Showing 24001 words to 27000 words out of 117873 words

Chapter 9 - Masarautar Mu 1 to 4 Complete

na kasar.
Tuni sun manta daga gidan sarauta suka fito, sun karbi rayuwar gidan Amb. Hassan wanda bazaka taba sanin ba shi ya haife su ba. Rayuwar kasar Amstedam ta karbe su sosai, sun tara arziki nasu na kansu, ga aiki ga muhalli ga ababen hawa. Amma duk da haka a gidan Amb. Suke zaune.
Tun barin sa gida sai a shekarar baya ne maimartaba da Ya Gumsu suka kai masa ziyara, bisa tsananin rokon Amb. Hassan don maimartaba yace shi har abada Sageer bazai dawo masa gida ba, ya barwa Amb. Hassan shi duniya da lahira sabida gamsuwa da irin rikon da yake musu shi da Awaisu, shi kansa Waziri bai taba bada shawarar su dawo gida ba.
Sai kuma ga abinda Ya Gumsu ta zo da shi yau, na nema masa alfarmar zuwa gida yayi ko sati daya ne.
Ya sake lumshe idon sa ya bude a hankali. A fili ya furta "nima ina kewar ka Muhammad Sageer, tsoron abinda zai je ya zo nake. Ina tattalin mutuncin ka a idon al'ummarka. Duk da Baban ka ya tabbatar min baka da matsala yanzu".
****
A shawarar da suka yi da Waziri ya karfafe shi akan ya bar Yarima ya zo gida, koda sati dayan ne, tunda dai bazai dawwama a kasar da ba tasa ba, dole watarana zai zo gida, sannan Amb. Hassan ya tabbatar musu komai lafiya a tareda Yarima. Awaisu ne dai da yafi kowa kusanci da shi ya ce da Babansa Waziri da saura. Wazirin kuma bai gayawa sarki hakan ba don ya samu nutsuwar barin dan sa ya shiga cikin 'yan uwan sa ko yaya ne. A gefe ya saka limamin Askira da sauran malaman fada yin addu'a ta musamman akan zuwan Yarima Sageer, Allah ya kintsawa mahafin sa shi a matsayin sa na magajin sa.
Da wannan sarki ya yiwa Yarima umarnin zuwa gida don yayi sati daya. A wannan lokacin Amb. Hassan ya gama tenure dinsa na aikin jakadanci yana shirin dawowa gida gabadaya, don haka tare suka soma shirin tahowa shi da 'ya'yan nasa Sageer da Awaisu, inda Amb. Hassan zai sauka a kasar shi ta haihuwa Kanon Dabo, kafun ya koma Birnin Tarayya da zama.
*****
"Na ga sai wani zumudi kake zaka je gida, kamar wani special abu ne zamu je mu taras banda zafin Maiduguri, ni banda Ya Gumsu ta dage sai naje ai har abada na bar Askira kenan, tunda Alanguburo baya son gani na".
Awaisu yayi murmushi yana ninke kayan Yarima yana jera masa cikin tsadaddiyar trolley din sa. Bai yi niyyar bashi amsa ba sai da ya ji Yarima ya sake yin kwafa, "ni ko satin ma bazan cika ba zan dawo, ka san nextweek akwai birthday din da na hadawa (Rose), kawai sai jin zancen tafiyar nan na yi, da na san da ita da tun satin da ya wuce mun yi mun gama, she will be 26 by next week". (Rose, yarinyar Yarima ce da yake ji da ita, 'yar asalin kasar Korea ta kudu), Awaisu ya tamke fuska kamar bai ji shi ba, ya cigaba da jera masa kaya. Daga baya kuma ya ce "ayya! Ai kawai ka tafi da ita Askira ka hada mata birthday din acan zai fi bada ma'ana" Yarima yayi miskilin murmushin sa, ya ce "me kake ci na baka na zuba? Ka zuba ido zuwa shekaru biyu zan kaita Askiran ne, amma a matsayin matata ba budurwa ta ba".
