Showing 87001 words to 90000 words out of 115153 words

Chapter 30 - DANGIN RABI COMPLETE

23 Aug 2025

1567

dare kafin na kwanta Bayan nayi wanka na lasa na shafe jikina kamar yanda aka ce,Ranar da ciwon Kai na kwana Kamar Zan mutu,Ina kallon Wayar Fu'ad ban samu damar dagawa ba,nayi na kwana biyu da kyar ranar ji nayi Kamar ana hura min wuta a jikina,nace Iya a bar maganin Nan bazan Iya ba,Iya Tace wallahi ko Suma kike Yi Sai kinyi,Har kuka nayi nace sai na bar gidan Iya Tace tashi ki fita na gani,Gaba Daya haushin kowa nake ji ko Fu'ad ya Kira bana dagawa har ya gaji da Kira ransa ya baci Ina Masa Yanga Dan Naga Yana so na sai ya daina kirana.
Ni dai Iya ce ke tsayin daga sai na tabbatar maganin Nan anyi shi,Bana Jin dadin duniya ko kadan a Haka har akayi kwana hudu,Affa ne Muka ji ance Bai da lafiya Yana ta cuta,naje na duba shi Yana kwance sosai Zazzabi yake Yi yaki Jin magani,Ina shiga Dakinsa Kamshin magani na Kawai ya Shaka sai ga shi ya tashi a firgice sai ya koma ya kwanta ya sume Kamar gawa,Ihu na kwalla Ina kuka na,Matar Affa ta shigo da gudu itama fita tayi ta kirawo maza,Ana yayyafa Masa ruwa Amma Bai farka ba Ana Kansa mun zagaye shi sai da ya Dade sannan ya farka a nutse ya Bude idanuwansa ya hada Zufa Ina ta Masa fifita,Jikinsa ya kalla ya ganshi daure da zani,cikin fada yace Ubanwaye ya daura min zani Kamar mace?Dandaudu ne Ni? Ke Rumaila ko kece? Duk Mukayi cirko cirko mamaki ya Kama mu Affa ya Mike ya cire zanin ya jefar yace aikin banza a Kai min ruwan Wanka zanyi, nice na zuba na Kai Toilet, bayan yayi wanka ya canja kaya complete na maza,Gaba Daya ya nuna Bai san ma yayi Daudu ba,Matarsa da mu yaransa murna ta kamamu,mazan ma Suka ce Alhmdllh Ashe Aljanu ne Suka shafe shi ko Asiri aka Masa Yanzu ya Gane Kai Madalla,Zama Mukayi Muka bashi labarin Abinda yayi,Yana ta mamaki Wai Bai ma San yayi ba,Kayan suyar yace a nuna Masa,Ya eba zai Watso su waje Matarsa Tace bar min shi Ni sai na dinga Suyar doya da kwan na samu sana'a na gaje suyar Ni Zan ci gaba a gida, Affa yace ku matsa in tafi gona yau sai na yini Ina aikin mazaje,Kai Allah na gode maka,sai Affa ya zari fatanyar noma ya rataya a kafada ya fice,kowa ya ganshi mamaki yakeyi ya dawo nagartaccen namijinsa,Yan Uwa sai murna da abokan Arziki,zance ya watsu a Kauye Ana ta mamaki.

Ina komawa gida Iya na hau Bawa Labari Iya Tace ko tantama babu Aljanin jikinki ne,lokacin na tuna na dinga Kiran Wayar Fu'ad na bashi labari yaki dagawa Wai yayi fushi,Abbi na Kira Muka gaisa na Basu labari sai godiya yake ga Allah,Ana cikin haka mun Gama murna, Fu'ad kullum a kunci yake,fuska ba Rahma yaje gida Umma ta bashi labari shima da yayi murna yaji Dadi.

