Showing 66001 words to 69000 words out of 133505 words

Chapter 23 - Yar Aikin Karuwai Book 1

22 Oct 2024

3878

ihu Yana Karuwai in action wlh an taro Barcelona da Madrid Dole a caskale wuuuuuu yau ana batakashi da kyar makwafta Suka kwaci Gwaggo Amma duk da haka zage zage take tana haki,Aunty Amarya suna fitowa ta sawa dakinta key,Dagaci Kansa buya yayi a dakinsa yaga shima zamu iya dukansa, mu kuwa ficewa Muka yi mun Gama kullawa dagaci yanzu kam,Dagaci yace ayi auren mu gani idan Zaki ji dadinsa gobe Kuma iya yina saina rusa auren nan kwafa ya ja ya tafi Yana lallashin matansa,Mero ta fara kuri tace ai sun tafi da su tsaya Mana su gani Ina ma Gaji tana nan yau da sai dai a mutu.

Sai da Muka gama yawonmu sannan Muka koma gida 11pm Muka kwanta bacci, a ranar Mairo ta Kira Gaji ta fada Mata abinda muka Yi musu,ita ga yar masifa tace gobe da wuri zanzo zasu ga inda ake masifa. washe gari tea Muka Sha harda harda kwai aka soya Mana duk kudi Muka bada aka siya, su Inna sun gama tuwon daurin aure da akeyi a kauyen tuwon danyar shinkafa miyar taushe duk an kwashe a Leda an adana a manyan cooler, 11:30am ne daurin auren,sabo da haka 11am angwaye Suka zo,duk munyi wanka ko wacce ta saka sabon kayan data dinka na kece raini Malika ta iya make up itace ke musu tana musu dauri,ni kuwa Amarya tsadajjen leshi na saka white and golden takalmina golden da jakata da mayafina,wata gown aka dinka min fitted amma a tsakiya an yanke rabi anbi wajen da adon abu,ta gaba sai kace riga da skert ne amma ta baya kuma fitted gown ce nayi mugun kyau, dake mulmul nake dai dai dani ga mazaunai manya sai na fito wata Queen,Mandula ce tayi parking da mota a gaban angwaye dake sanye cikin manyan shaddoji abokan ango da Yan uwan Baffa na can maiduguri da shi Kansa Baffan suna cikin hadaddiyar mota Baffa Kamar ya fasa ihu Yana ta kunci dansa zai auri bare marar asali Kuma ga Kauye ma abin ta ko Ina ba kyau, Nawwar da rukunin abokansa sun Kai su ashirin da wani abu harda Auta Nawaf kanin Nawwar, ango ya sha wata farar shadda da babbar riga ta zamani ya coka Yar hula kalar takalminsa farare komai fari,motar ma da aka dakko shi daga airport Fara,irin kyan da ya zuba ba a cewa komai kowa shi yake kallo a wajen,Ni Kam me Make up tana ta tsarani tsaf,Mandula ce ta murzo motar da Nawwar yasa aka Kai Mata a cikin birnin Kano taci wankanta itama cikin wani danyen material peach ta Sha make up light,takalminta me tsini ta fito gasu dama da kibarsu ba rammiya sakamakon supplement na yanzu da Mata ke dannawa cikinsu,Fitowa tayi tare da bude bayan motar komai an shirya shi na musamman take away dinmu ma da aka zuba abincin na daban ne,har lemuka duk an zuba a jakar take away din,su Sera ne Suka fito Suka tayata shigar da kayan ciki,ta Kira Khaleel ya bude bayan motarsa ta zuba musu nasu abincin na angwaye,aka bude mota Daya cikin na Iyayen Ango aka basu nasu da yawa, Suma aka ware nasu aka saka musu a mota sai da Mandula ta sallami kowa Saura na Yan daurin aure mutan kauye za a karasa basu,sun ware nasu Dana bakin su,tana gamawa ta kulle motar ta tako zata wuce Nawwar tace ango tana Murmushi yace sannunki kirjin biki,Auta ne yazo da sauri yace Ina Amaryar Yaya,Nawwar yace ga kawarta nan bita ta kaika wajenta,Mandula ta rike hannun Auta,tace ya sunanka yace shi Auta Kawai ake fada masa tace to,ya zama dan saurayi suka shiga gidan da shi, Kawai yaga Yan Mata iya Yan manta ya rasa wace Amaryar ma, an Gama kwalliya dauri ake min Yana ganina yace wannan ce ma amaryar naga tafi kowa,gabana ya tsaya Ina ganinsa na gane kanin ango ne domin sunyi kama,yace Amarya nace Auta ne naji ai Mami tana zancen Autanta yace ai duk tafi so na,nayi dariya yace yunwa nake ji Aunty,nace a bashi abinci ya zabi waina da miya yaci yasha lemo da ruwa yaci ya koshi yace anjima zanci fried rice nace to Allah ya kaimu,masallaci ana shirye shiryen daurin aure Dagaci yazo aka nuna Masa uban Ango da Ango Kansa

