Showing 6001 words to 9000 words out of 133505 words

Chapter 3 - Yar Aikin Karuwai Book 1

22 Oct 2024

3870

Shuru bata fito ba duk ihun da akeyi dakinta ya koma da sauri ya sameta a saman gado tana ta shakar bacci,mamaki ya kamashi yanzu yanzu ta bar dakinsa amma har tayi baci,ke...ke..ke...ya furta Shuru inda kasan gawa ya sake bubbuga gadon duf Hannu yasa ya dagata Shuru a hankali ta Dan bude idonta ta lumshe ta koma baccinta tashin duniya taki tashi har Yan kwana kwana sunzo ma sun kashe wutar kitchen dai ya kone kurmus,Mama tace Oh Allah ya takaita wahala,Nawwar ya fito yace Mama kuzo kuga Sabreen irin baccin da takeyi ban sani ba ko ta mutu ne,Mama da Papa suka ruga cikin dakinta,Suma yin duniya sunyi ko motsi ko ta Bude Ido sai ta lumshe,Mama cikin mantuwa tace Ni Kam papan Sabreen ko cocaine dinne ta Sha yau,da sauri Nawwar ya kalleta,Papa ya kyaftawa Mama Ido nan take Mama ta canja zancen tana wayancewa ai nufina sai kace me shaye shaye cocaine Naga a turai itace ke sa Haka,Papa yace no Sabreen bata Shan komai Suka canja zancen,Nawwar tunani ya shiga sai Kuma Kawai ya basar bayan komai ya lafa a ranar ya Kira masu aikin gini Suka rushe kitchen din ba garen da yaci wuta akayi sabo cikin kwana uku aka Gama komai aka gyara ka rantse ba ayi gobara ba ko daya,daga ranar Kuma Nawwar ya hana Sabreen girki yasa Mami ta samo Masa dattijuwa Uwale da Ladidi me aiki dama akwai maza masu kula da compound etc,Daya ita zata dinga shara da mopping da duk wani tsafta,Uwale ta kware a girki iri iri itace me abinci Kawai.

Waye Nawwar da Sabreen.




Sabuwar Number ta
08061929616




AsmaBaffa
[7/22, 11:38 PM] AsmaBaffa: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI🌼
LITTAFIN KYAUTA NE


11-15


Official

By
AsmaBaffa
08061929616



SADAUKARWA ZUWA GA DUK YARAN TSUNTUWA






Page naki ne
MARYAM T BALIYA







Nawwar a gurguje ya fito cikin shiri yasha wankan wani danyen yadi milk shara shara,gashinsa yaci gyara na gogaggun matasa kamar wani bature Yana zuba kamshi,agogonsa me azabar tsada yake daurawa yana sakkowa daga steps wani Yaronsa ne ya fito Masa da Yar karamar jakarsa wacce ya shirya kayansa da sauran abin bukata ya wuce Masa da ita ya saka a boot din mota,Sabreen tana dining tana breakfast sanye cikin kayan bacci tana ganinsa ta dauke Kai Wai ita me aji, kallo ma bata isheshi ba,har yanzu bai duba inda ya ajiye kudinsa ba bare yasan ta ebi wasu ba,Zama yayi ya hadawa Kansa tea yana Sha Yana cin chips sai da ya koshi sannan ya dauki wayarsa yace na wuce Kano Ina da meeting a can har na 2weeks,shekeke ta kalleshi ko a dawo lafiya babu tace to Kawai ta mike tare da haurawa sama,baki Nawwar ya tabe ya daga Kiran wani abokinsa Khaleel suna waya Yana fada Masa ya tafi kano,fita yayi ya shiga mota ya kame a baya securities a mota uku suna take Masa baya,gidansu ya fara zuwa tare da yiwa Maminsa sallama sai yaje ya samu Papa Yana gida har dakinsa ya shiga bayan sun gaisa Mama tace kaga dana ga iya wanka ga kyau,Murmushi Nawwar yayi ba shiri,Papa yace ai Yar mu ta dace,Sumarsa Nawwar ya shafa sannan yace Papa dama Kano zanje Ina da meeting da wasu turawa sunzo daga Finland akan business dinmu zanyi sati biyu,Papa yace a'a to Allah ya bada sa'a ubangiji ya ida nufi,Mama ta furta Allah ya tsare hanya yace ameen ya mike yace na tafi sabo da jirgi ya musu sallama ya fito direct part din Iyamami ya nufa kakarsa kenan,zaune ya isketa a kujera ta tasa katuwar tv gaba tana kallo tana tauna goro,Dan Nema sai yau aka ga damar zuwar min dama nasan ni ba kaunata kake Yi ba sai kayi sati ban ganka ba auren ma bana Yi na sake ka,Murmushi Nawwar ya saki yace dama ni me zanyi da tsohuwa ga matata sabon jini dama sallama nazo na Miki zanje Kano Ina da wani meeting, Iyamami tace aikin kenan to Allah ya tsare na zaci da matarka zaka tafi ma,ai ba dadewa zanyi ba,to Allah ya bada abinda ake Nema yace ameen tare da zaro kudi da yawa ya bata yace ga kudin cefanenki tunda na bawa Amarya karki ce na zalunce ki,dariya ta dinga Yi tayi godiya ya wuce Suka wuce airport.