Bayan komai ya lafa kullum sai naje wajen Affa mun Sha Hira yayi ta tambayar yaushe Zaki koma dakin Mijin ne ai yanzu Ina tunanin kema kin warke Kai wannan Aljani ya cuce mu Allah ya saka Mana Ashe duk shine yake Abu daya Yana ta cin ubanmu Daya Bayan daya,washe gari Iya Ina kitchen Ina girki tana fitowa waje sai gani nayi ta sulale kasa ta Fadi sharaf,da gudu nayi kanta Nan ma Ina Ihu na Yi waje ko Mayafi babu Jauro da Iro na hango na kwala musu Kira Suka shigo da gudu,Ana ta yayyafawa Iya ruwa sai da ta dauki lokaci sannan ta fara atishawa ba ji ba gani sai da ta Dade sannan ta tsagaita ta farka,Iya ta Mike Zaune garau Tace Rumaila nace Na'am Iya Ina Hawaye Tace yanzu Dan Rashin Basira me ya kaini aure Aure Haka? Duk na Raba Yara waje waje,na dinga son kudi Haka Kai nayi abin kunya,Gaskiya na zalunci maza da yawa ya kamata na nemi afwarsu nace Iya kyale su Kawai ai Allah ya San ba kece da yin kanki ba,Iya kema da Alama Salahu Dake ya hada shi yasa kika dinga kashe aure,Iya tace au kaji Dan Iska Ina cewa nafi karfinsa Ashe har su goggonsa duk a kaina Suka tare to ya Riga ma shiga jikina shi yasa nake ta aure aure oh Allah ya Mana Hisabi tambadadde wannan a jinsin nasu ma shi Gantalalle ne, Haba shi yasa Allah sarki me shayi ba kaunar da Bai nuna min ba Amma akan kudi sai na dinga kwana a Zaure,Su Jauro suna ta mamaki bayan dai sunga komai lafiya suka tafi daga Ni sai Iya Muna ta jimami,Iya Tace cab Kuma Ina Farkawa aure auren Dana Yi ne ya fara Fado min a Rai,Wai Suma nayi ne ko kuwa?

Nace Faduwa kika Yi Iya, ku tafi Dani Birni wannan garin ba gari bane Aljanu sun cika shi Wala'allah Nan gidan Boarder dinsu ce a Nan matafiya ke sauka,nace yanzu Haka ma Nan kasuwar su ce Bamu sani ba,Iya Tace dole na rasa Basira da hazaka,a gari Ana ta kallo na a me kwadayi na Gane gaskiya wannan Dangin Su Rabin mu Alheri ne a wajenmu,Wannan mu suka taimakawa har gida Allah ya kaiki inda zamu samu magani Kai Allah Sarkin Iko,Dakko min buta nayi Alwala na Mika godiya ga Allah,Iya ranar Yini tayi tana cakaki,Salahu ya Sha tsinuwa,Tace wannan ba sunansa Salahu ba,baiyi kala da shi ba,wannan jarumi ne tunda ya Iya Haddasa tsiya Haka,Ni takaici na ma Dana je gidan Sanata nace ya aureni,na hau har mota na biya kudi naje wannan abin kunya da yawa yake da gani kasan ba Basira a Nan an toshe min ita.

To Rumaila ko kin warke ko Baki warke ba Oho,nace Ni dai Ina Jin na warke Iya tunda naji canji a jikina sayau nake jina lafiya Lau,a daure a karasa maganin kaf,nace to,Ni yanzu fushin da Fu'ad keyi Dani shine damuwa ta,nayi Kiran duniya na tura text Shuru,na bashi Hakuri a text Amma yaki magana har na hakura na zubawa sarautar Allah Ido,damuwa Kam Ina cikinta.
Su Umma duk Ina Basu labarin magani Abun da mamaki Ashe har da Iya a ciki shi yasa malamin yace ayi maganin a garin,shima Malam Abbi ya sanar masa komai yace Inshaallah idan ta Gama ko jifa ko Shafar Aljanu ita da su sunyi Hannun Riga,Shima Mijin nata Haka.

Yau Sunday Yar kawar Momy ta sauka gidan da Trolley dinta katuwa tana ja,Yusra kenan ansha gayu anzo za a tallatawa Fu'ad Kai ko za a samu shiga,Ni Kam na Matsu na dawo Abuja na bawa Fu'ad Hakuri,na gaji da Rashin sa,shima ya kasa jurewa sai ya dauki waya zai kirani sai ya fasa,idan ya fara rubuta min sako sai ya goge ya fasa.

