Showing 87001 words to 90000 words out of 133505 words

Chapter 30 - Yar Aikin Karuwai Book 1

22 Oct 2024

3876

gobe.

Sabreen a waya ta Kira ta sanarwa da Mama da Papa tare da Iyamami,Iyamami har part din Mami taje taci mutuncin Mami tace Kuma wallahi Matukar bai dawo da Sabreen ba baza kiji da dadi ba,Mami ta kalleta Kawai tace shashasha Jahila Wacce bata San me take ba,Mama ta ja kwafa tayi waje, Lokaci Amaryar Baffa Ummin Haidar ta shigo sashen Mami taji abinda ke faruwa bata ce komai ba sabo da ita duk abinda ake Yi a gidan bata Shiga daga ita sai yaranta sai danginta miji ne Kuma a hannunta yake sai abinda tace to mene abin da zata zafafa shi yasa har wajen Mami take shigowa idan taga dama,tana Jin ma abinda ake magana akai Kawai ta fice ta koma part dinta ta dauki waya ta Kira Sahibinta Baffa suka shiga hira suna soyewa ita Kuwa Mami bata San ma number dinsa ba in Banda ta Nigeria,Iyamami tana Gama masifarta Mami ta Kira Nawwar, Yana Shirin fita ta Kira wayarsa,dagawa yayi suna gaisawa tace da gaske ka saki Sabreen? Nawwar a Palo ya zauna ya bawa Mami labarin abinda tayi,yace dama na gaji wallahi da abinda Yarinyar nan ke min,Mami tace kayi hakuri Nawwar ka maidata dakinta,zaiyi magana tace bana son ji umarni na baka kawai, to kawai yace ya kashe wayarsa ya fita abinsa bai dawo gidan da wuri ba ma har 11pm Shuru Shuru,gajiya nayi da jiransa ga abinci Ina ta gadi sabo da Matukar kana da kishiya to sai ka kula da abincinka sosai Kar a hada maka mugunta Ina Palo Ina gadin abinci,har naje nayi Shirin bacci cikin Yar guntuwar rigar baccina Purple Ina zaune a palon har na Fara gyangyadi,wayarsa na Kira bata Shiga ba naci gaba da jira,sai gashi ya dawo ko karar mota banji ba sai sallamarsa naji Kawai Ina dan gyangyadi na,idona na bude a hankali na kalle shi Ina murmushi na amsa sallamarsa tare da mikewa nace Sannu da zuwa yace yawwa shima da Murmushi Yana kallona rigar baccin ta Masa kyau nayi kyau a ciki,yace baki bacci ba?

