Showing 96001 words to 99000 words out of 133505 words

Chapter 33 - Yar Aikin Karuwai Book 1

22 Oct 2024

3898

haka shine abin proud adduar tasu ta Dan lokaci a fili ya furta karki dameni ni,nace a hankali yanda bazai ji ba na furta almasifatu kanwar azaba,Ashe yaji ya tambaya me Kika ce? Cewa nayi ka jawo na rame kalleni rama har nono sun dawo wasu gasu nan Allah ya taimakeka baka tabawa da kaga ta kanka ji zaka Yi Kamar ka tsinko dan lemon zaki karami,dariya ta Kama Nawwar ya kasa dannewa sai da ya murmusa,nace tsaya a siyi pad matar taka an jima kadan Zan Fara yoyo na kusa,slow yayi yace ta Kare ne duk yawan wacce na siya Miki? nace ai kyauta na yiwa su Sera Kawai ka siya min wata sannan accnt dina ba kudi ka tura min sannan dinkuna na an dinka ban karbo ba,yasan halinmu da kashewa Kai kudi Kawai parking yayi a wani Shopping mall,nace ka taho da ice cream,kamar bai ji ba sai gashi ya siyo min har ice cream din, ya kawo min,tun a motar na Fara Shan abina,Muna tafiya Wai a Dole haushina yake ji,dariya ya bani nace dinkunan kala uku ne Dan fake fake ne 20k,yace sai kace ke aka zana a jikin kayan,dariya nayi nace ka dinga kyautatawa iyalinka Allah zai Kara buda maka duk nasan komai kanayi karka ji komai kayi komai ba komai duniya ce dole mu baza mu bita a Sannu ba da gudu zamu bi a barmu, nace Addua ta karbu, kunnawa min kida yanzu na warwasa,hmm yace Kawai Yana kallon na kunna kidana.

Sabreen tana Palo ita daya gidan duk dirty kaca kaca amma ko a jikinta sai sallamata taji mun shigo tare da Nawwar, Nace Honey Kauye tayi na gode da barina da kayi naje unguwar nan kaga ko ba komai na gaisa da iyayena da Suka rikeni,naji dadin tafiyar nan kaga ai nayi zumunci,Sabreen a ranta tace wato dama ba sakinta yayi ba unguwa taje Kauye ashe Kuwa akwai bala'i wlh Zan iya kisan kai bari nayi sabon shiri,kwafa ta ja Ina kallonta bata ko kalle mu ba sai da kyar ta kalli Nawwar ta dauke kanta,ice cream Dina naci gaba da tsotsa na Mika Mata roba daya tare da furta uwar gidana ga roba daya nasa hannuna a saman kanta nace wannan gashin ai sai a zaci dambu ne mu rufa Masa wawa,kutmar....keda ice cream din ta kutuntuma min ashariya ko a jikina,shi kuwa tuni ya wuce samansa nima bangarena na wuce.

Ina hutawa Fitowa nayi na zage na Fara gyara gidan,Da dakinsa na Fara lokacin hankalinsa ya kwanta Yana zaune gefen bed dinsa Yana latsa system dinsa na wanke toilet kal kal na fito nasa Hannu tare da dauke system din daga gefen bed din na matsar da ita gefe sannan nazo na riko hannayensa biyu nace Yi hakuri ka tashi,mikewa yayi Yana Jin sanyi a ransa,bed din nake gyarawa Yana Kare min kallo kamar zai cinyeni sabo da sanye nake da guntun wando da kyar ya rufe min duwawu da rigata t-shirt peach wandon Maroon,Shi kuwa sanye yake cikin dogon wando da riga iri daya farare tas rigar me dogon Hannu harda hularta yayi kyau sai kamshi yake,Yana kallona Yana ganin girmana sabo da Ina da tsayi da Yar kibata normal komai yaji,sai da na gama da gadon nasa sannan nace zauna tare da rungume shi na zaunar dashi a haka na dawo Masa da system dinsa inda take sannan na share nayi mopping ko Ina ya dauki kamshi sannan na fito ko Ina sai da na gyara banda bangaren Sabreen,kitchen na Shiga na fara girkina gida ya dauki kamshi,Nawwar ya dade rabon da yaji kamshin nan sai ya dawo Palo ko Ina Yana shining ya zauna a nutse,su Sultana ne Suka shigo da sallamar su,na fito Muka gaisa na zauna Muna surutu Nawwar yace yunwa nake ji fa,tashi nayi na koma dakina na dauro zanin Atamfa akan dan gutun wandona,hakan ya Masa Dadi yace a ransa lallai kin Fara hankali.

