Showing 42001 words to 45000 words out of 117873 words
zuba abinda zata iya ci, duk yunwar data ke ji sai taji ta rasa appetite din ta, sabida irin tarbar da masu gidan suka yi mata.
A can kofar gida rigima ake tsakanin Sultana da Yarima, ta ce ita sam bata yarda su dinga tafiya tare ba, ko dai ya daukar mata direba ko ta dinga tafiya da kanta tunda babu nisa zuwa cikin makaranta. Ya san halin nacin Sultana in bai yi mata abinda take so ba bazata barshi ya fita ba, don haka yace zai daukar mata direba amma for the mean time zasu dinga tafiya tare kafin a samu direban kuma ta gama registration dinta. Daga bisani ya sassauta murya "you want to me into trouble with my father? Do you know how much he loves this girl?" Sultana tayi narai - narai da ido, sai ya sunkuya ya sumbaci bakin ta cikin lallashi. "Ki kwantar da hankalin ki ni babu wata bakar mace a gabana, look at you me zan nema a wurin sauran mata? I just want to live in peace with my father shiyasa na karbi yarinyar kuma da an yi hutu zan maida ita Askira sai an koma makaranta".
Dai-dai lokacin da Sa'ade ta fito ta gansu a haka kamar zasu manne cikin jikin juna, sai ta samu kanta da jin kunya tayi maza ta juya don bata taba ganin namiji da mace so close hakan ba. Sultana ta harareta sannan ta ja da baya ta budewa Yarima kofa shikuma ya budewa Sa'ade kofar gefensa ya ce ta shigo. Don haushi bata iya ta tsaya ta ga fitar su ba ta juya ta dauki tata motar don tafiya nata wajen aikin. Tana tafe tana tunanin irin takurawar da zaman Sa'ade zai yi mata don tun shekaranjiya Yarima ya kwashe duk wata kwalbar giya dake cikin gidan ya zubar. Jiya sai Bar ta je ta sha abinda ta dade rabon ta da yi.
Suna shiga cikin makaranta Sa'ade ta bude ido tana shan kallon NTNU (Nigerian Turkish Nile University). Its various faculties and administrative offices...the equisite lecture halls and different departments. Wani shauki na diban ta idan ta tuna ta zama cikakkiyar dalibar NTNU yanzu.
Haduwar ofis din YARIMA Sageer Yusuf Askira ya tafi da ita, ko'ina sai raba da sanyi da kamshi mai sanyi. Sai da ta jira ya gama abinda zaiyi sannan ya hadata da assistant dinsa ya taimaka mata ta fara registration. Cikin kwana na uku ta gama, ta zama cikakkiyar dalibar tsangayar (Pure and Appplied Chemistry). Ranar litinin zata fara daukar lacca.
****
Yau asabar, daga matar har mijin duk suna gida, Sa'ade in ta gansu a falo bata fitowa tayi ta zama a dakin ta kenan, ko abinci bata yarda ta zauna ci tare dasu sai ta jira sun gama sun tashi, sannan zata zo ta zuba ta ci ta kwashe kayan ta kai kicin, Uche ya karba ya wanke ya dora wani. Saidai ita sam ba jin dadin abincin gidan take ba sabida abincin turawa ne ake yi kullum, wani ma bata san da me aka sarrafashi ba ko sunan sa, ga kaguwa (shrimps) da ake zubawa a kowanne girki, don haka yau da bazasu je cikin makaranta ba kasancewar hutun karshen mako ne sai tace da Uche kada ya sanya abincin su da ita, she want to cook for herself (tana so ta dafa da kanta).
Uche ya bata duk abinda zata bukata don ta ce tuwon acca zata yi miyar egusi. Nan da nan ta hau girkin ta cikin kula da takatsan-tsan da kuma kwarewa.
A can falo Sultana ke tambayar Yarima yaya zacen direvan da ya ce zai daukarwa Sa'adatu?
"Ana nan ana bincikawa", yace da ita, a lokaci guda yana cigaba da marking takardun dalibansa ba tareda ya bata hankalin sa ba. Ya rasa me yarinyar ta tare mata, bata da zance sai na Sa'adatu a tsayin satinnan bakidaya. Shikuma a yadda ya lura sam yarinyar bata da matsala, sannan bata takura musu, bata sa musu ido kamar yadda suka yi tsammani, tana da tsananin kamun kai da gudun zuciya. Sannan rayuwar ta is very simple.
