Showing 108001 words to 111000 words out of 115153 words

Chapter 37 - DANGIN RABI COMPLETE

23 Aug 2025

1542

sakko wulakanci da Rashin mutunci ya kare,kafin na musu magana ma sun min magana mun gaisa,suna Neman shiri da mu ko yaushe suna zuwa gidana.

Karatuna yayi Nisa Sosai,Bayan wata hudu da auren Rabi ta samu ciki itama ga Fadila nata ya girma,Hajara ma laulayi take fama,nice dai Kawai har yanzu ba rabo, Fu'ad na sa a gaba Ni Wallahi Nima sai an min ciki,kowa Yana ta samu mun Riga su aure Amma Ni Shuru, Fu'ad muna zaune a Palo Yana Aiki a system dinsa Yana Kora lemon Kwakwa Dana hada Masa,Nace Ni kowa Yana ta samun ciki ban Dani, Fu'ad yayi Dariya yace to me zanyi Aiki na Riga nayi Allah shike ba da Haihuwa ba Ni ba,kici gaba da Hakuri Allah zai bamu ya kike Abu kamar bakya zuwa makaranta Babyna,a kafadarsa na Daura kaina nace Kaine dai baka dagewa sosai idan da kana dagewa ai da tuni na samu ai Allah yace Tashi in taimakeka,Yanzu machine kike so na koma fisabilillahi Abu sau Uku sau hudu har fa cewa kikeyi kin gaji Amma kice bana kokari? Nace Kaine Mana baza ka dinga tuttula madarar taka a ciki ba Taya Receptors zasu sakalo Sperm din su kaishi shi cikin Mahaifa ta su Dora saman kwai, kullum sai saka kwai nakeyi a banza sai Ina Sa Rai sai Naga Kawai Ina period Ina ta saka kwai Haba Dan Allah Dan Annabi,Idan ka kawo ka barshi can ciki jikin Mahaifa sabo da Sinadarin dake Jan sperm ya fisge shi yayi ciki da shi shuuuuuuu ya dasa shi jikin kwai Haba Ni fa Ana mana Genetic a school rashin dagiyarka ce Baby Kawai kayi min ciki yawwa, Fu'ad Dariya yake ta Yi Bai ce komai ba sabo da abin Nawa ya wuce hankalinsa,Aikinsa Kawai ya keyi,System din na rufe nace dare yayi kazo a samo me Sunan Abbi,Ina ta so naji Ana Mama Mama a gidan Nan muje, Fu'ad yace to an gama,dama a ransa yace sai yayi maganina,Ko da muka fara soyewa Fu'ad kin gajiya yayi kamar Engine,sai da ya kure min maleji,Ga mugunta yana ta min kuka na saki tun Ina daurewa,Kuma yaki ya Kyaleni yace yau sai kin samu ciki Baby,nace wallahi Wasa nakeyi nasan Allah ne ke badawa Dan Allah kayi Hakuri,Ba karamar wahala ya bani ba Daren Nan guda,washe gari da safe yace zai sake tashi nayi na gudu dakina na datse da key.