Waina da miyar da na Fara Yi na zubo musu da kemo da ruwa sannan na kawo musu chin chin,kitchen naje Ina aikina har na gama suna hira abinsu sai da na gama na zubo Masa nasa wainar inda yake na kawo gabansa a manyan flasks na koma kitchen Ina cewa da Kannensa kuci fa kun San dai nan ba bakon gida bane,idan bata Isa ba sai na Kara musu dan Allah kar ku ji kunya,Su Sultana sai Murna sukeyi sun samu aunty me kirki,sai da na kawo Masa komai gabansa sannan na zauna,sai da suka ci Suka koshi nace Mami tana son Masa?Suka ce ae nace to na zuba muku sai ku Kai Mata,shi kanshi yaci wainar nan sosai fiye da zato na,da zasu tafi haka na cika musu flask sannan miyar daban suka tafi da ita,suna tafiya na cire zanin na fito kusan tumbur dani, kallona Nawwar yayi kawai Ina mamaki a raina wai ya akayi bana birge shi ne,Sam baya sha'awata,cinyoyina na tale yanda Muka saba zaman mu na Yan kwalta,Muka sake hada Ido ya maida Kansa ga tv,gabansa na dawo na tsaya tare da furta ban gane ba fa,yace what? Nace Kai billahillazi sai kayi sha'awata na gaji koma yane Kawai kayi sha'awata yawwa ehe Indai ana so a zauna lafiya Kawai ayi sha'awata haka Kawai sai gana min azaba akeyi,Dariya na bashi ya dinga Kuwa kyalkyalawa Kamar ba Nawwar ba,tsayawa nayi Ina kallonsa,sai da ya gama yace dama wai dan ni kike yi? baki na turo nace ban sani ba,Hannu ya miko min na kalli hannunsa na Mika masa nawa hannun nayi a hankali ya jawoni na zauna a hannun kujerarsa ya Kare min kallo ya sake tuntsirewa da dariya,Fuska na kwabe cike da shagwaba na mike a fusace Zan bar wajen ya sake riko hannuna naji wani yarrrrr a jikina, jikinsa ya jawo ni na fado saman cinyarsa bayana yake karewa kallo ko Ina fari luwai luwai,a saman dokin wuyana ya dora bakinsa a hankali cikin wata irin murya me rikita mata ya furta me kike so? nace ba komai Kawai,oya Ina jinki me ya faru naga gardi rungume da matata? Sannan Wanda ya Kira fa Yana Miki ya gajiya? Nan take idona ya ciko da hawaye na zame a hankali na koma kasa na zauna sosai sannan na dago idona Ina hawaye,yace ba kuka nace ki min ba,nace idan na rantse zaka yarda? Kasan bana karya wallahi duk abinda nasan nayi shi Zan fada maka,ban San komai ba akan Wanda ya kirani a waya Kai sheda ne da ace Ina da maza masu kirana da ka sani amma Inshaallah very soon zaka fahimta,sannan Wanda yazo gidan kawai ganinsa nayi a Palo ya fado Ina kokarin guduwa ya damko ni Kawai na barwa Allah duk Wanda ya min haka Inshaallah asirinsa sai ya tonu,Kawai kasan mu a baya an San mu a duniyanci ko yaushe a zargi muke shi yasa da anga irin wannan za a yarda kasan a inda ka dakko ni Kuma na yarda na zauna da kai Kuma bana boye maka komai tsakani da Allah nake zaune da Kai,mu yanzu ba Wanda bazai Mana sharri ba sai ka Kai zuciyarka nesa fa sannan akwai abinda nake kokari ka samu shine shedata lokacin zaka yarda dani .

