Showing 54001 words to 57000 words out of 133505 words

Chapter 19 - Yar Aikin Karuwai Book 1

22 Oct 2024

3874

Shan gabansa nace kayi hakuri please nima Watarana mamakin kaina nake yi ban San Sanda nake furta irin wannan maganganun ba Ina so na daina na kasa,wallahi da ba haka nake ba idan kaga Saliha Shuru Shuru to nice,Indai kina so in hakura sai kin yarda Za kiyi aure,Nan take idona ya ciko da kwalla nace wlh ni bana son aure idan ana min zancensa ma ji nake zuciyata Kamar zata fito,Salati yayi a ransa a fili yace sunnar kike adawa da ita lallai bariki ta Miki illa ya taka zai fita,da sauri na riko hannunsa Yana juyowa ya kasheni da mari yana huci idonsa ya canja Kamar wani zaki,tsoronsa ya kamani na dafe kumatuna na tsaya na zaci akan auren ya mareni sai na fada kirjinsa na fashe da kuka wani wawan hankadarwa ya min Kamar me Aljanu ya fisgo Wayar Tv ya Fara zuba min Yana masifa yace sa'anki ne ni Ina daga Miki kafa bakya ji ko muharraminki ne ni ko an fada Miki ni Dan kwalta ne irinki, ihu nake yi na zube a kasa Ina bashi hakuri,Baba kulu tana ji tace lallai ba shakka zaman bariki suke in ba Haka ba wacece Namiji na dukanta tana bashi hakuri haka,Fitowa tayi ta rike wire din dake hannunsa tana cewa haba Alhaji kayi hakuri Mana,shi kuwa sai kokarin fisge Wayar yake yi yace kyaleta bata Sanni bane dan Ina kyaleta,da yatsa ya nuna Ni yace duk ranar da Kika sake min Maganar banza wallahi sai kin gane kurenki Kuma Allah yasa na dawo gidan naji kin fita wani wajen nonsense ya furta tare da dungure min kai ya zuba min rankwashi kwasss....Ina kuka ban San Sanda nayi dariya ba yanda ya dungure min kai ne ya bani dariya,ganin Ina dariya ba karamin daure Masa Kai yayi ba yace Yar nan ba kalau take ba Rukiyya Zan kaita wata rana, Tsaki ya ja ya juya ya fice Ina cewa abincinka fa? Bai kulani ba na mike da sauri na Bude kofa har ya kai jikin mota nace Zan turo maka list din abinda muke bukata na kayan abinci,ko kallona baiyi ba ya shiga motarsa benz baka ya bar Estate din.

Sabreen Kuwa ganin bata ganni ba tasan na bar Mata gida sai Murna har da Kiran kawarta Jamcy ta fada Mata suna murna Jamcy tace Saura ke sai na hada Miki masifa a fili kuwa tace Ina tayaki murna kawata,Haka Sabreen ta sanarwa Mamanta na bar gidan Mama tace shege aka ce baya ji ai duk wani Namiji dole yaji tsoron matarsa yanzu dai ki rage shaye shayen nan dan Allah ki lallaba ki samu ciki kinji Sabreen Mama tayi Maganar da lallashi Sabreen tace an gama Mama.
Baffa ne ya samu Mamin Nawwar yake balbala Mata masifa ta ya Auta Nawaf zaizo na uku a ajinsu,tace yaro a ajinsu yazo na uku ai yayi kokari

