Showing 93001 words to 96000 words out of 133505 words

Chapter 32 - Yar Aikin Karuwai Book 1

22 Oct 2024

3894

lemo ta zauna itama tace ke lafiya Miracle kike kuka haka,a nutse na basu labarin komai karshe nace ni bana so mijina ya sakeni shi yasa na gudo,Wise tace tab wannan bazai wuce aikin kishiya ba idan itace ma zata Yi bayani da kanta ta tabo bala'i ta jawa kanta,Star ta furta yanzu bai baki takarda ba baza ki zauna a nan ba duk tsiya aure Yana da daraja ga mu da muke kaunarki da gaskiya tashi mu tafi na kaiki gidan wata kawata ce, babbar mace ce Bata da aure mijinta ya mutu ya bar Mata dukiya na taba taimaka Mata lokacin da motarta ta samu matsala a daji Hanya zata je arewa shine dalilin haduwar mu tayi tayi na daina karuwanci na koma gidanta zata rike ni naki yarda muje can ki zauna ko Nawwar yazo mu Kuma zamu ce baki zo nan ba gudun Kar ma ya ganki ya sakeki,dariya Sera tayi tace wato Miracle kice gudun saki ne ya fito dake tun kafin ya dankara miki saki? Nace ae Suka kwashe da dariya,nace ba Maganar Wasa bace wannan tam Ina zumbura baki,Sera tace ga abinci nan yanzu na dafa sai ki ci ki tashi ku tafi, dama yunwa nake ji naci na koshi Muka fito ni,Sera,wise da Star muka tafi can wajen Matar me suna Hajiya Abida, Muna zuwa ta karbe mu da murna gida ne hadadde me kyau da motocinta biyu tana da Yara uku duk suna Arewa Bauchi a nan suke makaranta sabo da su samu tarbiyya ta addinin musulunci,gata da Yar aikinta mace daya,sai Namiji a bakin gate shi ke Mata wanki da guga da kula da gidan,gida ya Sha flowers da furniture masu kyau.

Muna zuwa ta karrama mu sosai aka kawo Mana kayan motsa baki,sai da Muka danyi hira da ita sannan Star tace Hajiya Yar uwata na kawo miki ajiya tana da aure sai ta fadawa Hajiya abinda ya faru dani a gidan Nawwar,Hajiya Abida ta tausaya tace bazai wuce sharrin kishiya ba so take a koreta Kuma ta Allah ba tata ba,da sauri na furta Inshaallah Ina nan da mijina mutu ka raba,na kalli Hajiya nace Ina son mijina sosai da ban damu da auren ba amma zuwana Makkah Allah ya amsa Addua ta yanzu bana sha'awar bariki ko kadan mijina da aurena sune a gabana,tallan duwawu na gama Inshaallah,Hajiya Abida tayi dariya ita kunya ma muke bata sabo da magana direct muke fada ba wani sakayawa,a nan gidan su Star suka barni, Suka koma gida Suka tattara mutanen gidan Wanda ake mutunci su Yar Zabil duk dai wanda suka je bikina suka zauna sama katuwar tabarma guda biyu da alawoyi da yawa a leda suna zaune sunfi mutum ashirin,Santana yace dan Allah wai Kun taramu kunce akwai magana Yar uwarmu Miracle tana da matsala a gidan miji,Madula tace to me za muyi Mata itace ta Kai kanta in Banda Addua me zamuyi Mata,Seraline tace yawwa duk da mun San mu masu laifine a wajen Allah amma Addua itace zamu hadu muyi shi yasa na tara mu,wata me suna Destiny tare da Peace Wanda su arna ne dama Suka ce muma zamu Yi Mata irin tamu oya a fara.

