Showing 21001 words to 24000 words out of 133505 words
shima yayi nasa Suka fito Yana ta Jin Dadi suna zuwa gida dubu goma kacal ya bawa Gaji bayan siyayya Daya dan mata wacce bata taka Kara ta karya ba,tayi godiya Itama ta tafi tana tuna irin dadin da taji tace dama haka abin yake masu aure Kun ci uwaku da bakwa fada Mana gaskiya sai kowacce kinibabba tayi mukus a gidan mijinta sai da ta gama haukarta sannan ta shige gida, su Gwaggo harda guda yarsu tayi goshi,Aunty Amarya tace ke Kam Yar nan kinyi goshi Gaji tace rankwalele ma Kuwa goshi Kato sai kyalli suna ta dariya Mairo tace Sis Ina tayaki murna,Gaji tana murna ta furta don't worry sister verysoon Zaki samu naki kema,Mairo tace Allah yasa.
Nawwar ne zaune a dakinsa yana tunani yace Oh God karfa na Shiga hakkin yarinya ni bani da cikakkiyar lafiya gaskiya nayi magani har na gaji, yace dole na hakura da ita haka naci gaba da neman magani,kudin da ya ajiye bai kai bank ba da dadewa ya tuna wajen ya Bude kudi yace daukeni inda ka ganni sisi babu a ciki,Sabreen duk ta sace su a hankali wasu ta bawa mama wasu Kuma tayi shaye shaye da su,Kira ya kwala mata tana jinsa tana Palo tana latsa wayarta yar aiki tana Mata tausa a kafafu tace banza,me aikin tace Auzubillahi wallahi a Zamanin nan ana kuskure da yawa matan yanzu koya miji ya bata musu sai ta dinga zaginsa wasu a gaban kawaye idan an hadu ana zancen halin maza,wasu idan sunje gida wajen Yan uwansu ko a gaban iyayensu su dinga zagin miji sabo da ya musu laifi wlh ba kyau Mata ku gyara,tsawa Sabreen ta bugawa dattijuwar da ta haife ta tace wallahi Zan koreki a aiki banza munafuka Ina ruwanki ko kanin ubanki ne dan an zage shi to na zage shi na Kara taja tsaki ta mike tana kutuntuma ashar ta haura sama a gaban Nawwar Kuwa mukus tayi ta tsaya tare da furta gani,yace baki ga kudin Dana ajiye ba ko kin canja musu wajen ajiya? Direct tace nayi amfani dasu nayi uzurin rayuwa da su,Ido ya zaro tare da furta for real? tace ae Ina bukatar kudade Kawai na kwashe,kin San nawa ne Kuwa? Oho maka,cikin tsananin Fushi ya furta are you out of your mind? baki ta tabe tare da gyara dan guntun wandon da ta saka tace nifa kaga ka daina min tsawa akan wasu chicken change me yasa ka fiye takur....Mari taji ta ko ina yace kudin ubanki ne ya nemo min Ina tunanin baki da hankali ke karamar Yar iska ce bari na nuna Miki na fiki Iskanci waya ya jawo tace Allah ya Isa shege ai Kuwa ya hau tafkarta sai da ya fasa Mata jiki ta gudu da kanta tana kuka wiwi,kayanta ta shiga hadawa ya fito zai fita sanye cikin 3qtr da riga me gajeren Hannu yayi kyau,ganinta yayi ta saka akwatinta a motarta taja ta bar gidan a fusace yace tafi nono fari Ina tunanin faranta Miki kina min shirme yaja tsaki ya shiga motarsa rantsatsiya ya bar gidan zuwa gidan babban abokinsa Wanda shi Yana da mace da yaransa biyu Khaleel kenan.