Tsawa ya Mata ke dalla rufe min baki ke dai baki iya tarbiyya ba bakya nuna musu Abu yanda ya kamata kin jawo Ina asarar kudin tara ni ga me kudin banza, duk yaranki basu da kokari dakikai ne,Amma ai yaran amaryarka masu kokari ne tunda naga Haidar yazo na 10 amma ita nata kokari Suka Yi Nawa yazo na uku kazo kana min fada ita ka kyaleta har murna kake yi ni sabo da baka so na ka tsaneni,in Banda ma ka rainani da nuna banbanci mene Nawa a position na yaro ita Ummyn Haidar bata laifi a wajenka kullum nice sabo da yanzu na girma na tsufa ga matashiya wallahi kaji tsoron Allah hakkina sai ya kamaka kwanana ma da kake tauye min ka bata sai dai na dafa na Kai maka itace da kwanan Miji Allah sai ya saka min inyi girki wata katuwa da kwana da miji bazan yafe ba,Mari ya zabgawa Mami dai dai Sanda Nawwar ya shigo Marin nan me karfi sai da fuskar Mami ta tasa yatsunsa reras a kumatunta abinka da fara,Ido Nawwar ya runtse hannunsa ya nutsa a cikin sumarsa me yawa da santsi ya hangitsa,nan take idonsa ya canja kamanninsa Suka sauya ransa ya Matukar baci amma ba abinda ya Isa yayi dagowa yayi yace Baffa....ba ruwanka muryar Mami ta ratsa kunnuwansa,bai hakura ba yace amma...shut up ta furta cikin karaji Shuru yayi,Baffa Yana muzurai Yana wani cin magani ya bige babbar rigarsa tare da furta da kayi magana Mana, uwarku ko ba mahaukaciyar bace dabba ce bata da hankali Kuma Watarana idan bata taka a Sannu ba sai na tsinke ragowar igiyar rubbish ya sake bige babbar riga fat ya fice a fusashe,domin shi ba sai Mami taje bangarensa ba da Kansa yake zuwa yaci mutuncinta ya Kara gaba,Yana fita Ummyn Haidar ta cakare matar so kenan ta sa Kaya na gagara ta kwama glass dinta tayi kyau itama kyakyawa ce amma bata Kama kafar Mami ba a kyau,Baffa Murmushi ya saki ya karasa inda take tare da furta sorry my love I keep you waiting,tace ba komai ka dinga dan sassautawa Mamin Sultana kasanta ballagaza ce duk da bata da nutsuwa ka dinga binta a hankali har Sanda zaku rabu lafiya,yace ai ba karamin hakuri nake da ita ba,Hmm na sanka sarkin hakuri ne ka Kara akan Wanda kake da,yace Inshaallah ya rike hannunta tare da furta muje ki rakani meeting din nan ni ake jira ya rike hannunta Suka shiga rantsatsiyar motarsa driver ya ja suna baya.

Bangaren Mami Kuwa Samanta ta haura Kawai ta Shige bedroom dinta,Nawwar ya bi bayanta Idonsa yayi ja da gani kasan Yana cikin tashin hankali,Mami ya iske a tsaye ta juya baya hawaye Yana sintiri a kumatunta bakin cikinta yanda yake zaginta a gaban yayanta, Nawwar gabanta ya zagayo ya tsaya ya rungumeta kokari tayi irin na iyaye ta danne kukanta ta maida shi ta shanye abinta hawayen dake kumatunta yasa hannu ya goge Mata tas ta kalle shi Suka hada Ido tayi murmushin karfin hali,a hankali ya furta kiyi hakuri Mami ko ki muje ki koma gidana ki huta tare da su Sultana,ko kin tafi Kinga yace ko Ina Zaki ba ruwansa karki sake tambayarsa unguwa baki da amfani a wajensa yace idan ma sama Zaki tashi ki tashi,Ki taho mu koma ko Zaki samu sauki,Mami ta kalle shi tace da wata me hankali ka aura sai na koma amma Sabreen ce Nawwar sai ta karasani,yace to ga sauran gidajen nawa Mana ciki ki zabi Wanda yafi Miki,Mami tace na zabi gidan nan na can nesa inda ba mutane sosai is better amma kasan bazai bari na daukar Masa Yara ba ko Daya Kuma idan na barsu za a gallaza musu ne gwara na zauna kusa da Yara na sadaukar da farin cikina ga yarana duk tsiya gwara na bawa yarana tarbiyya da kaina idan na tafi ma hankalina Yana kansu,to idan sakin ki yayi fa sannan da yaran da su ya auro ki ba sai a bar Masa abinsa ba,no Nawwar uwa daban take ba irinku uba bane kayi hakuri Kawai Zan dai iya zuwa gidanka nayi sati biyu idan na huta sai na dawo,Yace Alright wancan gidan dai na wajen gari inda ba mutane? Mami ta daga Kai inda ba Wanda zai dameni,yace an gama gobe zan kaiki bari a zuba Masa Kaya wani part dinma ba a Gama ba ginawa akeyi na
sani Dan Albarka Allah ya muku Albarka,yace su Hamra suna school Kai Kawai Mami ta daga masa yace to yaje ya kawo Mata ruwa me sanyi yace Dan Sha ta karba ta sha sannan ya fita ya bar gidan yasan tana bukatar a barta ita daya, hankalinsa bai kwanta ba sai da ya Kira company na wata masu tsara gida a zuba furniture da komai na buka ko cokali baza ka nema ba,suka je Suka ga gida ya Fadi yanda yake son komai ya biya kudi washe gari da wuri aka hada komai da yace yanda ya dace na Yan gayu,abinci ma Mami baza tayi ba shi zaina kawo Mata Kawai hutawa zata yi ga gidan daf da bakin ruwa.