Wani unique kamshin girki da bai saba ji ba ya bakunci hancin sa, dama kuma yunwa yake ji, ya kwalawa Uche kira. Ya fito da sauri har yana tuntube. Daidai lokacin da Sa'ade ta zo ta wuce su da food flask biyu a hannun ta na tuwo da miya da plate da cokali tayi dakin ta. Ya dan kalle ta ta gefen ido yadda bazaka taba zaton ya kalletan ba yace "Uche, me kake girkawa haka?" "Ba ni bane Oga, Sa'adu ne" yayi murmushi jin sunan da ya kira Sa'ade dashi yace "me ta girka?" "Tuwo ne Oga, with egusi soup" "ok idan da saura debo ka kawo min" "ya kwashe duka ya tafi daki" "saboda rowa ko saboda me?" Uche yayi dariya, "Oga akwai wanda ta diba min, lemme bring it" "thank you Uche".
Uche yaje ya kawo abincin a kyakkyawan flasks a rufe ya aza bisa dining. Sultana na daga kwance tana kallon Yarima yana cin tuwon nan zuciyarta na tafasa, bata isa kuma tayi magana ba yace zai bar gidan, don yace duk renakun weekends baya son korafi, in ta yi masa complain ko guda daya ne zai bar mata gidan ya tafi gun Dr. Ziyad. Ita kuma sam bata son alaqarsa da Ziyad don bashi da aure kuma kullum tana ganin shi yana kwashe-kwashen mata a motar sa zuwa gidan sa. Shiyasa take making sure bata yi abinda baya so ba a kowanne weekend don dai su zauna tare.
Bai san yayi missing cimar gida ba sai yau, sosai ya ji dadin tuwon, da izzar shi zata barshi ai da yace da daddare ma ta kara yi masa, musamman mai miyar ganyen Ugu, yana son ganyen sosai.
Shikuma Uche tunda ya lura Ogan sa na son tuwo sai yake kokarin yi masa, amma sam baya kyau da dandano kamar na Sa'ade don bai kware ba, a wurin Sa'ade ya koya don ya ce mata ta koya masa ya dinga yiwa Ogansa. To amma kullum yayi haka yake dauko shi Oga ya yi loma daya ya ajiye, ko yace ya dafa masa wani abun. Don haka Uche yake mata wayo, kullum zata dora girki sai ya ce ta dora da dan yawa, shima yana so, tana bada baya zai shirya abincin ya kaiwa Yarima, ya gaya masa Sa'adu ne ya girka, ya rasa ya aka yi Uche ya dago shi kan yana son cin girkin Sa'adatu. Duk ranar da bata yi girkin ba ta wuni a makaranta ne yake cin na Uche.
Sultana ta shigo gida yau da sabon bed-side fridge wanda babu a dakin ta. Washegari kuma data dawo aiki ta dawo da manya-manyan kwalaye. Tana kokarin fito dasu daga mota direban da Yarima ya dauka ya sauke Sa'ade. Ganin tana kiciniyar ciccibar kwalayen Sa'ade ta karasa da sauri ta ce.
"Can i help you aunty?"
"No, thank you"
In ji Sultana.
Ta ciccibi manyan kwalayen ta daya kan daya tayi cikin gida.
****
Tun daga ranar Sultana ta daina zuwa Bar ta koma shaye-shayen ta a dakin ta, a zuciyar ta tana tsinewa Sa'adatu, ita da gidanta an zo an takura ta. Bata sha a weekend sabida Yarima yana gida, da yamma kuma sanda ta dawo shima ya dawo, don haka sai ta tsiri kulle kanta da zarar ta dawo aiki bata kara fitowa sai lokacin barcin su.
Dr. Sageer yana lura da sabon sauyin nata, ya rasa me take kulle kanta tayi a daki, bugun duniya in zai yi bazata bude ba sai ta ga damar fitowa wajen sha biyun dare. Tuni ya harbo jirgin ta. Rannan ya faki idon ta ya dauke safayan mukullin. Tana tsaka da shan whisky ya bude kofar dakin ya shigo ya mayar ya rufe.
Kayan barci ne na RALPH LAUREN farare sol a jikin sa. He never looked so handsome in her eyes like today. Ya tsaya a kanta ya harde hannayensa a kirji yana kallon ta with furious eyes... "Sultana why? Ba na hana ki shan giya ba? Ko syrup ban hana ki sha ba? Ban gaya miki haramun ne a muslunci ba? Idan da kin yi na kyale ki yanzu kin sani ba mu kadai bane a gidannan, a slight mistake will probably go to my father, har yanzu jiki na na bani spy ce ya sanya mun. Ki yi a hankali idan ba kina son janyo min bala'i ba".
