nan ya bar jikin Rumaila? Gaskiya hankali na bazai kwanta ba sai Naga Rumaila, Fu'ad Umma ta Kira Suka gaisa Tace Ina Rumaila bani ita, Yace bacci takeyi,Iya Tace kinji ko,Umma Tace ka tasheta to Iya ce zata zo ta duba lafiyarta,da sauri Fu'ad yace a'a Kar tazo Dan Allah Umma karki Bari tazo,Wai daga tafiya jiya za a fara zuwa ganinta gaskiya Banda yau,Umma Tace baka da gaskiya ne? Iya tana zargin Aljanin Bai bar jikinta ba jiya tayi mafarki, Fu'ad yayi Dariya yace ai ya Dade da barinta ta warke ras,Iya dai Bata yarda ba,ganin hankalinta yaki kwanciya sai Tace to Iya dai yanzu Driver zai kawo ta, Fu'ad ya Gama abinda yakeyi Rumaila ya tasa yace ga Iya Nan Wai tayi mafarkinki sai tazo taga lafiyarki,a rude nayi sama tare da canja wata Shadda Dark purple ta Sha kyau,Ni nasan azabar Dana ke Sha Amma na Danne nayi Kamar bani da matsala Muka dawo palon kasa Muna kallo.
Bamu fi 10mnt ba lokacin na gaji da Zama na kwanta tare da Dora kaina akan cinyar Fu'ad,Gashina yake shafawa a hankali hannunsa daya Kuma waya ce Yana latsawa,Mota muka ji ta tsaya Mikewa nayi zaune ba a Dade ba sai Iya muka ji tana Kwankwasa kofa, Fu'ad ne ya tashi ya Bude kofa Iya ya gani tare da Naila,murmushi ya saki yace Sannu da zuwa Iya,Tace Yawwa Fu'ad,Naila ya kalla yace yaushe ke Kuma kika dawo? Jiya na dawo da dare Yaya Ina kwana? Lfy ya amsa,Iya dai Suka shugo,Sai murmushin yake nakeyi Ina washe Baki Dan Iya ta tabbatar Kalau nake,Iya tunda ta shigo Ni take karewa kallo,Durkusawa nake so nayi Amma bazan Iya ba Haka na gaida Iya a zaune,Naila nayiwa Sannu da zuwa Muka gaisa ba yabo ba fallasa ta amsa tana wani sha min kamshi, Fu'ad Yana kallonta,Kwafa yayi nasan sai yaci ubanta.
Iya ce ta kalleni kamar tana son magana Dani,nace Iya zo mu shiga Bedroom,Iya na janye Muka Shiga Bedroom din dake palon,Bakin Gado Muka zauna Iya ta kalleni tace Rumaila Baki da lafiya a jikina naji kina wani Hali,Murmushi nayi nace ba komai Iya Ni lafiya nake,Rumaila ko dai Fu'ad sai jiya yayi wani abin ne? Nace a'a Iya,to Dan Ubanki a baya kina da Aljani Bai samu komai ba kin warke ya bazai Yi komai ba? Dama magani Zan Baki shi yasa na matsa sai na ganki Amma ai na koya Miki yanda Zaki kula da kanki,Ba yanda Iya Bata Yi ba naki fada Mata komai,Nan ta bani dai wani gayye da sassaken wata Bishiyar Tace tafasawa Zaki Yi ki dinga Zama a ciki,ko kin warke ki dinga shiga kina Zama Yana maganin cuttuttukan Mata Infection,Yana sa matsi da abuwawa da yawa Zaki ji dadinsa,Karba nayi a katuwar Leda baka nayi godiya,Tace Ni Zan wuce dama abinda ya kawo Ni kenan ki daure kiyi amfani da shi yau,to nace,nace Iya me Zaki ci? Baki ta tabe Tace ai ke za a bawa abin ci Rumaila,kece kike cikin wani Hali,Murmushi nayi nace Kai Iya,Tace to abinda Zan fada Miki sai kinyi Hakuri Rumaila,sai kin koyi juriya, Kiyi hakuri karki dinga nunawa Namiji kin gaji da shi,karki nuna Masa