Showing 27001 words to 30000 words out of 133505 words

Chapter 10 - Yar Aikin Karuwai Book 1

22 Oct 2024

3864

kike Yi kenan duk gidan nan Kuna shaye shaye ni dai bazan taba yin shaye shaye ba,baki Sera ta tabe tace karuwancin ma haka kika ce gashi Kuma kin fara,kallonta nayi nace kawata ya yau Naga kina cikin fushi ne? Sera tace ke dai bari wani banza ne shege ya daukeni ya nuna min me kudi ne ashe ba motarsa bace baida sisi motar ogansa ya aro ya bari na saki jiki da shi a gidan karki ga yanda yayi min kaca kaca ba style din da baiyi ba Ina tunanin na Zama big girl ashe me gadi ne a gidan me gidan yazo ya kore mu ya wulakanta mu in fada Miki sisi dai ban samo ba,dariya nayi na kwanta a gadon nace ke ya akayi haka Sera kece fa Kika koya min Harkar nan Kika ce Kar na sake nayi sex da Namiji sai munyi tsada ya bani kudina cash sannan na yarda da shi karki damu na samo kudi zan iya baki ko dala dari ce kya rage zafi na zaro dalolin a jakata nace Kinga wani me dabban kudi na hadu da shi in fada Miki ko tabani baiyi ba ya bani kudi haka,Nan take Seraline wani kishi ya kamata yarinya tazo a bayanta ta samu kudin da ita tunda take bata samu ba a duniya,ita dare daya ta samu haka Kuma ko taba ta ba ayi ba su kuwa sai sunci sa'a ake samun me biyansu 10k ma Watarana Kuma har 50k sukan samu, wani bakin ciki da hassada ya Kama Seraline itace fa ta koyawa Rabi Harkar amma tazo dare daya ta fita.

Ni dai naga ranta ya Kara baci na nuna Mata dala dari dari nace kin gani yanzu zanje na canja a min transfer accnt dina ga dala dari in Kika canja ta Kai wajen dubu saba'in,Wata tsawa Saratu ta buga min tace bana son kudinki an fada Miki talaka ce ni,nace kyauta na Miki fa,to bana so ko dole ne ta ja tsaki,baki na tabe nace shike nan kinwa kanki na tashi na fita naje a layinmu dake wajen bariki ne komai akwai a nan na canja aka min tsansfer na cire dubu dari biyu naje shopping na siyo kayan sawa masu kyau kana kana iri iri harda Atamfa da leshi da material irin dinkakkun nan,na siyo takalma da jakankuna dai karfina ba masu tsada can ba amma suna da kyau.
Tunda na samu kudina washe gari hutawa nayi a gida ba inda naje,sai a kwana na biyu na fita yau ma ban samu Wanda ya min ba haka na koma gida abina.
Washe gari Kuwa na dauki wanka cikin legins fari da rigata blue na rataya jakata da takalmina me igiya flat me kyau na sa hular gashi brown color, Ina tsaye sai ga motar Nawwar ta tsaya Ina hangoshi ta glass zuwa nayi nace ni kazo dauka? Kai ya daga min ai Kuwa na bude gaban mota na shiga Ina girmamashi shegu kudi wani kwarjini da tsoronsa nake ji.

