Showing 63001 words to 66000 words out of 117873 words
a raunane ya ce.
Fulanin Maimartaba, Allah ya baki yawan rai, na gode. Allah ya jikan magabata, insha Allahu ba zan ba ku kunya ba. Na karbi auren Saadatu da hannu bibbiyu. Allah ya ba ni ikon yin adalci a tsakaninsu.
Sosai Fulani ta ji dadin kalaman Yarima Sageer, suka wanke damuwarta kaso hamsin cikin dari na tunanin Yarimazai wulakanta mata Saade tunda yar talaka ce kuma yana da mata Baturiya, damuwar hakanta ragu daga ranta, don ba ta zaci haka zai karbi maganar ba with due respect, tunda uwar shi ma ba ta so. Ta ce,
Da kai da Saade duk daya ne a wurina Yarima, kamar yadda Askirama bai taba bambantata da ku yayan da ya haifa ba. Rokona daya gare ka Yarima ina so ka raba musu gida, sabida Saade ba za ta iya zama waje daya da Aisha - Sultana ba, shekarun su, tunanin su, akidunsu da halayyar su ba zai taba zuwa daya ba. Ka ga kuwa zama da juna zai musu wahala.
Ya saci kallon Askirama ta kasan idanun sa,sabida tsoron ko ya ji abin da Baggarar matar san nan ta ke fadi? Sai ya ga hankalin shi ba ya kan su sam, waya yake yi ma da yar sa Yaa Maira lokacin, wadda ke aure a masarautar Biu. Tana gaya masa cewa sun taso suna hanya har sun wuce Maiduguri.
Wani sigh of relief Yarima ya sauke da ya fahimci Askirama bai ji ta ba. A ran sa fadi ya ke na tabbata sanda aka yi miki aure da Baban Saade baki yi girman ta ba kuma kin haifeta lafiya. A fili kuma ya ce,
Insha Allah zan nema mata nata muhallin, daya bukatar kuma zan duba insha Allahu ran ki ya dade. Ai ba abinda zai gagara.
Da wannan ya yi musu sallama ya mike zai fita. Sai Askirama ya sake yafito shi.
Be a man also, after being a Prince (ka zama namiji bayan zama Yarima) wanda ba mai iya juya raayin sa, wanda ya san cewa mata da karkataccen haqarqari aka halicce su tunanin su ba kamar na maza bane, ka san yadda za ka lallaba mahaifiyarka har ta sauko daga dokin fushinta, ta karbi Saadatu matsayin diyar ta, ta sanyawa auren ku albarka. Tashi ka je ku tsara komai kai da Awaisu. Allah ya yi wa rayuwarku ku duka albarka.
*****
Yaa Maira ta iso daga masarautar Biu kamar yadda mahaifinta ya kira ta don ta zo su yi shirye-shiryen bikin dan uwansu. Haka Murjanatu ta taso dagaIstanbul tun jiya ta sauka Abuja. Zata biyo connecting flight zuwa Maiduguri yau.
Kamar yadda Maimartaba ya yi mata umarni cewa, idan ta iso kafin ta shiga koina ta fara ganinsa tukunna. Yaa Maira, ta bi wannan umarnin na mahaifin ta, ta yi saa babu kowa tare da Mai Askira lokacin da ta shiga falon ganawarsa da iyalinsa.
Ta same shi yana cin abinci. Ita dai ta ji an daura wa kanin ta Yareema aure, amma ba ta san da wa Askirama ya daura ba. Yanzu da ta ke durkushe a gabansa suna magana ta Da da mahaifi, bayan ya kare cin abincin sa sun gaisa, ta fahimci ko wace ce Maimartaba ya zaba wa kanin ta Yareema Sageer. Ba kowa bace face Saadatun Fulani Bilkisu!!!
Yaa Maira, wadda sunan ta na sarauta kenan, tana da wata baiwa ta daban kamar yadda na fada a baya ta sunsunar kaddara. Tun ganinta da Saadatu na farko jikinta ya ba ta wannan yarinyar will some day become part of them, za kuma ta zamo wani jigo a rayuwarsu. Zubin halitta da komai nata na Fulani Bilkisu ne, Bilkisun da ke juya zuciyar Maimartaba a halin yanzu. Bilkisun da babu tauraruwa mai hasken ta a idanun Mai Askira. Sai ba ta yi mamaki ba ko kadan da wannan zabin na mahaifin su domin BAGGARA matan manya ne. Abu daya ta ke so ta tantance yanzu shi ne hakikanin alakar dake tsakanin Bilkisu da Saadatu.
Mai Askira sai bai boye mata ba, ya gaya mata hakikanin alakar da ta hada Bilkisu da Saadatu.