Ni Kam tun Ina zuba Ido har na hakura Nima Kawai,har na Gama maganin kaf ya Kare,Iya Tace to sai ki fara shirye Shiryen tafiya Zan sanarwa Umma sai muje mu maida ki gidan, Iya ce ta dinga bani kayan tsumi na Mata Ina amfani da su sosai,har kiba nayi da kyau sabo da na samu lafiya gaskiya ko a jikina garau nake ji na,Umma Bata fadawa Fu'ad Zan dawo ba sabo da tana Kallonsa duk ya rasa sukuni,Fara'a ma ya daina,Yana cin Abinci Yusra tana palon Umma tana ta kallon Fu'ad da kallo irin na so, Umma ta kalli Fu'ad sai juya cokalin yakeyi ya kasa cin abincin Tace lafiya dai ko? Tsaki ya dan ja tare da furta lafiya Lau Umma,Umma Murmushi tayi Tace ko Kai da mutuniyar taka ne? Yusra ta tabe Baki Tace yo Dama Allah na tuba auren Yara Yan 16-17 ai masifa ne,Umma ta kalle ta kawai,tashi Fu'ad yayi ya bar palon ya Fisgi mota ya bar gidan zuwa wajen abokansa gidan Khaleed,su Khaleed sunga kwana biyu kullum a damuwa yake ko sun tambaye shi baya fada musu dama sun San shi da zurfin ciki.

Ni kuwa Bayan mun Gama duk wani shiri Iya,Affa da matarsa,Kawu Haruna da Yar Uwar Iya Yafendo,sai Aunty Rukayya da Haleesa yarta Muka tafi a mota Sharon Drop na daukar Mana karamar mota Amma me cin mutane da yawa,atamfa na sa baka me adon golden,takalmina Goldin me Dan tudu da jakata me tsada kayan Lefe nace ban taba sata ba sai yau, Umma da Abbi sun San da zuwanmu,duk munyi shiga me kyau ba Wanda zai wulakanta mu,Iya a Hanya Tace bazanyi ko gyangyadi ba Ina kallon gari abina,Ni nasan gidan nice jagora,sai wurin 4pm Muka karasa gidan,Direct Tace na wuce da su masaukin Baki,Su Affa duk zaucewa sukayi da ganin gida irin wannan,Iya Tace Uhmmm kudi suna magana da kansu a wannan gida,ai sun zarta yanda nake zato Rumaila,ko dai ya taba yin shugabansa ne me gidan? Nace a'a,Iya tace to zallan Iya kasuwanci ne Haka?Kai gaskiya Ina yinsu Iya wuya ko Dan kudin Nan Ni sun Gama Dani,Affa yace me Hali baya fasawa dama ciwo ma Yana tadda Hali sai ya Dora daga inda ake,Allah yasa babu kowa sai masu Aiki a compound,Ta garden nabi dasu,Iya Tace kaga guri Kore Shar shi yasa idanuwansu farare tas to kullum Ana zuwa a kafe shuke shuke da Ido ana Shan Madara Ana kallo Ana gyangyadi.

Iya ta sake cewa wannan ma'aikata Haka Kamar gidan sarauta Kuma duk biyansu akeyi? Nace ae,Iya Tace ai kuwa gasu Nan Bulbul dasu,Kawu yace a koshe suke ba yunwa wallahi,Affa yace ku ai Baku zaga duniya bane Amma Ni Dana Yi zaman Lagos na Saba da wannan,Yafendo Tace to sarki Shugaban wayayyu,Matar Affa Tace gaskiya mu nutsu,muyi Ubanki idan mun nutsun da hauka mukeyi ba a nutse muke ba? shegen Baki kamar bututu cewar Iya,Ina ta dariya sai da na zage gidan Nan da su kaf gida gari Guda Suka Sha kallo,Kawu Haruna yace gidan Yan gayu kowa yayi luf a bangarensa,da mune kuwa Yara na ihu,can suna Wasan kasa,can Ana dambe ga mahaukatan samari,To sun koshi me zasu Yi cewar Affa.
Sai Dana kaisu masaukin sannan na gwada musu yanda ake amfani da toilet da sauransu na nuna musu gabas,bayan munyi Sallah kowa ta ajiye Jakarta a Bedroom,Yafendo da Iya,Matar Kawu da Aunty Rukayya da Haleesa,Affa da Kawu na Nuna musu nasu wajen a kebe, Wanka Muka Yi kowa ya huta,na Kira wata me Aiki ta kawo musu abinci Iri iri Dama Umma ta Gama komai,Iya kasa magana tayi tagumi Kawai ta zuba.

nace Iya lafiya? Kudi Rumaila suna magana a Nan gidan,Hhh Dariya Mukayi, tare da su na zauna Muka ci abinci kowa ya nutsu, Ina yin wanka Na canja wata sabuwar Abaya Golden ce ta hadu karshe ga tsada kamar zanje party,Powder na shafa da lipgloss na fito wani fes Kamar daga Engine aka fito Dani na fita a kayan,turaruka na shafa sama sama masu dadin kamshi,Takalmina da handbag Dina na dauka Ina tafiya a nutse na taka har part din Umma.