Gidan da muka je Rannan shi ya sake kaini Muna shiga katuwar tv din a kunne take kidan turawa na tashi ban San Sanda na Fara bi da bakina ba Ina girgiza Kai tsabar rashin kunya da lalacewa wanda ta hadu ta min yawa,dama ance a kiyayi irinmu na Allah idan Muka tashi lalacewa abin ba kyau, Kamar me shaye shaye ko Sabreen uwar Yan Coccaine baza tayi abinda nake ba,remote ya dauka ya canja channel ya Kai news, saman kujera na fada na zauna Ina Sosa Kai kunyarsa ta kamani sabo da baida Wasa Kuma ya tsare mutuncinsa ga uwa uba kudinsa tsoronsa nake ji,Shuru nayi na nutsu Ina Wasa da yatsuna,kallona yayi ya jefo min tambaya yace me yasa baza ki daina karuwanci ba baidace dake ba,gaki kin Kai mace Kuma musulma hausa Fulani ace kin maida kanki Yar kwalta mene dalili ai gwara kiyi aure,nace aure fa kace? Ni nayi aure tab ai ni ba ta gari bace Kuma bani da asali ba ruwana bazan dorawa kaina ba azo a dameni ana ce min karuwa marar asali ba ruwana Kai nifa bata gari bace da har Zan samu Miji nayi aure ni Kam baruwana,sana'ata Kuma Ina sonta akwai nishadi ga yanci inci gashin kaina,yace ba kudi kike so ba? Nace sosai ai ni bani da Kamar kudi a duniya,to Zan na biyanki Albashi duk wata ki zauna a nan gidan ki daina karuwanci,kallonsa nayi nace idan kasan zaka biyani kudi yanda ya kamata Zan iya gwada Zama amma idan na gaji Naga bazan iya ba Zan koma inda na fito,yace Zan dinga biyanki da tsada ki zauna a nan,Nifa bazan zauna ni kadai ba ko ma mene sai dai in kana gidan nan sabo da ni na Saba da surutu idan ba kowa da wa zanyi Hira sai kace Ina prison,yace Alright Zan zauna Indai Zaki daina Zama a titi ana daukanki ana sex dake uban kowa bakya Jin kazanta ko wanne Namiji ya jaki wannan kazanta ce,baki na bude nace ahhh Antaina ai tayi a rayuwa Mene abin kazanta Kai.....shut up ya furta a fusace,Shuru nayi