ragwancinki a fili ko ki dinga raki,Ki dinga Hakuri ko yaushe yazo ki nuna kina murna,kiyi Hakuri yanzu sabo da Zaki Sha wahala,ki bada hadin Kai sabo da ki samu sauki Amma idan kika ce Zaki rigima bazai kyaleki ba Kuma a banza zai Miki ta karfi ki Sha wahala,Kunya nake ta ji,Iya Tace magana ce ta gaskiya ba mafarkinki nayi ko Baki da lafiya ba,wannan fadan shi ya kawo Ni wajenki, dadin gidan su Fu'ad yasa na sha'afa ban Miki ba,Ki nutsu kiyi Biyayya irin wannan mazan ba kowa ke samun irinsu ba,Allah ya zabe ki ya Baki,ki tsaya ki nutsu Banda shashanci,karki ga Yana lallaba ki Yana nuna Miki kauna ki bullo da halin banza,ba ruwan maza wallahi Basu da tabbas,gwara ko Allah yayi za a Miki kishiya dama ace ke ta kirkice babu wata da za a kawo ace tana abinda Baki Yi,ta sameki ko Mene takeyi na mace wajen farantawa me gida ke kin Rigata kina Yi,a dage da Addini a rike Addua sosai itace makaminki, ko Mene ya dameki ki roki Allah,komai roka akeyi,murmushi nayi Iya Tace ba Dariya zakiyi ba Dan Ubanki ko Sugar ko gishirin Miya kike Nema roki Allah Office dinsa kullum a Bude yake,bare mallakar miji fadawa Allah ki mallake abinki a rasa dalili ba asan Allah kike roka ba, Iya ta dinga min Nasiha karshe Tace muje ki bani lemon gidan Nan shima na Dan Dana Irinsa naji,Dariya nayi na Mike Iya Tace boye Ledar maganin Nan Kar ya gani ba a magani a Gaban maza ki kula,ki nuna Kawai Baiwa ce daga Allah, a cikin Sip na saka,Iya Tace taka a hankali Naga da kyar kike tafiya,Ina tafiya a hankali Iya Tace Uhm wannan ko Dan Iskan Suriki,Haka akeyi wannan ba karamar Illa yayi ba,dole idan na koma kauye na yo Miki Hadi na musamman,Dama da ganin wannan ba tausayi zaiyi ba.
Fu'ad kuwa Sanda Muka shige daki da Iya Naila ya fara yiwa Fada,Yace karki sake zuwa min gida Matukar Zaki dinga yiwa matata kallon banza,kiyi a hankali matsayinki daban matsayinta daban,Baki da hankali Wai Naila? Muna Uwa Daya dake kina biyewa su Khaleesat Kuna shirme da Hassada,Duk Wanda Bai kaunar Rumaila wlh ba masoyi na bane,matata Uwar Yarana wacce nake kauna ai duk me so na ya kamata ya so abinda nake so,Indai baza ki gyara Halinki ba wlh Sam baza mu shirya ba,Kuma sai na fadawa Umma,duk abinda kikeyi ban taba fada Mata ba Amma yanzu Kam bazan dauki wannan ba,Kayi Hakuri Yaya Dan Allah cewar Naila, Fu'ad yace ki gyara Halinki ko ke kina so idan kinyi aure dangin mijinki suyi Miki Haka? Kai ta girgiza,Yace shine kike yiwa Wife Dina sabo da ita Basu da kudi? Daga Sam's ta fado? Ko iyayenta ba mutane bane? Shuru Naila tayi ya Mata kaca kaca tayi luf,mun fito na kawowa Iya lemo Iri iri,Itama Naila ta Sha sannan suka tafi,Iya tayi mamakin ganin canjin fuskar Naila tana ta yiwa Iya surutu,Iya kuwa Darajar Umma da Abbi da Kuma sanin ita surukace shi yasa ta sake nutsuwa ta kyale su Momy sai dai Bata kula su basa kulata,daga wajen Umma sai wajen Nenen Kauye.
