Showing 108001 words to 111000 words out of 117873 words

Chapter 37 - Masarautar Mu 1 to 4 Complete

me ke damunta.
Ita dai Fulani tuni ta sha jinin jikinta. Tun daga sanda Saade ta ce ba ta son warin turarenta. Amma kuwa Yarima bai kyauta ba, ya saba alkawarin da ya yi mata. Saade is too young da haihuwa wani matsanancin tausayi ya kama ta.
Amma da ta tuna ba haramci suka aikata ba sai ta rage wa kanta damuwa. Wannan rabo na kurkusa da kofar daki ina Ya Gumsu za ta kai shi?
Ko kusa abin da Ya Gumsu ta yi wa Saade bai sa ta ji tana so a raba auren ba, ko don ganin halin bacin ran da Askirama ke ciki, wanda ko ita da ta haifi Saaden abin bai tabata har haka ba. Ta sa a ranta Ya Gumsu za ta yi fiye da wannan in dai a kanta ne.
Kuma a washegarin ranar bayan fitar Dr. Zainab da ta duba Saade ta tabbatar wa Fulani akwai ciki na sati Shidda, ta shiga don ta yi wa Askirama wannan albishir ta ji yana amsa waya. Sai kuma ta ji ya ce, Stroke? Cikin tsananin mamaki.
Gumsun da ko jiya na yi magana da ita a waya lafiya lau?
Aka yi magana daga daya bangaren wanda ita ba ta ji ba, sai ta ji ya ce, Ai shi ke nan, Allah ya ba ta lafiya. Yayanta sai su je Abujar su yi jinyarta, amma Allah ya gani ni ba zan zo ba Daja, yar uwarki ta girma ba ta san ta girma ba.
Na dade ina hakuri da halayenta ta kasa gane gata na yi wa rayuwar Yareema da shi bakidaya da na aura masa Saadatu. Babu yadda ban yi da ita ba ta karbi hukuncin Ubangiji, ta nuna min ta hakura har za ta kai musu ziyara, shi ne ta yi tattaki har dakin yarinya, ta ci zarafin marainiyar Allah ta koro ta tun daga Abuja har Maiduguri da Askira ita kadai a wannan marrar ta satar dan mutum kamar satar takalmi.
Don haka ina nan a kan bakana, Gumsu ta ci gaba da maye gurbin Saadatu wajen Yareema Sageer. Babu Saadatu babu danta, sai ranar da ta yo tattaki har dakin Bilkisu ta ba ta hakuri a kan cin zarafin da ta yi wa yarta. Ta kuma furta da bakinta cewa ta amince su ci gaba da zaman aure da bakinta. In ba haka ba shi ma Yariman kada ya sake ya tako min gida.
Yana gama fadin haka ya kashe wayarsa yana maida numfashi cikin bacin rai. Fulani Bilkisu ta karasa ta gurfana a gabansa, tafukan hannunta bisa tafin kafarsa. Cikin muryar lallashi da son kwantar masa da hankali ta yi masa albishir din da ke bakinta.
Da gaske?
In ji Askirama. Cikin excitement din da ba zai misaltu ba.
Ta kashe shi da lallausar murmushi, ta ce, Da gaske Dr. Zainab ta tabbatar da ciki na sati shidda a jikin Saade. Sabida haka Askirama ka yi hakuri da duk wani bacin rai, tunda Ubangiji ya nuna mana ayarsa. Idan ta warware kwana biyu a manta da komai a mayar wa da Yarima matarsa.
Mai Askira ya girgiza kai ya ce, Ayoyi kam ai muna ta ganinsu. Yanzu kanwarta ta kira ni ta shaida min cewa, suna asibiti da Gumsun Gari, ta fadi a bayan gida ta samu stroke.
Innalillahi wainna ilaihi rajiun. In ji Fulani.
An gaya wa Yarima da su Yaa Maira?
Cikin damuwa ya ce, Yarima ya taho tun jiya ta mota, babu jirgi, amma Awaisu ya gayaminya samu minor accidentahanya, bai ji ciwo ba amma ya bugu, kuma motar sa ta jikkata, ya iso Askira tun jiya, ni na ce da Awaisu ya gaya masa kada ya sake in ganshi gabana ko bangarenki. Ya Maira kuma sun kama hanyar Abujan.
Cikin dimbin alhini Fulani ta ce, innalillahi wainna ilaihi rajioun. Zama bai ganmu ba, ya kamata a shirya mana tafiya mu uku, ni da Yakirjinoma da Hibbani. Yareema na tabbata Awaisu zai bashi duk kulawar data dace, amma don Allah Askirama ka bar shi ya dawo gidan nan.
Ya yi ajiyar zuciya, wannan karon cikin muryar sa akwai sassauci, ya ce,
Su za su je, amma ban da ke. In kin tafi wa zai kula min da Saadatu da Chiroman Gari?
Ta yi murmushi kadan, jin har ya bai wa dan cikin Saade Sarauta tun kan ya iso duniya.
Ta ce, Fanna za ta kula da su sosai. Bai kamata a ce su sun tafi ni na zauna ba, sai ta dauka sabida abin da ta yi wa Saade ne wanda ni sam bai shafe ni ba. Ta kare zancen ta da cewa.
Ai Saade yarta ce! Koda bata auren Yarima.