Tunda ya dakeni ya tafi bai dawo gidan ba sai kayan abinci Naga an kawo a mota an shigar da komai store na shirya kitchen Muna zaman mu da Baba kulu tana bani hakuri akan dukan da na Sha duk da bata San me nayi Masa ba,ranar girkinmu mukayi ban ganshi ba sai washe gari da rana 2pm Ina dakina a kwance Ina sauraron audio na novel Wanda S Zaria Tv ta karanta a YouTube channel a wayata sabo da na gaji da kallo,Sallamarsa naji a hankali cikin muryarsa me dadi,Fitowa nayi sanye nake cikin doguwar Riga kasancewar kaf kayana na gidan da ya Fara kaini ya Aiko min da su,Fitowa nayi a nutse ya Saba ganin Ina gaishe shi yau yaga na zauna a kujera nayi mirsisi yace baki iya gaisuwa ba,Ina yini nace Kawai na shiga harkata shi sai yanzu ma ya tuna ya zaneni,ya sake furta haka akeyi,banyi musu ba na durkusa nace ka yini lafiya tsaki ya ja ya zauna duk na ganshi wani iri ba yanda na Saba ganinsa ba,nace lafiya? ya furta me Kika gani

Nace na ganka kamar kana cikin damuwa ne,shi Kam yanda nake gane damuwarsa Yana birgeshi Kuma in tambaya,a fili yace ta ya Kika San a damuwa nake,ai ni Ina ganinka nasan idan ma kana good mood ko baka ciki,kitchen na shiga na tsiyayo Masa kunun ayar dana hada me shegen Dadi yayi sanyi na Mika Masa ya karba ba tare da ya kalleni ba,kayan jikinsa nake kallo kana shadda gani tsadar shaddar ta Isa wata fara, kafafu ya harde Yana karkada kafa Daya irin na masu izza da ji da kudi,tashi nayi na kawo Masa meat pie na nama da nayi yaci Kuwa sosai sabo da yunwa yake ji,nace ayi maka girki mun cinye Wanda na dafa,yace girki Zaki yiwa Mami...kafin ya rufe baki na mike tsaye Zan shiga kitchen yace to ki tsaya Mana kiji me za a dafa tukun da time din,nace me Zan dafa to Yi sauri ka fada min Mami guda ai dole kaga na mike, Murmushi yayi da bai shirya ba yace tuwon shinkafa danya miyar kubewa danya sai ki hada Mata wannan lemon da Kika bani na Sha yanzu nace to 5pm zanzo na dauka,sai tea da kayan kamshi nace ka dauka anyi angama ma, tashi yayi zai fita nace zanje siyo kubewa da kayan Miya bamu da ita yace okay ya fice,ba ko mayafi hulace Kawai a kaina sai Yar doguwar rigata me garen Hannu yellow a haka naje har kasuwa na dawo Ina Hanya Ina tafiya na kusa gida har Ina cewa Allah yasa bai ganni ba ya tafi,Kawai naji mota a bayana ana bina a hankali Ina juyawa naganshi da sauri yayi parking ya bude mota ya fito a fusace na kwashe da gudu dauke da ledata Ina gudu na fada gida na rufe gate din har da saka sakata,Tsaki ya ja ya shiga mota ya koma abinsa Yana huci har kasuwa konmayafi baby Haba.