Bayan Sun tafi Fu'ad Bai tambayi me Iya Tace ba,Nima ban fada Masa ba,Hannuna ya rike Yana Bina da kallo na so da kauna yace kiyi hakuri Akan abinda Yan Uwana suke Miki,Murmushi nayi nace Haba ba komai ai Watarana sai labari dole zasu gaji su zauna,Kitchen na Shiga, Fu'ad ya shigo yace Baby kina jinya aikin me zakiyi,Nace Iya ce Wai ta kawo min magani Wanda Zan na Zama a ciki Wai zai sa na warke,Ta baya ya Rungume ya daura Kansa a dokin wuyana tare da furta Iya ta gano mu kenan? Kai na daga masa,yace to Bari Ni na dafa maganin idan har naji tsarin Iya me kyau ne Idan naji zam zam to.......kasa karasawa yayi sabo da yanda na kwabe fuska zanyi kuka, Rungumeni ya sakeyi sosai a jikinsa tare da Furta Wasa nake Miki Baby,sai kin warke,Hawaye na goge nace Dln Allah ka Bari na warke,tauyi na bashi yace Inshaallah duk da Zan cutu zanyi Hakuri Ki warke,farin ciki nayi,maganin Iya na dinga tafawa kullum Ina Zama ciki Kuma Alhmdllh yayi min Aiki sosai, Fu'ad Bai sake min komai ba yayi Hakuri matuka Yana so Amma ya hakura,ko Kiss idan Naga zai min kuka nake saki Dan karma ya fasa yin hakurin yace sai yayi,Kullum cikin dare da kyar yake Iya bacci sabo da sha'awa Amma Haka nake hanashi ko tabani sai Dana Yi kwana uku, yau Bayan Munyi Shirin bacci ya kasa hakurin kwata kwata,Wayo ya min yace ko Muyi Romance na samu sauki ko Kuma yau dole nayi ki zabi Daya,Nace ayi Romance din, gaba Daya a haukace yake yau,Kamar Zaki me Jin yunwa Haka yake sarrafani,Ina Jin dadin hakan a nutse yake sarrafani cikin salonsa na wayayyu,Nima duk na saki jiki Ina Taya shi Mun Gama tsunduma duniyar Dadi,Albarkatun Kirjina yau sunji jiki a hannun Fu'ad,sai da ya min abinda nake fita a hayyaci na gaba Daya Ina kukan Dadi tare da furta Masa kalamai masu Kara birkitawa mutum lissafi,a hankali ya nemi hanyarsa,da sauri na firgita Zan kwace Amma Ina ya min wayo ya Gama sakalkaleni Wanda ko motsi kasawa nayi,kuka na saki nace yanzu yau ma abin Haka ne,kace fa baza ka Yi ba shine zaka ci Amanata,ko kallona baiyi ba abinda yasa a gaba shi yakeyi,jikinsa wani irin rawa yakeyi na daban,ya rude gaba Daya ya shiga duniyar Dadi,wani Gurnanin Dadi yakeyi tare da Nishi Kai abin dai ya girmama na Fu'ad,Naji zafi yau ma Amma ba Kamar farko ba,Ya Dade Yana Abu daya kafin ya samu nutsuwa ya Kankameni a jikinsa idonsa har wata kwalla ce ta cika taf sabo da Dadi,kalamai kuwa kunnuwa na sun gaji da ji ba Kalar da Bai fada min ba, sai Bayan komai ya lafa Ina kirjinsa a kwance Ina shakar kamshinsa yace Iya Allah ya Mata Albarka,Kin warke sosai gashi Baki Sha wahala sosai ba,nace ba Wani Nan Bayan ka Hana na Gama warkewa tunda kaji dadinka dai kayi shuru,Dariya yayi ya kunna haske yace Bari na kalli abubuwan Nan sosai,da sauri na kashe hasken Ina Masa kukan shagwaba,sai wani nishadi yakeyi Yana ta Bina da kiss a ko ina na jiki na,gaba Daya yaki kwanciya,daga ya taba can sai yayi can kiss aikinsa kenan Yana ta faman yabo na,Dan Allah kayi bacci na furta Ina murmushin Jin dadi yanda yake ta faman yabo na Yana nuna min kauna.