Shuru mukayi yace Ina Neman Alfarma a wajenki tunani sex zai ce muyi yanda ya kyautata min da sauri na mike na fada jikinsa tare da cewa gani an gama muyi, yace no ba wannan ba,na sake cewa gani kayi ko Mene,yace ba shi nake nufi ba,komawa nayi na zauna tare da furta okay Ina jinka,yace Ina da aure Kinga dole Zan dinga kwana a wajen matata ba kullum zan na kwana a gidan nan ba,nace ba damuwa Indai zaka biya ai an gama,yanzu Naga gidan nan da kayan abinci komai akwai sai kudin siyen nama da kayan Miya tunda Zan na girki,yace Ina sane Zan baki gobe da rana sai ki fara nace to,canja min channel Nigerian film nake so,haka ya kamomin tashar yace gashi wannan ce me sa latest film kullum,okay na furta Ina murmushi, mikewa yayi zai fita,da sauri nace Ina zaka je? Wajen matata,ka gaishe ta,inji wa zance ya furta ko Murmushi babu a fuskarsa,inji Karuwarka zaka ce,hmm Kawai yace ya fice Yana fita nace ban zo da Kaya ba sai dai na dinga saka naka Amma ba kyau saka kayan maza to ya zanyi tashi nayi tare da yin wanka na linke kayana na zaro gajeren wandonsa na saka har gwiwa ya kawo min Yana da Fadi na zurma rigarsa wata me santsi milk me dogon hannun,hannun gaba daya hannayena sun kule a ciki, Ina Fitowa na zaga gidan na Sha kallo sannan na dawo wajen me gadi na kalle shi shima kallona yake yi sanye da kayan ogansa yace Sannu Hajiya,Murmushi nayi tare da tambaya ya sunanka? yace Ilu sunana Yana zaune saman wani dogon bench nace Ilu dan matsa gefe na zauna,Ilu ya matsa gefe na zauna a gefensa dama matashi ne,nace Ilu Kai Dan wanne state ne? Ilu yace Hajiya ai ni dan Kano ne a garin albasu cirani nazo Allah ya hadani da Ogana,nace ashe garinmu daya,yace yanzu a haka ke bahaushiya ce Yar Kano ma musulma Kuma? Nace kwarai kuwa kasan karuwa ce ni amma karma ka fara tunanin zaka kulani ko da wasa kazo sai na fasa maka Kai da kwalaba bana yi da irinku sai me kudi ko da kudinka sai da rabonka,idan ka kawo min raini Sai na sake Yi maka sabuwar kaciya da girmanka, ka ganni paradise kenan ta duniy ..horn Muka ji Ilu ya tashi ya bude gate Yana dariyar maganata shi ya Isa ya kula matar da ogansa ya kula,Nawwar ya shigo da wata jar mota ba irin wacce ya fita da ita ba,Ilu dawowa yayi ya zauna Muka ci gaba da labarin mu sai ga Nawwar ya fito ya hade rai tsoro naji Zumbur na mike nabi bayansa da sauri,ledojin hannunsa na karba Ina cewa Sannu da zuwa Oga, muna shiga Palo ya dinga balbala min masifa bana son rashin kamun Kai,me gadin zaki fita a haka kalli kaurinki duk a waje surarki ta fito a cikin kayana zaki fita harda Zama a gefensa bana so respect your self,dan bakina na turo gaba Ina Kunkuni Ina tsoron fada Masa magana nace ni sabo da Allah shike nan bani da yanci ka takura min a cikin gida,shut up....ya furta a tsawace,Shuru nayi Ina doka kafafu tare da kukan shagwaba nace ni na takur...quite ya min tsawa nace Hmmm ummmm ahhhhh uhmmm....harara ya watsa min nasa hannuna tare da toshe bakina na tsaya gefe tare da yin kasa da kaina,waye yace ki saka min kayana da wannan kazamin jikin naki duk maza sun gama da shi,Murmushi na saki nace neman kudi ne kaima in kana so kazo naka sai yafi na kowa na karaso gaf da shi,hannunsa na riko ya fisge abinsa ke bakya tunanin shedan ko Ina so na rabaki da masifa kina sake jefa kanki,to Ni kadai ce ga wasu can Ashawon ka raba wata da karuwanci mana dole sai ni,kalleki bakya kunyar kanki,bakya tausayin iyayenki,bakya tunanin ayiwa Yan uwanki abinda Kika yi ko kannenki, da karfi nace hehe ai bani da kowa Yar shege ce ni,bani da kanne bare yayye bani da kowa kaga ni kadai ta shafa Kuma ba aure zanyi ba bare ayiwa yarana, abinda Iyayena sukayi suka haifeni shi nake yi,Yan Uwa ma banda kowa a duniya ni kadai ce a duniya sai kuwa na fara hawaye ban San Sanda na Fara zubar da hawaye ba kuka ne ya kwace min sosai na Shiga yinsa a tsaye,baki ya saki Yana kallona,na kalleshi idona jage jage da hawaye na karasa gabansa nasan idan yasan Zan rungume shi bazai yarda ba sai nayi wuf na fada jikinsa Ina goge hawayena kamshinsa yasa har wani lumshe Ido nake nace please ka lalata ni,dan Allah muyi iskanci,tureni yayi da karfi na fada saman kujera yace look bana son Iskanci Ina Wasa dake ne? Zan daina zuwa gidan nan Kuma wallahi zan kulleki a gidan nan babu ta inda Zaki fita ki koma hankalinki ni ba Dan Iska bane,duk lalacewar da Kika yi wacce kike so kiyi Kuma,Shuru nayi ya Gama sababinsa ya haura sama abinsa,baki na tabe nace ai dama na sani da ganinsa nasan Dan love ne da alama ya iya soyayya matarsa tana Jin dadi.