Seraline tace ni shugaba da na tara wannan taro zan Fara,Salati goma ga annabi,Mandula tace ya ma akeyi ku dan tuna min,Allahuma salli ala muhammadun wasallim na Fadi dai dai ko? Yar Zabil tace to Allah ya amsa hakane tana wani fari da Ido tana karairaya,Santana yace karami ne a salatin akwai na Ibrahimiyya shine darrr amma wannan yafi sauki Suka karanta,Seraline ta sake cewa suratul bakara kafa uku uku,Allah ya daidaita Miracle da mijinta Nawwar su dawo su jone su manne Kamar da,Allah ka duba kawar mu Miracle Kar ka bari Aurenta ya mutu Allah karka bari Nawwar ya saketa,ko wace ta hada Mata wannan tuggu Allanmu kayi fata fata da koma waye kayi raga raga da ko waye,kasa gobara ta kone dakin ko waye,Idan Sabreen ce Allah kasa duwawunta yayi tsutsa,su Kuma sauran suna cewa Ameen Seraline ta furta fatiha ta shafa tace wata tayi Mana itama,kowa a ciki yayi Miki Miki suna kallon kallo duk sun manta ma adinnin nasu sai sunyi tunanin yanda ake yi.

Wise ta daga hannu sama tace Suratul Tauba kafa daya,ba Wanda ya iya har ita me fadar,Suratul bakara ma ko aya daya ba wacce ta iya fada bare Tauba,ai Kuwa bata jira ba itama taci gaba ta daga Kai sama da hannaye tace Ya Allah mun San mu masu laifi ne kullum sai munyi maka laifi ita kanta Miracle babu irin laifin da bata maka ba ta bada gabanta da baya duk har center an daki harka da ita yanzu ta tuba tayi aure tana son mijinta tana son aurenta,Ya Allah Muma gamu dai Muna ta siyar da local government dinmu masu laifi ne mu ya Allah ta Kara kwalawa da karfi ya Allah duk Dan iskan cikinmu Wanda baya ji Allah kayi daga daga damu...kowa baki ya bude yana kallon Wise tana jawo musu masifa duk cikin addua,Santana yace ke rufani ki sayani ke Wise min Shiga Uku,wise da taci gaba tace tunda munki ji gamu ya Allah kayi maganinmu Allah karka kalli laifinmu ka yafewa miracle ka yafe Mana karka bari Nawwar ya sake ka barta da mijinta ya Allah karshe tace Fatiha Alhmdllh an karba Addua ta karbu,Star ce itama ta daga hannu sama ana cewa Ameen tace Ya Allah Suka hada baki tare da furta Ameen,ta sake Furta Allanmu Suka ce Ameen wannan haka yake Allah ga bayinka,Star tace Allah Nawwar,Nawwar,Nawwar mijin Miracle zai saketa ya Allah karka bashi dama,Ya Allah ka sa Masa tausayin miracle da kaunarta Allah karka bashi damar sakin Yar uwar mu,Miracle tana son bawanka Allah karka bari a saketa kasa ya nemi matarsa miracle ta koma gidanta Allah kasa tana komawa ya Mata ciki ta haifo Yan biyu,Ameen Suka hada baki.

Madula ce ta karbe Adduar da furta istingifari kafa dari,kowa ya Fara Astagafurillah har kafa dari dari Suka Yi abinsu sannan bata rokawa Rabin komai ba ta shafa tace Ameen,Santana ya karbe Yana cewa Allah ka daga gidan Nawwar kayi sama da shi ka kife shi a kasa ka hada da Sabreen din a juya kanta kasa a cake ta karairaye Allah karka kashe ta a barta ko Ina a karairaye shike nan ya Allah Suka furta Ameen,Manduwa tace Allah kasa mota ta kade Sabreen tayi Mata markaden kayan Miya a kwalta,Yar Zabil ta saki wakar kasida ta yabon manzo suna amsawa tayi baiti Daya suka Shafa da Ameen..Daya bayan daya kowa da Kalar adduar sa,Peace christain itace ta karba ta Fara wakar church sannan tace Papa God tana wani fari tace Jesus abeg ka taimaki Miracle mijinta ya maidata gidanta,we are all sinners kullum sai munyi zunubi Papa God ka taimaki Yar uwar mu Suka hada baki da Ameen,Peace ma wakar church tayi ta yabi Jesus sosai sannan tace Ameen a haka sai da kowa yayi adduarsa ya Gama sannan Sera ta bude Alawa chocolate me shegen dadi Suka rabawa junansu ko wacce guda biyar biyar Suka bare suna ta sha Wai Sadaka ce maganin masifa ,Suna haka Saurayin Seraline ya buga Mata waya yace ya dawo gari daga Dubai tazo zata Taya shi kwana daga nan ta kwashi kayanta sai hotel dinsa,Suma sauran haka duk sunyi Shirin tafiya aikinsu kamar ba sune Suka Gama Addua yanzu ba.

