Showing 60001 words to 63000 words out of 133505 words

Chapter 21 - Yar Aikin Karuwai Book 1

22 Oct 2024

3877

biyar zaka ga tsiya a haka ya kaita toilet tare sukayi wanka Suka tsarkake ya gasata sosai da sosai sannan Suka kwanta bacci tana harararsa tana yatsina fuska tare da furta a banza.

Sabreen Kuwa shaye shayen nata kullum Kara karfi yake duk kudinta sun Kare haka duk abinda ta samu a hannun Nawwar kayan maye take Sha,hakan bai isheta ba har wajen Baffan Nawwar take zuwa ta hada Masa karya tace Nawwar ya hanata kudin cefane babu kayan abinci a gidan haka zai bata kudi ta siyo kayan shaye shayenta,Yau ma ta Kai kwana biyu bata Sha komai ba,bata tambayi Nawwar ba take ficewa Yana Saudiyya Umrah ya kirata Kuma tana da number dinsa domin kullum sai ya kirata a waya sabo da ko a gida yanzu Yana bata hakkinta sai dai in bata so,idan bukatarta ta taso Yana biya Mata shima Kuma Yana nemanta duk da ba son hakan yake ba amma shi aure ba ayin abinda aka ga dama sabo da ibadane kowa sai ya kiyaye hakkinsa ko kana so ko baka so,Baffa ya fito zai fita sai ga Sabreen tayi parking din motarta ta tsuguna har kasa ta fashe da kuka tare da gaisar da Baffa da muryar kuka,Baffa yace lafiya dai Sabreen? Sabreen tace Baffa Nawwar ne zai tafi Umrah amma ko sisi bai bani ba na cefane duk da gidan akwai kayan abinci Amma Baffa da yatsuna yake so nayi girkin,Baffa yace ai Nawwar baida hankali bai gajeni ba Kamar ba ni na haife shi ba duk horon da zaka Yi to karka cuci mutum da hanashi abinci nan take ya ja tsaki tare da bude mota ya dakko dubu dari cash ya bata ta karba tana murna tayi godiya sannan tace Baffa a dawo lafiya bari naje na gaida su Papa yace to ba laifi ya shiga mota driver ya ja,ita kuma ta nufi bangaren Papa taje nan ma bayan sun gaisa hira tayi hira tace ai haka ya tafi ya barta ba kudin cefane ta langabe tana kuka sai da Papa ya bata 50k Suka Gama zage Nawwar tas Mama har da cewa yo uwarsa ta mallake danta komai sai ita zai bawa in banda Iskanci mace harda wani tafiya gidan danta Wai na bakin ruwa ta tafi hutu tsofai tsofai,Sabreen tace wa ya sani ko wani dadiro ne da ita a boye ba a sani ba,haka Suka dinga sharri kala kala sai dare Sabreen ta koma gida sabo da ta biya gidan su Jamcy.

Ni Kuwa ya Kai sati a makka bai ko kirani ba tunda ya bani kudi sosai,baya gari na kirawo Seraline Suka zo su shida haka muke girkimu muyi hira kullum sai sunzo gidana munci kudi,yau ma cewa nayi su shirya zamu fita Shan ice cream ni Zan kaisu,key din motarsa Daya da ya bari gidana wata GLK na dauka na Shiga na Mata key na fita ba sosai na iya ba Wise ce take koya Mana tun Ina gidan karuwai, na kwashi kawayena Seraline,Star,Wise sai Dan daudu Santana Muka fita na fito da kudi na kashe mana,yanda nake murza motar nan a titi Kamar ta ubana,Seraline tace Dan ubanki gobe muje gidan su Nawwar wannan tsohuwar kakar tasu da Kika ce ta takurawa Maminsa muyi Mata warning,nace ku bari ba ruwanku sai sun shigo gonar mu rukun,Wise tace ai idan ta shiga gonarmu hhhhhhh tayi dariya tace sai taga shege,sai na Mata shege she go see Shege, Seraline tace gobe ko jibi zanje kauyen mu naga Innaya,muje a motar Nawwar Miracle muyi karya mu fita da Asuba muje muga su Dagaci mu cusa musu haushi dariya nayi nace kin kawo shawara

