Showing 117001 words to 120000 words out of 133505 words
91-95
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA DUKKAN YARAN TSUNTUWA
Page naku ne
Mum Amatullah
Pharteema Muhammed
Hajiya Hauwa
Ummu Shureim
Hassana Habeeb
Zainab ashiru Adamu
Saudatu Abdullahi
Ammin Airah
Malam kunya ta Kama shi bai taba ganin irin wannan rashin kunya ba,Wise ce ta mikawa Santana Hannu Suka kawo zasu tafa sai Suka janye tare da hada Baki suka furta ba kyau kowa ya maida hannunsa, ana Mana babin wanka Mandula tace ai ni bana wani gaggautawa da cuccudawa ai kawai Malam na kwara da roba na wuce wajen to Yar degree faranti ce ni, Santana da su Star harda shewa,Star tace ashe a ruwan ma akwai me tsarki da tsarkakewa to idan Mata da miji suna wanka fa amma dai shi ba matsala,Malam dai yace ai Yana da kyau sunna ce wanka da matarka,Wise ta rufe baki tana kunshe dariya tace Malam to kaima kana Yi wai,yace ae Alhmdllh Muna dan tabawa,Ido Muka zaro ai mun zaci banda ustazai yo Ustaz yayi ma bare tubabbun karuwai Papa kaga ta kanka cewar Wise ,Star ta kalli Malam tace Abul khairi Mazarawi? Yace naam dariya tayi tare da kifa kanta a saman cinyoyinta tace ya amsa wlh gaskiya Ina sonka ni Kaine ka birgeni da gani dai dai dani kake tana karewa wandon Malam kallo tace amma Malam daga wajejen Isra'ila kake ko, Malam ya Sha kunu Kawai irin ba Wasa, nidai Nace Malam ni Ina da aure ya mazaunin mace yake idan tana yiwa miji kukan shagwaba,Malam yace ba laifi wannan Abu ne me kyau duk cikin kara dankon kauna ne,nace tab Nawwar ka shiga Uku Malam yace da kyau,ya daina Wasa yaci gaba da biya mana Muna ta iya shege ya gama da sauri ya sake Mana nasiha sosai sannan yace gobe cikin darasi harda tarihin annabawa,Star tace toooo an kusa zuwa Suratul Yusuf suna ta murna Ina jinsu Dan ni na fisu ilimin addini da Wise ma tana da nata ba laifi,Malam ya tafi da yamma Me English tazo,tace banda hausa a nan ta Mana darasi Muna ji,tana ta Mana iyayin turanci,tace zamu Fara da Noun,nace now ta yanzu yanzu ko kuwa wata Hajiya Now din ce daban,Wise ta dinga dariya da malamar ma haka,munyi nisa da karatu Nawwar ya shigo a mota yayi parking cikin jerin motocinsa,a fili nace Excuse Zan karasa Ilimina a can tare da dafe kirjina nace My life ya dawo,Malama tace karatu muke fa,baki na bude nace Man of the world fa ake ce miki,My Hero,My Star haba malama ko daga birtaniya kika zo ai kya saurara min,tashi nayi na wuce abina,fitowarsa kenan na taho da gudu na fada kirjinsa nace I wanna be in your life,dariya ya saki yace ko karatun ne ya Fara aiki,dariya nayi nace a street na tsinta, daukana yayi kamar Baby a haka Muka wuce part dinmu
Bedroom na tayashi ya cire kayansa ya fada toilet,lekowa yayi yace Miko min key din can,daukowa nayi na Mika Masa ya damko Hannu na tare da jawoni cikin toilet din,nace yanzu fa nayi wanka,ai tayani zakiyi Yana min rada a kunne haka na hakura Muka yi wankan tare yana Wasa da sassan jikina haka Muka Gama muka fito tare da shiryawa,ya sa Kaya marasa nauyi sea blue ni kuwa guntuwar gown na saka peach and green me kyau sannan na fita kitchen na kawo Masa abinci,nice na ciyar da shi Yana danna waya har ya gama ci Muna hirar masoya, yace jibi zanje Abuja,murna nayi sabo da dama na gaji da irin yanda baya barina na huta,nace ai kuwa sai muyi ta karatunmu Allah ya dawo da Kai lafiya,Kallona yayi ganin Ina ta Jin dadi,kwafa ya ja wato murna ma kike yi to na fasa kuma ma Zan iya tafiya dake ai kina da ilimin addini, wani dukul naji yace ki hada Mana kayanmu sati zamuyi amarci sabo,tagumi na zuba haka na kumbura baki tare da cewa to,Murmushi ya shiga yi,Ashe tsokanata yayi dama ban sani ba haka na shiga hada mana kaya yace Wasa nake Miki,nace Allah ba matsala muje ko da gaske ne ai kana so Ina son abinda kake so,tsokanarki nayi tsakanin kafafunsa na dawo na zauna tare da maida kaina da gadon bayana saman kirjinsa, Wayar dake hannunsa ya ajiye gefe ya shiga Wasa da jikina sai da ya murzani son ransa sannan ya kyaleni lokacin malama ta gama darasinta har ta tafi ma,suna part dinsu sun saki kida sai cashewa suke yi Kamar basu ji Nasihar Malam ba Santana Yana can Yana ta faman murguda duwunsa Kamar na dan tsako.