Har na gama bashi cikakkiyar amsa Yana kallona yace na gamsu da ke,nace na gode da fahimta da wani ne da tuni ya dade da sakina,me zance da Kai sai godiya,Ni Kuwa me zance da kai ai a duniya bani da kamarka Kuma na gode Allah ya saka a Aljanna firdausi,Ameen ya furta Yana Jin sanyi da wata nutsuwa a ransa,ya akayi kika daina min kiss? nace Naga Kamar baka so,ki daina daka tani ni kunya ce dani ba iya komai nayi ba yayi min wayo ban gane ba,dariya nayi na koma saman cinyarsa na zauna nace ka daina Jin kunyata nifa ba kunya ce dani ba zan iya tubewa a gabanka,yace Allah? nace ae to mu a fada Mana fitsara shi yasa nake so kaji dadi kaki Kai Kuma,Ni mene ma zaka ji kunyata ni ba malama ba bare ace Ina kwarjini,yace to ku ai Kun waye da irin wannan harka ni ai sai dai ki koya min,duk ban gane wayo bane,nace Kai da kake da mata bata baka ne? Yace to ita kunya ni kunya bama iyawa sosai, dariya nayi tare da furta ba wani ka iya kowa fa a fagen nan dan iskane Allah nayi kasa da muryata cikin rada na furta harda ubana tunda yayiwa uwata cikina,baki ya rufe da hannu yace Kika zagi Daddy,nace waye Daddy din ni bani da kowa gashi nan ana cewa Yar shege ce ni,mikewa nayi nace good night na wuce part dina,wanka nayi tare da tsaftace lungu da sakona yanda na Saba sannan na fito nan haka bayan nayi shirin bacci cikin wata guntuwar rigata pink,Ina Shirin kwanciya naji wayata tayi kara na duba Nawwar ne,Ina dagawa yace zo ki kawo min green tea, Fitowa nayi naje na hada Masa na nufi dakinsa Sabreen an Sha kwaya ana ta uban bacci.

Shiga nayi daga shi sai boxers jikinsa ne me kyau ya dauki hankali na ina satar kallonsa na ajiye masa Zan juya yace Kun rainani a gidan nan ko wacce ranar girkinta sai tayi tafiyarta part din ta to daga yau nan kwana,Dadi naji amma na danne,kallona yake yi na zauna a gefe nima Ina kallonsa,muryarsa na tsinta yace kina son hakkinki ne a baki? Kai na girgiza alamar a'a,yayi mamaki yanda da nake roko amma yanzu nace a'a, Ido ya tsura min yace da gaske? nace da gaske na furta babu alamar wasa,to ni idan Ina so fa? dariya ya bani na danne sannan nace ni bana so yanzu,Zan iya tayaka kwana kamar da yanda baka taba ni,Amma yanzu ni harkar ciye ciyen nan ba so nake ba,ba kalau kike ba to infection ya kamaki,dariya na dinga yi nace akan me Infection zai kamani a toilet dinku ta gidan yawa da kike zuwa kina shiga ya Miki illa baki sani,3days Indai Kika ci gaba a haka asibiti zan kaiki dole kina da infection matar da kullum kike roko sai an lalata ki,pillow na dauka tare da rufe fuskata,baki ya bude yace ahhhhh gaskiya ba kalau ba ruqiyya kike bukata yau kece da kunya? harda rufe Fuska? Saman gadon na kwanta tare da kife kaina a Kan katifar Ina dariya kasa kasa yace Wai da gaske kike kunyata kike ji yau? mikewa nayi zaune duk na rasa inda Zan saka kaina wata kunyarsa nake ji,kaina na dauke na kalli gefe Ina murmushi na zaro harshe kadan duk cikin kunya,dariya yayi tare da furta ikon Allah Miracle guda yau da kunya addua tayi Allah ya amsa,dama kiss dinki da Kika Saba danne Ni ki min da shi Kika min yafi kunyar nan taki ni ban Saba gani ba,Jin yace Kiss na tashi na fece da gudu na bar dakin,ya tsaya baki bude yace kalau take Kuwa.