Amarya Gaji Kuwa ana mota an shigo city cikin Kano tana baza Ido taga ya gidan, ta ga an wuce cikin unguwanni masu kyau sai da a kazo unguwa wata marar kyau ko Ina kwata sai doyi da wari gidajen unguwar duk talakawa ne sai me dama dama gaba Daya rubabbun gidaje ne,Gaji tuni gumi ya lullubeta Gaban wata katuwar kwata aka yi parking bakin wani gida me dama dama ko sabon paint babu Wanda zai nuna alamar gidan Amarya ne,Gaji kasa hakuri tayi tace wai ko karamin Gate babu? Jama'a ku tayani gani ko idona ne,Aunty Amarya Fuska murtuke tace da driver yaro nan ne Kuwa? Da masifa yace idan ba nan bane Zan kawo ku ne dan Allah ku fita Ina da wajen zuwa Kuma kafin na dawo ku tabbatar Kun Gama idan ba haka ba wallahi duk wacce bata fito ba sai dai ta kwana a gidan Amarya,Gaji Fitowa akayi da ita haka kowa jiki yayi sanyi amma Banda motar dattijai Kawai guda sukeyi suna murna su Kam,motoci Suka juya Suka barsu a kofar gida,

Aunty Amarya ce ta dakawa tsofaffi tsawa tace Kai dan Allah Kun damemu da guda,yo ayi Shuru Kamar gidan mutuwa ai Amarya sai da guda ayiririri Suka ci gaba da yi sai da Gaji ta dora hannaye a ka tare da kurma uban ihu a unguwar kowa yayi tsit Dangin Uwar gida Zayyanatu Suka fito da kawayenta makwafta ma Suka yo waje ana kallo,Yara Yan Mata har da maza sai da Suka zo sabo da ihun da Gaji take kurmawa hannaye ta daga sama sosai tace jama'a an munafunce mu anci amanar mu an yaudare mu an nuna Mana kudi wayyoooo....ta sake Dora hannaye a Kai Aunty Amarya ta rufewa Gaji baki ta jata sum sum tace ku muje ciki aka tafi,wata tsohuwa tace a tsaya Amarya tayi addua...kafin ta rufe baki Gaji tace baza ayi ba Ina wani Alkhairi anan,bana son zaman Lafiya Allah ya ruguza wannan aure Inshaallah bazan Yi sati biyu ba za a sake ni,Dangin Uwargida Suka saki shewa kwadayi mabudin wahala Yan Kauye anji kamshin birni,Aunty Amarya tace doyi dai wai ku nan har birni ne unguwa duk doyi talauci ya dinka Muku Riga da wando Ina kamshi a nan unguwa sai kace masai,Kawayen Zayyanatu Suka saki sowa, Zayyanatu ana daki Suka tafa da kawaye tace wlh sai ta bar gidan nan ko na haukatata,dama Zayyanatu irin masu bakin kishin nan ne Babu abinda baza su iya ba akan kishi.