Star tace idan kunje ku tabbatar sunji kunya, Sera ki kwana ki hakura da aikin nan na siyar da Gomnatinki gobe mu fita sai mu kwana a hotel jibi sai mu shiga kauyen Kinga kwana biyu mun dawo Nawwar bai San naje ba tace haka za ayi tace muje mu siyi sababbin Kaya na kece raini, direct wajen inda ake siyar da leshi Muka je ko wacce ta zabi Dan dubu Hamsim da gani ba karya,muka Siyi Shadda itama ta kece raini, Sai wata gown ready made kowa ta zabi wacce ta Mata, wajen masu dinkinmu Muka je su dama telolin na layin mu dinkin Yan karya suke irin mu Yan duniya ko yanzu kake so za a dinka maka in zaka cake kudi na zabi dinkuna irin na manyan Yara Muka ce a Daren zamu Zo mu karba suna da yawan gaske telolin katon hole ne teloli sunfi ashirin a ciki, ina da takalma da jakankuna masu tsada Suma da Nawwar ya siya min daga nan har yawo Muka fita Muka je Shan ice cream.

Ai Kuwa dan Muna son karya da mota ne da a jirgi zamu tafi amma sai Muka tafi a mota,Muna zuwa mun San sai an zargi karuwanci muke Dole tunda zaman kanmu muke babu me aure ko a jikinmu sabo da alfahari muke da barikinmu,Mun ware wuta da asuba,Seraline ke tuka motar sabo da ta fini kwarewa Kuma ta Sha bin hanyar, ko hutawa bamu yi ba wuta muke Kawai ba tsoro ba tunanin rayuwa, sai dare Muka iso cikin Kano,tuni Sera tayiwa wani Alhajinta waya ta shigo kano,Har ya Kama mana hotel me tsada kowacce da dakinta Muna zuwa sauka Kawai Muka Yi,sai da Muka huta Muka Yi wanka tare da cin abinci, sannan Alhajin Sera yazo wani dan Majalisar tarayya ne me kudin gaske ne dan kasuwa ga siyasa ya rike mukamai da dama, ya shigo ya iskeni a dakinta ya dinga kallona Yana hadiyar yawu,Ido Muka hada ya kashe min ido,ya kalli Sera ya furta wannan kawarki ce? tace ae sunanta Miracle itama tamu ce,yace Ina so ko nawa Zan kashe tace bazan baka ita ba sai da sharadi yace na mene Fadi ko nawa ne, tace aikin Hajji zaka biya min,dariya ya kyalkyale da ita da wani Jan Idonsa gashi fari tas kyakyawa sai Jan Ido,yace an gama wallahi Zan na biya an gama bana da ke za a tafi,tace sai na tafi Ina can Zan hada ku yace kin San bana karya Alkawari karki damu,na kalli Sera Kawai nace to ka biya Mata ni kuwa zaka samu Local government, ya sheke da dariya yana nuna ni Kamar sabon Kamu irinku nake so kin min,nace Sera enjoy bari naje na kwanta na mata sai da safe.

Sera Kuwa da Alhajinta zasu kwana,condom ta Mika Masa ya saka sannan Suka fara shoshalewa,washe gari Alhaji ya tafi, motar mu na bada wanki aka Mata wanki na musamman ta fito kal, a nan Muka shirya Sera leshi blue ta Sanya ni kuwa shaddata na sa pink straight skert da wata riga hadaddiya nayi mugun kyau takalmi na da mayafi da jaka silver, sai kace yaran gomna haka Muka fito na maka glass na manyan yara irin kyan da nayi ba a fada naci dauri na musamman domin Sera ce ta Kira Mana wata me dauri tayi mana kawai abinka da yan duniya,Muna Fitowa a hotel din kowa sai kallonmu akeyi musamman ni da nake fara ana cewa da gani yaran masu hanu da shuni ne,Muna Jin wani Yana cewa ba zai wuce yaran gomna ba, dariya nayi a raina Seraline tace da zasu je suga gidan kasar mu da sai sun tsine mana nace ai jefe mu da duwatsu zasu Yi da zasu San asalinmu, yanzu tunda anzo inda Zan dan iya tuki nice driver

