Showing 39001 words to 42000 words out of 133505 words
ba gyara Kuma yasan farko ma haka ya ji ta,dannewa yayi kawai ya zaiyi da kaddara tunda ta same shi,badan Yana tsoron Allah ba da tuni ya fada neman Mata sosai, Yana wannan tunanin bacci ya dauke shi yau itama a jikinsa ta kwana bata Sha komai ba, sai da safe tana yin wanka ta tsarkake jikinta taje ta dafa zallan ruwan zafi empty ta zuba a cup ta hada Madara da Milo ta Sha tea dinta da bread da ragowar naman jiya,sai da ya fito Sunday ba aiki zai fita sanye cikin 3qrt da riga me gajeren Hannu marasa nauyi ne sosai,Wai a tunaninta ta bashi abinci tace ga ruwan zafi kazo ka hada tea in zaka Sha,ko kulata baiyi ba ya fice daga gidan,Yana fita tace kai kaga duhu tana gamawa ta maida kwanikan kitchen anci sa'a ta dan gyara gidan sama sama gashi nan dai ta koma dakinta ta Fara shaye shaye ta fada saman bed tana shakar hanci idonta nan take yayi jajir da shi Ido ta lumshe Kamar zata Yi bacci sai ga su Sultana kannen znawwar sun zo gidan su ukun,Sultana,Nasira da Hamra sallamar duniya gidan Shuru ba kowa,ita Kuwa ko motsi ta kasa tana jinsu sama sama har bacci ya kwashe ta,dakinta Sultana ta leka ta dawo tace Kai kuzo mu koma yau ma baccin asara take fa,baki suka tabe suna kallon gidan Suka fice driver ya maida su gida suna ta bawa Mami labarin gidan,Mami tace oh wannan yaro Yana hakuri Allah ya bashi mace ta gari an hadashi da kaddara Ni dama tun farko hadin nan bai min ba amma ba yanda zanyi sai hakuri.
Yau ni kuwa na gama karyawa na bar Masa nasa a dining na gyara ko Ina kwanciya a kujera da Niyyar hutawa bacci ya kwasheni har yazo ya karya a gidan ban sani ba baccina nake yi,bai tasheni ba ya fice ya tafi gidan abokinsa Khaleel,Yana zuwa ya sameshi zaune tare da matarsa da yaransa biyu,,matar Khaleel Sufia tace na Sabreen Ina kwana ya amsa Yana cewa ya kamata na Miki kyautar kirarin nan,dan Khaleel ya dauka yana Masa Wasa sannan ya ajiye shi Suka koma part din Khaleel suna palonsa,Khaleel yace Wai Dan Allah wace wacce na ganka da ita? Nasan abinda ya dameka kenan dan sa Ido labarin Rabi ya bawa Khaleel bai boye Masa ba,Khaleel yana gama ji yace haba Ina ganinta nasan ban santa ba, ba yar uwarku bace,Amma fa tana da kyau ba karya inda kasan itace tayi kanta,sai dai bata da kunya ashe karuwa ce Kuma bata yi kala da karuwan ba,ita Kuwa karuwancin bai nunata ba ashe Yar kwalta ce,amma Kai tunda harka bata yuwu ba Allah ya tsareka Ina ruwanka da ita ka rabu da ita Mana,Nawwar yace ni so nake ta daina ta koma gaban iyayenta,Yarinyar ta lalace da yawa yarinya karama tausayi ta bani so nake ta shiryu,dariya Khaleel ya dinga shekawa yace ko dai sonta kake Yi? Haba Khaleel amma baka kaunata wlh me zanyi da karuwa,Khaleel yace kaga Wanda ya kangare sai Allah shi yake shirya bawansa a Sanda yaso kaga tun bata jawo maka masifa ba iyayenka sun gano ka rabu da ita,kasan Baffanka baida hakuri tam Kai Ina Kai Ina Yar bariki,Nawwar yace tab ai ka fada a banza ma Sai ta shiryu Inshaallah gidana ma Zan kaita ta zauna a can sabo da gudun shedan Kar ya shiga tsakani,Ashe zaka hada yaki,ai a matsayin Yar aiki Zan kaita ko me na ce zata yi bata da matsala ita Indai zaka biyata kudi,Khaleel yace bana goyon baya wlh Kuma duk abinda ya faru Ka kuka da kanka,ae naji cewar Nawwar ya canja zancen ma don Kar Khaleel ya dame shi.