Sabreen da kuka ta shiga gida Mama ta tare ta tana tambayar lafiya? tace wannan Dan burar...Dan kutmar....tsinanne azzalumi mugu shine ya dakeni akan kudin nan, Mama tace Yar tamu guda lallai Nawwar baida mutunci bari Papanki ya dawo a sanarwa kakarku Iyamami ita zata dauki mataki tunda ita ta haifi ubansa,suna zaune Papa ya shugo da murna ya samu wata kwangila zai samu kudade ya iske Sabreen ya tambaya lafiya? Mama ce ta fada Masa komai harda cewa bazan yarda ba a kashe min yarinya ta tilo,Papa yace akan wasu Yan milliyan biyu zai kashe min ya lallai yaron nan Wasa yake dani wlh Naga dama sai na hanashi sakewa a rayuwa,bari naje ai Iyamami ce maganinsa Kuma duk abinda nace ta zauna daram.
Bai ko zauna ba ya nufi part din Iyamami inda Yar aiki ke Mata gyare gyare tana ganin Dan nata tasan ba lafiya, tace lafiya Yusufa? Ya kwashe zance ya fada Mata harda cewa yanzu Sabreen ba Yar uwarsa bace ai shi me bata kudi ne bare gata matarsa,Iyamami tace itama bata kyauta ba da ta satar masa shi Kuma Dan ubansa sai ya dake ta,dama na fahimci yaron nan yanda yake jiji da Kai magana ma aikine a wajensa ni gaskiya ki yiwa ubansa da uwarsa magana,Iyamami wayarta ta jawo tace kamo min number dinsa,Lokacin Nawwar suna ta labarin kwallon kafa da abokansa yaga Kiran Iyamami,Tsaki ya dan ja yasan zancen Khaleel Yana kallonsa ya daga Iyamami ko jira batayi yayi magana ba tace Dan ubanka kazo Ina neman ka,to yace Kawai ya kashe wayarsa,Khaleel ya kalle shi yace lafiya dai? yace hmm Kai dai bari wannan Yarinyar Sabreen Mana tunda na aureta wlh Banga amfaninta ba a wajena daga bacci sai sata,sata kuma? Ae sata fa dama Ina ganin ana sace min kananun kudi to yanzu har million biyu ta kwashe ban sani ba,gata bata da kunya bata da respect zata iya cin mutuncin kowa Dan iskan baccin nan nata na rasa na mene mace ta kwana ta yini tana uban bacci,kasan Ina ta Shirin ci gaba da magani akan rashin feeling dina sabo da na dinga bata hakkinta amma Yarinyar nan harda zagi,Khaleel yana tausayin abokinsa yace eyya sorry kaji sai hakuri kaci gaba da hakuri,yace bari naje sabo da Iyamami itace ta haifi Baffa Ina girmama su sannan Mami zasu ciwa mutunci idan Baffa yana gari bazai so na wulakanta Masa uwa ba shi yasa nake Mata biyayya su Kuma gani sukeyi Kamar isarsu ce ta sa,shima Papa Ina ganin girmansa shi yasa nake zaune da yarinyar,Khaleel rokonshi yayi yace ka Kara hakuri kaji yace Inshaallah ya wuce gida.
Yana zuwa Iyamami ta hau bala'i harda kuka tana cewa inama ubanka zai dawo yau ko gobe daga kasar waje ya gani yanda kake wulakanta jininsa wallahi kabi duniya a sannu Yarinyar tace baka kwana da ita,Nawwar idan baka da lafiya ka fada na tafi Kauye na hado maka magani,Shi dai Yana jinsu har ta gama yace bani da lafiya Iyamami abar bata tashi,a gaban kowa ya fada ko kunya,Iyamami tace Sannu Allah sarki za'a Nemo maka magani dan Allah kayi hakuri ku zauna lafiya da Sabreen, Sabreen tana daki aka kirata ta fito idonta duk ya kumbura,Mama tana Fushi tace ke koma ki huta gobe na maidata da kaina ko nace idan ta warke,Iyamami tace to kaji,yace ba damuwa,Iyamami tace gobe Zan tafi Kauye kaji,yace to,Papa yace Dan Allah Nawwar Dana karka sake kaji kaida Yar uwarka itama munyi Mata fada baza ta sake ba,Nawwar dai yace to Suka gama ya wuce gida ,Mama da Papa suka sa Sabreen a daki suna fada Mata lallai Yana warkewa ta saki jiki ta haihu da shi idan ta haihu da shi to sun gama mallakar dukiyarsa da komai sai yanda Suka yi,haka suka zugata sosai ita Kuma Iyamami an tafi Kauye karbo magani,kwana daya tsakani sai gata ta dawo da tarin magungunan gargajiyar ciki harda rubutu har gida ta samu Nawwar ta karanta Masa yanda zaiyi amfani da magunguna,wani dan itace ta Mika Masa tace rike idan abar ta harba ko ta mike ka fada min,Nawwar ya karba ya rike Shuru ko motsi tace,yana rikewa ta furta to ya? yace ai ko motsi bata yi ba ko na nuna Miki? Iyamami tace gidanku fitsararre dariya yayi sosai hakoransa kyawawa Suka bayyana,Iyamami tace ji yanda kayi kyau kana Murmushi ashe mijin nawa dai yana dariya,yace idan magani yayi aiki sai a fara ta kanki dukansa tayi ta mike tace marar kunya ba ta tafi abinta,shi dai bai zaci magani zaiyi ba a banza yake kallonsa sabo da yayi masu tsada ma baiyi ba har na asibiti Shuru sai wannan garin ganyen bishiyar haka yana tabe baki yana wani kyankyami a haka ya fara amfani da magunguna.