Kamar motar ubana yanda nake wani gadara da Fadi na bude na Shiga Ina baza kamshi me tsayawa a rai,sai dariya muke da Sera mun cuci mutane masu kallo,nace Seraline kinga mu Fara yawo duk inda Muka hango Majalisar matasa muje muyi parking idan da dan shago ko ya yake muje mu dinga siyo Dan abu muyi show a garin nan ko banza babu kara'i nan gaba mun more,Sera tace irin wannan mota haka muje muyiwa maza kwalele yanda kike haka haukacewa za ayi Muka sheke da dariya naja mota Muka wuce, Muna tafiya a hankali tace yawwa shiga ta nan akwai taron maza matasa suna nan Yan zaman banza Kuma akwai kanti a wajen ko pad mu siyo,shiga layin nayi ai Kuwa dake Sunday ne yamma ta Fara duk sun fito wasu a tabarma wasu a bench gasu nan da Yan kwalisa,a opposite nayi parking tunda Muka shigo Suka tsare motar da kallo an hango farar Mata mazan Kano mayun fararen Mata,Seraline ce ta Fara fita ta zaga ta jikin kofata tana jirana na bude na Fara zuro kafata matasan nan Suka bi kafa da kallo sannan na fito da Yar jakata Muna tafiya ta gabansu Muka wuce Suka shaki kamshi Muna ji suna kus kus harda wow wani matashi yace da waccen zata so ni wallahi na yarda na Zama dan rikon Jakarta da na Shana gata da kudi ga mota na zabi wacce nake so na fita ta kashe min kudi ko kishiya bazan Mata ba babu ruwana biyayya Zan mata, Muka wuce muna shiga karamin shagon nace akwai chewgum orbit yace ai na Mika Masa kudi ya bamu guda Uku tun a nan Muka bare kwali daya Muka dauka sannan Muka fito tare da mota yo mu ba Jin kunyar uban wani muke bare mu dinga hardewa sabo da kunya.

Muna Jin wani Yana cewa sai kace daga kasar waje Suka sauka,haka muka dinga nuna wankan mu a gari muna yiwa maza Yan zaman baza masu matacciyar zuciya Wanda yanzu da yawa Samari mace me kudi suke nema wacce zasu ci banza, sun sha kwalele sannan Muka nufi kauyen mu, Seraline Kam Mamanta tana zargin ko karuwanci take ne amma Dan da yafi karfinka kana kallo sai addua ba yanda zaka iya da shi gashi idan an tambayi Yar uwarsu da aka turata can wajenta sai tace ai aikin restaurant sukeyi akwai wasu ayyukan na kamfani da suke Yi sabo da har ita din karuwa ce ba a sani ba,Kuma dalilin da yasa aka tura Seraline wajenta ba me Dadi bane idan ta zauna ma a kauyen surutu ne za ayi ta fama shi yasa basu damu su dai sai Addua.