Bangaren su Mama Kuwa Yana tafiya Papa yace bar shege ya gama tara Mana mu gaje dukiyar,wani ma yaji cewar Mama.
Nawwar yana zuwa Kano wani Yaronsa yazo da mota ya kaishi green palace hotel inda aka sauki turawan kuma a nan hotel din zasuyi meeting din kullum har a Gama,bai ko zauna ba kayansa Kawai ya ajiye yaje inda zasuyi meeting din dama shi ake jira,Yana zuwa suka Fara basu gama ba sai bayan Sallar Isha,wanka yayi da Sallah sannan ya zari motar da aka bar Masa ya fita dan zaga gari sanye cikin farar jallabiya me tsada.

Rabi ina sauka a Kano ban San inda nake ba haka na samu wani lungu na fito da yagaggen Hijab dina ja,ya gama fatattakewa haka na saka nace Neman Sadaka yo ai sai anyi Kalar tausayi sosai a kasar nan basa ba da Sadaka sai anga mutum ya kusa mutuwa sabo da wahala,ni Rabi ina maganganuna ina canja kamanni nace gani jajir ai dole na Zama Yar dukununu na nemo gawayi a hanya da kyar na samu na dandaka da dutse na dan shafa kadan a fuskata Kamar me shafa powder nayi wani duhu,hakorana ma duk na goga musu bakin sukayi Kamar sunyi tsatsa in ka kalli Rabi Kamar ba ni ba,tafiya nayi me uban nisa ga rana tayi sosai sai da na samo wata makaranta wacce babu gate ta gomnati ce na shiga na samu saman baranda na ajiye kayana a nan sannan na fito gefen titi tare da shanye hannuna Daya ya dawo Kamar me shanyayyen hannu ina tafiya ina cewa a taimaka min sabo da annabi a taimakeni na samu abinci, na koma dai dai wajen danger inda motoci ke tsayawa jiran a basu hannu su wuce ina bi ta tsakiyar motoci ina a taimakeni sabo da Annabi,dan me Mana ruwa da iska abinci ya gagare mu,wani ya sauke glass zai siyi charger naje wajen ina Alhaji adubi girman Allah Allah ya kaika gida lafiya canjin ishiri ya mika min ni Rabi na karbe ina Allah shi Albarka,matarsa dake Gaban mota tace na tsani almajiran Nan duk su damu mutane wasu ma sunfi ka kudi da gatansu sabo da mutuwar zuciya sai su fito bara,mijin yace ai baka San wa zaka taimakawa ba a haka wasu ne Suka bata wasu,wasu da kike gani dole ce ta sasu bara baki San mene dalili ba.