Awaisu ya dauka ya fada ne kawai don ya ji dadin bakin sa, ya manta da wani hali na Yarima Sageer Yusuf Askira, duk abinda ya furta yana nufin sa ne har zuciyar sa. Amma akan zancen Rose bayahudiya bai taba kawowa Yarima da gaske aurenta yake da niyyar yi ba.

A halayen Yarima in ka dauke son matan sa, sauran duka ababen sha'awa ne, Awaisu ba zai daina kiran sa (his role model) ba. Mutum ne mai muhimmanta sallah da kiyaye lokutanta, mai kirki mai kyauta, abun hannun sa bai taba rufe mai ido ba. Ga jin kan na kasa da shi, ga girmama iyaye, sannan ga kokari wajen neman na kai kamar ba dan sarki ba.
Bayan kamfanin da yake yiwa aiki yana kasuwancin automobile daga Amurka zuwa Amsterdam. Duk da haka maimartaba bai taba fasa turo masa kudi duk karshen wata ba, shi Awaisun shine akan komai na kasuwancin nasa kuma kyautatawar da Yarima yake masa a ciki sai ka rantse su biyu suka mallaki jarin kasuwancin.
Babban abunda ke burge Awaisu a halayen Yarima Sageer shine submissiveness, ya san shi mai laifi ne a gurin Ubangiji, amma yana yawan ce da Awaisu ya kasa dainawa, kuma yana so ya daina din, mata sun zame masa barin rayuwa da baya iya rayuwa daidai sai tare da su, don haka kullum cikin istigfari yake yana fadin yana rokon Allah yasa kada ya mutu yana aikata laifin da yake aikatawa.
Ko Awaisu ya soma wa'azi, baya arguing da shi, cewa ya ke ya sani babu kyau ya taya shi addu'a. Sai Awaisu ya koma yi masa yakin karkashin kasa, don kuwa yarima tausayi yake bashi, kana sabo ka san kana yi amma ka ce ba zaka iya dainawa ba, duk yarinyar da ya gani tare da shi zai bi ta bayan idon sa ya ci mutuncin ta ya razanata akan tarayya da Sageer, wani zubin har ya ce Sageer nada cuta, ga turawa da shegen tsoro, saidai Sageer ya nemi yarinyar sa sama ko kasa ya rasa, a karshe saidai ya nemo wata, shi kuma Awaisu baya gajiya da lalatawa, kamar yadda shima baya gajiya da sake nemowa.
Wannan itace rayuwar Yarima Sageer da dan uwan sa Awaisu a kasar Amsterdam. Tamkar ciki daya suka fito, sha'awar su akan komai daya ce ra'ayin su daya, sannan zuciyar su tsayayya ce akan junan su, saidai hali kowa nasa daban.
Jirgin su ya sauka a filin jirgin saman Maiduguri da asubahin safiyar Litinin, zaratan matasan suka soma saukowa daga matattakalar jirgin 'AZMAN' cikin shiga ta barebarin usli, wadanda fatar jikin su ta jiku da boko da kasar sanyi, kai da ganin su ka san sun fito ne daga sarauta ta ainahi ko daga irin takun su da kasaitar su.
Suna sauka motar 'Askira Emirate' na jiran su. Tun a Abuja suka rabu da Amb. Hassan da Mama Laila wadanda suka hau jirgin Kano, su kuma suka hawo na Maiduguri.
Dogarawa bila- adadin duk daga motocin masarautar Askira, suka bude musu kofar motar BMW wadda maimartaba kadai ke hawan ta a gidan. Daga nan basu bata lokaci ba suka kama hanyar Askira da motar civilian mai dauke da wasu fadawan cike fal a cikin ta.