Haka naci gaba da Zama a gidan Nawwar Kamar wata matar aure na gaji ji na nake Kamar a kurkuku yau da yamma ya kwana biyu bai zo ba,sai na gudu daga gidan tare da kashe wayata tunda yanzu Yana da number ta Kar ma ya sameni na gaji yanci nake so,Saratu ta ganni katsam bayan Sallar Isha ta dinga min dariya,nace na gaji wlh bazan iya ba,Kinga bari nayi Sallar Isha mu fita yau Zan fita titi abina bazai hanani yanci ba,Sera tace har yau fa ke kina Sallah nace sosai ma,Ina yin Sallah na dakko wata sabuwar gown dita da kadan ta haura duwawu na saka na saka takalmi me tsini naci kwalliya tare da saka hular gashi wata sabuwa me kitson twisting Wanda tsayinsa ya wuce duwawu Muka gama shiryawa Muka fice titi inda muke tsaiwa, a daren Nawwar yazo gidan amma ya samu bana nan,Ilu ya tambaya Ina Rabiah fa? yace ai ta fita gaf da Sallar Isha,da fada yace me yasa baza ka fada min ba ka barta ta fice,ai ni ganin bata fita shi yasa kuma tace abu zata siyo a chemist,Tsaki ya ja ya shige mota hankalinsa tashe ya duba bai ganni ba direct gidanmu ya wuce na karuwai,motar yayi parking ya fito ransa a bace Kamar zaiyi duka ba kowa a gidan sai wani Dandaudu,yace Miracle fa tana gida? Dandaudu shewa yayi Yana tafa Hannu yace karuwai dama suna Zama da dare ne? Ehehe ai baka sani ba ai karuwai basa bacci da dare sun fita aiki zauna nan kana jira baza ka gansu ba sai da safe ai suna street nima yau hutawa nake shi yasa ka ganni a gida ni kaga nayi nan yayi tafiyarsa,Shuru yayi ya tsaya Kamar gunki sai da ya gaji ya shiga motarsa ya fito daga layi ya nufi inda yasan muna tsayawa,tun kafin ya karasa ya hangoni da tsinannun Kaya a tsaye, a gabanmu yayi parking ya bude mota ya fito,ina ganinsa haushi ya kamani na zumburo Masa baki.
Tsawa ya buga min Shiga mota muje,harara na watsa Masa Ina dire diren kafafu nace ni Allah bana so na gaji kamar Ina prison ni ko kudin ne bana so ka barni nayi rayuwata kaje kayi taka,mota nace ki Shiga ya furta Kamar zai dakeni sauran karuwan suna kallonmu baki bude, hannuna ya fisga ya jani na tirje ni ka kyaleni bazan je ba,Ina tirjewa harna zube a kasa Ina ta burburwa Ina Shure shure,Tsaki ya ja ya sakar min hannu,sai ya daukeni cak Ina wutsil wutsil ya bude gaban mota tare da jefa ni ciki ya rufe ya Shiga mota yaja muka wuce gidan dai da ya ajiyeni,Yana yin parking ya fito na fito Zan sake guduwa tsawa ya buga min na tsaya cak tare da juyowa yace come karasawa nayi gabansa Ina Kunkuni mari ya kwada min na dafe kumatuna da sauri na kalle shi cikin karaji yace Ina alkawarin da Kika min Zaki zauna? Mene a cikin karuwanci,karuwancin ma na titi ke bakya Jin kunya musulma dake hausa Fulani mene birgewa a karuwanci,bance Miki Zan biyaki kudi ba,har albashi na saka Miki duk wata,nace Zan maidaki school dan Kawai