Ta daga rinannun idanun ta ta dube shi, cikin maye tace "I....i cannot live without beer, a haka ka ganni ka aure ni, kai ma ka sani bazan taba iya barin giya ba". "Sai ki zaba ko aure na ko giya, tunda na sanar dake addinina ya haramta kika ce kin amince zaki daina, tunda kika fara aiki na san kin koma shan beer, sallah kin dade da daina ta, na sa miki ido ne don in ga iya gudun ruwan ki, and now na lura duk musluncin ki ba na gaskiya bane kin dade da daina sallah. Ni kuma bazan zauna da kafira ba".
Ya fadi yana watso kwalaben dake jere cikin firji, ya hada su da bango ji kake taratsatsa! "Kika sake shigo min da wannan kazantar gida, zaki ga yadda zamu kwashe, i'm not that fool and i respect my religion......". Wani wulakantaccen kallo Sultana tayi masa....tace "addini! Kai nan har kana da bakin cewa ka san addini? Addinin naka ne ya baka damar yin adultery? Tunda na san ka na san you are an adultrer wanda baya iya rayuwa sai da mata. Na dauka in mun yi aure shikenan zaka bari, gara ni giya da kayan maye kawai nake sha amma bana zina, balle da aure na".
Tamkar ta watsa masa garwashin wuta haka fuskarsa ta koma, bai taba sanin ta san wannan side din nashi ba, abinda bai sani ba shine tana bibiyar wayar sa. Sultana ta lura da efffect din kalamanta akan sa, sai ta yi wani miskilin murmushi "tunda na barka kana zina, ban taba takura maka ba, sai ka bar ni in sha giya, ko wannan yarinyar ta bar min gida......" ta mike tana layi tayi toilet ta bar shi a wajen.
****
Kwana biyu basa magana da juna, abinda basu taba yi ba a rayuwar auren su, wani abu da Sultana ta tsiro da shi don ta baiwa Yarima haushi shine ta daina boye shan giyar da kayan mayen ta, nan falo take zama ta baje tana abin ta. A ranta ta kudure duk ranar da ya gayawa iyayensa tana shan giya itama tace musu yana neman mata. Gara ma yayi hakuri su ci gaba da zaman su yadda suke yin sa, wata figigiyar yarinya bakauyiya bata isa ta canza mata rayuwa ba.
Sa'ade ta shigo falon da sallama, misalin karfe shidda na yamma, direbanta Salis ya riko mata manyan littafan chemistry har zuwa kofar shiga falo, ya mika mata tayi masa godiya. Tana kokarin shiga Yarima na parking. Ta juya suka hada ido ta cikin gilashin motar sa, sai ya yafito ta, yace "Sa'adatu help me with these files" ta karasa cikin nutsuwa ta karba, shi kuma ya dauko daurin answer sheets na daliban sa ya bi bayan ta suka shiga falon tare. Nan idanun sa suka yi kyakkyawan gani.
Kamewa yayi a inda yake tsaye, a lokacin ta kai bottle na whisky bakin ta, ta gefen idon sa ya saci kallon Sa'ade don ganin reaction din ta, sai ya ga babu wani sauyi a tare da ita, ga dukkan alamu bata san menene a hannun Sultana ba, ta dauka just lemo ne.
Sannu da gida kawai ta yiwa Sultana ta ajiye masa takardunsa bisa centre table, daga nan bata kara kallon su ba tayi shigewar ta daki. Yayi catching breadth din sa da karfi tana bada baya ya wankawa Sultana mari, ya sake wanka mata, sai da ta nemi jin ta da ganin ta na wucin gadi ta rasa. Tana farfadowa ta kai hannu zata rama ya kama hannun ya murde shi. Ta saki karar data kai kunnen Sa'ade. Har zata fito da gudu ta tuna hudubar Fulani (ba ruwan ki da shiga shirgin da ba'a sanya ki ba) tunda dai ta san su biyu ta bar su.
Kwanan tashin hankali aka yi tsakanin ma'auratan, irin wanda bai taba faruwa tsakanin su ba, zagi ta uwa ta uba babu irin wanda Sultana bata yi wa Dr. Sageer ba, har tace duk da kasancewarta kafira kamar yadda yake kiranta bata taba zina ba shi ya koya mata, shi yayi disvirgining din ta, musluncin sa bai kare shi da komai ba, fasiqi mara tsoron Allah. Gara ita giya kawai take sha.