Nawwar bai San na bar gidan bama,Bai neme ni ba gudun Kar ya yanke hukunci cikin fushi,kwana daya Shuru bai ga ko gilmawata Sabreen ma tayi mamaki bata ganni ba tace ko ya sakeni ne sai da ta duba ko Ina na gidan bana nan wani farin ciki ya kamata burinta ya cika tunda bata ganni ba tasan ma ya sakeni,Nan take ta Kira Jamcy tana bata labari tace ke aiki ya Kare ma mu kwanta mu huta ya saki shegiya,Jamcy a ranta tace Saura ke dan ubanki duk ku fita ku bani waje a gidan sannan na samu damar shigowa gidan.
Wasa Wasa har kwana uku Nawwar bai ji ko motsi na ba,kasa daurewa yayi ya nufi dakina ya duba wayam,ko Ina sai da ya duba babu ni, wajen masu gadi yazo ya tambaya Suka ce oga ai tayi kwana uku da Muka ganta da akwati tana kuka ta bar gidan nan,hankalinsa tashi yayi yace to ni me nace Mata nayi magana ne da zata bar gida ya ja tsaki yace idan ta gaji ta dawo ya koma ciki amma me tunaninta sai ya hanashi sakat in banda Rabia babu abinda yake tunawa yace idan ta koma gidan jiya fa tsaki ya ja tare da furta to ni mene abin damuwa da ita tunda nasan ba sonta nake ba,ni kuwa har na Saba da Hajiya Abida Muna zaman mu girki ma tare da ni da Yar aiki muke yi na bata labarin ni Yar tsuntuwa ce taji tausayina, kullum Nawwar Yana raina in Banda tunaninsa bani da aikin yi,Ina tuna rayuwar mu tare da duk wani moment da muka Yi spending tare,yanda yake nuna min kulawa,yau ma bayan na gama komai dama wayata na kasheta gaba daya tunda na bar gidansa ban sake kunnawa ba,a saman bed dina nake kwance Ina tunaninsa ban San Sanda na Fara hawaye ba,a haka Hajiya Abida ta sameni,ta zauna ta taba kafata dan ban San ta shigo ba,a firgice na motsa na ganta,hawayena na goge a hankali,tace Rabiah yaushe Zaki daina kuka hakuri shi zakiyi Inshaallah zai neme ki,murmushin yake nayi har hakorin makana na Gold ya bayyana a hankali nace kina gani kwana na Uku su Sera sunce bai je Nema na ba Kinga Kawai ya kyaleni nayi rayuwata ya manta dani,Yana da Mata ba abinda ya dame shi dani, dama ba so na yake ba nice nake sonsa na rushe da kuka sosai,Hajiya Abida babu irin lallashin da bata min ba amma naki Shuru sai kyaleni tayi ta tafi.