Yau tun safe masarautar Askira ta tashi da bushe-bushen algaita da kalankuwa da goge irin na masarautar, baka jin komai sai tashin kirarin gidan sarautar Askira, maroka da makada daga kowane bangare na garin sun barko sun cika kofar fada, haka tun jiya 'ya'yan sarki maza da mata na nesa dana kusa sun hallara a gida dakunan iyayen su mata ba don komai ba sai don marabtar Yarima Sageer wanda ya kwashe shekaru goma baya cikin masarautar gabadaya. Mairam Murjanatu ce kawai bata samu halarta ba saboda ta yi nisa tana kasar Turkiya.
Naja'atu da Humaira kusan sun fi kowa zaquwa da murnar ganin Yariman domin sune basu san shi ba, suna kanana sosai ya tafi, sai kuma jikokin gidan wato 'ya'yan Ya Maira su wajen takwas. Lokacin da motocin su suka iso fada, sai kade'kaden da bushe-bushen ya karu. Wani abu ne da Sa'ade bata saba ji a cikin masarautar ba in ba wani muhimmin abu ake ba, kamar nadin sarauta ko bikin aure. Duka-duka ma dai tun zuwan ta Askira bai fi sau biyu ta ji irin wannan ba, don haka ta gane akwai muhimmin abin da ke faruwa yau a masarautar.
Tana so ta san me ake yi, amma ta rasa wanda zata tambaya, don Fulani ma tun safe tasa aka shirya Zarah suka wuce babban falon ganawar sarki da iyalin sa, inda sauran iyalin gidan suka hallara, ko ta kanta bata bi ba. Fanna ma dai ta lura yau dukkan su busy suke a cikin gida da girke-girken da iyalin gidan zasu ci da wanda za'a tarbi Yarima Sageer da shi.
Don haka itama tun safe bata sa ta a idanun ta ba.
Sa'ade duk ta zama curious ga son sanin me ake yi haka cikin gidan, a ranta tace yau dai zata yiwa Fulani laifi sau daya, dole taje ta baiwa idon ta abinci, iyakaci Fulani in ta kamata ta murde mata kunne ko ta mare ta.
Da wannan tunanin ta dau mayafin ta, sadaf-sadaf ta fita daga sassansu, a falon daya raba sassan Fulani da inda sauran bayinta ke shige da fice ta ci karo da wasu duk suka zubo mata ido, bata ko kallesu ba ta daga kafa ta fice daga unguwar Fulani Bilkisu.
Mayafin ta ta janyo ta rufe rabin fuskarta, idanun ta kawai ake gani. Ta rasa ina zata dosa? Dan ba sanin kan gidan tayi ba, daga bisani ta lura da inda bayi ke karakaina da manyan farantai, kanta tsaye ta doshi wajen.
Wani babban falo ne ta ga bayin suna shiga da sundukan abinci da katon katon na lemukan gongoni, ta bi bayan su a hankali har zuwa kofar falon, sai ta zagaya ta bayan tangamemeiyar tagar gilashi ta falon ta leka a hankali. Ba zata iya shaida fuskokin data gani ba don tagar ta baya ce duk sun juya bayan su, ta dai hango Alanguburo akan kujerar mulkin sa, zagaye da shi kananan yara maza da mata har da matasan 'yammata kamar ta, a gefensa daura da shi bisa kujerar da bata kai tasa ado ba wani zankadeden matashi ne, duk da bata yi nasarar ganin fuskar sa gabadaya ba ta ga gefen fuskarsa, da dogon karan hancin sa, kalar bakar fatar sa kamar ta mutanen kasar Morocco, hular sa ta nitse a cikin tarin sumar kansa sannan fararen kayan dake jikin sa babu ado irin na sarauta a jikin su. Normal tsadadden yadi ne (filtex London) mai taushi a idon mai kallon sa, sauran mata da mazan dake zagaye dasu duk bata ganin fuskar su, amma ta shaida bayan uwarta Fulani da kalar tufafin dake jikin ta kasancewar ta san ta da kayan. Wata zuciyar ta ce "yi ta kanki Sa'ade, idan Fulani ta kama ki a gaban kowa sai ta yi miki dan banzan duka. Tunda dai kin gani taro ne suke yi nasu su-ya-su (family get together)".
