Showing 78001 words to 81000 words out of 133505 words

Chapter 27 - Yar Aikin Karuwai Book 1

22 Oct 2024

3880

ku kalli abin farin ciki ko yarinya me iyaye bata isa ta Kama kafar Rabi ba, kawai ta juya tayi tariyarta,su Kuma da son gulma da wuri Suka fice har Mairo ita da Aunty Marya ga Gwaggo Suka je tun daga ganin Mami Suka tsorata sun San ba talaka ne ba yaron,suka ga Kaya iya Kaya Saratu tana daga musu tana cewa Kudirar Allah ta sauka a kauyen nan idan da hankali ya Isa izina,Rabi yanzu tafi karfin mota sai dai yawo a jirgi, Gwaggo hassada ta motsa kasa karasa gani Suka yi harda cewa komai sai anyi karya ai Zamanin nan ba lefen ba ciyarwar shine aikin,Mairo tace uhmm ayi mu gani Suka juya Suka fice,Mami Murmushi tayi tace sune Suka rike Rabiah lallai dole taci wahala, da Yamma Suka koma a jirgi aka bar lefen a dakin Inna.
Dagaci sabo da bakin cikin Jin labarin ya nemi Yara Yan daba ya biyasu kudi yace suje cikin dare su zarewa Inna wuka su sato Masa kayan lefen tas,Kamar Inna ta sani a daren tasa Jangudo yazo da yaransa maza samari Suka kwashe lefen tas aka maida gidansa,tana bacci cikin dare sai gasu sun banko kofarta dama bata rufe ba,makamai Suka zare Mata,Inna ta saki Salati tana hawaye suka ce Ina lefen da aka kawo wani ya shaki wuyanta,Inna ta rafka salati tace ai sun koma da abinsu inda Amarya take me za a bar lefe a nan ayi da shi,ku duba dakin,dakin gaba Daya Suka caje ba komai sakinta suka yi Suka koma a daren suka sanarwa Dagaci Suka Kara gaba abinsu.

Kayana da ango duk mun dinka na fitar biki kaf, ba Wanda yasan ana biki a gidan Baffa sai Mami sai Baffa,yau ta Kama ranar dinner tunda aka sa bikin banga Nawwar ba komai Khaleel yake aikowa,ya Sha tsiya wajen Khaleel Kawai share shi yake yi, itama Sufia tace ai Dole nabi Mijina Khaleel musha kallon bikin Yan bariki dole akwai show,yace ai komai shigar dai hausawa za ayi inda kisan kina Kano, ranar 8pm za a fara sabo da haka wajen make up kowa cikinmu da inda ya tafi, nikam tawa inda sai wane da wane ke zuwa nan naje Wanda Ango ne ya biya,su Sera suna can tasu,abinka da masu samari kala kala dukkan matan kusan kowacce ta karbo shegiyar mota a wajen samarinsu,mota ce da mota ke tashi sai wadda ka gani,har wasu masu abota da yaran masu kudi duk an gayyato su sunyi anko Kuma Yan Mata na kece raini ba a magana Sabo da masu kawaye ma sun gayyace su, Kai kace bikin wata Yar wani ce da, waje ya hadu dama na manya ne, 8:30pm an gama min make up, munsha kayan namu Kalar decoration din wajen da aka yi Fari da dark pink sai Silver gaba Daya wajen walwali yake, ni rigar Amaryar tawa gown ce daga kasar waje yayi order online dark pink tana Jan kasa daga baya,sama ta kamani me dogon Hannu Net,sai gogoron da aka daura min Silver da takalmi da jaka silver Kalar shaddar jikinsa,hularsa da takalminsa duk Kalar shaddarsa Yar gaske an Masa babbar riga ta matasa dai dai shi, Khaleel ke driving dinsa a bayan sabuwar motarsa ta bugawa a news fara duk ta Sha adon flower da zare pink kana gani kasan ta Amarya da ango ce, daga wajen makeup din na fito wacce ta min ta rike min kasan rigar har motar na shiga ta rufe tana mana murna Khaleel yaja Muka wuce,hannuna wata a layinmu bahaushiya ta iya lalle tana yiwa hausawa karuwai, ita ta zana min ta gani ta fada ja da baki hannu da kafa nayi kyau abin ba a cewa komai, Khaleel yace Amarya kinyi kyau sosai wlh dama me kyau ce,nace na gode Friend