Na hada uwar zufa sosai amma daga goma sai biyar sai ishirin yinin ranar gaba daya kudin abinci naci dasu zuwa Yamma na koma makarantar inda kayana suke naci sa'a Kuwa lokacin Yan makaranta suna hutu sai na fito wasu gidaje dake kusa da makarantar na lallaba na leka wani gida na talakawa sosai ai Kuwa a zaure na iske wani dan baho karami na dauke shi na gudu tare da komawa makarantar na ebi ruwa a tuka tuka din na duba jakar kayana na dakko sabulun wankina na zaga bayan aji tunda ajujuwan a rufe suke me gadi ma ya tafi hutu abinsa a can a tsorace nayi wanka na canja Kaya sannan na Kara Nemo gawayi na mulke Fuska ta na kwanta a barandar Ina hutawa bacci ya sace ni sai bayan Sallar Isha na farka,a gurguje nayi Alwala tare da Sallah sannan na sake Fitowa cikin dare ko zan dace,ko da na fito ban iya bara ba sai yawo Ina ta kallon birni ko Ina haske Kamar Rana Yan Mata da samari da Yan gayu ana ta lailaya Kan mota gaba Daya kallo ya dauke min hankali Ina ta yawona har nazo bakin wani hamshakin Hotel na tsaya Kawai Ina kallon haduwa motoci sai parking suke wasu a ciki wasu a waje,Yan Mata Kuwa Subhannallahi ana ta shiga dasu da manyan Alhazawa wasu ana sauke su a napep,wasu sunyi gayu suna zaga wajen masu so suna samu suna Shiga dasu ciki,sai zare Ido nakeyi Ina kallo.

Ina nan tsaye wani kamshi ya daki hancina Wanda ban taba Jin irinsa a duniya ba,kafin nayi motsi wani azababben matashi ya wuce ta gefena,Nawwar kenan hannunsa dauke da ledojin take away,wayarsa ce tayi Kara ya Fara lalubota ya zaro Wayar ya daga tare da shigewa cikin Hotel din, Wallet dinsa ce ta Fadi bai kula ba sabo da ga waya ga ledoji a hannunsa har ta Fadi bai sani ba,Ina kallo da sauri na karasa kanta na dauka tare da budewa ATM card ne kala sun Kai biyar a ciki sai wasu kudin Amurka dollars amma dake ni Yar Kauye ce ban San Mene ba sai na tabe baki nace aikin banza babu abin arziki a ciki ma bari na jira ko zai fito ya amshi abarsa,waje na samu nesa da wurin na zauna a jikin wata bishiya,shi Kam bai San ma ya jefar da wallet dinsa ba wanka yayi ya kwanta bacci abinsa,Ni Kam a jikin bishiyar bacci ya kwashe ni sai farkawa nayi Naga rana a kaina,tashi nayi da sauri na koma makarantar da masaukina yake Alwala nayi nayi Sallah wallet din tana wajena,itacen bishiya na balla na zauna na goge bakina tas na kuskure da ruwa,Fitowa nayi Ina dubawa har naje wajen da mutane suke sosai da manyan shaguna ga me kosai a wajen na siyo cikin kudin barata na jiya,na siyo bredi da shayina ba Madara aka zuba min a Leda na dawo makarantar na zauna naci na koshi,na sake shafa bakina a Fuska duk nayi Mata dabbara dabbara da bakin gawayi na saka yagaggun kayana na bara na fito rike da wallet a hannuna

Ina tafiya Ina kalle kalle Ina zare idanuwa wani ne ya tare ni a hanya ganin Kamar ko zararriya ce ni,yace ke...a gabansa na tsaya Ina kalle kalle,gashina na sosa na kasa tsayawa kyam,kana ganinsa kaga kamili yace Ina Zaki je? nace ai Almajira ce ni,kai ya jinjina yace kina zuwa makaranta Kuwa? Murmushi na saki nace tab ai ni Jahila ce bani da ilimin komai yanzu ma littafi da karatu bazai Shiga kaina ba,galala ya kalleni yace kina so ki iya? da sauri nace ae,yace Okay da zaki iya zuwa dakina da na koya Miki dole sai karatu ya shigeki da yatsansa ya nuna kirjina yace idan bai shiga ta kanki ba dole zai shiga ta nan idan bai shiga ta nan ba to Dole zai shiga ta nan ya nuna gabana da yatsa,nace har ta nan karatu Yana shiga kaji karya,to Malam Iskanci aka ce ana yi da wajen,Kai baka sani ba Iskanci fa akeyi da wajen ba ruwana wajen Iskanci ne,na ja tsaki na juya nayi tafiya ta abina Ina masifa ya dauka bani da wayo zai taba min wajen Iskanci na Allah ya kiyaye.

