Showing 132001 words to 133505 words out of 133505 words

Chapter 45 - Yar Aikin Karuwai Book 1

22 Oct 2024

3882

ya dauki nauyin yarsa,yanzu Haka shine ya siyar da wasu kadarori na Baffa ba tare da shi Baffan ya sani ba,na gaji da rufa Masa asiri,gwara ayi uwar watsi,Papa ya taho wajen Iyamami yaji abinda Mama ke fada jikinsa ya hau tsuma,lokacin tare suke da Wise,ta rufe baki tace cab di,Iyamami ta kwashe Mama da Mari tace Yar sharri,Papa ne ya shiga yace gaskiya ta fada ya zube gwiwoyinsa a kasa hawaye Yana zuba a idanuwansa yace wannan abin da nayi shine mafi Muni a rayuwata na rasa yanda zanyi na iya fada amma abin Yana damuna bana samun sukuni idan na tuna nine sanadin dan Uwana,Ki Kira Sulaiman ya kaini kotu a yanke min hukuncin kisa ko naji sanyi a raina,ya kalli Mama yace kema a yau dole na Fadi naki kece Kika Hana faccalarki zaman lafiya kece munafuka.

Labari ya Fara bayarwa yace Sanda taga faccalarta Mamin Nawwar tana zaune lafiya da mijinta gashi mijinta yafini kudi shine ta hada baki da wani mutum a matsayin babban malami ne yake zuwa Yana fadawa Baffa Mami tana Neman ransa tana Masa asiri nan gaba idan bai gujeta ya kaurace Mata ba zata iya kashe shi,kullum malamin nan Yana zuga Baffan Nawwar Yana fada Masa karairayi tun baya yarda har ya yarda ya Fara wulakanta Mami da yaranta Kuma da sa hannunki kema Iyamami ko Baki San da zancen ba? Iyamami tayi mukus yaci gaba yace sabo da kin tsani Mami kina ganin ta mallake Miki danki kuka hada Baki,sannan ke Kika jawo har na iya kashe Dan uwana kullum sai ki dinga cewa nine abin tausayi bani da komai sai dai na zauna a karkashin Yan Uwana Kika dinga cewa Mami ce tasa Baffa Bai maidani me kudin gaske ba duk kuwa da kokarin da yake ke ba kya gani ai wani baya yiwa wani arziki Kuma gidajen da na siyar na Baffa kece Kika zugani Kika ce na siyar ai bazai gane ba,duk kece Kika dinga hada Yan Uwa fada dama irin wannan wasu Iyayen suke raba Kan yaynsu ya karasa Yana kuka,Iyamami tana kuka wiwi tace ai bance ka kashe Sunusi ba,ke Kika zugani Kika ce sun hada Kai sun ware Ni sun fini arziki kece wallahi ko me ya faru kece kika dinga zugani, Baffa da ya Riga ya shugo tare da Nawwar kafarsa kasa daukansa tayi ya zube saman kujera sabo da bacin rai, Maman Sabreen asirinta ya tonu Sai kuka, Iyamami kuka Papa ma kuka,Nawwar mamaki yake abin kamar a mafarki,Iyamami faduwa tayi ta sume aka kwasheta zuwa asibiti gaba daya Kuma aka tattara har Wise zuwa asibitin,an Dade kafin Iyamami ta farfado,Baffa da Papa sune a kanta a hankali ta Bude idonta tana magana a hankali tace ku yafe min dan Allah,Hannun Baffa ta kamo ta kamo na Papa tace ku yafe min dan Allah ku hada kanki ku yafi juna,Yusuf kayi kuskure Amma da hannuna a ciki ban San abin zai Kai ga kisa ba,tunda ka Gane gaskiya ka tuba ga Allah kabi Allah ka gyara kuskurenka yanzu a Zamanin nan ko an kaika kotu ba lallai ma a yanke maka hukunci dai dai da laifinka ba,Abu ya faru sama da shekara talatin me za ayi,Papa yace za a iya yanke min hukunci Mana Sulaiman ya kaini kotu ko naji sanyi a raina ya sake fashewa da kuka yace wlh tun daga ranar da Sunusi ya mutu na rasa kwanciyar hankali in na tuna nakan kasa bacci ya zanyi da hakkinsa,Baffa bai iya magana ba ma bare Nawwar,Mama tana gida tana tattara nata ya nata ta gudu gida garinsu itama tana ta kuka,Sabreen ce tazo da gudu tace Papa Mama ta tafi,Papa yace tafi ruwa gudu na saketa saki daya Zan rubuta Mata takardarta,Sulaiman yace shashasha mutumin banza mene amfanin sakin nata,Papa Wise ya ruko ta fisge hannunta tace yo Ni ai ban San laifin naka yakai haka ba wlh bazan zauna da makashi ba,Nawwar yace ai Kuwa kinyi karya,wani yace kice kina sonsa ba inda zaije Kuma Zama a gidansa ba fashi idan Kuma kece kike da kanki sai ki tafi gida na gani,Wise tace gidanka Zan koma ai,yace badai gidana ba,tace idan banzo gidanka ba gidan wa zanzo wallahi nan Zan dawo dole ne na taho ta fice daga Asibitin hankalin Papa ya sake tashi shi Kam a baya Dan kudi auri Wise amma tunda tazo gidansa ya fada kaunarta da gaske son da bai taba yin irinsa ba,Nawwar yace Papa kayi kuskure da badan abin nan ya Dade ba wlh da kaina Zan Kai kararka,yanzu ma zaka iya Nawwar mene amfanina,Baffa ne ya harari Nawwar yace Wai Ina ruwanka ne bana son rashin kunya,Nawwar yace ai gashi nan garin son malamanku masu kudinmu sai a samu wani banza kazamin malami ya dinga zugaku tunaninku yasan gaibu,Kuma karya ce sannan ma malamin ma kaji fake ne wani katon banza ne ya shiga rigar Yan tsubu yace Yana hango maka Mami tana Neman ranka wannan daga ji kasan ba gaskiya bane,Mami kafi kowa sanin wacece,Zanci ubanka idan baka min Shuru ba Saura naji zancen a wajen matarka,Nawwar yace ita da take kawarka baka suruka da ita sai kawance kuyi ta hirarku bakwa so ma naji zancenku dan taji Mene.