Muna shiga kauyen Allah yasa a Majalisar su Dagaci ta dattijai da suke Zama sai na hango wata me gyada gashi nike tuka motar, Seraline tace karki sake ko gidan Dagaci kije har mu koma naji ance anyi auren Gaji ai,matar na shararo da uban gudu Kamar Zan bi takan su Dagaci suka mike da gudu, parking nayi a gefen inda Dagaci suke sun zaci wasu manyan ma'aikata ne,Glass na sauke a hankali nace da me gyada siiiiiiii......motar na bude na fito gaba daya,da kyar Suka gane ni Suka tsura min ido suna kus kus wace wannan haka ko Yar Gomna ce ne? Jin magana ta nace ya ke me gyada nawa? Me gyada tace laaa Rabi Murmushi nayi tare da gyara glass dina da yatsa nace ashe kin gane nice,Dagaci yace Rabi ce wallahi yace Yar tsuntuwa ai Kuwa itace nan take yace ta tabbata Karuwanci yayi riba ashe a Karuwancin ma ci gaba akeyi haka,wasu da suke Zama wasu abin kyama,wani dattijo a ciki yace idan karuwancin na kucakai ne ba ai idan harka suke da manyan masu kudi ai ko Yar shugaban kasa Albarka,bakin ciki ya Kama Dagaci shi yafi so Rabi ta dawo abin tausayi ta bar gidansa wannan ai gaba ta ci,wani a ciki yace dama Dagaci ya fada Mana ance ta fada karuwanci ashe da gaske ne,Dagaci Yana da tabbacin asirinsa yaci Rabi yace ai Babu zargi tunda ka ganta tare da Saratu to sana'arsu kenan,Saratu Yar gidan Inna Wuro wacce ta Fara cikin Shege a kauyen nan aka dauke ta aka kaita Lagos wajen Yar uwarsu,ai ba wani aiki duk karya ce karuwanci take,dama ai Yar macece tunda Ubanta ya mutu kanin ubanta Bila ba ana zargin shi yayi cikin ba,to ga Rabi ashe can ta je dama abokin barawo ai barawo ne tun a kauyen nan halinsu daya,Dagaci a ransa yace da nasan haka zata ci gaba bazan ma yi Mata asiri ta fada bariki ba,idan ta sake zuwa naga taci gaba to asirin zanje na karya muga ta tsiya naga inda zata samu kudin,ai tunda ta hanani na sadu da ita baza ta zauna lafiya ba,a fili kuwa suna ta gulmarmu ni dai na koma mota Suka bude baki tunaninsu Zan gaishe su ko Dagaci,Amma motata nayiwa key na bula musu wata muguwar kasa nayi gaba,Dagaci yace ta rika lallai Kun gani ko kallo ban isheta ba bare ta gaisar dani ai tun tana yarinya haka take min a gidana,Suka ce gaskiya kayi hakuri cab.

Gidan su Saratu Muka je,Inna Wuro sai ganin mu tayi katsam,tayi murnar ganin yarta,dakinta me kyau na bulon siminti harda tile sabo da Saratu ce ta rushe na kasar ta musu ginin bulon siminti ta saka tile ta zubawa Innarta kayan daki na zamani ta raba gidan ta barwa Kawu Bila kanin Babanta gidansa na kasa tunda baida mutunci,Inna sai murnar ganin mu takeyi tace ku zauna ta kawo Mana abinci dambu da ruwa tace gashi kuci,sai da Muka ci Muka Yi Sallah sannan Inna tace ashe Kuna tare ance Dagaci ne ya koreki ko,nace ae wlh na bawa Inna labari abinda ya faru Dagaci ya koreni dan gudun Kar ya hada min sharri a gari,Inna tace Allah ya saka Miki Yar nan, yanzu kema aikin gidan abincin kike Yi? Nace a'a ni Saratu ce ta hada ni da wani me kamfani ya bani aiki nice me kula da ma'aikatan ciki kaf Kinga dole na samu kudi,tace ai nafi yarda dake Rabi ke yarinya ce ta gari kowa ya sani a garin nan ke saliha ce tunda Naga Saratuna tare da ke nasan Alhmdllh yarinya ta bata lalace ba,ke ai duk garin nan an yarda dake,Kuma Indai bikinki yazo kizo na hadaki da dan uwana na Jangudo ya Zama waliyyinki dama Yana Jin tausayinki,dariya nayi nace Inshaallah Inna,Haka ta zauna tana ta Mana nasiha da fadan mu samu Miji muyi aure,Muka ce to Inna Inshaallah,yau zamu koma birni sabo da gobe da sassafe zamu koma can sabo da aiki,Inna tace oh bakwa gajiya to Allah ya tsare ai ni Alhmdllh Saratu ta gama min komai 'ya daya tamkar da dubu,yarana biyar Maza gasu nan tunda Suka Nausa kudu ban San inda suke ba ko nemana basu yi basu San halin da nake ciki ba sai Allah ya azurtani da Saratu ba abinda ta raga min ci Sha da sutura komai Allah dai ya Miki Albarka Saratu Allah ya tsare min ke Allah ya shirya min ke,Allah ya muku Albarka gaba daya Muka ce Ameen Muka mike tare da yiwa Inna Sallama Muka bata kudi.