Baffa kwana biyu ya rasa inda zai ga Mami Kawai sai ganinsa nayi a gidan yayi knocking Ina Budewa na ganshi na kalle shi Muka hada Ido kallon palon yayi ko Ina Kal Kal Yana zuba kamshi yace Yana nan Kuwa? Nace ae,shigo Mana,ya shigo ya zauna na durkusa na gaida shi sai kunyata yake ji ya tuna sanda ya kaini hotel,nace Baffa ya kawata Kuwa Star, har gumi yake yace dan Allah ki rufa min asiri karku fadawa iyalina da yarana ki rokar min kawar taki ta rufa min asiri,nace wlh ya wuce har abada baza mu fada ba amma idan ka daina fa,da sauri yace wallahi daga Sanda nasan kina tare da dana ban sake ba Kuma na tuba sahihin tuba bazan sake ba har abada Inshaallah,nace to ka dauka komai bai faru ba dan Allah ya wuce har abada Allah ya Kara kiyayewa ya Kare mu ya shirya mu,yace ameen Yar Albarka sai yanzu nasan Zina bata da amfani,ga zunubi,ga zubar da mutunci dama Indai sana'ar mutum kenan to Watarana sai yaji kunya zai iya Neman yarsa ma bai sani ba,nace wlh ai mu Kam Allah ya Kare mu yanzu ma duk su Star sun dauki hanyar tuba Nawwar ma ya samo Mana malami Yana koya Mana yaki da jahilci,Baffa yace madalla kaji Dan Albarka Allah yasa wannan ya Zama shine silar shigarsa Aljanna,nace Ameen Ameen Baffa Inshaallah damu daku a Aljannar ma a GRA muke,yayi dariy tare da furta ameen ameen,nace da anyi mashahuriyar Yar giya a aljanna,Baffa ya dinga dariya yace kin San inda Mamin Nawwar take kuwa? Nace Baffa ya akayi haka ta faru har saki uku kayi ganganci wlh uwar yaranka guda,Baffa yace to ba a kaunata a gidanmu shi yasa aka kyale ni babu me fada min gaskiya gashi nan yanzu kullum 'yata sai nayi kuka,dariyar Baffa ta kamani Kamar ba surukarsa ba sabo da a bariki Muka hadu shi yasa,nace kaga ko ni ban San inda take ba wlh Amma Watarana tana zuwa nan,Baffa yace kiyi amfani da damarki a wajen dana ki samo min inda take dan Allah Hakuri Zan bata Kawai ta yafe min tun kafin hakkinta ya kamani Allah yasa dai tayi aure da wuri mijin Kuma ya saketa ta dawo wajena,Nace Baffa ai ko ba'a saketa ba sai mun kaddamarwa mijin dole ya sako maka matarka,Baffa yace da kuwa bani da kamarki a duniya Allah ya Miki Albarka bana so ma ta fito ta hanyar da ba daidai ba Indai Allah yayi za'a saketa ne again Kinga dama kuskurena nake so na gyara,cikin magana kasa kasa nace an gama Inshaallah zata dawo muyi ta Addua Kuma zan tsaya maka iyakar iyawata Baffa ai Kai namu ne tun a baya,Baffa Yace daina tuna min na tuba wlh, Nawwar ne ya sakko daga sama ya iske mu Ina zaune Baffa ma Yana kujera a zaune Muna ta hira, yaji dadi a ransa sosai ya rasa alakarmu da Baffa da muke hira sosai, Yana zuwa na mike na kawo Baffa kayan ci da sha,Kuma ya zage yaci ya koshi,Nawwar sai mamamaki yake Suka gaisa da Baffa,yace yau ziyara na kawo muku,shi dai Nawwar yasan ko Sabreen bai taba zuwa gidan ba sai Rabiah da baya son auren.