A shekarar su Iya da Affa,tare da Yan Uwa na kaf suka tafi kasa me tsarki,Rabi da Fadila tare da Saddeeq Suma sai labari naji sun tafi,Saude Ma mijinta ya biya Mata sun tafi tare da Sauran matansa,Kuka na dinga Yi Ni Fu'ad Bai biya min ba,Yana baccin Rana na Shiga na kwanta tare da fashewa da kuka,Yana baccinsa me Dadi ya tashi nace Ni sai kullum ace Ana kauna ta,I love you Taki karewa Amma ga su Rabi can a Makkah da su Iya Ana ta Shagali idan Muka Yi waya suna tare Ana ta Jin dadi Ni kuwa Ina Nan sai dai naci soyayya na koshi cikin ma an kasa Yi min,yanzu Akan wannan kika tashe Ni a bacci? Gasa kikeyi da Mata? Abinda Zaki koya kenan daga Kinga kawa tayi Abu sai kice sai an Miki kema,Fuska ya Bata ya dinga min Masifa Ina kwaikayon wasu,rayuwarsu daban Taki daban Indai Abu ne Zan Miki Amma wlh daga yau idan na sake ji kince kawarki ko wata an Mata Abu ke ba a Miki wlh sai na Bata miki,ku daga Kun samu sake sai iskanci iri iri,wani kawa da Yan Uwa an biya musu ke ba a biya miki ba to wannan Hassada ne Idan Baki sani ba,nayi niyyar Next Year Amma na fasa tunda Tabara ta sa Zaki koyi Hassada,jarabar Su Rabin Nan ma Ni ban San ya akayi suka Yi aure a Nan ba kin wani koma kin jone dasu tashi kiyi waje,Ni fa ba Hassada nake musu ba wlh Kirana sukeyi kullum a waya naji su tare da su Iya Ana ta harka shine naji dama muna tare,shine Zaki zo Ina bacci na ki tashe ni? Kukanki ne zai sa na Miki abinda banyi niya ba? Ki kiyayeni wlh Naga Alama kishiya kike so ayi Miki kema,me yasa Baki Yi koyi da su Rabi ba kice na Miki kishiya kema irin Rabi,Kallonsa Nayi da sauri nace ah dama kace Kawai aure kake Nema,Dama Iya ta fada Baku da tabbas,kwanciya yayi tare da juya min baya Yana dariya a ransa har ya koma baccinsa,Na Gama kulewa dama Dan ya Bata min Rai ya fada,Fita nayi nace ai kuwa yau shima bazai bacci ba,Tsintsiyar shara na dakko na fara shara kuyasss...Kuyasss....Sip na Bude na mayar na zuge da karfi garam,,tsintsiyar na buga a jikin Mirror,juyi ya sakeyi sai Kuma ya Mike gaba Daya ya Shiga Toilet,Kitchen na Shiga na Daura Girkin dare,Yana kallo na Ina ta fushi bana kulashi,da dare ma ko da nayi Shirin bacci a dakina na kwanta,Ina ta juyi na kasa Bacci,sai gashi ya shigo,farin ciki ya kamani a Raina,kwanciya yayi Kawai a bayana tare da daura fuskarsa a dokin wuyana,Kissing bayana yakeyi,ban hanashi ba.

Nace baza kayi fushi da zuciya ba? Dariya yayi yace ai Ni a wannan bana fushi komai fushinki ni ba abinda zanji,wajen wa zanje nayi? Dole sai wajen matata idan kinyi fushi ma kinyi a banza,idan kin hanani ma wlh ta karfi Zan Miki ba ruwana,idan kinyi fushi tunaninki Zan fasa ki daina,Dazu Dan bakin ciki harda hanani bacci Kawai ki fara sharar banza Don kar na huta ko? Dariya nayi nace ai Kaine kace wata kishiya,Shagwabarki ce da neman magana yayi yawa ke baza a zauna lafiya ba sai kinyi Rigima kwana Nan kike wannan Hayyatar,kice wannan kice wancan Allah yasa ma ba ciki kika samu ba kike wannan abin,ba Wani ciki da ciki ne ai Zan Gane,Haka muka Sha soyayyar mu.

Bayan wasu kwanaki na fara zazzabi,Amma Fu'ad Bai sani ba,Sai Dana dawo daga School,ya dawo daga Office da wuri yau har yayi wanka Yana Hutawa na shigo,Yana Jin nice ya Mike ya Rungumeni yaji jikina zafi sosai,Wuyana ya taba da bayan Hannunsa yace Baki da Lfy Baby,tun yaushe kike zazzabi ban sani ba? Hawayen Shagwaba ya ziraro min nace Yau sati daya kenan kullum sai nayi idan naje makaranta,Amma shine baza ki fada min ba? Yace muje asibiti,Ko Uniform Bai Bari na cire ba ya rike Hannu na har cikin mota ya sani muka tafi shike Driving,Muna zuwa wani Hadadden Asibiti ya Bude min file a Private Hospital Likita ce ta min tambayoyi sannan tace na kawo mata fitsari a kwalaba, kwalabar na karba nayi Fitsarin na kawo ta auna,ta turani nayo wasu test din ta tattara bayanai a Result ta bani ta kalli Fu'ad tace matarka tana da ciki na wata Uku da sati daya,Sai Malaria dake damunta,zata fara zuwa awo duk sati,wasu Magungunan ta rubuta Fu'ad ya karba ya tafi zai siyo,sai murna yake Yi bakinsa yaki rufuwa, Ni Kuma na zauna tare da Likita muna Hira tana ta bani shawarwari da abubuwan da Zan na ci.