Ina ta jiranka ko lafiya ko ba lafiya ban sani ba gashi Ina ta kiranka taki Shiga,ya kalleni tare da cewa ashe kin damu dani haka? Ido na lumshe na bude su tare da cewa mace da mijinta ta ya baza ta damu da abinta ba, haka Kawai ya tsinci Kansa da Jin wani dadi a ransa har ya kasa boyewa sai da ya murmusa,nace abincin fa,wanka zanyi,nace no ai gwara kaci Kawai idan ka tafi sama ba sakkowa sai bacci ai yafi dadi,hannunsa na riko Muka zauna a dining nayi serving nasa ya dauki Spoon yana cewa Wai ke duk a wannan kazamin gidan naku Kika iya girki haka kullum da Kalar da kike yi,dariya nayi nace da fa Sanda nazo daga Kauye cewa nayi bazan Yi Iskanci ba,ba Wanda Zan bawa jikina,Kuma a gidan babu me baka abincinsa kyauta komai ba mutunci sai da kudi,kaga duk yanda muke da su Sera da ace yanzu Zan koma da Zama can to sai nayi bariki babu me iya bani ko ruwa kyauta,to da nazo gari Seraline ta dauki nauyina na 2wks kullum tana ce min na Fara fita street naki yarda,shine tace to baza ta sake ciyar dani ba tayi kokarinta sannan dakinta bazan kwana free ba sai na Fara biyan kudin haya,sai nace ni dai bazan siyar da jikina ba sai nace da Zan samu aikin wanke wanke da shara da nayi,sai tace ga masu dan kudi ne a gidan tsab zasu biyani,lokacin ta hadani da Wise,Star da Yar Zabil na Fara musu girki da ayyuka, aike etc kullum a gidan ana rainani ana min kallon banza,dare Daya naji babu abinda nake so face na fara karuwanci burina ya dawo Kawai so nake na shahara a karuwanci sunan har wani dadi yake min,Kamar fa me Aljanu lokaci daya naji idan ban fara Karuwanci ba sai naji kamar ma ni ba mutum bace Kawai burina ni dai maza su daukeni su bata ni, gaba daya kunyata ta gudu dama Zama a gidan tunda a gabanmu har sex ana yi,zancen banza tun kana da kunya har sai ta gudu,ai tunda na sa a raina Zan Fara duniyanci gaba daya sai da nafi Yan gidan fitsara amma lokacin ko an fita dani kwalta sai dai na gama tallan jikina a titi Ina azo aci dadi motoci maza iri iri suna zuwa sai nace sai idan za a biya daga million daya zuwa sama sabo da Headquarter dina a cikin GRA take komai akwai ciki, kowa sai yayi tafiyarsa hmm ai an Sha fama Kawai na yanke Masa labarin iya nan ganin Sabreen ta fito ta wuce kitchen,nace kaci abincin ka tsaya kana kallona ko spoon daya baka ci ba,labarin naku ne ba dadin ji,spoon din na karbe nace kawo na baka a baki,sake karbewa yayi abinsa ya fara cin abincinsa da Kansa

Sabreen ce ta fito ta ja tsaki tace aikin banza wa Zaki nunawa kula da miji,Nace ke Zan nunawa ke me Kika iya idan ba bacci ba,zuwana gidan nan bawan Allah bakya bashi hakkinsa gashi nan daga zuwana sabo da yawan amarci gaba daya na kwashe Vitamin c da b da e da a da d da f duk na kwashe su a jikinsa Babu Saura ko daya na barki nan, ke gashi nab kullum sai karmashewa kike Kamar ana yankar Naman jikinki ana Miya da shi to Babu Minalerals duk na hada na kwashe daga jikinsa ba abinda Kika iya sai fada, da bala'i Sabreen tace ke har wani dadi zakiyi,nace fes ma kuwa domin ance yanda bakin mace yake Kato can ma haka yake Kato,karamin Baki karamin can wajen.

Nawwar Yana jinmu ya gaji da fadanmu ya mike yace yanzu ku duk akan wannan kike fada ya nuna Antainarsa Yana cewa to ku yanke ku rabata kowacce ta dauki tata, nace kawo wuka kaga aiki dariya yayi yace muje ya janye ni, Sabreen tana tsaye sororo,Ina tafiya Ina girgiza Mata jiki nace muje Oven ya dauki dumi sai gashi kawai ya kamata a sa min memory Ni kaina dariya nayi nace yau da Sabreen taji kida Kuwa iri iri,yau Nawwar ba bacci sai kida Kawai na juyo na zuba Mata gwalo nace Wakar Sangaya zamu kamo, dariya ta Kama Nawwar yace wai dick din nawa ne Memory dinki? Nace ae Mana a saka shi cikin cellular sai kida da Sabreen ta Sha kida irin irin sai dai ta toshe kunnenta yo Ango yaji gashi a Oven,Nawwar ya dinga dariya iskancin nan na Rabia ya ishe shi.

Satinta biyu su Sera Suka zo min yini naji dadi mun tsula tsiya a gidan,da guzirin magangunansu na Mata washe gari kuma Baffa ya dawo gida,ko hutawa baiyi ba Papa yaje Masa da zancen auren Nawwar, barazana ya dinga Yi yana fada yace zan sa Nawwar ya saketa dole.