Direct hotel din nan na koma ko zanga mutumin jiya gashi bazan ma ganeshi a Fuska ba sai dai ko idan naji kamshinsa na dade Banga alamar shi ba na bar wajen na tafi barata yau ma iya kudin abinci na tara, Wasa Wasa kullum Ina zuwa Hotel har da dare ban sake Jin me irin kamshinsa ba har na kwashe kwana biyar,shi Kuma Nawwar bai ma duba wallet dinsa bata nan ba,yau da dare na sake komawa nace wallahi daga yau Matukar ban ji me kamshinsa ba bani sake zuwa, ranar Kuma Nawwar ya nemi wallet dinsa ya rasa musamman atm card dinsa sune Suka dame shi, Fitowa yayi ko zai iya gani a cikin motarsa Nan ma ya gama dubawa babu, Fitowa yayi dake da duhu a wajen ko fuskarsa ban gane ba nidai naga hadadde ya wuce,Yana wucewa wani kamshi ya dakeni naji Kamar irin kamshin Wanda ya jefar da wallet dinsa jiya,Ina juyawa Naga ya Dan min nisa da karfi nace Malam....tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba da gudu na fyalla naci wawan birki a gabansa Ina haki na zaro wallet din tare da Mika Masa nace t...taka..ce? Yau sati guda kenan ka jefar da ita na ganta kullum sai nazo ko zan ganka,kasan irin hatsarin da na Shiga a hanya sabo da zan kawo maka abarka ai Saura kadan wani ya taba min wajen Iskancina,wai dan Allah karatu ai baya Shiga ta wajen,Nawwar bai gane me nake nufi ba ko saurarar zancen nawa baiyi ba, farin ciki ya Kama Nawwar cikin muryarsa me dadin saurare yace ta ya Kika ganeni? Nace kamshinka yasa kawai danni ko yanzu in za a kasheni bazan ce ga fuskarka ba sabo da duhu,karbar wallet din yayi Ina kallo ya duba komai nasa Yana ciki inda suke ya fito da dalolin masu yawa ya irga ko wacce dala dari dari ce a ciki ya zaro guda Uku yace gashi na gode

Baki na turo nace Hmmm uhm jam ni me zanci da wannan takardar ai gwara ka bani dari biyar,dariya ta kamashi yace kudine fa idan Kika canja sunfi dubu dari nace wallahi bana so kaji mutum dama can baka yi Niyyar kyautata min ba in hakane ka bani dubu daya mana,Nawwar ya buga buga nace wlh bana so,yace to jirani a nan Ina tsaye a wajen ya koma cikin hotel din sai gashi da kudi Yan dubu dubu ya Mika min Yace gashi dubu talatin Kika samu ba cash a hannuna da yawa,da sauri na karba nace Allah ya shi Albarka za kaga daidai a rayuwarka bukatunka sai sun biya da iznin Allah na juya na take da gudu,yace jita Kamar yarinya da bakar Fuska kamar bayan tukunya Kai wannan da baki take,ni kuwa ko gane fuskarsa banyi ba nasan dai fari ne sosai dan dogo haka ,baki ya tabe ya juya ya koma ciki Yana cewa Kai amma tana da Amana a Zamanin nan.