Duka wannan a kunnen Sa'ade, wadda hayaniyar su ta hanata barci, ta tsaya jikin kofar dakin ta sai shivering take (karkarwa). Bata taba jin abinda ya kada ta ya gigitata irin wannan ba, gidan masu zina da shan giya aka kawo ta! Uncle Yarima da take gani da matukar girma da kima shine mai yin zinar? Ko dai Sultana karya take yi? Abinda ta gani tana sha dazu shine giyar kenan kuma shi ya hada fadan?
Tana jiyo kukan Sultana da alama marin ta ya kara yi, jikin ta na rawa ta dauki waya ta kira Fulani, hawayena zuba mata tace "Fulani! Ni dai gobe a zo a dauke ni bazan iya zama a gidannan ba, zan koma hostel" cikin muryar kwantar da hankali Fulani tace "take it easy....gaya min me ya faru? Ana miki wani abu da ba kya so ne?" Cikin kuka tace "no, Uncle Yarima is very nice to me....amma yana dukan matar sa....gata can sai ihu take.....kuma ta ce shi mazinaci ne...." ba shiri Fulani ta dauke wayar daga kunnen ta ta juya, sai idon ta cikin na Askirama da ke gefen ta da alama shima sauraron wayar yake yi don ta manta a (hands-free) take. Yanayin da ta ga fuskar sa a ciki yasa ta jin kamar ta shiga cikin wayar ta shaqe Sa'ade har sai ta daina numfashi.
"Wallahi maganar Sa'ade shirme ce ni na tabbata....". Fulani ta fada muryar ta na rawa, kwalla cike da idon ta. Daga taimako Sa'ade zata baro musu tashin hankali da yake ita butulu ce, ina ruwan ta da abinda ke faruwa tsakanin Yarima da matar sa? Bayan ta gargadeta? Sai ta tuna Sa'aden bata san tana turakar Askirama ba, kuma ita ta bata damar duk halin da take ciki ko karfe nawa ne ta kira ta ta gaya mata.
"Ba shirme bace Bilkisu..... he has this taboo since childhoood". Ya fada muryar sa abin tausayi. Har yaran bayi yake raping...na dauka ya bari, na dauka girma ya sa ya nutsu, na dauka aure ya canza shi...ashe i'm mistaken. To aikin zai bari ya dawo gida kusa da ni kawai ya karbi sarautar gidan su, in cika masa gida da mata da kwarkwara tunda hakan yake so.....da raina da lafiya ta bazan bar shi ya karasa rayuwar sa a haka ba........".
The way Mai Askira ke magana ya taba zuciyar Bilkisu, bata taba ganin sa cikin wannan sad mood din ba. A muryarsa da fuskarsa bakin ciki ne zallah. Ya kare zancen sa da cewa "zan raba Sa'adatu da gidan sa, tsoro na Allah yanzu tsoro na kada itama ya taba ta......" "Haba-haba Askirama! Kada bacin rai ya kai ku ga yi masa mugun fata, ni na tabbata ko Yarima na neman mata bazai nemi na cikin gida ba balle Sa'adatu kanwar sa, don Allah a kyautata masa zato, kada a raba shi da aikin sa he is very young da karbar sarauta yanzu, sannan kaima in ka zauna a gida me zaka yi? Da cikar lafiyar ka da shekarun da basu kai 70 ba. A yi masa hakuri ayi masa addu'a, ita ce kawai mafita. Kuma daga Sa'ade ta fadi abu ai bai kamata mu yarda ba tunda bamu gani da idon mu ba". Mai Askira yayi murmushi mai ciwo "baki san Yarima ba!"
Da kyar, da lallashi da ban baki Fulani ta ciwo fushin maimartaba ya fasa cewa Yarima Sageer ya dawo gida, amma ya ce dole zai dauki mataki. Shi ya gama amincewa Sa'ade ba karya take ba, ta fadi abinda ta gani ne da abinda ta ji tabbas. Koda ya tura Sa'ade gidan Yarima yana da dalilin sa, gashi tun ba'a je koina ba zuwan ta ya sa yanzu ya san halin da Yarima yake ciki.
****
Da asubah Fulani ta koma daki ta kira Sa'ade, wadda ta kwana zungurgur a bakin kofa, ta dade bata ji ma'auratan sun gama fadan nasu ba, ta ji abubuwa da yawa da suka razanata, Sultana ta dage in ya takura mata akan shan giya to zata koma addinin ta na Jew (ridda). Shikuma ya ce ta koma din, amma ta sani muddin ta bar muslunci a bakin auren ta. Zina