Askirama ya kura wa matarsa Bilkisu ido, yana mamakin kyawawan halayenta. Matansa sun kasa fahimtarta ne, amma duk ta fi su kyan hali, ba ta taba dauko zancen wata cikinsu ta kawo masa. Su kuwa basu da aiki sai fadin aibunta. Sun dauki kishin duniya su duka sun dora a kanta. Sun kasa gane ba kyawun halitta kadai ke rudarsa a kan Fulani Bilkisu ba, har da kyawawan halayenta.
Amma duk yadda ta so Askirama ya barta zuwa Abuja duba Ya Gumsu ya ki amincewa da hakan.
Yaa Maira ce ta zo ta hada kan sauran kannenta mata da maza aka ba su motoci da dogarai suka kama hanyar Abuja. Cikin tashin hankali. Hibbani da Yakirjinoma jirgi daya suka bi tare da Ahmad da Suhail wadanda za su kula da su.
Fulani ta kira Yareema a waya bayan ta koma dakinta. Muryar Yareema har ba ta fita sosai, kamar ta wanda ke fama da mura, shi kadai ya san halin da yake ciki. Ciwon da jikin sa ke masa sakamakon buguwar mota bai dame shi ba kamar hukuncin da Askirama ya yanke akan sa na nesanta shi da Saade.
Yana gidansa tun isowarsa ko falo bai leko ba tunda Askirama ya aiko Awaisu ya gaya masa sakon kada ya sake ya ganshi a fada ko shigifar sa, kuma kada ya sake ya je inda Saade ta ke. Har sai mahaifiyarsa ta bada hakurin cin zarafin da ta yi mata har dakin auren ta.
Ta kuma yi alkawarin karbar Saadatu matsayin suruka sannan ne shima zai janye nasa takunkumin.
Shi ya san wannan decision ba mai sauki ba ne ga Ya Gumsu, a yadda ya san kafaffiyar zuciya irin tata in tana kin abu. Kuma bai fita daga wannan zullumi da tashin hankalin ba a daren jiya Aunty Daja ta kira shi tana kuka, wai Ya Gumsun ta fadi a toilet ta samu stroke.
Ya kwana cikin wani hali na kaka-ni-ka-yi, and he is speachless.Wordless. Moodless. Ko magana ba ya iya yi. Awaisu ya so ya taya shi hira a daren ranar bayan ya bashi magani ya kira likita ya duba shi ya tabbatar babu mummunan rauni a jikin sa, ya ce ya tafi kawai ba ya bukata, sai kuma yanzu da wayewar garin yau ya samu wayar Fulani Bilkisu.
Yareemah, kana lafiya?
Ta fada cikin tausayawa. Ji ya yi idanunsa sun cicciko da kwalla, bai zaci wannan rahmar daga gare ta ba. Abin da bai sani ba shi ne, ita halinta ya bambanta da na sauran mata. Mace ce mai hangen nesa da tsananin kawaici da maida dan kowa nata.
Im sorry Fulani, Im sorry. Ya furta in a subdued voice.
Ta yi murmushi, ta ce, Ba zancen Saade ya sa na kira ka ba. Na kira ka ne in jajanta abin da ya faru da Ya Gumsu. Da accident da aka samu, Allah ya tsayar haka, Ya sa kaffara, Allah ya ba ta lafiya.
Na so in bi su Yaa Kirjinoma Abujan, Askirama ya hana ni, sabida ita ma Saade kwance ta ke babu lafiya tun isowarta.
Tamkar zuciyarsa za ta fito ta bakinsa sabida zullumi, ya ce cikin wata marainiyar murya,
Me ke damunta?
Fulani ta yi dan jimm! Kafin ta ce,
Na dauka ka sani ai.
Gabansa ya yi mugun faduwa, kada dai Saade ta gaya musu maganar Dr. Ziyad ne? Yau da ya shiga uku in Askirama ya ji zancen nan ya san aurensa da Saade ya kare.
Hawaye suka fito daga idanun Yareema Sageer ba tare da ya shirya ba. Amma sai Fulani ta fadi abin da ya gigita shi, ya wanke zuciyarsa daga duk wani rudani da dimauta da ta ke ciki.
Ciki ne tare da ita na kusan watanni biyu.
Yareema sai da ya cire wayar daga kunnensa, don ya tabbatar da wanda yake magana, My inlaw ba gizo kunnuwansa ke masa ba. Ya wani irin lumshe idanunsa yana karbar wani irin excitement a cikin kirjinsa.
Don haka ka kwantar da hankalinka ka koma Abuja ka kula da lafiyar mahaifiyarka. Saade tana karkashin kulawarmu insha Allah. Kafin sannan zuciyar Askirama ta huce sai a ba shi hakuri.
Abin da nake so yanzu shi ne ka koma Abuja ka yi jinyar mahaifiyarka.
Insha Allah, I will. Ya fada cikin girmamawa.
Har sun yi sallama ya kasa jurewa. Cikin jin nauyi ya ce,
Fulanin Sarki zan iya magana da Saadatu?
Fulani ta ce, Ta samu barci, in ka koma Abuja ka samu nutsuwa ka kira ni, zan ba ta wayar insha Allahu.
Da wannan suka yi sallama.
A washegarin ranar ya tattara ya koma Abuja.
*****