Haka muke zaune rayuwa tana tafiya sai dai nayi girki na gyara gida Sabreen da Nawwar suci su koshi,tun sau daya da ya taba romancing Dina washe garin kaini bai sake ba Nima ban sake ba,Muna zaman mu a haka na matsu ya sakeni na tafi tunda har na kwashe satikai a gidan Nawwar na gama gajiya da gidan,baya Zama sosai ya koma aiki sosai,Ina Shirin damunsa akan ya sakeni, yau ya dawo bayan yaci abinci dakinsa na bishi har yayi Shirin bacci zai kwanta na shiga fuskata ba walwala,Yana kwance a saman gadonsa Kawai na tsaya a kansa na turo baki Kuma na kasa magana,kallona yayi yaga naki kallonsa Kawai na tsurawa bango Ido,dariya na bashi ya murmusa ya dago ya sake kallona na sake cuna baki gaba,hannunsa ya mika saman drawer ta jikin gadonsa ya dakko wasu takardu tare da Miko min su,nayi banza da shi ban ko karba ba.

Yace rike cikewa zakiyi form ne na biya Miki aikin Hajji,zabura nayi na juyo da sauri na washe baki nace Allah? yace Zan Miki karya ne,ihun murna na saki tare da dira tsalle na dire a Kan kafafuna nace na fasa tambayar sakin karka sakeni kaji na fasa barin gidan Ina nan tare dakai ko Watarana nace ka sakeni ka kwada min Mari biyar ka cimin mutunci ko ka fada min bakar magana kace Yar tsuntuwa Yar kwararo,dariya yayi yace ba ruwana bare kice nace, takardun na karba na kalla nace Allah sarki ashe kana sane dani, takardun na ajiye da sauri nace me kake so Fadi ko Mene zanyi,yace bana son komai,na nuna gabana da hannuna nace dan baka sani bane kake gudun Oven dina a tsaftace yake kana cutar kanka baka sani ba,yace Indai wankewa ne da ruwa dama a tsaftace yake Mana,zancen na share na haura saman bed din,da sauri ya dauki pillow Yana dariya ya rufe fuskarsa pillow din na fisge yasa hannaye tare da Kare fuskarsa Ni Kuwa ko Ina kiss nake masa har na rike hannayensa biyu ai Kuwa ya maida labbansa ciki ya danne sai habar kawai

Nace au hakane shikenan hannayensa da na rike da hannayena na dora saman manyan boobs dina nace ai akwai wani idan kaki kiss,Ido ya bude ya kalleni Muka hada ido nace kasan mu fa Indai rashin kunya ce to a cikinta muka ginu,gwara ma ka taba,yace sakar min hannu,a zuciyarsa Yana cewa Allah yasa Kar ta saki hannun wlh dadi ne da ita ko hannuna ta rike Kamar zan zauce haka nake ji, ai Kuwa sakin hannun nayi na tashi na kwashi takardun nace na iya rubuta hausa da karantawa,turanci ma Ina dan iya rubuta wani abin kadan na karanta kadan bazan iya cikewa ba sai dai na fada maka ka cike,yace shi yasa nace na saka ki a school kinki,nace nifa Allah bazan iya karatun boko ba yanzu babu karatun da zanyi Zan dai iya yarda idan ka kawo min malamin turanci ya koya min karatun turanci da rubutu shike nan Kawai dama kaga Ina tsintar wani Kuma na iya pidgin ba laifi,yace to shike nan.

Tashi yayi yana tambayata abubuwa Yana cikewa har ya gama sannan yace Saura passport gobe ki shirya da wuri 8am zamu fita a miki,nace to Allah ya kaimu na gode Allah ya saka da Alkhairi Allah ya Kara budi,yace Addua zakiwa kanki sosai shi yasa tare zamu tafi nasan akan abinda nake so kiyi adduar idan ke kadai ce ba yi zakiyi ba,nace fada min wlh zanyi nasan akan me ma kake so nayi adduar,Kawai Allah ya shirya ni na daina zancen Karuwanci nayi zaman aurena,na dawo mace nutsatsiya,yace ae abinda ke damunki Allah ya yaye Miki ko? nace Ameen ai har abinda nake ji a zuciyata dan baza ku sani ba ni Ina ji,yace kafata dai kafarki,to na furta Ina murna.