Nawwar kwanansa bakwai bacci sai barawo ya kwashe shi ala dole,a daddafe ya kwashe sati sati duk ya rame sabo da tunanina, Kuma ko Mami bata sani ba a wajen su Iyamami taji ya saki amarya su ma Sabreen ce ta basu labari sai Murna suke suna jifan Mami da babake maganganu har ta gaji yau Nawwar yazo da Yamma ta kalleshi Yana cin abinci tace Nawwar lafiya kuwa? Me Kika gani Mami? hmm tace a baya naga tunda kake tare da Rabiah baka cin abincina amma yanzu kullum anan kake cin abinci safe rana da dare,sannan baka da nutsuwa duk ka rame na rasa gane Kan abin sannan naji wajen su Iyamami suna min dariya Wai ka saki Rabia ta kawo kwarto gida,murmushin yake yayi yace ba haka bane Mami Kawai dan fada Muka Yi bata Jin maganata shine fa na Mata fada sai tayi yaji ta tafi ni Kuma banje na dawo da ita ba,Mami tace Kana da hankali Kuwa Nawwar ya zaka bar matarka ta tafi Kuma baka je ba,kuma kasan bata da kowa sai Yan duniya bariki dai zata koma tunda can ne gidan nasu,ashe karya kakeyi ba taimakon nata zaka Yi ba,Mami ita fa tayi tafiyarta,Nawwar baka da hankali gashi nan ka damu kana son Yarinyar nan kaki ganewa ne Kawai,Allah ya kiyaye ya furta, ni bana sonta Kuma bazan so ta ba ni na gaji ma bazan iya taimakon ba na fasa Kawai a bar zancen,Murmushi Mami tayi tace wai me tayi maka ne? yace ba sai kinji ba,tace to ai duk so ne gashi nan baka so aji laifinta Kar wani yayi tunanin wani abu a kanta anyway yanda ka gani koma mene Watarana zaka fada min ni dai na baka shawara ba dai dai bane baka saki matarka ba ka barta ta koma bariki ba Allah zai tambayeka.

Shuru yayi ma Mami Yana cin abinci Yana tsaki har ya gama ya tashi ya fice ya bar gidan,layinmu na bariki ya nufa Yana zuwa ya samu Sera a waje,taje Suka gaisa tace Ina kawata? Kansa ya daure yace wacce kawar taki bayan satinta guda da yin yaji Kuma nasan nan zata zo,Sera tace bata zo ba gaskiya to Ina Kuwa Rabia zata tafi bata sanar min ba,Nawwar ya zaro Ido yace Wai da gaske kike ba nan tazo ba idan Wasa kike ma kin San dai bana Wasa dake, Sera tace tab ai kuwa ita tasan inda ta tafi bata nan gidan wlh,Nawwar yaga fa da gaske ne hankalinsa ya tashi matuka,yace kira Inna kiji ko can ta tafi,Inna aka kira tace bata je ba ko kauyen ma ba Wanda yaga Rabi a can,Nawwar ya rasa inda zai saka Kansa gashi an wuce sati Ina zai neme ta,haka ya koma gida jiki a sabule,Sabreen tana Shan kallonsa sai Dadi take ji burinta ya cika ga mijinta baya cikin farin ciki, Addua da sallar dare ya Fara ba ji ba gani,har aka sake kwashe sati shi kadai ya fara hawaye shi matarsa yake so,a Daren ya tafi wajen Mami sai ganinshi tayi duk ya fada Yana zuwa har da kwalla Ya shiga bawa Mami labarin komai da ya faru tsakaninsu karshe yace Ina ji a jikina akwai wani Abu a kasa gaskiya Rabia baza tayi haka ba shi yasa ban dauki mataki ba ita Kuma Kawai sai tayi tafiyarta ya karasa da marairaicewa yanzu Mami ya zanyi wallahi karya nakeyi Ina sonta ban taba son wata ba Kamar ta kawai na kasa yarda da ita ne ganin a inda na dakko ta farko,Mami dariya tayi sosai tace tun ba ayi nisa ba ka fadi gaskiya,Nawwar yace Mami kina dariya Allah ni Ina sonta bazan iya rayuwa ba sai da ita,Mami ta zuba Masa Ido tare da furta Nawwar In love Rabia ta ciri tuta,yanzu mafita daya kaje ka lallaba kawayenta zai wahala Basu san inda take ba,Mami kije wajensu zasu fi Jin maganarki please,ka bani number Sera din Kawai yace bani da ita,tace to bari na shirya muje da Kai yaji wani sanyi a ransa.