Bakin ciki ya kusa kashe shi yace da gaske masu kudi ne ai larabawa ne cab ai sai yaje wajen Baffa ya Mika Masa hannu Suka gaisa yace bawan Allah mutum me Kamala irinka ka yarda danka ya auri Yar tsuntuwa tsintarta fa akayi,Baffa a ransa yace wallahi nima dole ce ta sa,amma a fili sai yace ae ai mun sani ita Yar tsuntuwa ba mutum bace? Iyaye ne suka haife ta sabo da Haka yaro Yana so Allah ya nufa wa ya Isa ya ja da ikon Allah,jikin Dagaci yayi sanyi matuka yace Babu riba Kawai na koma wajen malamina yafi min a daura kawai sabo da bacin rai zamewa yayi bazai ji an daura a gabansa ba ya koma gida,Liman sai Neman Dagaci yake a matsayinsa na Babba a gari Kuma Wanda ya rike yarinya amma an neme shi an rasa ashe dan kar ma aje nemansa gona ya tafi ya samu bishiya yayi shimfida ya kwanta Yana bacci abinsa.

Mutanen garin sunyi Kara sun cika kamar kasa cikar da ba'a taba Yi ba a garin a daurin auren wata sai akan Yar tsuntuwa kaf garin nafi kowa tara dan Adam,wasu ma kallo ya kawo su,dubban jama'a ne Suka sheda daurin Auren Rabiah ta daina amfani da sunan Dagaci a matsayin Uba tuni ta koma Rabiah Muhammad Nawwar tunda bata da kowa a duniya ta zabi Muhammad Nawwar,Jin sunan da Liman ya kira ya sa Nawwar Jin dadi harda sunansa a sunanta Rabiah Muhammad Nawwar,shi Kuma Nawwar Ibrahim, Baffa shine waliyyin Amarya,Nawwar ya karbi Aurensa yanda yace babu Kara,ga masu uban Dj sun shirya tsaf,Sadakina dubu dari biyu,Jangudo da yaransa su Suka dinga raba goro a wajen da alawa sannan suka fitar musu da abinci tuwon da su Inna sukayi,Fitowa mukayi gaba daya kallo ya dawo kanmu,Nawwar ya tsaya a gabana nace to an daura? ya furta uhm,Nan aka Fara zuba ruwan pics ta ko Ina wayoyi ne ke tashi,ana haka me Dj suka saki ganga kida Kamar zai fasa kunnen mutane, Wise ce ta fara bude rawa a gaban dattijai Yan daurin aure Basu watse ba ta fara takawa kowa ita yake kallo,Abokan ango an baza Ido ana kallo wani Sabeer a cikinsu yace wannan tsagera ce ta kirki,Murmushi muka Yi mun San bai ga komai ba,Kafin mu rufe baki Malika taje tana mata liki farrrrrrrr da Yan dari dari tana gamawa tabi sahu tana cashewa,dariya ta Kama angwaye dan Kuwa Malika gwana ce a rawa yanda ta duka ta tana wargaza mazaunai tab,Wasu su Sera Suma suka shige suna zuba liki suna rawa,Angwaye ai sai Suka gyara tsaiwa Suka ce sun fasa tafiya yanzu Suka fito da take away dinsu,fararen kujerun da Muka aro haya aka jera musu da yawa Suka zauna a gaba sauran Yan kallo Mata da maza suna baya mu Kuwa iya kawaye Muna ciki,Mc yace Amarya kadai ake son gani a fili ai Nawwar yasan ya Zama dole nayi rawar nan ya sani ma shi yasa Bai ce ma komai ba.