Nawwar yace mu ganki na juyo sosai harda fari na lumshe Ido dan Wai yaga gashin idon da aka saka min sosai, hannayena da ya Sha lalle da abin hannu na amare na daga Masa ya gani na juya Masa tafin hannun ya gani,Khaleel yace kaiiiiii gaskiya lallen yayi,Nawwar yace Wai mene haka bana son munafunci,dariya yayi yace to sai ka bari a daura sai mu daina fada amma yanzu bata zama taka ba,Murmushi nayi na zare takalmin kafata tare da dago kafar daya nace ka gani, Khaleel ya leko da Kansa ya maida Kansa wajen tuki,Nawwar yace Allah ya kyauta maka Khaleel,kafar ya gani tayi kyau yace good, maidata dan Allah kin dameni,sai da na maidata yace muga hannun naki na Miko na dama,yace na hagu,na Miko masa hannunsa yasa a aljihu ya saka ya zaro gidan zobe ya bude naga zoben gold me tsada Dan karami hannuna ya rike ya saka min zoben a yatsana na kusa da karamin yatsan da kyar ya shiga yayi min cif cif,na washe baki nace yayi kyau thanks gidan zoben ya saka min a jaka tare da kudin liki masu yawa Yan dubu dubu sababbi,Khaleel yace gulmamme abinda kakeyi kenan,Bai kulashi ba, tun kafin mu karasa wajen event din muke jin kida na tashi Kamar hauka Yan gayu ana ta Shiga Su Sera Amarya suke jira suna waje wajen su goma sauran Kuwa an gama cika ana cashewa rawa suke ta rashin kunya ta fitsara Amma da aji ake yinta ba hauka ba yau ranar nutsuwace da yanga da aji, Yar zabil tana ciki itace MC ma,akwai wasu masu rawa a gidan karuwai ba rawar da basa Yi Mata da maza Yan rawar Solo ne ai kuwa sune suke takawa gwanin nishadi ana ta kallo suna mimimg wakokin hausa, a ciki Mc tayi magana da turanci Amarya da ango sun iso tayi da hausa kuma,kowa Zama yayi aka nutsu, mu Kuma muna mota me camera ya Mana pics iya Amarya da ango,Muka fito aka Yi mana harda frnds a wajen sannan a waje abokan ango sunfi su goma ga Mata kawayena Sufia ma tana cikin ayari mun gaisa da ita,Fara tafiya mukayi zamu shiga ango ya rike min hannu, Sera da wise suke rike min riga ta baya,Muna zuwa bakin kofa aka canja kidan Amarya da Ango muna tafiya ana fesa Mana snow da golden burzer kanana har sit dinmu na musamman.

Dinner ta Matukar kayatar duk da an zubar da daraja a wajen amma yanda muka tsara anyi abin da iyawa a tsari da birgewa kowa zaice wayewa ce tayi yawa a wajen, anci an Sha an zubar da liki,Ango har daloli ya lika ana ta sawa a tiktok da sauran media, Allah yasa Sabreen tana ta bacci Jamcy ta watso Mata pics da videos Amma tana ta baccin asara ta kashe wayar gaba daya an Sha kwaya, sai da aka gama Dinner angwaye a guess house dinsa aka sauke su komai a gidan Su Khaleel akayi Mami ma tana can duk da ba Wanda ya sani.

Washe gari Sunday Muka Yi Shirin tafiya Kano kauyen mu ai a ranar da yawanmu Mata munfi ashirin Muka dira a kauyen ango ya biya jirgi Muka zo Kano Muka shigo a taxi, angwaye sai da safe zasu zo a jirgi su ma da Iyayen Ango,Sabreen an manta da waya ana ta bacci in ta tashi ma wanka take taci abinci tayi Sallar da Zata iya ta koma bacci,gamu iya karuwan da yawan mu Muka dira Wise tace dole Dagaci yasan mun shigo gari.