Ni Kuwa cike da murna na kwana da sassafe Ina idar da Sallar Asuba wanka nayi da ragowar sabulun wankina na wanke fuskata tas duk da na dan canja sabo da yawon bara a rana,kayana dana jiya na wanke su tas jakata na dauka Yar wayata na Kira Saratu kawata tana shiga Kiran duniya ba a daga ba,nace ya zanyi haka Zan tafi Kawai,sai dana jira 8am tayi na samu na karya sannan na tambayi wani me Napep inda ake shiga motar su Anambra ya kaini Kuwa har can irin inda ake shiga mota haka Ina zuwa aka saka ni a motar Onitcha direct duk haka Ina ta Kiran Wayar Saratu amma taki dagawa Kuma tasan number ta haka mota ta ja Muka tafi,mun biya kudin mota tuni harda Yar ragowar kudina na adana abina cikin aljihun doguwar rigata domin sanye nake cikin doguwar rigar wani material orange rigar harda aljihu shine a kayana me Dan dama dama Yana min kyau,na yafa dan karamin mayafina,tunda muke kwarara tafiya nake uban bacci na farka na koma cike nake da nishadi Kamar ba gobe, sai tsakar dare Muka Isa Wanda mafi yawa a tasha muka kwana,in Banda turanci da Kuma pidgen English sai yaren Igbo shi Kawai ke tashi,gaba daya a tsorace nake,na matsu na ga Saratu nace yanzu Saratu dan masifa ta iya Zama a garin nan ko tsoro bata ji Kar fadan arna da musulmi ya barke a halakasu, gashi bana Jin turanci,Fitowa nayi daga tashar ba Wanda ya saurareni kowa Harkar gabansa yake yi, Napep na gani na tare iya sunan street din na iya fada masa yace you be Hausa? Yana cewa Hausa na washe baki na daga Kai sama kamar naga Dan uwana bahaushe,shiga nayi ya Fara tafiya Naga haduwar birni gidaje na gani na fada Muna tafiya Ina ta farin ciki,a fili nace yanzu nasan nazo birni, Birni na shigo,Yan Kudu gani sunana Rabi ae Rabi me zamani dariya na saki hahahaha kamar sabon kamu,nace wuhuhu kuturun dosan uwa ana bala'i a kudu, na nuna wasu Yan Mata da yatsa nace kalli cinyoyi Kai cinya a waje haka da Dan wando gajere wasu da mini sun Sha takalma masu tsini,na saki ihu nace yehoho ana tsiya nayi tafi da hannayena nace naga waje.

Munzo wucewa ta wata GRA nace wuhuhu Kai Saratu lallai kinci gaba haka Zan zauna a katon gidanki,bani ba Arewa dole sai nayi kudi inzo inyi ta aikina in tara kudi ba inda zanje naga waje,Kai Rabi kin dace Ina magana da karfi Ina dariya Ina zazzare Ido Ina nunawa da yatsa Ina ta kallo,Me Napep bai San me nake cewa ba, tafiya mukeyi kamar zamu bar gari tafiya taki karewa tun Ina nishadi har na gaji nace Allah dai yasa yasan unguwar da nace,tafiya akeyi na gaji ma tun Ina magana har na gaji nayi shuru ga yunwa na cina,cikin birnin naga mun bari munzo wasu unguwanni Ghetto area unguwar talakawa da Yan jagwal badan ginin bulo bane da yawa sai nace kauyenmu yafi nan komai da komai.

Sai da muka zo daidai wani lalataccen gida yayi parking Yana min alama da na fito,Ina mamaki na fito dauke da jakata a Hannu nace ya za ayi ka kawoni kauye ni da nace birni dan mugunta sai da ka wuce duk wurare masu kyau sanna ka kawo ni lalataccen wuri ni nasan wacce nazo wajenta baza ta zauna a nan ba Yar gayu ce me kudi tace Mansion ta gina a birni wata ce ta karaso wajen tana Jin hausa da alama ma bahaushiya ce itace ta tambaye shi da turanci meke faruwa? Yace shi bai San me nake cewa ba,tace ke meke faruwa? Ina masifa nace Odimgbe Street nace ya kawoni shine ya kawoni kauye Kuma wajen kawata nazo Saratu Amma kamar ana kiranta da Seraline,nan take matar ta sheke da dariya tace nan ne Abeg dauki jaka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login