Yar ta ce ta cikin ta!
Mamaki, alajabi da tuajjibi kamar ya zauta Yaa Maira, kodayake dama ta dade tana kiyasta hakan, kawai sai ta ji ta karbi Saade da dukkan zuciyar ta matsayin suruka. Duk da aibanta ta da Humaira ke yi duk sanda suka taru bata taba fadin wani mugun hali a tare da ita ba, in ka fahimci duka kushen Humaira akan Saade to kishi ne na son da Askirama ke mata da daidaita musu matsayi da yake yi lokacin suna makaranta. Sai ko taya uwar ta Yaa Hibbani kishi da Fulani Bilkisu. Sai kuma kyawun Saaden da take cewa irin na shegu ne.
Ita ta sani uwar Saade mai nagarta ce, cikin matan gidan kaf babu mai kirkin ta, saidai kishi ya hana aga hakan a kare da fadin aibun ta. Maimartaba ya sa mata albarka domin ta ce ta karbi amanar Saadatu a dakin su, ita ce uwardakinta daga yau, za kuma ta yi duk irin kokarin da za ta iya wajen ganin cewa mahaifiyarsu (Ya Gumsu) ta sauko ta sanya wa alamarin albarka.
Da wannan ta bar falon Askirama zuwa unguwar Ya Gumsu. Tana tafe tana saka irin lallashin da zata yi mata.
*****
Yaa Gumsu ta yi mamakin ganin Yaa Maira a daidai wannan lokacin, don dai ita da kanta ba ta gaya ko dayan su zancen auren Yarima da Saade ba saboda tsananin kiyayyarta ga auren. Yaa Maira ta kwaso gabadaya yayanta maza da mata sun taho, kallo daya ta yi wa Ya Gumsu, ta tabbatar da abin da Askirama ya gaya mata na cewa tana matukar adawa da auren, ba kuma don komai ba sai don kishinta da Fulani Bilkisu.
Ya Gumsu hakimce cikin royal chair ta babban falon ta, kuyangi na yi mata firfita da maficin gashin dawisu. Wasu na tausa mata kafafu, wasu na zubo kirari amma duka basu ishe ta kallo ba sai kumburi take kamar zata fashe. Ta daga ido tana kallon Yaa Maira da ke warware lafiyayyar laffayar jikinta don ta ji dadin hutawa, sun sha zaman mota daga Biu zuwa Askira. Take gayawa Yaa Gumsu. Ya Gumsu ta harare ta sosai, sannan a hassale ta ce.
To da ki ka kwaso bataliyar yayanki ku ka zo kuka cika min gida me ku ka zo yi? Wa ya gayyato ku? Na ayya gayyar sodi?”
Dariya Yaa Maira ta yi, ta ce,
Allah ya taimaki Gumsun Gari, mu ai ba sai an gayyace mu ba. Su Murjanatu ma duk suna hanya.
Ya Gumsu ta kara shaka sosai, amma ta ja bakinta ta yi shiru sabida kuyangin da ke zazzaune wasu a tsaitsaye, zuciyar ta na tafasa. Ta kara ganewa Mai Askira bai dauki auren nan da ya daura da sauki ba tunda har da kan sa yake gayyatar yayan sa abinda bai taba yi ba. Allah kadai yasan iya gayyatar da yayi da irin hamshaqan sarakunan da ya gayyato akan auren nan. Bata kara magana ba sabida kunar zuci. Kallo daya Yaa Maira ta yi wa kuyangin da ke wurin duk suka mike suka bar falon, suna masu yi mata kirari irin wanda suke yi wa diyan Ya Gumsu.
A tashi lafiya Yaa Mairar gida,
A gana lafiya uwar marayun Askira,
A fito lafiya cikin alheri Yaa Maira uwar diyan Yaa Gumsun Askira bakidaya..
Daidai kafafun ta Yaa Maira ta zauna suke kara gaisawa a nitse, gaisuwa irin ta Da da mahaifi, Yaa Gumsu na kokarin hadiye fushin ta, yaran duk sun bazama cikin gida, kowa ya tafi wurin saanninsa yadda suka saba in sun zo gidan. Yaa Maira ta ce da mahaifiyar ta cikin sanyin murya.
Sai muka ji abin alheri Yaa Gumsu, da ma zaman Yarima da mace daya ai ba yi ba ne, Yarima fa, Yariman Askira Mai jiran gado! Balle wadda ba ta fito daga jinsinmu ba balle addinin mu.
Na yi farin ciki kwarai da gaske don dama ni auren nan na farko na Yarima bai kwanta min ba ko kadan, babu wani biki na alaadunmu da muka yi sabida abin kunya ne ma mu fito mu fadi ga wadda ya aura a cikin masarautun da ke zagaye da mu.