Ya zaci kunyar ta wasa ce,sai da ya fito breakfast dake yau bazai fita ba,sai yaga har na gaishe shi bana kallonsa Kuma gaisuwar ba irin wacce mafi akasari nake Masa ba to yane? ya akayi? Ya garin ne? Ina serving nasa ban kula shi ba Kuma ban kalle shi ba ,dariya ta kamashi Kamar wata sabuwa haka na koma masa, yace to za kawo English teacher din? nace Inshaallah,Baki ya saki yace wai kece da Inshaallah har kin San Allah yanzu? na sake cewa Alhmdllh ba laifi,tagumi ya zuba Yana kallo na,yace ko dama Ustaziya ce ne ta lalace,dariya nayi bai gama Shan mamaki ba sai da yaga na canja channel na kamo sunna tv, dama karatun Qur'ani inayi idan na ga dama sabo da yanda na Saba tun Ina kauye,Sabreen ce ta fito taga mun Gama break Muna kallon wa'azi dariya ta tuntsire da shi tace ba wani alaye da zaki mana Kai Allah ya tsinewa karuwa kaji,karuwa ta Kai duk inda ta Kai a duniyanci wato sabo da an kamaki da kwarto shine Zaki canja salo,kallonta nayi nace Subhannallahi wannan kazafi ne Allah ya hana, kiyi harkarki nayi tawa idan ba haka ba Zan ladabtar dake da ayoyin Allah,Nawwar dariya ta kamashi ya Saba shi ashariya da zagin fitsara iri iri a gidansa, Sabreen ma dariyar ce ta kamata ta wuce dining,Nawwar na kalla nace ka kaini gidanmu,me zaki yi Kuma da'awa zanje,Sabreen ta kwashe da dariya sai ga su Sera su wurin bakwai sun shigo,tashi nayi Muka Yi ihun mu da Muka saba tare da rungume juna,Nawwar ne yace sannunku da zuwa shi Kam suna birge shi da kaunar junansu da hadin kai,Zama sukayi Suka gaisa nace me zaku ci,Suka ce sai da rana yanzu sun koshi,Kallo na sukayi Wise tace Miracle ya hasken musulunci? Nace Alhmdllh ai na baku labari tun a waya sai naji Kawai tuba da nadama tazo min lokaci daya Kamar ana ruwan sama haka nake ji addini na zubo min da tsoron Allah kafin safiya na cika makil da tsoron Allah,Tagumi Suka zuba Suka kafe ni da Ido,nace Ina fada muku Kamar a mafarki na tashi naji tuba da tsoron Allah sun fado min Kamar yanda naji farar daya karuwanci nake so, Seraline tace no wonder gashi nan goshinki sai shekin addini yake,nace ah ai walwali nake yi,Yaranki sun samu uwa ta gari nace wallahi ku tayani murna Ina haihuwa yarana zasu Sha tarbiyya tun Ina da ciki yaron zai iya Karatun fatiha dariya mukayi gaba daya,na nuna Nawwar nace idan muna saduwar sunna ma idan ya gasu cikin Oven Babu kiri'ar da baya ja,

Star tana dariya tace au memory din nasa ashe yanzu ba waka bace karatune a ciki? nace ae Mana,Nawwar Jin fitsarar tamu ta daban ya mike tsaye Star tace mu Kuwa Muna nan sai siyar da takashi mukeyi,nayi dariya nace Allah ya shiryeku kawayena Zan ta muku addua,yawwa ki Mana Addua mu yanzu mun manta rabanmu da karanta ko Bismillah, Nawwar yaji tausayinsu Mandula tace Ina so na shiryu wlh Amma bazan iya ba karuwanci ya shiga jini na sosai bana so ma na daina dan a Ina Zan iya Shan sigari? Kun San bana free da hayaki duk yanda akayi Bob marly ya biyo ta tsatson mu shi yasa na gado shi,dariya Muka Yi nace wlh kuwa baki Isa ba gidan aurena ne nan ba bariki ba sai dai ki fita daga gidan ki Sha abarki,tace an gama ta mike ta fice daga gidan gaba daya a can Kan layi ta dinga bulbula hayaki,Baki da wani aiki mu tayaki? Nawwar a ransa yace Allah sarki ji kauna dan Allah kamar yan uwa,cikina Sera ta shafa tace Wai har yanzu baza muyi Yara bane kinki samun ciki haba Miracle ni wlh kin bani haushi ko bakya zagewa ne a daki harka,ki dage rana daya zaki samu,nace ke muke jira kizo ki koya Mana yanda akeyi dan uwarki kaji min yarinya,haka muke ta hira har Nawwar yayi bako Khaleel ne yazo gidan Suka ma can bangaren baki,Sabreen kuwa tana part dinta tana Jin haushi Nawwar Yana barina ina abinda Naga dama Kuma tana ganin wani kallo da yake min kullum kamar zai cinye ni.