Haka shima ya zauna Muka dinga ta hira,ya Dade a gidan sannan ya tafi,Yana tafiya Auta Nawaf yazo tsabar tsaurin Ido na yaron nan mota ya dakko ba a sani ba da kyar yake kallon gabansa haka yazo har gidanmu na fito zanje part din su Star na ganshi harda jakar kayansa, Nawwar ya fito zai fito shima ya ganshi yace Kai motar ubanwa ka dakko motar Baffa fa yaushe ma ka iya ganin gabanka? Auta yace Yaya Ina kallon gabana Mana idan naje fitsari,dariya ta kamani Nawwar harda min dakuwa ya min ambola Yana dariya,Jakar Auta na karba nace wata daya zanyi Aunty,Nace oyoyo muje ciki muka koma na Kai Masa jakarsa part din Sabreen data bari ya Sha gyara,yana zuwa harda cire agogo ya ajiye a saman gado yace kawo min shinkafa ni idan banci shinkafa ba bana Jin dadin duniya,kawo Masa nayi da ruwa da lemo wai yace ki kawo min fresh milk nace wannan Kuma baka Isa ba sai dai kaje da kanka,Zan fita yace Ina kawayenki ne Aunty? nace ai suna gidan nan an basu part guda amma wasu duk sun mutu na bawa Auta labari yace Allah sarki Allah yaji kansu fatan dai ba wannan Wise din ni kin San ita nake so,Kai Amma da tsaurin Ido kake Nawaf tafi karfinka ai nawa kake,yace wallahi da za a aura min ita Zan iya Zama Kuma na riketa tsaf nifa a SS2 nake fa ai na Isa aure,to girman aji ne aure,ke dai ba ruwanki ki hadani da ita, nace Indai itace gata gaka ba ruwana idan ka Sha mari.
Part din su Wise na Shiga Ina dariya na basu labarin Nawaf,Wise tace kaji shegen yaro sai dai ubansa,nace ke karki zagar min uba wallahi uban miji uba ne,to Allah ya baki hakuri Mrs Nawwar nace Ameen Ina masifa,Wise tace wannan Ina zai iya dani, Wai ba yaron nan da yazo da biki ba? Nace ae Suka Yi dariya Sera tace karki kawo shi wallahi yaro haka Kawai a koya Masa fitsara nace hauka nake Nawwar yace mun lalata Masa kani domin bakin nan naku da babu sakata,shi kuwa Auta Yana Gama cin abinci sai ganinsa mukayi a part din ya shigo yayi sallama yana wani iyayi,su Star sai kunshe dariya suke,Wise tace Dana yau kazo,Auta yaji haushi yace a ransa wannan ta Isa ta haifi kamata ita din wa,a fili kuwa ya basar ya zauna a gefe,Santana ya fita baya gida ya tafi kasuwa Wai girki zai musu a part dinsu na musamman su Star duk zaman da suke kenan su ci girkin Santana ya kware da girki.
Wise tace Nawaf Naga kana hamma,yace bacci nake ji Yana ta kallonta ta dakko zanin Atamfa tare da furta zo dan ubanka na goyaka na jijjiga ai Kai a wajenmu jariri ne,Nawaf harda harara ance za a goya shi da zani ana maida shi yaro tashi yayi ya fice ya tafi kallon ball wai yayi fushi,Mandula tace yau Naga balagaggen yaro,wlh Yana Isa aure suyi Masa Kar ya lalace cewar Seraline.