na inganta rayuwarki ba sonki nake yi ba karki Raina min hankali wallahi Kika sake barin gidan nan ba izinina sai Kinga abinda zan Miki useless girl baki San ciwon kanki ba kina yamace kalleki karuwanci bai dace dake ba,kuka zanyi Masa nace ai ni Kawai so nake nayi Ina so ne sai naji Ina son Karuwancin,shut up ya buga min tsawa shashasha wacce bata San darajar kanta ba wuce ciki,tsayawa nayi ya buga min tsawa shiga nace ya furta a tsawace, da gudu na fada ciki,Yana shigowa ya matso kusa dani ihun tsoro na saki na ja baya Kar ya dukeni, yace karki sake karki sake, kika sake zaki ga ba daidai ba yaja tsaki ya koma wajen me gadi yace idan ka sake barinta ta fita a bakin aikinka,Ilu yace Zan kiyaye, ciki ya koma Yana shiga yace tashi ki canja Kaya wannan yan iskan kayan sai na Kona su mijinki Kawai Zaki sakawa,tashi nayi Sadaf Sadaf na koma na canja silk material marar nauyi na fito,Ina Fitowa Kamar ba nice ya gama zazzagawa ba nace abinci fa a dafa,shi da Kansa a ransa yace bata da zuciya ya tabbata da wata ce ranar ko kulashi baza ta sake Yi ba ko matarsa ai sai suyi watanni tana gaba da shi,yace kin bani ne abincin,sum sum na Shiga kitchen na Masa jullof din taliya ta Sha kifi da kayan lambu, kawo Masa nayi har gabansa nayi serving dinsa Nima na zuba tawa Muna ci muna kallo,yace baza ki fada min wace ke ba I mean tarihinki,Ina cin abincina Ina bashi labarina komai ban boye Masa ba,yaji tausayina da yaji bani da kowa a duniya Yar tsuntuwa ce Ni,yace Kuma shine baza kiwa maraicinki gata ba ki Zama ta gari sai ki lalace,Shuru nayi Ina jinsa yana ta min fada ni dai bance komai ba, yace gobe ki shirya gidana Zan maidaki, kallonsa nayi nace matarka fa ni kasan bani da kunya Kar nayi abinda zata ji haushi in ta min ba kyaleta zanyi ba kasan halinmu,ai yar aiki Zaki zama aiki Zan daukeki tunda kince ke baza ki aure ba baza ki makaranta ba Mene amfaninki Kawai na kaiki can kiyi aiki ki gyara gida kiyi girki,nace yanzu Yar aiki zan koma haka gaskiya tace? Cutar dani zaka yi,ko baza ki abinda nace ba? Kamar zanyi kuka nace zanyi,Kuma kina kwalliya zata ce kwace Mata miji Zaki Yi ta Miki dukan tsiya,Nace wlh sai dai na daketa Kai kasan karfina kuwa hmm amma tunda kace nayi zanyi ai zaka biyani ko? Yace kudi ma Zan Kara miki, ihu na saki nace wane ni nace bazan Yi ba ai ya Zama dole,yace Good girl Kinga mun huta da tsoron shedan,ka huta dai Amma Ni kaina ai shedaniyace me zaman kanta na furta,yace to babu kyau dai kebewa mace da Namiji shi yasa Zan maidaki a matsayin Yar aiki sabo da dangina da iyayena da matata ce za a dameni amma idan a Yar Aiki Kika je sai kiyi zamanki a haka dama aikinki kenan aikin gida da girki,nace rashin yanci dai ya Kara tabbata a kaina ka bari sai jibi to na Kara hutawa,yace Allah ya kaimu.