Nace Likita Dan Allah ki fada min tsakani da Allah ya zafin nakuda yake?Likita ta dinga dariya tace sai lokaci yayi Zaki ji,Nace Allah yasa kece Zaki karbi haihuwar Nan na yarda da ke Doctor,na damu Likita da surutu nace Oh Allah sarki Dan mijina na dinga Masa masifa naki samun ciki Ashe ma Ina da cikin,Bari na Kira Iya na fada Mata ta fara tanadi.
Lambar Iya ta Makkah na Kira ta daga Tace Dawafi Zan Shiga Rumaila,nace Iya ki min Dawafi Bakwai sau Bakwai sau goma Sha biyu, jikanki ya fito lafiya Iya ciki ne Dani ki siyowa jariri Kaya masu kyau a Nan,idan kin dawo ki fara tanadin yajin jego,Iya kaji Ashirin Zaki soyo min idan na Haihu,Iya Tace gwara da kika fada min kullum a masallacin Kaaba Zan dinga kwana Ina Miki Addua Allah ya saukeki lafiya,Cikin watansa Nawa?nace Iya Ni kunyarki nake ji idan na Haihu Kyaji Kawai,ki lissafa da kanki,Iya Tace anyi shashasha a Nan Amma kin Gama fada min Zaki ce kunya Kuma? Wayata na kashe Dan kar ma na kauce hanya na fadawa Iya, Fu'ad Yana dawowa muka tafi,Zan Dan tsallaka wani tudu na rike Hannun Fu'ad Nace tsallakar Dani Kar cikin Nan ya zube,Dauka na yayi ya ajiye,a hanya ma tafiya ta sadaf Sadaf nake yi Kar ciki ya zube,Girki yanzu kafin na Gama Aiki ne ko cokali Zan dauka a hankali a hankali nake lallabawa,Ko Xxx zamuyi Fu'ad sai dai yayi a hankali idan ba Haka ba bazan yarda ba,tun Yana dariya abin har ya zame masa jiki,Gajiya yayi da Jin yunwa sai na Dade ban Gama abinci ba akan Ina lallaba ciki,shine yaje ya shirya min tsiya da Likita,ranar da ya kaini Awo tace ai me ciki anfi so ta dinga jijjiga jikinta tana yin komai cikin sauri idan ba Haka ba za a haifo jariri nakasashe,Ai tunda Likita ta fada kamar fadar Allah aiki bana gajiya komai na dawo yinsa normal,Haka Kawai ma har wanki nakeyi da Hannu bazanyi a Injin wanki ba, Fu'ad Yana ta kallon ikon Allah ko ya hanani bana yarda.

Yau ma Sai da na Gama komai Amma wata Jallabiya Yana cireta na dakko Ina wankewa yace Wai bakya gajiya ne Baby? Nace baka ji me Likita Tace ba? Ai yanzu kabi doka ka zauna lafiya kawai,Yaron Nan da Alama me Energy Zan haifo, Fu'ad yace ai Haka ake so,yau Baku gaisa ba,ya kamata ka shafa masa Kai ka sa Masa Albarka,Likita Tace idan ana musu magana tun a ciki to da basira ake haifo su ko baka so ya dinga zuwa na Daya a school? Fu'ad yace Ni kuwa nake so,na Mike tsaye Fu'ad Yana shafa cikin Yana kwararawa jariri Addua Ina amsawa da Ameen Ameen,Yace Allah yasa yazama na gari lafiyayye kyakyawa,nace Ameen,yace Allah yasa ya Zama mahadaddacin Alqur'ani,nace Ameen,Allah yasa ya Zama Wanda Musulmai da Musulunci zaiyi Alfahari da shi ko ita, Allah yasa me Biyayyar Iyaye ne,Ameen, Ba mazinaci ba,Ameen,Ba masifaffe ba ko masifaffiya,Ameen, Allah yasa ya Zama nagari mutumin kwarai,Wanda bazai Zama Dan fashi ba,Ameen,ba Dan Kidnapping ba,Ameen,Nace Allah yasa Gomna Zan haifo ko wani minister ko wani Sanata me kishin kasa da Alumma,me kishin Musulunci Fu'ad yace Ameen,Ido Muka hada ya kashe min Ido daya Muka dinga dariya,zai Kuma shafawa na rufe Rigata nace ya Isa Haka Mana Kai baka San kadan ba,sai ka gajiyar da shi Kuma.