Duk fili suka bani na shiga aka canja min kida tun Ina Yi kadan kida Yana ratsani na karbi speaker nace Ango ka yafe min Zan tsokani shari'a da Speaker a hannu nake rawar Ina Jin kunya Wai a haka amma yanda nake Cashewa,Auta kanin Nawwar ya shigo Yana min liki hannayensa na rike da hannayena biyu Muna facing juna a haka muna rawa kasa ai Kuwa kawaye Suka rufe ni da ruwan Naira Dj yana caskar kudi,suna fita Angwaye Suka shigo Kai an zubar da Naira Kan uba,gajiya nayi na fita sabo da make up dina,Nawwar ko daya bai ma tashi ba tukun yace zaiyi nasa, Kawayene Suka shiga su Uku Malika da Wise tare da Manduwa yau ana Shan kallo Yan kauyen sai ihu suke ana kallon iya shege karara a haka ma munyi da sauki,suna fita aka Kira Ango da Amarya Muka mike muka shiga sabo da iyayin Nawwar Wai a filin rawar za a sa Masa kujera kamar wani sarki ya zauna a tsakiyar wajen Yana Shan ruwan roba,ni kuwa rawata na dinga yin cin koshi ka rantse ba Amaryar bace,mikewa yayi ya dinga zuba min ruwan Yan dubu dubu, ana ta dauka a wayayi,Sera ce tazo ta min rada kuyi kiss zamu dauka a waya nace bazai yarda ba,sai kace ba mace ba ai karuwancin Zaki tuna,dariya nayi Ina dan takawa yana min liki,na dora hannuna daya a kafadarsa na maida dayan ma a kafadar na dora yace ta ya Zan Miki likin Wai bakya Jin kunyar mutane ne fa abokaina zasu ce baki da tarbiyya nace sai yanzu suka sani kiss zamuyi dauka za ayi zai zame nace Allah kana guduwa sai na kunyataka a wajen nan ka sanni, ai Kai kace kaji ka gani ka aureni, mu bama Jin magana ka bani hadin kai,yace to kiyi sauri na gaji,Yatsa na dagawa su saira su dauka haushina yaji Yana ta fada bai Dace ba wannan a musulunci Wanda yanzu ya Zama ruwan dare mutane da yaran masu kudi gani suke birgewa ce wayewa ce,a hankali nace kaine fa zaka min Ido ya zaro tare da furta na shiga Uku nidai,please karka kunyata ni Zan kunyataka wallahi, Ido ya rufe aka canja slow music a hankali na dora bakina a saman nasa ya min kiss a nutse ana dauka na rungume shi sai aka dauki tafi da ihu yeeeeeeee Yan kauyen Suka Fara cewa yeee ya tsotsi bakinta alquran,billahillazi bakinta ya lasa kunga sun rungume da gani sun Saba tun a waje,Yan matan kauyen shewa Suka dauka yau Muna ganin bariki yehoho ahayye chasss...,Khaleel bai taba zaton abokinsa ya fetse haka ba sai yau dariya ya dinga yi, sai da Muka gama likawa juna kudi Yana min Ina Masa sannan Muka fita,Khaleel yace Lover boy,Nawwar ya hade rai tare da Zama,abokai su abin ya birge su sosai dama duk gasu Yan gayu yaran masu kudi,Wise bata gajiya sake shiga tayi tana yiwa kanta da kanta liki tana cashewa,Autan su Nawwar yaga duwawuka sai tsalle suke yace wow ya radawa Nawwar irin wannan Zan Aura nima Yaya idan na girma da wuri za a min aure,Nawwar yayi dariya a ransa a fili yace sai kaci ubanka wlh ni ban San ma ya akayi ka biyo mu ba,Mami ce tace nazo yaci gaba da cewa Auren Kauye za a min da wuri ni wallahi ba sai na girma ba,na daina kula Yan class dinmu wajen Aunty Rabiah zanzo ta hadani da kawarta,Nawwar yace sai na zaneka bari mu koma gida tunda baka kunya,Shuru yayi bai sai sake magana amma ya zurawa Mata ido.