Yau asibitin national hospital Abuja ya ga iyalin masarautar Askira, ko ina ka wulga motoci ne cike da dogarai masu rubutun Askira Emirate. Tabbacin mara lafiyar na da alaka da hamshakiyar masarautar Askira. Lokacin da Yareema ya iso an kai Ya Gumsu daki na musamman (V.I.P room) an ba ta kwanciya.
Sanda suka shiga shi da Awaisu Ya Gumsu barci ta ke yi. Amma jin muryar Yareema na magana da likita sai ta hau kokarin bude idonta.
Duk da barcin da ya ci karfinta kokarin magana ta ke yi da bakinta da ya karkace, amma ta kasa. Yareema ya matsa daidai kanta yana hawaye yana fadin,
Ki yafe ni ya Gumsu, na kasa cika alkawarin da na yi miki, amma na alakanta hakan da rabon gaggawar da ya rantse a tsakaninmu.
Ya Gumsu Saadatu ciki gare ta, na kasa cika alkawarin ki Ya Gumsu na kasa. Ya saka kuka tare da kifa kansa a kan cikinta.
Da hannunta mai lafiyar ta mika tana shafa sumar kansa, tana ci gaba da kokarin furta magana abu ya gagara, sai hawaye ke bi ta gefen idonta. Amma daga yadda ta kama shi da hannu daya ta kankame tana hawaye ya san alheri ta ke son fada.
“Is ok Ya Gumsu, ki yi barci. Ni dai fatana ki fahimci cewa Saadatu alkhairi ce a gare mu kamar yadda Alanguburo ya hango. Ya Gumsu ki kwantar da hankalinki a kan Fulani Bilkisu da ahalinta, wallahi ba ta nufinki da sharri. Idan Askirama ya fi sonta ba ya nufin ke uwar yayansa ba ya sonki. Yana son ta ne saboda kyautatawar ta gareshi tafi taku. Amma kowa da gurbinta, kuma kowa da matsayinta.
Sai ki duba ki tace ki ga shin me take yi wanda Askirama ke so? Kema sai ki kwaikwaya.
Shaidan ne ya ke kambama miki soyayyar Askirama ga Fulani Bilkisu, amma ita in ya sa ta tana yi, in ya hana ta tana hanuwa. Ke kuwa fa Ya Gumsu? Abin da ki ka ga dama shi ki ke masa, yana hakuri saboda mu, Ya Gumsu lokaci bai yi ba da girma zai bayyana a halayenki?
Hawayenta ya dadu, sai gyada masa kai ta ke akai-akai kamar kadangaruwa. Yarima ya ci gaba da cewa.
Ya Gumsu ki yafe mini ban cika alkawarin da na yi miki ba, musamman da na ji kin ce bayan watanni uku za ki raba mu. Na kasa Ya Gumsu, na kasa Saadatu ciki ne da ita, zan yi azumin kaffara ki yafe mini.
Tana so ta ce masa babu kaffara a kanka, tunda ba fadar Ubangiji ba ce, sannan baka sabi Allah ba, amma ta kasa. Yarima ya rungume ta yana ci gaba da rokonta rangwame da afuwa a kan aurensa da Saadatu wanda ya kara karya zuciyar Ya Gumsu, ta amince soyayyar danta ga yar Fulanin Askirama wani hadi ne daga Allah, domin ya dinke barakar da ke tsakaninsu. Ya kawo maslaha da fahimtar juna ga iyalan Maimartaba Sarkin Askira.