Miracle...Miracle....Fitowa nayi da gudu naji muryar Yar zabil Ina Fitowa tace wanke wanken fa waye zai miki? nace kiyi hakuri na tafi nayi Mata na gama dakinmu na koma na samu Seraline ta kalleni tace Rabi ki daina zubar da mutuncinki a gidan nan duk layin nan babu me kyawunki Rabi kin tsaya a wanke wanke da shara wasu banzaye suna wahalar dake Wanda da zaki Fara sana'ar nan nasan sai kinfi kowa customers,yanzu kudin da kike samu basu isarki ci da sha da biyan haya bare kiyi saving ki fara gaki yanzu kin waye kin goge kin Zama tsagera wata Maganar da kike fada ko ni Watarana sai na daure zan iya furtawa,nace sana'ar ku bazan iya ba Ina tsoron Allah duk iskancina a baki ne wlh,to naji Kinga yanzu dare ya kusa zamu je aiki ki shirya muje dake kiga yanda ake harkar ki bawa idonki abinci ko banza kyayi kallo Zaki ga yanda ake aikin sai ki dawo gida nace wannan dai zan iya,to ai bani da Kaya masu kyau na fita,Sera cikin kayanta ta zabo min wata gown silver and black me tsadar gaske amma bata fi rabin cinya ba,ta fito min da dankunne da agogo me kyau da takalmi me dan tudu sai hular gashi dogo me tsada tace shirya,kayan na kalla nace a haka Zan fita tsirara haba Sera Allah Yana kallonmu fa,tace Kinga idan zaki sa kisa malama tana min masifa haka ta tayani na shirya,wani mahaukacin kyau da nayi itace ta min make up me kyau sama sama,duwawukana Kamar zasu fado ita kanta Sera sai data tsaya tana kallona tana yaba surata,Fitowa mukayi matan gidan duk sun shirya wasu ma tuni suna can gefen kwalta titin da ake zuwa me kyau inda yake kusa da layin masu Hannu da shuni,yan daudu na gani sun cakare Suma sun tsaya a titin Mata masu kudi suna zuwa suna daukansu wasu Kuma maza yan luwadi suke daukansu abin ya bani mamaki ga haske kamar rana wani nishadi nake ji,duk motar data wuce su Sera suna binta suna furta customer,suna nuna musu jiki suna tura musu duwawu,Idan me mota Daya ya tsaya sai su yanyame motar Kamar zasu afkawa Namiji ya fito ya zabi wacce ta masa,Ina kallon ikon Allah sai dariya nake yi.
Wata mota ce me tsada ta tsaya Suka tafi da gudu tare da yanyameta sai Kuwa Suka ga mace Yar gayu babbar mace ta fito ta duba cikin Yan daudun ta zabi Wanda ake Kira da Santana ya balle Mata botin rigarsa Yana karairaya taga ya Mata ta jashi Suka Shige mota,ihu na saki Ina Dariya nace wayyo ana tallan duwawu,ba shegen da zai bi ta local government dina my GRA wlh lala babu me shiga GRA na,juyawa nayi Ina tafiya dagwas dagwas na koma gida abina Ina Allah wadai da wannan sana'a Wanda Hausawa musulmai Suka Fara tsunduma kansu cikin irinta su hada jaka su tafi street Ashawo.