Fu'ad Yace to Dinkunan me cikin da kika ce za a miki Baki zabi kayan ba na siyo a Kai dinki,Nace sai ya Dan Kara girma sai Tela ya Dinka min manyan riguna Wanda zasu dinga shanye cikin,Sai Uniform dole a dinka na me ciki,yace an gama Princess,nace sai takalma flat over Size sabo da nasan Nan gaba Zan kumbura,cutar kumburi irin ta me ciki wacce ta kusa Haihuwa zanyi ta,takalma zasu Yi min kadan a siyo Over Size, Fu'ad Dariya ta isheshi ya hadu da me ciki yace to sai me? Nace a cika min Drower da Shaving Stick sabo da idan na kusa Haihuwa kullum Shaving sabo da dubani da Likita zata dinga yi, Fu'ad yace Ni ba nace style Zaki nayin shaving ba Ni bana son kwalkwal,Kai ba Wani style sai an haihu,kullum Kai kace sai an maka me tozon zakara bazan iya ba baza ka jawo Likita ta rainani ba taga sirri na ba, Fu'ad ya dinga dariya kamar me,ko da dare da yaje wajen Umma sai dai taga ya Kama Dariya shi kadai,Umma Tace maza ka Zama kwarkwar Allah ya kawo sauki.

A makaranta malaman har sun gaji da Halina sai nayi kwanciyata a zaune Ana magana zance bani da lfy,ai Ina da ciki ba abinda ake cewa sai a Kyaleni,ko Assignment Ina sani sai naki Yi Ana tambayata zance bana Jin dadi,Wani malamin Biology ya shigo aji ya tashe Ni yace ke Wai ke kadai ce me ciki a duniya? Nace Malam Kai da kake Biology ai nasan kasan komai da yanayi na me ciki,ya zaka takura min,Ido ya zare min yace ke mu fa Nan karatu akeyi ba ruwanmu da cikin ki,nace lalala Ina matar Aure kake kashe min Ido daya wlh sai na Kai kararka ai Rannan ma Haka kayi min Dan Kira kace kana so na,nace Ina da aure kace baka da matsala akan naki sonka sai kazo kana min Maganar batsa a aji,har kana cewa ta Yaya ciki yake samuwa,Malami ya tsorata yaji sharri na Zan sa a daure shi,dama an tsani malamin Bai da mutunci,ganin Zan tozarta shi ya bani Hakuri yace kwanta kiyi ta baccinki,nace Ni kake kashewa Murya Kamar Mijina? Malam yayi mukus,ai kuwa na kwanta Ina Jinsa Yana ta ciwa student mutunci.


















AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈












THE END (KARSHE)








NA KUDI NE









DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM













111-115













Official










By
AsmaBaffa









Page naku ne

DANGIN RABI FANS













Yau Fu'ad da Kansa yazo daukana,Ina school an tashi mun fito da Kawayena su Laila muna Hira har mota suka rakani,Laila ta rike min jaka Wai tana tausayin me ciki,Sai da suka gaisar da Fu'ad,ya fito da Kansa tare da Bude min gaba na Shiga ya Rufe sannan ya zaga ya Shiga Muka tafi,Yana tuki yana satar kallo,Baki na turo gaba cike da Shagwaba,Murmushi ya saki tare da Furta Anya kuwa Baby kina karatun Nan? Kafadarsa na dafa tare da Furta sosai ma ai baka ga kokarin da nakeyi ba,kullum sai an tafa min a class duk period,Shawarma joint muka nufa a can yayi parking Zan bude ya Kai Hannunsa jikin sit Belt zai cire sai Kuma ya kwanta a kirjina,ka zare min Belt pls,Sake kankame Ni yayi yace Dan tsaya na huta,munkai minti 5 a Haka sannan ya tasar min a jiki muka Shiga ciki,mun ci chips da Shawarma tare da Ice cream Dake dama Ina son sanyi abina,sai da muka Gama ya mana take away na wasu kayan tande tande sannan muka koma gida.