Wata kyakkyawar mata ta juyo tana magana da wata dattijuwa, sai ta gane fuskar ta, tana daga cikin wadanda suka je wa Humaira visiting har suka kira ta (Ya Maira). Salin-alin ta soma ja da baya, sawun ta a likkafa, sannan ta juya da sassarfa akan kafafun ta ta koma inda ta fito. Ko ba komai ta ba idon ta hakkin sa.
Da Fanna ta fara cin karo ta saka bayin dake sassan a gaba tana ta yi musu fada don me suka barta ta fita, sai gata ta shigo kamar an koro ta, da sauri Fanna ta doshe ta tana hamdala. "Daga ina kike Sa'adatu?" "Kai Fanna, sai kace wata karamar yarinya zan bata a cikin gidannan ne da wayo na da idanuna da komai?" "Ba cewa na yi zaki bata ba ranki ya dade, inda Fulani ta shigo ta nemeki bata gan ki ba me kike so mu ce mata?" Sa'ade ta murguda baki tayi shigewar ta ciki tana kunkuni.
"Haka kawai ayi ta kulle mutum a daki sai ka ce wani daddawa, su suna can suna jin dadin su cikin jama'a, bata so a ganni don me ta haifo ni?"
Wunin ranar zungur bata ga Fulani ba, sai washegari da safe ta fito don ta gaisheta kamar yadda ta saba duk safiya in dai tana garin, ta same ta ta hargitsa bayi suna ta gyare-gyare a sassan wai Yarima zai shigo ganin Zarah, yau zai shiga kowanne sassa na gidan. Sama-sama Fulani ta amsa gaisuwar ta sannan ta cigaba da bada umarni, ta juya cikin jin haushi, ta tsani wannan rashin bata muhimmancin da Fulani take yi amma ba yadda zata yi.

Bakon da ake ta shirye-shiryen domin sa bai shigo sassan nasu ba sai bayan sallar la'asar. Tana jin wani irin kirari yana tashi daga bakin bayi (Gyara kimtsi da kyau... Lafiya dan zakin duniya. Lafiya dan malafar duniya. Lafiya dan mai fada da cikawa. Lafiya dan masha-sha. Lafiyar ka dama da hauni mai nasara. Zauna dai-dai dan bawan Allah. Zauna dai-dai dan waliyin Allah. Aminchinka rike linzamin ka dan bawan Allah....zauna dai-dai dan masu Alheri...) daga bisani ta ji muryoyin mutane da alama ba shi kadai bane, mazane sun kai su biyar, bayan Yarima Sageer akwai Awaisun sa, kannen sa maza su hudu tareda Ashgar duk da ba lafiya ce da shi ba hannun sa na cikin na Yarima kamar zai maida shi cikin sa. Tana so ta yi leke tana tsoron Fulani, sai ta zo bakin kofar dakin ta ta kasa kunne ita a dole sai taji me ake yi kuma su wanene? Lol.
"Yarima in a hanya na ganka ai bazan taba gane ka ba, sabida a hoto kawai nake ganin ku wajen Askirama, gara kai kana nan a bakin ka, amma Awaisu ya koma bature sak!" Inji Fulani.
Awaisu yayi murmushi ya ce "duk da haka gara ni ban manta Kanuri ba, amma wannan ko Hausa da kyar yake yin ta, su sanya alkyabba kuwa tuni ya manta yadda ake yin su balle yadda zai wara kafafu ya hau doki". Yarima ya harareshi a lokaci guda yana jijjiga Zarah dake hannun sa, wadda tun ganin sa da ita jiya Allah ya sanya matsananciyar kaunar ta a zuciyar sa musamman da ya ji cewa sikila ce, yayi kissing kumatun ta yace.