Washe gari ma haka na cakare cikin kayan Seraline Muka je Nasha kallo tun abin baya birgeni har naga suna ta tara kudi ni ana ta barni a baya sai tura kudi sukeyi gida ana siya musu gida da filaye da kudin ashawo duk sun tara kudi a tunanina fa,ni kuwa kowa sai kallon banza suke min,sannan ba mutunci kwandala babu me baka kyauta,bayan satikai haka kawai Katsam ba abinda nake so nima sai Karuwanci yau dai na sa a raina zan fara Karuwancin nan nima na samu kudi amma me tsada zan yi sai idan namijin yayi min sannan sai idan da kudi da yawa,Shigowa nayi dakinmu da dare na samu Seraline tana shirin fita nace Kawata na sa Raina yanzu Kam Zan Fara Ashawo work dinan ki ci gaba da bani aron kayanki kafin na samu customers na siyi nawa,Saratu taji dadi tace ko kefa maza shirya baki da matsalar kayan sawa Kinga yanzu 10pm Kar mu makara,da sauri na Fara shiri na dau wanka cikin dogon wando tight da Yar riga karama nayi kyau matuka Muka tafi,gefen titin Muka tsaya tunda naje motoci ke tsayawa daukana amma kowa yazo sai nace Million daya daga nan me motar zai dauki wata ya barni nan tunda wasu gasu nan 2k 5k ma daukansu akeyi idan customers basu zo da yawa ba,Haka yau ma na koma gida ba kowa,washe gari aka sake fitowa dani nan ma nace sai Million daya kowa sai ya min kallon banda hankali, wani bahaushe ne yazo a Yar karamar motarsa ya tsaya tare da Fitowa Yana Kare mana kallo ya kalli mandula yace juya na gani ta juya sosai ya barta nan ya karaso wajena baki na tabe,yace juya na gani na juya a gabansa ya jinjina Kai yace kinyi muje ko nace kaje da wa? You dey craze? Kasan kudina Kuwa? Nawa to ya furta Yana kallona nace million daya zuwa sama,Ido ya zaro yace ke Kuwa sai kace matan gidan Aljanna zunubi ne fa ga tarin zunubi sannan ga tsada haka,kaga ja kayi gaba ko yanzu na tarwatsa maka kwakwalwa wlh bani da mutunci da kake gani na ja tsaki, wuyana ya shafo kafin ya zare hannunsa na kwashe shi da Marin da yasa ya gigice sauran karuwan Suka goya min baya gamu da hadin Kai kafin kace me mun kashe titi da fada da kyar ya kwaci Kansa ya bar wajen a guje cikin motarsa muna binsa da zagi nace shege ko maza sun Kare me zanyi da Kai na ja tsaki Ina gyara gashina sannan Ina tauna chewgum kas kas kas...