Sallama nayi Fu'ad ya juya baya Yana Shan ruwa a glass cup da Remote a hannunsa,yaji muryata nayi Sallama zo kuga saurin juyowa wajen Fu'ad,Ido Biyu Mukayi ya kafe Ni da Ido Yana kallona Nima Haka Ina murmushi na Shiga ciki,sallamar ya amsa Bai ma Sanda ya amsa min ba duk fushinsa sai ya neme shi ya rasa,Ina yini Yaya Fu'ad na Furta kallo na Kawai yakeyi kamar zai hadiye Ni Bai amsa ba,Wucewa nayi da sauri Zan haura saman Umma ya riko Hannu na da sauri,na fisge Hannu na nayi sama,Sallama nayi Umma tana daga ciki Tace Rumaila shigo Mana,Shiga nayi Muka gaisa Umma Tace wannan Irin gayu Haka Rumaila kin samu lafiya kinyi wata Yar kiba Dariya nayi Ina Jin kunya na durkusa tare da gaisar da Umma ta amsa tana jikin mirror tana gyara daurin dankwalinta ta atamfa super,Kinyi yanda nace ko nace ae Umma sun Gama komai ma ke Kawai suke jira, Fu'ad ne ya shugo dakin,Umma Tace da su Iya fa suke suna bangaren Baki kaje ku gaisa, Fu'ad yace to zanje Amma ke Umma fara zuwa zamu zo daga baya,Umma ta Gane shi tsaf Tace to da Rumailan zamu tafi ai, Fu'ad ya Bata fuska yace Umma Wai me nayi Miki ne? Share shi tayi ta Mike ta yafa Mayafin ta fita na bita a baya ya rike Hannu na kam,Mur na Sha nace ka sake Ni na tafi Mana,Yace kwace ki tafi Mana idan Zaki Iya,Ba yanda banyi ba Amma na kasa kwacewa,yace Zaki dawo baza ki fada min ba? Kana daga wayata ne? Ko idan na tura maka text kana gani? Ni Dana dinga kiranki kin San an hanani zuwa Garinku kin dauka ne? Wanne wulakanci ne Baki min ba Dan Kinga na damu dake,Baka San bani da lafiya ba lokacin?na fara magani Ina ta rashin lafiya ai baka tambayi dalili ba,ai sai ki fada min Baki da lafiya ko a text,ince bani da lafiya ka zo garin Kuma bayan Umma sunce karka zo,Shuru yayi Yana Bina da kallo yace ban sani ba ai Fushi nake Yi dake I'm so sorry,ya jikin? Ai Naga kiba ma kika Yi ke kina ta Kara kyau kullum,Naji su Iya ma Ashe harda su Salahu ya hada Haba shi yasa abin akwai mamaki Ashe ba yin kansu bane,nace Uhm Allah ya taimake mu,yace naji dadin hakan,kin barni Ina ta Shan wahala Ni daya duk na rame,Dariya nayi nace Ni banga ka rame ba,Kiji Tsoron Allah Baby nace to Ni dai banga ka rame ba kiba kayi ma,Yana murza yatsu na a hankali yace muje to wajen su Iyan tamu, Rungumeni yayi sosai a jikinsa,Nima na kankame shi zai min kiss na zille Muka fita,Mun sakko Kasa Naga Bakuwa Yusra ta Sha gayu an hakimce Ana canja Chanel da Remote, Fu'ad Yana rike da Hannu na Muka wuce Yusra,Yusra ta kafe Ni da Ido sai ta Raina kanta Kuma,ko kallonta Fu'ad baiyi ba Nima ban kulata ba haushi ma ta bani ta wani fito da kirji Ana hango shatin Breast dinta,Nace Wannan fa itama Yar gidan Nan ce? Yar kawar Momy ce tazo hutu Wai yace,nace Kuma shine take wannan abin kamar gidan Ubanta ita Wai balagaggiya zata ci Ubanta ne Bari na dawo wajen Allah yasa ta kulani ko ta min Shishigi sai dura mata ashariya,gantalalliyar banza Haka akeyi kizo palon mutane ki saki jiki wani sharab taje can wajen Momy din mana, Fu'ad Yana jina Ina ta masifa har muka karasa wajen su Iya na kwace Hannuna Muka Shiga da Sallama.