"Ranki ya dade da fatan zaki bani Zarah in tafi da ita Amsterdam in kin yaye ta in sa ta a makaranta?" Fulani ta ce "in ka yi aure ba? Kuma matar 'yar gida ka aura wadda bazata ji kyashin rike maka diyar ba" Awaisu ya fashe da dariya da ya tuna wadda Yarima yake shirin aure, dan kuikuiwo ne pet din ta dake biye da ita duk inda zata, ya ga yadda zata rike dan mutum sukutum ko sallah bata yi.
Ta kasan ido Yarima ke kallon sa, shi kadai ya gane me yake nufi da kallon da yayi masan, don haka ya ja bakin sa yayi shiru yana cigaba da dariya. Yarima ya dago manyan idanun sa farare kal, ya sauke su a kan maridin dan uwan sa wato Ashgar, ya ce.
"Ashgar, ina labari?" Murmushi Ashgar din yayi, sannan ya maimaita abinda Yarima ya ce, ba tare da ya san me ya fada ba, Awaisu yace "ya kamata ace Ashgar yana karbar rehabilitation therapy, da an samu cigaba sosai a rayuwar sa, a can kasashen da muka fito ana bawa irin wadannan lalurorin muhimmanci sosai su yi rayuwa mai ma'ana kamar kowa". Suhail dan Ya Kirjinoma yayi tsaki ya ce "da dai Ya Kirjinoma zata yarda cewa ciwo ne daga Allah mai zaman kansa, amma ita kullum zancen ta bakaken aljanu ne aka tura masa" haka hirar ta koma a kan Ashgar, Yarima da Awaisu na fadin ba wani aljanu, in maimartaba zai amince da Ashgar zasu koma Amsterdam su kai shi rehabilitation center na masu lalurar sa. Yarima ya ki ajiye Zarah a tsayin zaman su a falon, tana rungume a hannun sa, baya gajiya da kallon ta yana mata wasa jefi-jefi.
Aka gabatar musu da kabakin da Fulani ta shiryawa Yarima na barka da zuwa, sosai suka ci abincin suna hira a tsakanin su cike da kaunar juna, duk cikin matan maimartaba sai yaji Fulani Bilkisu tafi kowacce samun matsayi a zuciyar sa akan dalilin da bai sani ba. Koda yake a fili yake; Fulani na da matukar kirki sannan tana kaunar 'ya'yan Askirama da zuciya daya kamar yadda yake kaunar ta. Hassada ce kawai da kishi irin na mata zasu sa ka kushe Fulani Bilkisu ko wani hali na ta, domin ita din ta yi ta kowanne bangare.
Basu bar sassan ba sai ana gab da kiran sallahr magriba, shima din sai da Ya Maira ta biyo bayan su don ganin uwar da suke kullawa a unguwar Fulani Bilkisu wajen awanni biyu, tana shigowa ta ce in ya gama yaje Ya Gumsu da bakin ta na jiran sa, dole suka yi haramar tafiyar yana gayawa Fulani gobe in ya dawo daga hawan kilisar da zasu yi zai dawo ya ga Zarah. Tayi murmushi tace "Zarah na murna da dawowar wannan babban Yaya nata, mai ji da ita, bakon Amsterdam!". Yayi murmushin da ya kara masa kyau da ilhama ya sunkuyar da kai sannan ya fita, ya bar kamshin turarensa INVICTUS (by Paco Rabbanne) a sassan Fulani bakidaya.
Zata wuce daki ta hango Sa'ade na leke ta tsakanin kofa, murmushi tayi tace "uwar gulma". Sa'ade bata ankara ba sai ganin Fulani tayi agabanta, sosai ta razana ta ja da baya, Fulani tace "uban me kike lekawa?" Ta zumburi baki. "Ni ba abinda nake lekawa, maganar maza na ji, nikuma na san maza basa shigowa sassan nan".

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login