Wata dattijuwa tace Ina Uwargida ta fito ga Amana mun kawo Mata, Zayyanatu ba mutunci ko Kara babu ta leko sabo da haukar kishi ya zautata tace ni Allah ya gani ma ko wacce irin Amana aka bani sai na ci,karku ce ban fada muku ba wallahi sai naci amanarta,Amanarku sai na kafa Mata hakora na yageta yo ni ai duk unguwar nan ku tambaya kuji bani da Amana,Kinyi Asara Kuwa cewar Aunty Amarya,Zayyanatu tace uwarki ce tayi asara tazo har Gaban Aunty Amarya taci kwalarta ta haukace kishi ya rufe Mata Ido,Aunty Amarya ma Yar ta kife ce ta kwashe Zayyanatu da Mari har biyu nan take Dangin Amarya dana uwar gida Suka yamutse ko wacce ta cafki daya Suka Fara bata Kashi, Amarya Gaji ta jefar da mayafi tare da ture Aunty Amarya tace bani ita itace dai dai dani kishiyita ce Gaji ta fyallar da mayafin amarci kasa tayi tafiyar ruwa da Uwargida zayyantu abinka da girman Kauye ga Gaji da mugun karfi taci kwalar Zayyantu ta makureta da bango sosai tasa kirijinta ta daki kirjin Zayyanatu tace kishi hauka ne Zan gwada miki na fiki hauka,gaba daya ganin Abin na Zayyanatu da Gaji yayi yawa kowa ya tsaya akayi cirko cirko ana kallonsu,Zayyanatu ta samu ta kifawa Gaji mari kafin ta dauke hannunta Gaji ta bata mari biyu ta shaketa a jikin bango tana wani shidewa sabo da bala'i idon Gaji har wani kakkafewa yakeyi Kamar me Aljanu ta juya ta hango kwalabar lemo 7up ta wawuro ta fasa a kasa tace me tsoron ta mutu shike rai Zan iya zuwa prison a kanki Dan kut.....Zayyantu taji wuta itama turmin daka ta dauka ta yo Kan gaji ta jefo Mata sai da ya samu Gaji a goshi kadan,goshin Gaji ya fashe, suna haka sai ga Dangin ango da ganinsu kaga talakawa futuk wata a ciki tace me Zan gani haka na shiga Uku kashe kanku zakuyi akan kishi,wannan tozarci da me yayi Kama wannan abin kunya da Danbinni ya jawo Mana da me yayi kama,Gaji huci Kawai take yi sai lokacin ta saki Zayyantu dake shake a hannunta,Zayya ta Fara shakar iska ta fashe da kukan munafunci,Wanda suke wajen abin ya faru sune Suka ce uwar gida itace da Laifi itace bata ja mutuncinta ba ai ko ba komai ko zaginta Suka Yi sai tayi hakuri ai ranar farko ce Amma har da marar musu dattijuwa Kuma basu kulata ba ta fito,

Wata a Dangin ango tace kinyi asara Zayya tunda akace za a Miki kishiya Kika haukace a kanki aka Fara kishiya,duk unguwa gulmarki akeyi akan Namiji irin Danbinni talaka uban me kike tsinta a wajensa sai ma wahala mahaukaciyar shashasha,Gaji tace a fada mata wallahi da nasan haka yake ma bazan aure shi ba,ta sani da saninta Ni bala'i ce da kanta Nice jarabar duniya maganin duk wani Dan Iska ko wa ya ja da Gaji sai yayi kasa,Gaji Kamar Yar daba har da cije baki tana nuna kanta tare da sake furtawa a fada mata bada Wasa nazo ba na shigo da kafar haggu tunda tace bala'i za ayi wallah ta taro bantan bala'i ta ta taro alkaba'i icen kabari ce ni,yanzu ba zaman Danbinni zanyi ba Zaman zayya zanyi mu zuba ni da ke, wallahi tunda Kika mari uwata sai na mari taki uwar Allah ya kawota gidan nan dan me dirkawa uwarki ciki,Dan me dafa miki abinci kina yarinya,Dan wacce take Miki tsarki kina karama sai na ci uban da ya haifi babarki,shegiya me idon fatalwa sai kin San wace Gaji,Zayya taga ruwan bala'i tsoro ne ya kamata sai kuka,Gaji tace baki Fara kuka ba bari tukunna naci burar mijinki tukun sai naji madarar mijinki ta ratsani Zaki San wace ni,Oh yau na shiga Uku ni Binta Danbinni ya hadawa Kansa bala'i,Aunty Amarya tace yawwa ki rama min Marina akan uwarta,Gaji tace for sure tana zaga gidan tana kallon kowa dai dai taga buta tayi ball da ita ta daki bango ruwa tul tul buta ta fashe,Da kyar aka kwantar da hankalin Gaji sabo da Gaji su ko me zasu Yi da sa hannun iyayensu suke yi Kuma ba a musu fada ko me Suka Yi dai dai ne,Rabi Yar tsuntuwa ce kawai me hankali Shuru Shuru me ladabi da biyayya saliha yanzu Kam basu sani ba asirin Dagaci da ya Mata ba ya sa taci uwarsu a hauka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login