Washe gari Jamcy ce tazo ta bawa Sabreen wani magani tace guba ce ke tunda ita take yin abincinta ki sa Mata a abinci taci dan ubanta ba a lokacin zata mutu ba bare a gane a hankali zata fara aiki a jikinta tana lalata Mata kayan ciki a hankali har ta Fara cuta slowly sai mutuwa Kinga babu me ganewa,tafawa sukayi Sabreen tace an gama Indai ba mutuwa Yarinyar tayi ba to bazan ji dadi ba.




Masu Neman Jin wasu Audio na novels Dina kuje YouTube channel na S ZARIA TV


MASU SHARHI INA GODIYA MUSAMMAN YAN GROUP DIN YAR AIKIN KARUWAI.




AsmaBaffa
08061929616
[7/22, 11:38 PM] AsmaBaffa: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI🌼
LITTAFIN KYAUTA NE


81-85


Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA DUKKAN YARAN TSUNTUWA


Page naku ne

Mamu Galadima
Gimbiya Diyar Katibi
Mom Khalisat
Ummul Ayyan
Mmn Nasrin
Haleemat
Hajjora
Oum Abrar
Shertuh
DeeDee
Hafsat A Shehu
Maman Ammar
Oum Darajat
Zainab Usman
Salamatu Oniyanga


Gaisuwa ga
AIDA MAMAN TASNIM





Star ce ta fara bamu tarihinta Wanda ko ni ban sani ba tace Sunana Aisha Usman ni Yar asalin Yobe ce Baba na Malam Usman dake dan gajere ne ni tsayin Mamana nayi sabo da Banana inda kasan Inuwar Battery haka yake guntu ne sosai,Mamata ita kadai ya aura tunda suke dama suna da rufin asari daga ni sai Kanwata Saima Allah yayiwa Baban mu rasuwa ,dama sai rufin asiri sana'ar kayan Miya yake,tunda ya rasu bamu da karfi,Mamanmu ta tsufa da yawa sabo da Basu samu haihuwa da wuri ba,na kusa gama secondary Saima Kuma tana primary tsakanin mu akwai tazara,duk layinmu babu Wanda ya iya taimaka Mana,Dan cikin mu uku amma sabo da lalacewar wasu Musulman yanzu ana kallonmu muna Fadi tashi kowa ya kasa taimaka Mana,Watarana sai mu kwana uku bamu dora tukunya ba sai yawon mu zamu fita gidajen da ake mutunci ko zamu samu kalaci,makarantar gomnati muke Yi amma sai da ta gagare mu uniform dinmu ya yayyage kudin makaranta Dan kadan littafa da sauransu bamu da yanda zamuyi mu biya Muna ji Muna gani Muka hakura Kuma a layinmu ko Yan uwanmu daga na uwa har na uba babu Wanda ke bamu sisinsa kulamu ma ba ayi sabo da bamu da abin duniya.

Mu Yara matane Muna bukatar sutura da kayan kwalliya sabo da rayuwarmu ta inganta har mu samu masu auren mu amma wannan ya gagara kayanmu gaba Daya sai maho muyi kuka mu godewa Allah Muka Fara sana'ar wankau shima dai baya isarmu,an kasa tallafa mana,mutanen layinmu makwafta nayi Imanin sai Allah ya tambaye su hakkin makfataka domin basu sauke ba,akwai wani me hali a unguwarmu ganin bamu da gata Muna zuwa Neman taimako wajensa sai yace na

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login