AsmaBaffa
08061929616
[7/22, 11:38 PM] AsmaBaffa: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI🌼
LITTAFIN KYAUTA NE



61-65



Official

By
AsmaBaffa




SADAUKARWA NE GA DUKKAN YARAN TSUNTUWA



Page naku ne

Haleemart Ameenu
Maman Zulaihat
Khadeedodo
Nererh
Nanah
Zainabgohe
Mmn Humaira
Saudat Safiyan Maman Inam
Amatullah Kamshi
Firdausi A Nagwaggo
Ummiauwalu72
Alhamdulillah


Injija ta gare ki
Ummulkhair
Mrs Chief






Sullubewa nayi tare da tsayawa a gabansa Ina kallon Sabreen a kafar bene, Sabreen ta sandare a tsaye na bishi zamu hau sama na juyo nace kuma idan na ganki a part dina wallahi sai kin karba a jikinki,yanzu zamu shiga ciki Kuma kin San idan akace mace da Namiji sun kebe a daki kin san me zai faru,sannan a wannan harkar ta dadi na Saba ihu sosai,I like to shout well well,I like to cry well so Kar na ganki kusa da part dina lokacin Ina enjoying life dina, juyawa nayi Ina wasa da botin din rigar Nawwar nace Honey hoho My Baby, ka tuna na jiya irinsa nake so ai ban San da salon ba sai jiya ya bani sweet,hannunsa na rike nace muje local government kaikayi take naja hannunsa Muka Yi ciki mamaki yasa ya bini da kallo abin Nawa daure Masa Kai yake,Muna shiga part dinsa Sabreen ta rushe da kuka ta kifa kanta a table tana ta faman kuka,tashi tayi fuuuu tayi dakinta ta Sha kwayoyi ta fada bed sai bacci.

Ni Kuwa Muna shiga bedroom dinsa na fashe da dariya na zauna a gefensa inda yake zaune nace nasan yanzu tana can tana kuka,ai mu ka fada Mana Daya sai mun fada maka goma bata San mu bane wajen fada ba a jayayya da Yan duniya, yace kinji dadi to? Nace sosai na fada saman bed dinsa Ina dariya Ina tsalle,karki lalata min gado,wuyansa na shako ya fado saman gadon ya kwace jikinsa nace yau baza kaje Office bane ka tashi ka tafi,yace ba inda zanje shike nan bazan huta ba,tunda ba amarci kake ba mene amfaninka ka tafi kawai,a gidana Wai ki dinga korata kin takura min fa,Hannu na na tura a rigata Ina Sosa gefen Boobs dina nace kurji ne ya fito taba kaji na rike hannunsa ya fisge abinsa Yana dariya yayi kwanciyarsa,nace kaje ka gaida Mami Wai mutum bazai fita ba,banza ya min nace ayi mace shike nan sai kace an auro kwarkwara sai dai a dinga kulani da rana dare ba nawa bane,dariya yayi ba shiri yace kin dameni wlh ki tafi ki bani waje,tashi nayi na fita ya bini da kallo tare da lumshe Ido bai sani ba bacci yayi gaba da shi,Nima kwanciya nayi a dakina sai bacci sai 12pm na tashi a gurguje na fada kitchen na shirya girkina lafiyayye sai 2:30 na gama komai na jera a dining naje nayi wanka dama nayi Sallah,leshi na zaba cikin kayan lefena maroon doguwar Riga ne dinkin manyan Mata na saka na fito Ina walkiya,Ina zama a dining naji ya shugo naga har yayi wanka ya canja cikin Jallabiya ashe masallaci yaje ya dawo, a palon ya zauna ya dauki remote,tashi nayi na tuna Izzarsa shi yasa na karasa kusa da shi na zauna a gefensa sannan a hankali nace abincin fa ko nan zan kawo