Dagaci kullum ramewa yake Yana tumburewa sai dan ciki kwajaja a gaba wuya Kamar Sandar kiwo,Gwaggo ma duk sun rasa sukuni,suna haka manyan garin kowa yaji asirin Dagaci ya tonu an gama gane gaskiya yanzu,su Star da shigigi har kotu Suka je a kano,ni naji suna yawan tafiya kano ashe Kara suka shigar akan abinda Dagaci yayi min ni Rabiah,aka Nemo hukumar gidan reno da su ake zuwa kotu har garin Suka je Suka ji gaskiyar labari abinda ya faru da yarsu nan da nan aka fara kawo labarin karar a gidajen Radio,sakayya ni ban San me akeyi ba sai ji nayi kotu na nemana a Kano lokacin Suka bani labarin komai suna cewa wlh baza su kyale ba, da Nawwar Muka je sai da Muka halacci kotu sau biyu sannan aka samu sarki da Kansa yasa aka tugewa Dagaci rawani aka sauke shi daga sarautarsa tare da cinsa tara ta kudade masu yawan gaske,Haka ya siyar da gonakinsa kusan gaba daya gonarsa ta gado ce kawai ta rage,ya bani kudi ni Kuma ba mutunci na karbe na Kai tallafi gidan marayu gaba daya kudin, Dagaci harda cewa Rabi babu tausayi? Ki tausaya min,nace Ni Sanda kuka min mugunta tun Ina yarinya Kun tausaya min ne,abinda Zan iya muku Kawai yafiya ce amma ni bani da hadi da ku bani ba ku kuje Kuma abinda kuka min kanku kuka yiwa,gashi ban fasa ci gaba ba na juya Muka tafi ,Gwaggo tayi tsumu tsumu itama, da kotu cewa Suka yi za a kaita prison nice na nemar musu Alfarma aka kyale su a haka.
Dagaci fa duniyar ta Masa zafi Aunty Amarya Kuma sun daura gaba da Gwaggo kullum basa zaman lafiya,Dagaci ya Gaji ya saki Aunty Amarya, da Gaji da Gwaggo Suka nada Mata dukan tsiya ta fito zata tafi Suka bita da duka ko kunya basa ji har gefen babban titi suna kokawa mota tazo wacce birkinta yaki tsayawa Kawai ta banke su gaba daya har Gaji.
Mutane Suka cika wajen aka kwashe su zuwa asibiti,Dagaci ya tafi asibitin Yana kuka abubuwa sun Masa yawa Yana zuwa ya samu Aunty Amarya tayi karaya wajen biyar itama Gwaggo karaya ta Kai hudu,Gaji Kuwa Allah yasa motar kadan ta shafeta bata karye ba.
Me chemist din kuwa da Gaji Suka je Suka sashi ya min sharrin ciki gaba daya yanzu bashi da kasuwa duk da ba a San me yayi min ba babu Wanda ke saurar chemist dinsa sabo da an bude sababbin chemist,Ni Kuwa Nawwar nasa ya bawa Bala Babban jari ya tura Masa dubu dari uku ya ja jari sai godiya yake min kamar ba gobe.