Washe gari Kuwa na shirya cikin Abaya me kyau blue naci takalmi da jakata masu tsada,shima ya zuba kyau cikin kana nan kayansa,Muka fita tare uwar baccin tana ta fama ya kaini aka min international passport daga nan nace ka kaini wajen su Sera idan ka tashi daga Office Sai ka biyo ka daukeni,yace na kaiki dai Ina tsaye ku gaisa mu wuce idan Kun matsu da hirar suzo gida wajenki,nace to shike nan kaini hakan,har can ya kaini Yana parking na fito a mota da Santana dandaudu naci karo ya rike baki tare da furta wow Miracle kinganki Kuwa yanda Kika koma sai kace daga inji aka fito dake gaskiya auren nan ya karbeki nima da Zan samu Wanda zai aureni haka a Yar iskata ai da naji dadi,dariya nayi nace Santana kenan,Wise ce ta fito sanye da guntun wando da riga hannunta sigari ce take sha tana ganina ta saki ihun murna sai ga Mata suna fitowa,Star ce ta karaso daga ita vest Bumshort ta fada jikina tana cewa shegiya kin ganki Kuwa wlh kinyi kiba kinyi kyau Kinga duwawunki Kuwa yanda suka sake komawa,Seraline tana Fitowa itama ta shafa fuskata tace kaji laushi oh Karuwanci ya taimaki Yar uwa,dariya nayi sai ga Mandula tana gani ta Fara rawa suna ta zuwa Muna gaisawa nace sauri nakeyi amma Zan samu time na dawo Suka ce ai ko baki zo ba Zaki ganmu ma nace good Muka danyi hira sama sama sai taba jikina sukeyi Wai na Kara kyau,damuna yayi da horn dole na musu sallama Muka tafi,Muna Hanya yace sai wani tabaki sukeyi sai kace yar lesbian yana jan Tsaki nace sai gidan Mami,dake Maminsa ce ba musu sai gamu a wani katafaren gida gari guda gidane na ubansu muka shiga.

Parking yayi sannan Muka fito Muka jera zuwa part din Mami direct gaskiya ba karya,palon Muka shiga da sallama,Mami tana palon da yaranta kaf suna hira suna kallo,ganinmu da Nawwar Mami ta washe baki tana Jin dadi tace sannunku da zuwa,Durkusawa nayi tare da gaisheta kannen Nawwar sai kallona sukeyi har Suka gaishe ni Suka gaida Nawwar sannan muka zauna,Mami ta sa aka kawo Mana kayan ci iri iri mun dade kafin muyi musu sallama muka tafi ko wajen su Iyamami bamu leka ba yace baza mu je ba sabo da maganganu marasa dadi gida Muka nufa kawai,ai Muna Fitowa sai ga Iyamami ta shigo daga waje alamar unguwa taje,kallona tayi tace ke Hala kece amaryar tana yatsina fuska nace ae,ke farin naki ma Kamar ba na Allah ba sai kace jikin kazar da aka fige Kalar kyankyami amma a haka a kanki ake gallazawa Yar dangi Yar asali ba Yar tsuntuwa ba,Murmushi nayi nace tunda nayiwa Ogan ai dama bana bukatar yabawar wani Yar katuwa,Kuma kowa ya ganni wlh yasan gaskiya ba farin kanti bane Kuma har abada Sabreen baza ta Kama kafata ba,Kuma sai dai hassadar mutum ta cishi ko wanene billahillazi, Iyamami baki ta rike tace ke Allah daga kawo ki wato dangi ma baza ki mutuntasu ba da sauri na bata amsa da ae duk wanda ya dagulamin rai sai na dagula masa nasa bare ke da baku ja girmanku da mutuncinku ba Kun isheni wlh ki kiyayeni Iya Watarana sai na sa an Miki fyade wlh ki kiyayeni kinci darajar Nawwar amma ba a Shiga gonarmu,Dan ubanki kisa ayi min fyaden ban taba Jin Yar iska irinki ba tsofai tsofai Dani zaki ce zaki sa a mini fyade sai ta fashe da kuka tana salati tayi ciki.
Nawwar farin ciki yayi shi Kansa Iyamami ta isheshi a rayuwa.