Yace sai anjima,sabo da me? ya furta Kawai,nace a'a gaskiya ban yarda ba sai Mami taga ka rame tace laifina ne,a hankali ya juyo ya kalleni tare da cewa Wai ni yaro ne shike nan ban Isa nace a'a ba sai kin min musu,ka bari idan ka koma bangaren Uwar yaranka sai ka Mata wannan na furta tare da mikewa na jawo hannunsa,mikewa yayi ya Isa dining nayi serving nasa Muka Fara cin abincinmu,Yana ta yanga nace idan baza ka iya ci ba nazo na baka a baki ni a wajena ba komai bane,Tsaki ya ja yana wani ci a hankali na taso na dawo gabansa na jawo kujera na zauna,Sai ga Sabreen ta fito itama ta Sha wankan shadda,ai ganinta da sauri na tsiri shafa Masa gashi,shi bai ma San ta shugo ba,nace Babyna abincin yayi dadi ko,Sabreen ya gani sai lokaci ya gane abinda nake Yi sabo da itane ashe, Sabreen Tsaki ta ja tace mu bama Kai kanmu sai di azo a same mu a haka ma Muna yanga Mata masu aji kenan,nace ke kenan baki ji sunanki ba Sabreen ni Rabiah babu hadi,ga baya ga gaba dan Allah kalle shi baki ga ya Kara fresh ba? Girarsa na koma shafawa da yatsa nace ya samu me Nono kirjin ba faranti bane cika Masa hannaye sukeyi, Sabreen ta hayayyako da bala'i ya daka Mana tsawa Enough......nace zaren ba Kalar yadin bane shegiya Yar gidan Zuwaira me wagegen baki Kamar kofar gari ko ubanki Yusufa ya Isa ya kawo min walgi wlh kina bude baki sai na tashi na tafasa Miki jiki....tsawa ya min bana son shirme Shuru Muka yi yaja tsaki yaci gaba da cin abincinsa.

Sumarsa naci gaba da shafa masa Ina Wasa da ita wani dadi yake ji Yana so a dinga taba masa ya Kan sashi bacci ma,Sabreen baki ta tabe ta ebi abincin tace baiwa wahalalliya dole ki dafa naci ta wuce room dinta a ranta tace zaku gane kurenku ai Iyamami dan bata samu Baffa ba ne,wannan auren sai an raba shi,ni kuwa lemon na tsiyaya masa nace Wai har yanzu bamu kwana biyu ba ne na matsu aurena ya kare, bai ce min komai ba har ya gama ya sha ruwa tare da goge bakinsa da tissue ya mike yace jeki ki dakko min mukullin mota a Kan gadona Zaki ganshi,a gabansa na tsaya Ina murmushi nace kaga dalilin da yasa bana son auren nan sai kana zamanka me dadi a dinga aikenka Kawai wani yazo ya dinga saka mutum aiki dakko min kaza bani kaza,haba Wai shike nan kana aure baza ka huta ba,Ido ya zaro tare da furta oh magana Zaki fada min kawai kice baza kije ba alright ya juya da sauri zai dakko da Kansa da sauri na rungumo kugunsa nace wayyo zanje Wasa fa nake yi na kankame shi sosai,sake ni dariya nayi tare da jawo shi baya da dukkanin karfina ban San Kawai sakar min jiki yayi ba gani nake yi karfina nane Ina haki na haura sama da dan gudu na naje na dakko na dawo da gudu nace gashi yace ba na wannan motar ba na manta Yana kasan pillow na juya da gudu Ina juyawa ya dinga dariya Yana sani ya min haka dana yi gudu sai na birgeshi yanda komai na jikina ke rawa,dawowa nayi Kamar zanyi kuka nace babu fa key na gani da yawa a wajen, yace Zaki ga yafi kowanne girma sauri karki bata min rai na juya da gudu gudu gudu sauri sauri naje na dakko na tako steps da gudu sosai sallamai Mami Muka ji ta shigo ni ta hango Ina gudu,tace sai kin fadi ko Rabiah,Ina haki nace Sannu da zuwa Mami Ina murmushi