Iyamami duk ta cika dakin da kuka tana kaicona nayi asara gwara na mutu na huta,Papa yace ba inda Zaki tafi Dake zamuyi nadama muna nan Allah ya Kara tsawon rai.
Wise ma kayanta ta iba sai gidan Nawwar,ta shigo min tana kuka nace lafiya tace Sweety ne,nace sakinki yayi? tace a'a,nace to mene ke da bakya sonsa Kika ce asirinsa Zaki tono,wlh Ina sonsa yanzu ni na kamu da son mijina,to Mene Wise taki fada wai an iya boye laifin miji ba a so a tonawa miji asiri,Nayi nayi ta fada min taki fada,nace ke Kika jiyo kuma,sai da ta gaji sannan ta bani labarin komai mamaki ya kamani nace tab aiki ja,Kuma sai ki taho tunda dai Yana nan Abu ya faru shekara aru aru mene amfanin tahowar,Wise ta zumburo baki tace bazan koma ba idan Zaki koreni Kuma to,nace a'a me yayi zafi idan Nawwar yazo dai kin san sai ya koraki.
Nawwar Kuwa Yana dawowa ya dauki wise ya maidata da kansa,ana mayar da ita ta daina kula Papa.
Sabreen sai ita kadai tace gwara ma na samu mijina nayi aure na huta da wannan bala'in na gidanmu,shaye shayen ma yaushe rabo tunda aka kawo wannan shegiyar Papa ya daina bani kudi ta hana shi.