Ni Kuwa zuwansa na farko Sera ta Kirani a Wayar Hajiya Abida ta fada min na dinga murna Ina murna farin ciki nake ji marar misaltuwa amma Jin Shuru bai koma ba naji na koma gidan jiya,Bayan Mami ta shirya har layin Suka je yaci sa'a ya hadu da Star, Bayan sun gaisa ta gaida Mami wacce ta fito ta jingina a jikin motar tana kallon barikin da yanayin mutanen Dake wajen,tace lallai wannan bariki ce ta kirki,Star ai Sera ta samu tace dan Allah kizo mijin Miracle sun zo da Maminsa,wlh tausayinsa nake ji naga Kamar shima ya rame irin Miracle mu hadasu Kawai ko dan halin da Miracle ke ciki,Seraline Fitowa tayi Suka zo wajen Mami bayan sun gaisa Mami tace dan Allah Saratu idan Kun San inda Rabia take ku fada mana kunga harka ce ta aure ba abin Wasa bane please,Star ce tace mun sani amma mufa gaskiya baza a dinga dukar Mana Yar uwa ba,miji ya dinga dukanta yana Mata wulakanci sabo da bata da gata ya sameta a bariki a bagas shike nan da me zata ji da kishiya ko da su Dagaci ko kuwa da halin Dangin miji zata ji ga kuma uwa uba miji haka Kawai wlh baza mu yarda ba idan ba a sonta a kyaleta mu Muna son a barmu, Nawwar ya harari Sera sai da tayi dariya ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa Kika ce baki sani ba,Sera tace tuba nake amma Kar a sake taba mana Yar uwa Suka shiga bayan mota har gidan Hajiya Abida mace me Kamala da mutunci,yayi farin ciki ganin ba a bariki ta zauna ba yaji wani Karin kaunarta a ransa,Suna shiga Haj Abida ta fito Suka gaisa shima Yana palon,tace shine mijin Rabia akace ae,tace Kai mashaallah tayi dace bari na kirawota tana dakinta,tana Shiga ta samu Ina bacci,Fitowa tayi tace ai bacci takeyi,Nawwar yace bari na ganta ya mike tare da shiga dakin Kawai kayana ya harhada a kwati ya fito da su ya saka a mota ya dawo har inda nake kwance ya daukeni Kamar jaririya ya kaini gaban mota ya ajiyeni,Sera tace su a nan zasu yini gidan Hajiya Abida,Mami tace wato mace tafi uwa ni sai dai na zauna a gidan baya tana dariya ta shiga ta zauna Ina ta baccina sanye nake cikin doguwar Riga marar nauyi ta yadi me santsi kaina da hula a Kai me kyau,Mami ya sauke a bakin gate tare da cewa thanks sai nazo,ciki ta shiga tana Masa tsiya,Yana Hawa titi Kamar Zan farka Kuma ban farka ba sabo da na tara bacci Kuma ni Ina da nauyin bacci sosai, a hankali yake tafiya gudun Kar na tashi

A hankali na bude idona bacci bai sakeni ba gefena na kalla na hango Nawwar Kamar a mafarki na zaci mafarki nakeyi idona na murza sosai naga dai ba bacci nake Yi ba a hankali na furta Ina yini,Tsaki ya ja ya kalleni Kawai tare da maida Kansa ga tukinsa,nace baka sakeni ba dama? Kafadarsa na dafa nace Wai Kaine Nawwar ba mafarki nake Yi ba? Shuru bai kulani ba,na sake cewa Wai kaina so nane da yawa haka baka Fushi da ni,Nawwar ne kuwa? Fuskarsa na leka tare da furta Nawwaru...Muka dinga Addua a kanka rabona da nayi Addua tun a Makkah sai da na bar gidanka,su Seraline Suka dinga taruwa irin yanda ake adduar rokon ruwa suna ta Mana Addua zo kaga yanda fuskar mu ke kyallin musulunci sabo da tsabar Addua wani haske goshin mu yayi na musulunci su Seraline Suka Yi wani hasken musulunci adduar da Suka min kaiiiiii gaskiya munyi addini Addua Kamar ba gobe kalli yanda nayi wata Kamala sai fa da na Zama wata Yar kwarya kwaryar waliyya gaskiya na Sha Addua ji nake wani fresh sabo da tsoron Allah

Dariya yayi a ransa Wai a

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login