Bayan mun dawo gida Sabreen ya nema anci sa'a bata Yi baccin ba bata da kudi kayan maye sun Kare,Nawwar ya sameta tana gyara part dinta yace Zan biya Miki Makkah Aikin hajji ko Umrah? tace a'a ni kudin nake so Zan siyi abu me muhimmanci na gaji da zuwa makka,Bai kawo komai ba yace Zan tura Miki kudin aikin Hajji ya juya ya fita,Yana fita ta hau tsalle da murna,nan take ta Kira Jamcy tace kudi sun samu ki sa Mana ranar zuwa Kauye karbo maganin,tace to an gama ki shirya next week mu tafi,tace to an gama ya batun Fara kasuwancina naki? Sabreen tace Zan Fara mana ki hadani da Wanda Zan Sara a wajensu Ina son kayan maye kin San yanzu cinikinsu akeyi matan aure ma Sha suke a boye,Jamcy tana Dariya tace baki da matsala,a ranta tace Indai wajen boka ne na gama hada baki da shi za a iya kamaki a abinda zai baki idan na koreta sai na kori Karuwar Karuwar tafi min wahalar kora,kawaye a daina yarda da kawaye wajen abubuwa musamman Harkar malamai za a iya hada Baki a dinga damfararki kudi ko wani Abu.
Ni Kuwa Nawwar ke koya min aikin hajjin da zamuje yanda ake komai duk da cewa tare zamu amma duk wani hukunce hukunce sai da ya sanar dani na rike komai,a international zamu je ba a hukumar alhazai ba shi yasa komai aka gama Mana sharp sharp cikin sati daya.

Ana gobe zamu tafi duk wani shiri munyi,ga Seraline,star da Wise mazaje sun biya musu suma dama yanzu Mata sai ayi badala Kawai dan an biya musu Makkah aje ayi pics ayi karya aikin kenan duk wasu sabo da ayi karya ake zuwa ko ta hanyar haramci ne Kamar yanda su Seraline Suka bada kansu aka biya musu aikin hajji,Sera Alhajin da yace ta bashi ni shi ya biya Mata taki ce Masa nayi aure tace sai ta dawo zata hada shi da ni bayan tasan Karya ne,su sun riga mu tafiya ma,kafin mu tafi Nawwar ya siya min Sabuwar iPhone me shegen tsada itama Sabreen ya tura Mata kudin,ranar Kuma tace zataje wajen kanwar Mamanta bai hanata ba tace yini zata Yi yace a dawo lafiya dama idan Zaki fita ai ba a fada min kike ba,ita dai tafiyarta tayi Suka hadu da Jamcy ashe kauyen ma a nan Anambra yake wajen wani matsafi in Suka maka aiki Kamar yankan wuka sabo da tsafi ne.

Suna zuwa wajen wani Jan bedsheet ne an zagaye wajen da shi ko Ina wasu kaho ne mutumin jikinsa daure da Jan yadi a jikinsa Yana zaune suka shiga,bayan sun zauna da turanci yace meke tafe da ku,Sabreen da turanci tace kishiyata ce ta dame ni a gidan mijina ta sa mijina ya tsaneni gaba daya ta ita yake ko banda ni ,a baya bana sonsa aka Mana aure amma yanzu Ina sonsa.
Matsafin ya daga Kai sama sai da ya dauki wasu mintuna sannan ya kalle su yace me kike so ayi Mata?Kawai a sa ya saketa saki uku ya Mata dukan tsiya shine Kawai bukatata,Arnen nan yayi dariya ya dakko wani kullin magani dan kadan yace gashi ta karba yace kiyi Masa abinci ki juye masa shi du a abinci idan ya ci an zakiga aiki,farin ciki ya Kama Sabreen tace kudinka nawa ne? Yace dubu dari biyu nan take ta zaro a jaka ta bashi tana godiya Suka tafi,Jamcy tace

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login