Washe gari a gidan ya kwana Sai ga su Sera su bakwai sunzo gidan da kyar Suka gane gidan sabo da na taba fadawa Sera address,da masifa Suka shigo suna kwala min Kira, miracle...Miracle.. na fito Suka hauni da masifa Zaki tafi baza ki dinga fada Mana ba sai mu dinga tunanin saceki akayi,Nawwar ne shima ya fito a tsaya a gefena tare da harde hannayensa a kirjinsa, ni Kuwa nace yarinya ce ni da zan bata kunzo Kuna min ihu a gida,Nawwar sanye cikin kayan baccinsa Yana jinsu suna cewa Kai karfa ka rabamu da yarinya abin ya isheka haka,da sauri nace Sera zanyi diban albarka a nan wlh ki tsaya haka, Kar wacce ta zagi saurayina yarinya ce ni da zaku zo Kuna min ihu,wannan ba Kalar Yan iskanku bane ku Shiga hankalinku,Au haka Kika ce? Nace ae kuje gida idan na gaji zanzo ai Kun ganni kalau nake,Sabo da haushi juyawa sukayi Suka tafi suna masifa, suna tafiya ni Kuma na juya Muna facing juna Ilu dai tana kallo,nace karka damu dasu kayi hakuri ko me kake so zanyi Kai mutumin kirki ne,Shuru ya min na shafa gemunsa nace inya.... inya... inya....dariya yayi ba shiri nace muje ciki na ja hannunsa muka shige ciki,Muna shiga na rungume shi nace kayi hakuri kaji,jikinsa ya janye da sauri yace naji na hakura ki daina tabani nace fa bakya ji, kasan me na furta Ina gabansa a tsaye muna facing juna nace kana da kyau,idanuwa ya lumshe tare da furta ba kya ji,dariya nayi Ina kida baki na shima dariya abin ya bashi yace kin haukace maybe.
Yau ma da dare cewa nayi sai mun fita haka na dau wanka Muka fita wajen Shan ice cream Muka je nan ma ya kashe kudi,daga nan muka wuce wani wajen na shakatawa.
Sabreen ce ta Kira Jamcy tace har yanzu fa bai dawo ba dan Allah ki Dan duba wuraren shakatawa ko Zaki ganshi da wata,Jamcy tana Dariya a ranta tace to,yau dai ta shirya a motar mamanta ta fito tana bi duk wajen joint tana zuwa Wanda Nawwar muke Kawai ta hango shi tare dani mun fito da ledoji ga wani ice cream din a hannuna Ina Sha Muka shiga mota,Jamcy ta saki ashar tace cab Sabreen Kinga ta kanki amma sai ta bugawa Sabreen waya,tana dagawa tace kin ganshi Jamcy? Jamcy tace ke dalla banza kin cika zargi to na ganshi yanzu ma Yana ma unguwar taku Yana masallaci makarantar da magidanta ke daukan darasi Yana ciki karatu yake a can makarantar Malam maikudi, Sabreen tace dama nayi tunanin haka ai shi akwai addini,Jamcy tace ke dai bari tsaurin addininsa da tsoron Allah dinsa har tsoro yake bani kin ganshi rike da Fiqhu, Sabreen hankalinta ya kwanta abinta mijinta karatu yake dauka a masallaci.
Washe gari Kuwa Maminsa ya fadawa ya samo sabuwar Yar aiki me hankali,yaje ya fadawa Maman Sabreen,Mama tace ai Sabreen ta huta dama aikin ya Mata yawa har tausayi take bani Kamar ba me kudi take aure ba,itama Sabreen din yace Mata Maminsa ta samo Masa Yar aiki sabo da Kar ta zargi komai ma,tace sai ta zo tunda ita bauta ta zaba tazo tayi,ya kalleta yace dan Allah karki wulakantata ki zauna da ita lafiya,bata ce komai ba,ni kuwa tunda yace a yar aiki zai kaini gidansa sai na zabi wata Atamfa wacce ya dinka min dinkin ba wani na kuzo ku gani bane,na dauki wata atamfar sai Rigar material kayana kala biyu na hada da komai na bukata na zuba a jaka,makwaftanmu na shiga na samu wata me aikinsu budurwa na roketa akan ta bani kayanta kala uku ga sababbi nawa masu kyau,da gudu ta bani ta karbi nawa masu kyau ta bani wata kodaddiyar Atamfa Riga da zani dinkin kauye,sai wani tsohon leshi doguwar Riga da dankwali Wanda ake cewa disco tsoho,sai wata Atamfa ta ji jiki sosai Riga da katon skert marar fasali,sake wanke su nayi na goge washe gari ranar da zan koma can na shirya cikin rigar da zanin na tsohuwar atamfata sauran kala biyun Kuma na zuba a Leda Viva da sauran tarkacen bukata,dankwalin Disco na daura a kaina nan take na dinga yiwa kaina dariya irin watsewar kayan danma ni Fara da bazan ganu ba,Yana shigowa ya kalleni dariya ta kamashi yace gaskiya kina da kwakwalwa muje,na dauki ledar kayana Muka fita na Shiga gaban mota sai gidansa