Tashi nayi na haura sama nima dakinsa na kwankwasa yace shigo,shiga nayi Ina Sanda Ina tsoronsa Yana min kwarjini nace ya sunan matarka? yace Sabreen Kai na jinjina nace tayi sa'a tana kula da Kai ba ruwanka da karuwa, wani mugun kallo ya min nace na janye maganata bata kula da kai,amma kaje can wajenta Mana zan iya zama ni kadai kaje ka bata kulawa,ko kulani baiyi ba yana latsa wayarsa abinsa na gaji na fice,abinci naje na ci abina na koma dakina na kwanta sai bacci me dadi.
Cikin dare ya bar gidan ya koma gidansa Yana zuwa gida Sabreen ya iske a Palo yau bata bacci anci kwalliya sallama yayi ta amsa Kawai,gani yayi yau ta gyara gidan ko Ina fes yasan da wata a kasa,ai Kuwa yayi Shirin kwanciya sai gata cikin kayan baccinta wata munafukar riga maroon,ko kulata baiyi ba yayi kwanciyarsa zuwa tayi ta kwanta a bayansa tana faman tattaba Masa kunnuwa karshe taga ko kallo bata isheshi ba ta rungume shi tana so ta motsa Masa sha'awa hannunta ya janye daga jikinta yace ba nason naci fa bana bukatarki karki dameni,kankame shi ta sake yi tana rokonsa please harda kuka tace yanzu idan banzo wajenka waye zai biya min bukatata ko so kake Yi na Fara bin mazan banza yau nafi wata hudu sau daya ka taba sex dani, karki bata min rai Sanda na dinga binki wanne wulakanci ne baki min ba karki bata min rai wlh sai na tashi na Miki dukan tsiya gwara ma ki kyaleni,kuka ta fashe Masa tana shike nan tunda so kake na Fara bin maza da aure na,tashi yayi zaune ta bashi tausayi ko ba komai macece tana da rauni,yace badan halinki ba dai gani kiyi,au ba Kai ma zaka min ba Kinga idan kina so a haka to ki Fara idan baki so ki Kara gaba,ba yanda ta iya haka ta zare Masa riga ta shiga sarrafashi amma ba wani zaucewa da yayi yaji dai dadi tunda ya Zama dole,gani yayi ta wahala sosai ya fara sarrafata amma ba sosai ba duk ta susuce harda cewa i love you abinda babu Wanda ya taba fadawa wani a cikinsu

Shigarta yayi sabo da shegen baccin kwaya bata gyara kanta tana nan a wangale sai kace kofar gari,haka ya dinga Mata aiki ta Fara kawowa tana Jin zai kawo Kawai ta zare jikinta cikin zafin nama tana Sosa Kai tace bana so na haihu yanzu,wani bakin ciki ya Kama Nawwar a waje ya zubar da abinsa,ya kalleta ransa a bace yace karki ce ban fada Miki ba bazan sake kwanciya dake ba,tunowa tayi da hudubar Papa Kan tayi sauri ta samu ciki,hakuri ta shiga bashi tace Dan Allah kayi hakuri wlh Zan haihu ka yafe min,Tsaki yaja ya Shige toilet yayi wanka tare da tsarkake jikinsa Yana Fitowa Jallabiya ya saka a daren taga ya dauki key din mota ya fice, baki ta tabe tace cikin ma sabo da Papa Zan yarda nayi kafi ruwa gudu ta mike ta koma dakinta yau bata Sha komai ba bacci ya kwashe ta.

Gidan da ya kaini ya dawo lokacin nayi baccina na farka na fito palo Ina kallon wani hadadden American film adventure ne a MBC2,shigowa yayi ransa a bace sai da naji tsoro,remote din dake hannuna na ajiye nace Sannu da zuwa,Hannu Kawai ya daga min,nace lafiya Oga? Tsaki yaja tare da furta ba komai,mikewa nayi na shiga kitchen na zubo Masa fruits salat din Dana hada lafiyayye yayi sanyi a daren nayi, Mika Masa nayi ya tsaya Yana kallon glass cup din nace ko na baka a baki, karba yayi yasha yaji yayi dadi sosai yaci gaba da kurba har ya shanye,nace fada min me ya faru? Waye ya taba min Oga? Ido ya lumshe na matsa kusa dashi nace ga fuskarsa ta nuna ogana yana da damuwa ,yace ba huruminki bane abinda ya shafeni,Ni ai ka dauke ni sister dinka ka fada min ko zan iya baka shawara kasan mu karuwai mun san ta duniya,kallona yayi yana tabe baki yace fada mukayi da matata,nace dama nasan itace ai tunda naga ka dawo nasan da matsala,shine abin damuwa kana bata ranka akan mace,mace me rauni sai hakuri,ka dinga hakuri,ya kalleni yace kina wa'azi karuwa dake,a kula da fadar Malam Kar a kula da aikinsa na furta,yace ban San me yasa ba wasu dangina basa Sona,nace to sai me yanzu dan wani baya sonka sai ka tsaya kana batawa kanka lokaci,tunda kana kaunar kanka Allah Yana sonka ai ka gama,ko kowa baya sonka ai Allah yana sonka ko to mene na damuwa ai Kawai kayi komai ba komai kafadarsa na dafa nace kayi nishadinka Master kowa yaci kutmar....na dirko ashar,dariya na bashi yanda nake magana kamar Ina yi da duniyar gaba daya duk na tashi hankalina.