Cele Kuwa motarsu sai da Suka je tsakiyar Sahara ta lalace sunfi su ashirin a motar Mata duk sunfi yawa sai maza,Yan matan ciki kwata kwata mutum hudu ne,Cele,Sameera,lawisa,murja sai maza matasa su Uku,Abdul,Mustapha,Awwalu,sai irin su Kakan cele mutum biyu,sauran Kuma duk matane manya dasu.
Dake su Mairo a jirgi Suka tafi su har sun Isa kasa me tsarki,sai Wanda mazane matasa Kamfani ya kaisu ciki akwai Bashir,Bello,Aminu,Danlitu da sauransu,sai masu zuwa wasu kasashen daban daban.



KARSHEN YAR AIKIN KARUWAI KENAN

SAI BOOOK 2 ME TAKEN MATAFIYA DA ZAMU SHIGA BAYAN NA HUTA NA SATI BIYU ZAMU DAWO MU DORA DAGA INDA MUKA TSAYA.

WANNAN BOOK2 MATAFIYA, DARASINSA DABAN NE DA NA BOOK1,SANNAN WANNAN KARON STAR DINMU ITACE CELE A KASKO ME KAMA DA RABI SAK WATO RUFAIDA ,ZAMU DINGA TABO MUKU BANGAREN SU RABI SUMA TUNDA LABARIN YA SHAFE SU SUNA DA DANGANTA DA SHI SANNAN A BOOK1 KARKU MANTA BA A GAMA BA FA AKWAI SAURA DAN KO RABI BATA SAMU CIKI BA TUKUN,GASHI ZAMU JI YANDA ZAMAN AUREN WISE ZAI KAYA,SAI NA SU STAR SUMA,SAI MAKOMAR MAMI DA BAFFA,DAGACI SHIMA DUK SAI A BOOK2 MATAFIYA.
INSHAALLAH INA FATA LABARIN DAKE CIKIN BOOK2 MATAFIYA ZAI FADAR YA ILIMANTAR KUMA YA NISHADANTAR DOMIN AKWAI NISHADI SOSAI A GABA.
FANS INSHAALLAH ZAKU DARA A BOOK2 MATAFIYA.

LABARI NE AKAN MUTANEN MU YANZU WANDA SUKE TAFIYA NEMAN KUDI KASASHEN DUNIYA,WASU KASASHEN MUSAMMAN YANKIN LARABAWA,WASU IN SUNJE SUNA DACEWA SU SAMU ABINDA SUKA JE NEMA SHIMA ABU NE ME KYAU,SAI MASU AKASIN HAKA IDAN KA FADA HANNUN NA BANZA,KO KAJE DAGA NEMAN KUDI MATAN MU SUNA LALACEWA ACAN,WASU SU KOMA BARIKI,WASU SU FADA LESBIAN,WASU KUMA A SAMU WANDA YAN KASA NE SU BAUTAR DA MUTUM TA HANYA DA DAMA,GA MATAYENMU MUSAMMAN NA KAUYUKA DA AURENSU MACE TA BAR YARANTA TA TAFI TAKARCI WATA KASA,WATA TAJE A BASHI,WASU DA KUDINSU DA DUK WASU TAKARDU,WASU TA BARAUNIYAR HANYA KO GURBATACCIYAR HANYA SUKE TSALLAKAWA KASASHE,WASU SU TSIRA DA RAYUKANSU,WASU KUMA A HANYA MA SUKE MUTUWA WAHALA TASA SU RASA RANSU.
WASU WAJEN TAFIYAR MA SU FADA HANNUN YAN DAMFARA,SAI AN KIYAYE AN KULA SOSAI WANNAN BA KARAMIN ZUBAR MANA DA MUTUNCI YAKE BA A IDON DUNIYA.

INSHAALLAH BOOK2 SAI YA BAKU MAMAKI,KUMA A CIKI ZA A KARASA MUKU BANGAREN SU RABI

KARKU MANTA STAR DINMU CELE ME KAMA DA RABI SAK.



COPY BY ZAINAB BUTALAWA


ASMABAFFA

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login