Tsabar son abin duniya na Papa kullum sai ya Kira Wise tun Yana Kira yace ya Kira ne ya gaisheta har ya saba da hira,Yau da dare cikin dare suna kwance da Maman Sabreen ya lallaba ya tashi ya barta ya fito Palo ya Kira Wise bugu Daya ta dauka da muryar bacci,yace Sorry na tashe ki ko kiyi hakuri na riga na Saba da ke nifa Ina ganin kamar mun wuce matakin da muke na gaisawa ni gaskiya sonki nake Yi Kuma aurenki zanyi idan kin amince, Wise tayi Murmushi a hankali tace gaskiya anya Kuwa to ka bani dai lokaci nayi tunani yace na baki farin cikina,kece ruhina,Wise tana jinsa tace ji mutumin banza Yar cikinka a fili tace na gode yace dan Allah ki soni karki ce a'a na Riga na baki Amanar zuciya....Amanar zuciyaaaaaaa yaji Mama ta fito tana tambaya uban wa ka bawa amanar zuciyarka? Dama abinda kake kenan kullum tsakar dare sai waya waya haba Yusuf Ashe amanata zaka ci kace baza ka min kishiya ba ka tuna Alkawari fa kayi min,Papa yace na karya shi yau shike nan bazan Kara aure ba ance idan ka Kara aure kofofin budi zasu Kara bude maka shike nan so kike nayi asara tsaki yaja yaci gaba da wayar,Wise tace Uwargida ce ne? Yace itace take min ihu,tace kyaleta kishi ne ni gaskiya Zan fasa auren naka yace kiyi Hakuri Dan Allah kyale wannan tsohuwar hakorinta fa sun Fara cirewa,nace Allah sarki bata da hakora yace ai duk na gaba sun zube tsufa ya kamata da gaske, Wise tace gaskiya kana bukatar sabuwar zuma,dariya ya saki Hahahahaha shi yasa kike birgeni,Mama tayi sororo tana ji yace kiyi mafarki na sannan ki gaishe min da kudadenki, Wise Ido ta zaro tace amma wannan ya cika mayen kudi har kudin Nawa ma na gaishe Masa da su,Yana Gama wayar Mama tace yanzu Yusuf ni zaka cewa hakorana sun zube kayi min sharri,Tsaki ya ja ya mike Mama ta cakumo shi ta kafa Masa hakoran a gadon baya tana cizonsa Yana ihu,tace wannan mene kace sun zube,ranar sabo da bala'in Mama basu yi bacci ba.
Jamcy ce taci kwalliya ta shigo gidan Nawwar a motarta tana parking ta fito ita ga tsagera tana tauna chewgum tana taku,taci sa'a su Star suna palona gaba dayanmu ta shigo ko sallama,Yar zabil tsawa ta Mata ke koma kiyi sallama,ubanki ma yayi kadan bare ke cewar Jamcy,Ina shegiyar da akace ta gagari kowa ba wacce ta Isa ta auri mijinta gani ni na zo Kuma sai na auri mijinki Nawwar na dade Ina sonsa,Star basu ce Mata kala ba Suka maidata banza ta gama zage zagenta Shuru,Wise ce ta dakko sabuwar hira ya dinkunan Kuwa kin karbo? Nace sai gobe Inshaallah,Jamcy bata hakura ba tace ana magana Kun maida mutum mahaukaci nan ma Shuru basu ce kala ba sai hirarmu muke ta zubawa Muna tafawa,taci gaba da cewa idan Kun hana Sabreen Zama ni nafi karfinku baku Isa ba,Nan ma shewa mukayi muka tafa Muna hirar mu,Jamcy ta kule Kamar ta hadiyu zuciya tayi tsokanar tayi Shuru sabo da bata da abin fada,Tsaki ta ja tace karuwan banza karuwan wofi Yan Iska duk Wanda yake ba dan sunna bane ai dole yayi haka,idan Kun haifu kuyi magana banzaye karuwai,Ni dariya ta bani Kawai kizo ba gaira ba dalili ki dinga tsokana,ba Wanda ya kulata duk magana intayi sai mun saki shewa wannan yafi Mata ciwo ta juya ta fice tana Jan Tsaki,ko da ta tafi ko zancenta bamuyi ba hirar mu Muka ci gaba,Wise tace Allah yasa ta dawo yanzu mun Mata abinda yafi komai ciwo to nan gaba jini da majina zamu hada mata.
Baffa kwance yake a dakin Iyamami saman gadonta ya sata gaba ya hanata sukuni,yace gaskiya ni a san yanda za ayi dani dan ni gaskiya ku Nemo min matata ai da zugarku yasa na sake ta kune kuka dinga zugani,Iyamami ta juyo da masifa tace kai kaci ubanka yau naga marar mutuncin yaro abinda kake ko Auta bazai Yi ba,Nema kake ka susuce ta ja tsaki,Baffa yaki tafiya yace Allah sai Kun Nemo min matata ba inda zanje ai da Yusuf ne da tuni kuna tausayinsa Ni shike nan kamar bare an ware ni ba a so na ya karasa da muryar tausayi,Nawwar ne ya shigo bayan sun gaisa Baffa yace Nawwar wato