Dariya yayi sosai na tsaya Ina kallon irin kyan da yayi nace zaka ci indomie? Yace a yanzu Zaki dafa? Wai bakya bacci ne? Mu da bama bacci sabo da Aikinmu da muke fita sai mu Kai 5am bamu yi bacci ba sai da rana muke bacci,kitchen na Shiga sharp sharp na dafa indomie taji hadi da kwai na zubo Mana a plate daya da fruits salat din na kawo na zauna a saman center carpet nace sakko mu ci,yace bana zama a kasa ni,Kuma bazan ci dake ba ki bani tawa daban,Haka na koma na rabata biyu na zuba Masa tasa daban komawa nayi saman kujera na jawo center table gaban mu na bashi fork spoon daya Nima na rike daya nina Fara cin tawa sannan yaci tasa yaji dadi sosai bai taba cin idomie me dadinta ba,Yana cinyewa ya haura sama dakinsa ya kwanta bacci ya gama da shi,Ni Kuwa a palon na bingire sai da asuba na koma dakina bayan nayi Sallah bacci na koma,shi kuwa masallaci yaje daga can gidansa ya koma.

Saurayin Gaji Alhaji Kabiru Danbinni duk wata yaudara da ya so yayi wa Gaji ya samu yayi sex da ita amma taki dake zaman aji ba karya,gashi Yana mugun sha'awarta Kawai sai yace zai aureta zai turo manya,Dagaci ba wani bincike Kawai yace a kawo kudi sai Murna suke Gaji har rawa kafa ake Yi an samu Alhajin birni gashi katon gaske ga kiba ga tsayi babban mutum suna kawo kudi aka yanke ranar aure wata biyu masu zuwa,Aunty Amarya tace to da ace shegiyar Yar tsuntuwar tana nan da Kinga Yasin Alhaji Kabiru Danbinni ita zaice Yana so ba Gaji ba,Gwaggo tana yanka Kubewa tace kyale aljana kyawunta suke bi amma Wai duk Yan kauyen nan talakawa basu cewa suna sonta sai Yan birni masu kudi matsiyaciya yanzu wa ya sani ma ko ta shiga karuwanci,Dama ai karuwanci zata shiga me zata Yi idan ba shi ba ana can ana bin maza cewar Aunty Amarya,Mairo tace nidai Ina Jin tausayinta wlh Allah yasa baza ta lalace ba Kar ta samu cuta ta mutu,Gaji tace to ke Ina ruwanki ni zancen Yarinyar nan idan Ina kauna Allah ya konani,hirar aka canja suna ta Shirin bikin Gaji abinsu.

Papa ne a zaune yayi tagumi,Mama ce ta fito tare da tambayarsa lafiya? yace Wai Sabreen me take yi ne har yanzu bata samo min ko takarda Daya ta fili ba kin San ance kadarorinsa kusan gaba Daya a Arewa suke Kinga anjima kije gidan nan kiji ya ake ciki ne ki sake koya Mata dabarun mallakar kayan miji,nisawa Mama tayi tare da furta Yarinyar ce bata ganewa kasan shaye shayenta bazai Bari ta tsinana komai ba amma zanje gidan yau,yawwa kije dan Allah yaron nan naji ance sake bunkasa yake

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login