Sai Mukayi wanka tare da bacci Yana sake Farkawa Hannu na ya rike ya girgiza ban tashi ba,sama na ya haye tare da sakar min nauyinsa kadan ba shiri na farka,Yace Wai wanne irin bacci ne Haka? Tunda naji ya farka 2am nasan Abinda yake Nema,Boobs Dina yake shafawa Yana cewa ki daina baccin Nan please,Mamakinsa yasa na kasa magana,Shagwaba yake min sosai Yana kwanciya min a jiki,ya zanyi Haka na hakura ya sake yi,da Asuba ma Haka ba Imani ba tausayi Amma yayi Hakuri ya daga min kafa na kwana daya Wai na sake warkewa daga Nan ya Dora daga inda ya tsaya har na Saba ma na daina Jin zafi sosai,Kwanan mu shida na Masa zancen komawa makaranta yace sai ya Gama Amarcinsa Nan da 2mnths,Allah ya kaimu na furta.
Washe gari Su Rabi sati ya cika cib an Gama shiri,Fadila sai gani tayi daya part din Ana ta Kara gyara shi,Saddeeq ya zubawa Rabi kayan daki Yan kasar Dubai Yan gaske ko cokali baza suzo da shi,Mota biyu ya tura dakko Amarya aka dakko ta ita da kayan lefenta da gara tare da Dan Abinda ba a rasa ba na bukatun Amarya,Rabi ta Sha kyau sosai tayi gyaran jiki matuka,Sai da Yamma likis yasan an kusa Karasowa da Amarya ya samu Fadila tana kwance tana chat da kawaye yace Tashi zaune Ina so zamuyi muhimminyar magana,Fadila tana Yanga Tace gaskiya Ina Jin dadin kwanciya ta bazan iya tashi ba idan zaka fada ka fada a Haka,Takaici ya kamashi yace to shike Nan dama ce Miki zanyi last week an daura min aure yau Kuma za a kawo amarya sun kusa Karasowa,zumbur Fadila ta Mike Tace what? Ya sake maimaitawa tasan Kuma baya Wasa,Abinda yasa ta yarda Daya part din da taga an gyara kuma an zuba Kaya na Alfarma,Fadila ta fashe Da kuka, Saddeeq yace ai gashi yanzu kin tashi ko? Hannaye ta daura a Kai tare da rushewa da kuka,Zaucewa tayi gaba Daya ta koma kyakyata Dariya ita daya,sai Kuma ta sake fashewa da kuka,Wayarta ta sura ta Kira Momy tana kuka ta sanar Mata,Momy Tace cab idan ya isa kafira nake,Mama ta sanarwa,Mama ta Kira Abbi ta fada Masa tana bala'i, Abbi yace Kuma idan kuka dakko Fadila ta dawo gidana akan an Mata kishiya duk a bakin aurenku ke da Momy, Momy da Mama suka Shiga mota tare da su Khaleesat gaba daya Wai sun tafi zasu karairaya Amarya,Fadila ma Abbi ta Kira tana kuka Wai zata dawo gida Abbi yace idan kika dawo gidana Matukar ba sakinki yayi ba ban yafe Miki ba,Fadila ta sake Faduwa tana rusa Ihu,tabarya da muciya ta dakko a kitchen ta tsaya a tsakar gida tana jiran Amarya duk da Basu San wace Amaryar ba,Su Momy Dan Abin kunya Suma suna zuwa har guzirin Sanduna kowacce rike da katuwar sanda harda Khaleesat Safna da Farida sun tsaya a tsakar gida,Shi kuwa Saddeeq yasan za a Rina Yan Sanda Ya kirawo mota Guda ya Basu aikin kula da lafiyar Amarya da danginta,Amarya suna zuwa Abuja Yan Sanda Suka tare su a motarsu,Amarya suna gaba motar Yan Sanda tana binsu a baya da jiniya wiwiwi.....
AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈
NA KUDI NE
WACCE TA FITAR DA WACCE TA KARANTA BATA BIYA BA BAMU YAFE BA
ALLAH YA ISA
DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM
96-100
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne
Fans Masu Sharhi duk Ina kallon kowa Ina sonku,page naku ne.
Motocin Amarya ne Suka danno Hancin motarsu cikin Gida,Su Momy aka gyara tsaiwa ga Sanduna a Hannu,sai motoci biyu suka Yi parking a inda ya Dace motar Yan Sanda ta shigo tsoro ya shigi su Momy za a kamasu da makamai hukunci zai hau Kansu,Da Sauri Mama Tace ku zubar sai Yan Sanda sun