Nawwar magungunan Iyamami ya raina su ganin yayi masu tsadar gaske ma amma me sai yaji idan yaci ya koshi ba abinda yake bukata sai mace,sai da Sabreen tayi 3days sannan aka dawo da ita gidansa bata canja zani ba sai ma rashin mutunci data karo,Yan aikin ta fara ci musu mutunci dama hakuri suke yi da ita idan Coccaine dinta ta motsa haka take daddana musu ashar bata da respect,Daya Yar aikin ta hada kayanta ta gudu Sabo da zagi da cin mutunci sannan bata basu abincin kirki a dafa ayi komai amma ta hana su,Ladidi me girki ce ta rage sai maza masu aiki su dama yawanci kudi yake basu suci abinda suke su sunfi son ma a Basu kudin har canji suke samu kullum,Ladadi ce ta fito Kawar Sabreen tazo Jamcy ta kawo Mata lemo,Sabreen tace ke tsohuwa wannan Kawai zaki kawo shine kadai a gidan? Ladidi tace Zan kawo ai Hajiya ban gama abinci bane,Wai ke wacce irin dabba ce ne,Ladidi da mamaki ta kalli Sabreen domin tayi kusan jika da ita ma,tace dani kike Hajiya? No da uwarki nake dalla wuce ki kawo Mana snacks,Ladidi tace ko ba komai Sabreen ai naci darajar furfurata sannan ni nasan nayi jika dake amma ki iya kallona ki zageni, Sabreen daga Jin haka sai haukar kwaya ta motsa ta zabgawa Ladidi Mari,kumatu Ladidi ta dafe hawaye ya shiga sintiri a kumatunta juyawa Kawai tayi ta shiga bangarensu ta hado kayanta tana hawaye ta fito zata tafi,Jamcy tace wannan shine dai dai banzayen Yan aikin nan sai su dinga hada kansu da me gida, Sabreen ko a jikinta tace kina jina dan iskan mijin nan nawa Watarana Yana birgeni da baya shiga safgata inyi shaye shaye na lafiya lau dariya Suka Yi tare da tafawa dukkan sirrin Sabreen ba abinda Jamcy bata sani ba ko hannu Nawwar ya rike Mata to sai Jamcy taji labarin ita kuma Jamcy wayo gareta bata fadawa Sabreen sirrinta sai dai dai, Motar Nawwar ce ta kunno Kai cikin gidan cikin jerin motocinsa yayi parking sannan ya fito ya samu Ladidi da kayanta tana kuka zata tafi,da sauri ya fito ya tareta Yana Tambayarta lafiya tace matarkar ce ta zazzageni sannan ta mareni,Nawwar zuciyarsa ta harzuko tsohuwa haka, muje Baba Ladidi tabi bayansa tana cewa ni gida zan koma na zauna gaban yarana har abada na daina aiki a gidan masu kudi Ina da gata na,suna shiga palon a tsawace yace ke har kina da damar Marin Baba Ladidi ubanki ta miki ya karasa Gaban Sabreen tace dan Iskanci na....Saukar Mari taji ba daya ba ta ko Ina,Ladidi tace na gode Alhaji ka rama min, Wayar tv ya fisgo ya tsulawa Jamcy itama ya haukace musu,Jamcy ta mike ta fice da gudu ta bar gidan Sabreen ma taga zai Mata illa ta buya a kitchen ta saka key, Kudade masu yawa ya bawa Ladidi tana ta godiya ranta fes an rama Mata ta tafi gida.
Gidan ya zama babu me girki Kuma Babu me gyara ciki Sabreen tace itama ba baiwa bace baza tayi ba,Dakinsa ma da Kansa yake gyarawa,kullum ita Kuma sai baccin asara,Yana gama shanye maganin Iyamami sha'awa Kamar ta kashe shi kullum da kyar yake bacci,haka ya gaji zai Kai Kansa wajen Sabreen,yau 10pm a Palo ya sameta tana kallo sanye cikin rigar baccinta, karasawa yayi sanye cikin kayan baccinsa masu kyau silk milk, Yana zuba kamshi da mamakinta sai ta ganshi ya zauna a gefenta yana kallonta a hankali yace nazo karbar hakkina yau,ban gane hakki ba? yace Sex I need you,a ranta tayi dariya tace dan iska akace baka mikewa an fada maka ni ta Wasa ce ai dole ayi Mana biyayya dole na ja Masa aji sai yayi kuka ya tsuguna a gabana dan iska,a fili kuwa tace bana bukatarka ni Kam,kallonta yayi ya saki wata Yar budurwar dariya yace sabo da na kawo kaina hakkinki zaki sauke Nima na sauke nawa Kuma Ina bukata ko na taba hanaki wani hakkinki? banda wannan Kuma shima kin San banda lafiya yanzu lafiya ta samu,wani kallo ta Masa na baka Isa ba ta mike tace bani bukata ta haura sama tare da shigewa dakinta ta fada saman bed tana uban dariya tace zaka ci ubanka sai ka durkusa min, tana tunanin zai biyota sai taji Shuru har tayi bacci,Shi kuwa wani bacin rai ne ya mamaye shi Wai kamarsa