mun Iske Abbi da Umma,naje kusa da Iya na zauna,Iya ta kalli Fu'ad Dake gaida su harda rusunawa,Iya Tace dama kana gidan ne? Yace ae Iya,Umma Suka ji Hira ta barke tsakanin Iya da Fu'ad,ya Iya biyewa Iya.
Iya Tace yaro ya bayan saduwa?ya akaji da mutuwar Nan ta zamani ta farar daya? Fu'ad yace Alhmdllh,dan kuwa ita ake fama yanzu wannan yanzu zakaji an kwanta dashi lafiya sai a tashi sai dai gawarsa,Iya Tace wallahi fa Kawai mutane a koma ga Allah yau mune gobe ba mu ba,wani Haka Rannan Dan makwafci na a gona suna noma Kawai sai gani akayi ya fadi,aka zo Kansa Ana Haladu Haladu Shuru kake ji Ashe har mala'ikan zare Rai yazo ba a sani ba, Fu'ad yace da Iya Eyyya Allah ya Masa Rahma Iya Tace ameen,ai Mata suna cikin wani Hali musamman Yan Mata Ana ta tsince mazajen Daya Bayan daya, Fu'ad yace Wanda sukayi saura sai su dinga auren Uku Uku biyu biyu hudu hudu,Iya Tace Kai Dan Nan Uwaka Fu'ad da 'yata a ciki bance ba to,Dariya aka dinga a palon Har Abbi da Umma Iya Bata so ayiwa yarta kishiya.

Iya sai ta daina zancen mutuwar mazaje ta koma wani zancen,Tace Fu'ad Ashe Haka Allah ya wadata ku? Dariya yayi yace Iya Ina ta fada Miki idan kin ganni Kinga kudi kika ki yarda,Iya Tace na yarda yanzu Naga zahiri Ina garin Nan sai ka cika min Alkawari na anyi min jiniya da motoci yanzu fara kunna min kallo ga Tv, Fu'ad ya kunna katuwar Plasma Chanel din Ball akeyi Wato kwallon kafa Ana ta Kokawa,Iya Tace Kamar zaka dakko mutum da Allah ji garau Kamar na shige ciki.

Yan Ball Ana ta Kokawa tace kayyasa Kai maza kauce Nan to Dan Ubanku Wai a Basu kwallon da yawa Mana kowa ya dauki tasa Dan jaraba akan kwallo Daya zaku kashe kanku,Da yatsa Iya ta nuna wani bature da Alama shine couch Iya Tace Kai Dan Ubanka ka zubo musu kwallaye da yawa kowa ya dau tasa banza dakiki,Dariya muke tayi Iya taga wani yaje har Gaban raga ya kasa ci,Iya Tace Amma wannan yayi asara ku cire shi,Haka akeyi Dan Ubanka ko Ni naje Gaban raga nayi wannan bugun, Fu'ad kaga wani buga kwallo Dan Allah wani shafal Shafal....aka nuna wani siriri Iya Tace da ganin wannan baturen matarsa Bata bashi abinci Yana koshi banza Mijin Tace,Fu'ad yace kamata yayi a daina biyansu Albashi,Iya Tace wallahi kuwa musamman wannan masu fararen kayan,kaga wani dai wannan da gani bazai tarbiyya ba,wannan Uwarsa da Alama fama takeyi da shi,wani ma yaje ya samu dama Amma ya kasa cin ball Iya Tace Dan Allah canja Mana Tasha wannan ba Yan kwallon kirki bane duk jakai ne,ko Ni na samu damar wannan sai na zura kwallo a raga,Dariya Mukayi.

Fu'ad ya Kai American film Ana ta harbi Kawu yace yawwa bar Mana Nan,Iya Tace karyar zaka kalla kai Canja min Tasha, Fu'ad ya kamo Hausa film Iya ta gyara zama Tace yanzu Naga dai dai,Umma ta kalla tace Ina abokan zaman naki Basu zo mun gaisa ba ko bakwa zaman arziki ne mu shirya cin ubansu muma? Umma Dariya tayi Tace haba zasu so ne,Abbi yace ai na Kira

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login