Kwanan Ya Gumsu da iyalanta uku a National Hospital, sauki na samuwa a hankali. Ya Maira ta kira Yareema gefe ta ce tunda jikin da sauki, kuma an ce gashi ya rage za a dinga yi mata, ko zai nema musu sallama su koma gida? Sai a yi hiring professional din da za ta dinga yi mata gashin a gida?
Sun yi yawa a asibiti, kuma ba wanda zai yarda a ce ya koma gida. Don wani hotel suka kama a nan kusa da asibitin mazansu da matansu.
Yareema ya amince da shawarar Yaa Maira, ya nema musu sallama a washegari. Daga asibitin koyarwa na Maiduguri aka dauko physiotherapist din da za ta dinga kula da Ya Gumsu a gida ana biyanta.
Yareema bai samu nutsuwa ba tun saukarsa Abuja, don haka bai kira Fulani Bilkisu ba. Amma ko me yake yi Saadatu na manne cikin ransa. Minti bayan minti, sakan bayan sakan son Saadatu karuwa yake a zuciyarsa. Tamkar nisa da suka yi da juna wani medium ne na linking zuciyoyinsu wuri guda.
Haka kuma yake ga Saade, wadda ke can tana fama da kanta, amma kullum hankalinta yana kan mijinta Yareema Sageer. Ko yana cin abinci? Ko yana cikin irin damuwar da ta ke ciki? Ko shi ma Ya Gumsu ta mare shi a kan ta? Tambayoyin da ta ke yawan yi wa kanta ke nan ba ta da mai amsa mata. Domin Fulani ta lafiyarta ta ke ba ta mata zancen Yarima sam-sam.
Sun dukufa ita da Fanna wajen kula da ita da dafa mata duk abin da suka san za ta iya ci ko da loma daya za ta yi masa.
Dr. Zainab ma na kokari a kanta matuka, ta taimaka aman ya tsaya, amma kullum cikin tashin zuciya ta ke, don haka Fanna ta samo mata goro tana taunawa.
Ta rame ta yi duhu, da ganinta za ka san a satin nan ta yi jinya ta sosai. Tana kwance a dakinta suna labari da Zarah Fulani ta shigo ta same su. Ta ce,
Saade su Yareema sun dawo fa, an sallamo Ya Gumsu, don haka ki daure, ki kwarara jikinki yanzun nan ki je ki duba ta, ko da kuwa ba za ta amsa ba.
Saadatu ta fiddo ido cikin razana, Fulani ta lumshe mata ido tare da girgiza mata kai, ta ce,
Do as I said, sai Fanna ta raka ki.
A sanyaye ta mike ta soma daura laffaya a jikinta.
Fanna ce ta yi mata jagora suka tafi unguwar Ya Gumsu. Wata kuyangarta ta shiga ta yi musu iso, sannan ta fito ta shiga da su har tankareren falon da Ya Gumsu ta ke kwance. Gabadaya yayanta maza da mata suna zaune a falon tun daga kan Yaa Maira har zuwa auta Ahmad.

Yareema Sageer na zaune a gefen Ya Maira daga kan tattausan kilishi, ya mike santala-santalan kafafunsa da waya a hannunsa yana latsawa. Sanye yake da alkyabba ruwan zuma wadda ta sha aiki da zare ruwan gwal. Duk hirarrakin da suke yi ba ya sanya musu baki domin gabadaya hankalinsa yana ga son ganin Saadatu, da sabon matsayin da zai kalle ta da shi na mother of his children.
Lokacin da wata baiwa ta shigo ta isar da sakon cewa ga matar Yarima nan za ta shigo duba Ya Gumsu ko kadan bai ji su ba. Text messages yake rubutawa yana aikawa wayar Saade mai dauke da alkawurruka na soyayya da kauna masu wuyar samuwa daga bakin mazan aure a wannan zamanin. Duk da ya san cewa ba ta tare da wayar tata ta baro ta Abuja.
Kamar cikin mafarki, kamar daga sama ya tsinkayi sassanyar muryar Saaden na sallama a falon. Ya riga kowa dagowa a rikice, a mamakance, sannan excitedly yake dubanta. Da shi ta fara hada ido, ta yi saurin sunkuyar da kanta. Idanuwan yayye da kannen Yareema suka yi mata caaa wanda hakan ya sa kafafunta hardewa kamar za ta fadi. Kafin Fanna ta riko ta Yareema ya riga ta. Babu wanda ya ga sanda ya mike cikin zafin nama

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login