Itama murmushin tayi tace Kuna lafiya,nace Bari nazo mu gaisa na shiga kitchen na kawo Mata abinci da ruwa da lemo sai fruits dana yanka,Nawwar Kuwa Zama yayi kusa da Maminsa Suka gaisa,zuwa nayi na durkusa har kasa na gaishe da Mami ta amsa da kulawa tare da furta Ina Sabreen din fa?nace tana dakinta,Kira min ita nace to na nufi sama har part dinta,bedroom dinta na tura Kawai na shiga na iske gabanta kayan maye ne iri iri,ta zuba garin Coccaine a yar takarda tana ta faman sheka tana bubbuga kanta idonta yayi jajir ta fita a hayyacinta,banyi mamaki ba tunda wannan shine Karo na biyu dana taba gani,Sanda nazo a matsayin Yar aiki na gani yanzu na sake gani,tana ganina tsoro ya kamata jikinta ya dauki rawa gashi tana wani fisge fisge ita kadai Murmushi nayi nace Karo na biyu kenan kinga da ace wata ce da tuni na tona Miki asiri,idonta Yana rufewa nace Mami ce ke kiranki,cinkin muryar Yan maye tace baaaa zaaaan iiiiiyaaaaa taaaaa shiiiii baaaa baaaaaaccci.....naaaaa.....keeeeee....ji...tana Gama fadin haka daga zaunen ta kwashe tarkacen ta tura kasan gadonta komai da komai ta fada saman bed sai bacci.

Fitowa nayi jikina yayi sanyi ace mace ta maida kanta marar amfani a duniya daga bacci shike nan bata da lokacin komai, Palo na koma nace bacci take Yi,Mami tace ki taso min ita Magana zanyi daku dukkanku,nace dazu fa tace kanta na ciwo ta Sha magani shine ta dan samu bacci,idan ta tashi zuwa dare sai ya kawo mu har gida ni da ita inaga zai fi,Murmushi Mami tayi tace to tunda bakya so a tashe ta ,Nawwar yace ita wace baza ta tashi ba,kyaleta Zan dawo zuwa daren dama gidan kawata zanje idan na gama abinda nake sai na sake biyowa,nace to nan taci abincinta sosai Muna hira ta mike Muka rakata har mota ta tuka ta tafi,hadari ne ya hado sosai nace ya zaka koma ciki Kai da zaka fita,na fasa dama wajen Mami zanje Kuma ta zo anjima zata dawo,a Palo Muka zauna na kamo mana Nigerian film Muna kallo,aka yi abin dariya ni ban San me akace ba sai gani nayi Yana dariya,nace Allah sarki Jahila Rabi dan Allah ka dinga fassara min ba iyawa nayi ba kasan kadan nake tsinta nafi Iya pidgin English,ance a saki a school kin ki fafur, nace Allah ya kiyaye katuwa dani bazan gane komai ba ni yanzu me Zan iya a karatun boko ai Ni yanzu duniya ce a gabana,dariya yayi yace kin san baki da hankali Rabi wai anya dai dai kike kuwa,kina da auren kike fada min duniya ce a gabanki, baki na turo nace lokaci ma baya sauri ni na matsu a sake ni na Kama gabana,wato fadan da Inna ta Miki Baki ji ba kenan? banji ba ai ni bana ji ba a fada min naji,Allah ya sawwake miki Kuwa me yasa yanzu tunda aka kusa biki kika daina cewa kina son Sex? ko a taba miki boobs, dariya nayi nace laaaa Allah ya yaye min ji nayi na daina fada Kawai yanzu ma tunda aka Yi bikin naji bana son sex din na tsani Harkar ma burina yanzu a sakeni na tafi,mamaki ya kashe Nawwar yace wato ke duk abinda Allah baya so shi kike so,anyi aure ai dole a cinye ki,Fuska na bata nace ni wallahi yanzu bana so Kawai saki nake so,ji nake Yi Kamar Ina prison bana son gidan nan ban san Sanda na Fara hawaye ba gaba daya ji nake Yi na tsani gidan bana son Zama wani zugi nake ji a raina na

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login