A hanya sai dariya yake min wai yayi winning bai taba zaton zan yarda naje gidansa a Yar Aiki ba,bai san duk abinda yace zanyi ba bai san yanda nake ganin girmansa ba,juyowa yayi kadan ya kalleni Yana Murmushi yace a Ina Kika samo kayan nan? baki na turo gaba tare da dora kaina a kafadarsa sannan na furta a wajen wata Yar aiki a makwaftanmu na bata masu kyau cikin nawa,Okay ya furta banda fitina da fada a gidana Kawai kiyi aikinki Zan biyaki ko nawa ne,yanzu nawa ma zan baki? kallonsa nayi lokacin ya juyo Muka hada Ido nace kana tunanin kudinka zasu sa na Zama yar aiki a gidanka? Karuwa ce ni fa kasan abinda muke siyarwa mu samu kudi wlh badan kudinka na yarda ba Kawai Ina ganin girmanka ne Ina Jin kunyarka Ina girmamaka shi yasa,Murmushi ya saki tare da furta a haka kina Jin kunyata Hannu na tafa Ina Dariya nace kasan Kuwa nifa ba karamar cikakkiyar Yar duniya bace,Yar duniya ce ni ta gaske ai nan daka ganni na Kama mutunci na ne ba karamin hakuri nake Yi ba,Allah? ya tambaya nace hmm yanda nake jina ko Namiji Zan iya Masa fyade,dariya yake sosai yace ya baki min ba ni? ai da kin sani kin min,karka cika baki Zan baka kunya a gaban matarka,karki Fara ya furta zamu bata bana so,daga min kafada,kafada ta na noke Wai naki,kyaleni yayi har Muka je katafaren gidansa na aure,sai Naga duk haduwar guess house dinsa da nake ciki ashe ba gida bane Yar Kauye na dawo sabo da tsabar tsaruwar gidan,Fitowa nayi da kayana a leda yace behave yourself,na nutsu tare da sadda kaina kasa Ina Wasa da yatsu na,dariya ce ta kule shi yau farin ciki ya isheshi yayi winning,Fuska na shagwabe,tun daga kofa Muka ji kida na tashi a hankali na furta zanyi loosing control rawa na kirana,yace dan Allah karki yi Yana rokata,nace wannan shine gidan Zama ai nan yafi mim dadi Matukar da wannan kida haka ai akwai nishadi,ciki Muka shiga Yana gaba Ina baya,Kannensa ne Ashe a gidan Suka kunna kida suna ta rawa gidan Suka zo Suka gyara ko Ina har dakinsa,Matar gidan Sabreen sanye take cikin kana nan Kaya tana zaune tana wani bata rai kannen Miji sun Zo Mata gida,suna ganinsa Suka kashe kidan tare da zuwa suka rungume shi dukansu suna Yaya Oyoyo tun dazu muke jiranka.
Yace sannunku Hamra ce idonta ya Kai kaina Dana shigo Ina tafiya salo salo ta furta wow kaga wata me kyau Suka juyo gaba daya yace me aikin da aka samo min ne sunanta Rabi,Suka ce Masha Allah suna cewa ai gwara daka samo Yar aikin, Sabreen sai lokacin ta juyo ta min wani kallon wulakanci da kaskanci tare da cewa baki iya gaisuwa bane ko ba a koya Miki ba a gidanku,nan take raina ya baci na harzuka Nawwar ya girgiza min kai,labbana na cije na daure nace Ina kwana tace yanzu ne kwanan Kuma haka ake gaida masu gida,Please karki fara bana so kina takurawa Yan aikina dukkansu Yan Adam ne kamarki,tashi Sabreen tayi ta wuce abinta,Raina a mugun bace Sultana tace kiyi hakuri Zama da ita sai hakuri muje na nuna Miki dakinki, yace bafa bangaren masu aiki Zaki kaita ba a nan zata zauna ga room a kasa wancan ki kaita can,Sultana ta kaini hadadden daki ne harda nuna min yanda ake amfani da toilet din ta fito dani