Muna Fitowa sai ga Gwaggo,Aunty Amarya,Mairo duk Dagaci ya basu labari baza su iya hakuri ba sai sunzo gulma,wani kallon banza na musu nayi ma Kamar naga kashi,baki Suka saki zance ya cika gari duk an cika wajen ana kallona,sai ga Bala me shago ya zo Wanda Zan tafi ya bani dubu daya Sanda aka koreni,nace Bala kayi gaggawa yanzu zanzo gidanka,ya washe baki yace Rabi nace Na'am na gaida shi na zaro kudi a jakata na irga dubu ashirin na bashi nace gashi ka Dan rage ayi hakuri sai na dawo,kowa sai kallo ya karba Yana ta godiya nace karka ce komai na fada maka a waya Ina aiki kasan kudu akwai kamfanunuwa nan gaba zan samo maka aiki kaima,Bala yace sai na jiki godiya nake,Yara Suka dinga Rabi Ina yini na dinga raba musu sababbin Yan dari dari dari biyu biyu,Wanda duk muke mutunci sai da na dan bashi wani abu Muka Gama karyar mu sannan zan shiga mota Gwaggo tace baza ki kulamu ba Rabi? wani kallon banza na mata na nuna kaina da yatsa nace ke baki da Chemistry a kanki ko? baki da Physics bare Biology ko? you dey mad na tofar Mata da yawu a gabanta na kalli Aunty Amarya nace Zan dawo ku jira sai na cire miki beli a gabanki na shige mita tare da daga glass din motar na bulbule su da Kura na ja Muka wuce,Muna tafiya Muka saki ihu a mota na daki sitiyari Ina dariya nace shegiya karya,kida Muka saki Muna tafiya muna dariya nace duniya da Dadi Allah ka bamu tsawon rai,Sera tace if you do anyhow you go see any how,shi yasa nayi shuru kiyi musu da kanki zai fi musu zafi, sai da Muka zo Kano nace Saura gidan Yan Uwana da Zan Kai ziyara gobe Zan kashe last Kobo na,Saratu gidan Marayu? Nace yes me Zan siya musu,Saratu tace har su biscuits da su Alawa ana siya kwali kwali a Kai idan kudinki ya karu sai kiyi dinkuna dana Yara da Yan mata etc duk a Kai,nace yanzu dai muje mall mu siya kayan Yara kanana Yan kanti mu gani,direct inda Kawai kayan Yara ake siyarwa Muka Fara zuwa,na siyi Kaya set sun fi set Hamsim dana Mata Dana maza dai dai karfina ba masu tsada can ba,sannan na siyi Inners panties da bra da vest ko wanne ya kai guda Hamsim Suma dai dai yanda Zan iya tunda Banda kudin da Zan iya siya su wuce masu araha,na siyi always pad yanda Zan iya na siyi Pampers na Yara itama da dan yawa, kudin da suka rage min gaba daya a jakata dubu goma ne,sabo da kudin Dana tara a iya accnt dina ya kusa million daya Kuma duk kudin Nawwar ne dake ba wani kashewa nake ba sai da dalili,Wanda nake kashewa a gari Wanda ya bani ne na cefane,Seraline tace to Nima bari dai na bada ko zan samu lada,nace naki kudin wallahi kudin Haram ne,Kuma wallahi Kika sake Alhajin nan ya biya miki Makkah da kudin karuwanci to ba lada ba na halak bane Kuma kin San bazan je ya kwashi dadina ba wallahi ki sani gwara ma ki sani ko kinje Allah bazai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login