Tunda na samu ciki ban damu ba bana Shan wahala har ya cika wata bakwai lokacin yayi girma sosai duk na sake kiba na bude,Sai Kuma yanzu nake wahalar cuta iri iri,daga wannan sai wannan,lokacin tuni Fadila ta Haifo yarta mace katuwa ko suna sai kusan dare Fuad ya kaini,Rabi itama ciki ya girma ita da Hajara,Saude ma haka,Su Naila kuwa dama sun samu Yaron ciki Farida ce Kawai Bata da komai ba a Dade ba Hajara ta Fara Haihuwar Yarta mace, Fu'ad yayi kokari da kyar ya barni nabi Flight zuwa Lagos suna tare da Rabi,Saude ma ta je,ko kwana daya Bai Bari nayi ba na dawo Haka,Kaya manya na masu ciki nake sawa,cikin Yana bani wahala sosai,Yana shiga wata takwas sai kuwa na fara kumbura a kafafuna,sabo da wahala Fu'ad baya zuwa Aiki sosai sabo da ko aikin Gidan kadan nake Yi,Umma me Aiki ta turo min take tayani wasu abun,Gaba Daya na karaya na koma ga Allah kusan kullum sai nayi kukan wahala,Yau ma da dare nayi Shirin bacci na kwanta da kyar, Fu'ad ya dinga rigima,Ya fara Wasa da sassan jikina Ina nokewa, yace Dan Allah Baby bakya tausayi na? Jiya banyi komai ba Kuma yau ma gashi komai ya Kara sweet,Dan Allah ka dinga barina in hutawa wlh bani da lafiya da me zanji da cikin danka ko da kai,Kullum fa da zazzabi ga ciwon kai Kawai Dan kina da ciki shike Nan Baki da lafiya Dan Allah Sweetheart,Ina ma cikin Nan zai dawo jikinka kaji abinda ake ji,ka tashi kayi Nafeela Allah ya sauke ni lafiya ma Kar nazo na sheka lahira,Ni duk na Mika alamura na ga Allah, Da sauri yace Inshaallah lafiya Zaki Haihu kinji,ganin na damu yace ankon sunan fa da kika ce Zaki fitar? Nace wa yake ta wani anko Ni ta kaina nakeyi ko suna bazan Yi ba Kawai Allah ya sauke ni lafiya,Ameen ya Furta Yana shafa gashi na,yace to Ni ki ji Dani Nima ga Form na kawo a cike min,Dariya nayi Muka Shiga kissing din juna tare da Sarrafa juna Yana abinda yaga dama,a hankali yake komai yanda bazai wahalar Dani ba.

Washe gari Khaleesat ce tazo sanye cikin Abaya Blue me tsada,Ina kwance a sama na sakko a hankali Ina tafiya da kyar, Khaleesat tana ta kallo na Ina sakkowa a steps Tace Rumaila wallahi ki rage kwailo gaki Nan Ras da ke kinyi wani kyau da kiba kin ganki kuwa? Amma ke kullum ban taba ganinki da lafiya ba sabo da kina da ciki,Dariya nayi Ina Zama kusa da ita sanye nake cikin doguwar Rigar atamfa Dinkin masu ciki,kaina ba dankwali nace ke kike ganin Haka Amma Ina lafiya ga mace me ciki,Gaisawa Mukayi Tace Ina Babyn naki? Allah ya dawo da shi na fada Masa abinda kika ce,tunda Rashin kunya kike Masa,Dariya Khaleesat tayi Tace Kawo min abin ci dama yunwa nake ji idan naje gida sai nayi girki nafi so Kuma Kawai sai abincin dare zanyi,me kika dafa? Nace pounded yam with Egg source Kuma ta Sha nama,Khaleesat Tace wow Abincin da Mijina yafi so kenan Zuba min a flask Kawai na tafi dashi na huta,ki shiga kitchen ki zuba Mana da kanki,Babyn naki fa? Haba ai kin San Flasks dinsa daban ke kin San bazan Baki nasa ba wlh,ai nasan komai nasa na daban ne,nace har spoons Nasa daban ne,babu abinda wani zaiyi amfani da shi sannan na Bawa Babyna shi, Khaleesat Tace Iyayi Kyaji da shi Ni bazan iya wannan abin ba,sai dai idan Kar ya ci,da kanta ta zuba a flasks ta fito ta min Sallama ta wuce.

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login