A wajen muma muke cin take away dinmu har Yan Kauye Suma sun samu da yawa sun samu, tare zamu tarkata da angwaye mu koma can Anambra, duk munfi yin rawar wakokin Yan kudu su Muka iya Kamar kannen Naira merly, 2pm aka tafi Sallah wanka Muka sake tare da canja Kaya wannan karon ba make up Kawai dauri mukayi kowa tayi wacce zata iya, muka fito na sha shadda dark purple nayi kyau, su Kuma ankon Atamfa Suka saka me kyau sunyi kyau daga nan aka dora da kida da rawa tare da sabon liki, babu Wanda zai so ya bar wajen nan,sai lokacin muka raba waina da miya aka sake ci da ruwa da lemo, bamu Ankara ba har 5:30pm sai Inna ce tazo tace Yan Kai Amarya sun shirya,sannan Muka tashi daga kida,masu kida Suka hada kayansu da motarsu suka tafi abinsu suna murna sun Sha kudi.
A gurguje nayi wanka sabo da zafi na canja cikin Net less fari yasha hadadden dinki na Sha takalmi da jaka fari aka min dauri na yafa mayafi me kyau fari da adon silver,turaruka na shafa Wanda kayana komai an tattara su tuni sunyi gaba Angwayen da Suka Fara tafiya su aka bawa Suka tafi da komai dama kayan lefe ne, Wanda na cire Kuma Sera ta ninke ta tattara komai a jakata da na zubo kayan sawa na biki suna wajenta tsinke namu bamu bari ba, Jangudo ne yace tunda Kai Amaryar ba addini bane iya kawayen ma sun Isa ga angwaye ai sun Isa Kai Amaryar

Ba sai an sake wahalar da Ango ba Watarana idan ta haihu sai aje Mata,Inna tace hakan ma shawara ce shike nan aka fasa a Raina nace da ace Ina da iyaye Dole sai an rakani dakin miji amma ya zanyi haka Allah ya tsara min wannan yasa zuciyata ta karye na fashe da kuka,duk sun zaci kukan Kai Amarya nakeyi Suka dinga dariya Yar bariki da kuka za a kaita dakin miji suna ta tsokanata, Nawwar ganin Ina kuka dariya ta Kama shi yace Amma Yarinyar nan ba karamar Yar rainin hankali bace lallai Ina ganin Yar duniya,ki gama tikar rawa gata dama zaman kanta takeyi ta Gama sanin da Namiji me yayi Saura.