Sai kuma ku yo gayya a auren shegiya mara asali? Tukunna ma kin san da wa ya daura masa auren da kike wannan giringidishin?
Subhanallah, Yaa Gumsu tofar da miyan bakinki tun kafin malaiku su rubuta. Saadatu ba shegiya ba ce, diyar Bilkisu ce ta cikinta
Tayi aure ta haife ta da mijin ta na fari kafin ta auri Askirama..!.
A razane Yaa Gumsu ta dago ta dubi diyar ta Yaa Maira. Sai Yaa Maira ta yi amfani da wannan damar data samu wajen luguiguita zuciyar ta.
Tiryan-tiryan ta soma bai wa Ya Gumsu labarin Bilkisu da yadda ta haifi Saade, sak yadda mahaifin su ya bata labari, ta kare da labarta mata Bilkisu ta boye musu Saade yarta ce sabida ba ta son gori musamman daga ita Yaa Gumsu in ta ji cewa ba a budurwa Mai Askira ya aure ta ba ta kade har ganyen ta da gori. Karshen maganar da Ya Maira ta fada shi ya kara sanyayar da jikin Ya Gumsu.
Dangin mahaifinta na hanya, wan mahaifinta uwa daya uba daya Alhaji Kyari Babagana, na tabbata kin san wannan sunan, don kuwa shi ne yake bai wa Bulama fatun da yake kai wa kasar Italiya. (Bulama kani ne ga ya Gumsu, wanda suke sanaa daya da Alhaji Kyari). Ita ma Ya Maira Askirama ne ya gaya mata hakan. A binciken da yasa aka yi masa akan asalin mahaifin Saade.
Ya Gumsu da ke ba ta son nuna karayarta, sai ta hau mitar rashin dalili.
Ban da munafurci me ye na boye mana cewa yarta ce? Ina ruwanmu don ta taba aure? Gori yana tsiro a goshi ne? Duk wata harka ta kishiya sai kin samu dunkulallen munafurci a ciki. Ashe ma a bazawara ta zo shi ne ta bi ta juye kan tsoho, kinibabbiya, haba! Ni fa in ce wannan so da Askirama ke wa yarinyar nan da walakin, ashe agola diyar mowa ce, to muna jira mu ga wan baban yarinyar da idanunmu don mu tabbatar ba shegiyar bace.
Kuma shi Yareema shi ke nan ba zai auri yar sarauta ba, auren misali sai dai ya gani a wurin tsararrakin sa? Alhalin ba gata aka fi shi ba? Daga jinsin yahudawa da masu kanan ido sai jinin talakka agola a matsayinsa na Yarima mai jiran gadon Askira?
Ya Maira ta yi kasa da murya ta ce.
Yaa Gumsu, gara talaka, agola tushen musulunci tashin musulunci a kan tubabben da aka ce daga kwalba ta ke yi a bar, sallar ma ta daina. Ki gode wa rahmar Allah Ya Gumsu alheri Askirama ke nufinmu da shi. Yariman ai ba wankakke ba ne kin fi kowa sani. 'Yar Bilkisu aka cutada auren Yarima ba Yarima ba.
Ni tun ganina da yarinyar na farko na san za ta zame mana wani jigo cikin zuriar mu. Tana da charisma mai yawa. Tana da wisdom bayyananne. Allah ne bai taba kai hankali na kan Yarima ba, musamman da ya zo ya yi auren sa daga baya. Amma na yi zaton Ashgar zaa bai wa, sai dai lalurar sa ba za ta bari ya yi aure ba,
Jiki na ya dade da bani hakan cewa bazata wuce mazan gidan nan ba koda ba daga dakin nan ba.
Yaa Gumsu Ta kyabe baki tace Mairam ki fita ido na in rufe, na bi wisdom da gudu na tattake babu takalmi a kafata me yasa baa baiwa dakin Yaa Kirjiloma ba? Uban wa yace miki Ashgar bazai iya aure ba? Sai Yarima na dana dora dukkan buri akan sa da yayan da zai haifa? Kawai sai kuka ya kwace mata.
Yaa Maira ta rasa yadda zata yi da Yaa Gumsu, duk dabarar ta ta kare. Haka ta yi ta tausar Ya Gumsu tana nuna mata muhimmancin wannan aure ga mutuncin Yarima da rayuwarsa, da alkhairin da ta ke hangowa a cikinsa na kimtsuwar Yarima.
Yaa Gumsu baki da masaniyar cewa har yanzu Yarima Sageer bai bar bin mata a garin Abuja ba? In baki sani ba ki sani, in kuma kin sani ki tuna.
Ko jikin ta ya yi sanyi dai ba ta nuna ba, Ya Gumsu akwai Ki-Fadi, ko ma me ye ba za ta so hada jini da Bilkisu ba gara dan kowa a kan nata. Da ta rasa hujjar kamawa sai ta ce da Yaa Maira.
Shi ke nan kuma shi ba zai yi aure irin na gidansu ba? Ba zai yi auren martaba (auren sarauta) ba sabida ubansa na auren uwarta?
Yaa Maira ta sake kwantar da murya, Allah ya taimaki Gumsun Askira, ai akwai sauran damarmaki. Yarima na da gurbin wasu matan biyu bayan Saadatu, ki ka sani ko duka ya auri yayan masarautu a sauran guraben yadda kike masa shaawa?
A nan ne Ya Gumsu ta yi ajiyar zuciya, don shaf bacin rai ya sa ta manta da hakan, yayi zabin sa ya yi zabin mahaifin sa dole nan gaba kadan ya yi nata zabin. Ta ce,
Yanzu ki ka yi magana Mairam, daga yau zan fara binciken yayan babban gida wa Yarima. Ba zai yiwu a ce duka aurarrakinsa babu zabina a ciki ba.
Yaa Maira ta ce, Oh ni ya su. Amma Ya Gumsu ki bari ki ga kamun ludayin zaman nasu tukunna, kafin ki nema masa sabon aure. Yarima kodayake basarake to bature ne na gani kashe ni. Ba zai so da kuruciyarsa a cika masa gida da mata ba. Ki yi hakuri ki daga masa kafa zuwa wani lokacin.
Haka ta yi ta lallashin Ya Gumsu cikin kwantar da kai da lalama, kodayake da ma cikin yayanta kakaf Yaa Maira ce kadai ta iya tafiyar da ita cikin hikima duk taurin kanta. Ko dai ba ta sauko duka ba, to Yaa Maira ta yi nasarar dakushe kiyayyarta da auren kashi talatin cikin dari. Tunda ta ji Saade ba shegiya ba ce sannan yar Fulani ce ta cikinta ba yar riko ba kamar yadda suke tsammani. Kuma ta ji cewa dangin ubanta za su bayyana kansu.
Wannan ne kadai ya sassauta zuciyar Ya Gumsu har ta yarda ta amince musu su je su shirya biki nasu na aladar masarautar Askira. Amma ita tana nan sassan ta ko waje bazata leka ba.
Don farin ciki Ya Maira a take ta hau buga wa kannenta mata da maza waya ta ce duk su hadu yau a Unguwar Fulani Bilkisu kan shirin bikin Yareema bayan sallar isha’.
Kafin lokacin Mairam-Murjanatu ta iso. Ko hutawa ba ta yi ba suka dinga firfitowa daga sassan iyayensu mata zuwa na Fulani Bilkisu.
Da ma kuma tun da yamma Yaa Maira ta aika wa da Fanna sakon zuwan nasu. Fanna kuma ta gaya wa uwargijiyarta. Don haka ba su zauna ba tun lokacin suke dafe-dafen abinci na alfarma domin saukar su Yaa Maira da sauran yayan Askirama maza.
Humaira ce kadai ta ki zuwa don ta shiga matukar damuwa da wannan auren da aka daura. Fulani Hibbani kuma ta ce ta raba kanta da wahala, fadan da ya fi karfin ka ka maida shi wasa, ta fita batun Fulani Bilkisu da yarta, don sun gama da ubanta saidai wani sarkin ba shi ba, in kuma ta ki ji ita ce a wahale.
Saade da ma ba ta yarda ta bar dakinta a bude tun daga lokacin da suka yi magana da Fulani a kan aurenta da Yareema, ita kanta Fulanin haushi take bata yanzu don ta lura ta gama mika wuya ga auren sabida son da take wa mijin ta Askirama, kuma bata dauki shirin sa da wasa ba, ko don bata san waye Dr. Sageer ba? Ko kuma bata dauki hakan da muhimmanci ba? Aisha Sultana bazata yi masa karya ba da ta ce hes committing adultery kuma SAI YA BARI ITAMA ZATA BAR GIYA, wannan ne gidan da Fulani ta amince a kai ta kuma cikin mutanen da take mata fatan rayuwa ta har abada?
Ita kuma Fulanin kamar ta san tunanin da take yi sai ta fita sabgarta, shirye-shiryenta ta ke kain da nain, ta ce cikin ran ta,
Allah shine mai shirya bawa bani da tsumi banida dabara sai abinda Allah ya shiryawa rayuwar ki Sa'ade. In kun tafi Abujar ku karata can, ni biki ne a gaba na. dama ai tare kuka zo, don