Muna jikin Motar da Ango yake tsaye mu da kawayena kaf Inna tana cewa Allah ya tsare kinji Allah ya kade fitina,a zauna lafiya kinji dai nasiha ta to Allah ya bada sa'a ya bada zuria dayyiba na manta ma kuka nakeyi nace Ameen Ameen Allah ya bani me hankali,Inna sai da tayi dariya da su Star ana ta dariya har angwaye, Inna tace aure sai hakuri kiyi hakuri da mijinki komai yace to banda musu da gardama da taurin Kai,ba a jayayya da miji,Miji yafi Gaban Wasa,Nawwar Yana gefe yace dama ta rainani Kuwa Inna,Inna tace wallahi idan kina so ki gama da duniya lafiya kibi Allah kibi mijinki yanzu ba da bane baki da kamarsa,yanzu mulkinki ya Kare shi zai haye karaga shi zai Fara nasa mulkin sai yanda yayi dake,Nawwar yace ai tuni ma na fara Inna,Inna tace lokacinka ne banga laifinka ba dan nan kayi abinka,Amma mace dai ki sani Rabi bata da wani yanci Matukar a gidan miji take,ta kalli Nawwar tace wallahi kai Kuma idan ka zalunci marainiya ubanka zaka ci a wajen Allah yo Allah ba ruwansa,ka kula da ita ka Zama gatanta ka Zama mijin marainiya,kaga Allah Kai ya damkawa amanarta Amana fa aka baka banda banbanci tsakanin matanka ka kamanta adalci, Kar kaji Daya tafi daya iya kwanciyar aure ka wulakanta daya,su Star suka kaure da shewa, Nawwar ya kalli Inna da sauri,Inna tace ae zaka zuba min Ido ku maza imaninku a nan yake da kunji ba bayani to mutunci ya Kare abinda kuka iya kenan soyayyarku kwanciya da mace ba uwar da kuka iya a nan kuka iya soyayya musamman hausawa sai a lokacin za a fara Ina sonki bani da kamarki,kece gwanata,jarumata,dausayin raina, kece tekun zuciyata,ya turmin dakan dake lugude a zuciyata Nawwar ya sheke da dariyar da bai shirya ba,kowa dake wajen motar dariya yake su Seraline harda ihu,Inna tace yo ai mun sani muma zamaninmu munyi soyayyar nan tsiyar maza wacce ce bamu gani ba,sai kana haihuwa shike nan an juya ma baya sabuwa ake nema Allah yasa kai a kudu kake Allah yasa dai ka koyi halin arziki,dariya na dinga Yi a boye cikin mayafi,Nawwar ma Dariya ta kume shi Khaleel dake Gaban mota da Driver sai dariya suke Kamar ba gobe,Nawwar yace mun gode Inna za a kiyaye,Inna ta furta ato kun girma dai idan Kun gyara ruwanku idan baku gyara ba ruwanku Inna tana gida tana baccinta.

Zamu Shiga mota tace ban Gama ba ke Rabi na sanki da zafi yanzu ba a wa miji Fushi,ba Kuma a juyawa miji baya ke gaki Allah ya albarkace ki da Ido kamar Madara ki dinga sanyaya Masa zuciya da kallo,ke bakisan da kallo ma idan mace ta Isa sai tayi juya Miji ba,Nawwar Yana ta dariya yace banda ni Inna,Inna tace wane mutum karya kake yaro baka hadu da tsohon Hannu bane mu irinmu muka sa Namiji a gaba ai ya shiga Uku,Muka sake kwashewa da dariya kaji tsohuwa wa zai kalleta ma harda yabon kai, Rabi nace Na'am tace kuka bazai fishshe ki ba sai kin tashi sosai gidan kishiya zaki, ba a kishin fada,duka ko zagi gasa ake a wajen me gida,idan ta bashi Onga Kinga kayan Miya ne dai ko to karki sake kuyi abu iri daya a'a ke karki bashi Onga ki bashi Madara,Idan ta bashi Milo ke ki bashi farfesu,haka akeyin tsere Nawwar kunya ta kamasu Ni Kuwa ko a jikina nace to Inna tace yawwa dare nayi kuje sai munyi waya,muka shiga mota kowa ya shiga Driver yaja mota dariya Kawai muke Yi Kamar me,Allah sarki Inna na bata Atamfa da leshi da sabulai cikin kayan lefena,sannan na bata kudi su Wise ma sun bata kudi akwai dadin Zama.

Sauran duk sun rigamu zuwa airport muna zuwa dama jirgi na kasa Muka shiga da kayan mu Nan ma an Mana pics duk an watsa a media,har Muka sauka lafiya na Kira Inna nace mun sauka ta Mana fatan Alheri na rufa mayafina a Kai Amarya sosai,Mami da kawayenta su Uku da Maman Khaleel da Sufia a Airport suka tarbemu cikin shigar su ta Alfarma, sauran abokan Ango da Ango bayan an sake pics suka tafi kowa sai Khaleel da Nawwar Suka shiga mota driver ya ja su zuwa gidan Khaleel can suka Yi wanka a part dinsa Suka canja Kaya sannan suka Yi Sallar magriba da Isha suka zauna suna kallon pics suna Hira da labarin irin dadin da bikin yayi.

Mu kuwa Mami tana gefe na a mota da sauran kawayena a wasu morocin Muka nufi gidan Sabreen,Mami a mota tana ta min Nasiha sosai akan zaman aure karshe tace dan Allah ki kiyaye ki farantawa Nawwar shima ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login