Showing 27001 words to 30000 words out of 117873 words

Chapter 10 - Masarautar Mu 1 to 4 Complete

Fulani tace "to ina ruwan ki da ko su waye? Ko maza na soma kawowa? Wallahi ki kiyaye ni bana son gulma, ba ruwan ki da duk abinda bai shafeki ba a gidannan don kuwa ba gidan ubanki bane, kara ki Uban su yayi". Hawaye suka ciko idon Sa'ade, ba yau Fulani ta soma cin mutuncin ta ba akan kankanin abu, amma sai ta ji na yau ya fi na kullum kona mata rai, ta yi alkawarin ta daina mayarwa Fulani magana amma tsabar bacin rai bata san sanda ta ce cikin hawaye.
"Tunda kin ce inada dan uwan uba ki kaini wajen sa mana!"
Fulani tace "an ki a kaiki, anan zaki zauna zaman AGOLANCI. Zaman da ubanki yake guje maki, gashi ya same ki bayan ran sa. Enjoy!".
Ta fice ta rufo mata kofar da karfi.
****

Ya Gumsu ta dubi Yarima yana shigowa babban falon ta, bayan dawowar su daga masallaci sallahr isha. Hararar sa ta yi cike da kauna da jin haushi, ba karamin haushi ya bata ba da ya ja kannen sa suka tafi sassan Bilkisu suka shantake bata san uwar da suke yi ba, abinda bazata taba lamunta bane wata alaqa ta shiga tsakanin Yarima da Fulani Bilkisu shima a sammace mata shi yadda aka sammace uban sa.
Yana zama ta soma fada Ya Maira na taya ta "ka san tsakanina da ita ne da zaka je ka rashe a unguwar ta har ta baka abinci ka ci? Meye hadin ka da ita? Gara kowa da ita, ita ce annamimiyar gidan nan bakidaya, kai bako ne baka san komai ba don haka ka tsaya a matsayin ka na bako. Ka kama 'yan uwan ka da na haifa kadai, ban yarda da wani hadin kai na munafunci ba kowa ya zauna da wanda uwar sa ta haifa".
In da sabo ya saba da halin mahaifiyar sa na kishi da korafi akan abokan zamanta, don haka bai wani damu ba har tayi iya fadan da zata iya ta bari, ta koma hirar arziki. Duk abubuwan da ke faruwa a gidan sai da ta labarta masa wanda ya shafe shi da wanda bai shafe shi ba. Har labarin Bilkisu ta dauko 'ya daga inda basu sani ba tana boyewa a sassan ta saida ta bashi "sabida ada haihuwa ta ki tsaya mata. Ka ga 'yar? Don an ce suna kama sosai" "ni ban ga kowa ba" ya fada (sounding uninterested). Sannan ya mike ya ce da ita zai je ya kwanta don a gajiye yake sosai, yau sun sha yawo.
A matsayin ta na mai girki ita ke da turakar maimartaba yau. Lokacin shigar ta na yi ta bar Ya Maira da yaranta ta tafi kasancewar anan zasu kwana sai gobe zasu koma Biu. Da sallama ta shiga ta samu Alanguburo yana addua ya fuskanci alkibla. Saida ya gama ya shafa sannan ya ankara da shigowar ta dakin. Ya dube ta daga inda yake zaune ya soma magana cikin yanayin data kasa fassarawa.
"A tabbatar duk bayin da aka zubawa Yarima babu mata a ciki, maza kadai na yarda suyi masa hidima har ya koma".
Yanayin fuskar Ya Gumsu ya nuna bacin rai tsantsa, har sai yaushe Mai Askira zai daina yiwa Sageer kallon tsohon laifin sa? Abu an yi shi tun kuruciya amma har gobe dan ta mai laifi ne dan kowa tsarkakakke. Dubi Yarima don Allah wanke hannu ka taba me zai yi da wasu matan bayi? Ya Gumsu ta juya kai cikin takaici tace "to ayi masa aure mana! Wannan irin takunkumi haka!" Sarki ya karanto tarin bacin ran da ke cikin kalamanta, kuma ta yi maganar ne da alama ta dade ta na cin ta a zucci. An kai mata Da wata uwa duniya an yasar ba wanda ya damu da halin da yake ciki, kuma a yanzu ma ana nufin ya koma babu aure ko me? Ta san duk laifin Waziri ne, don sai abinda ya ce Askirama ke amfani da shi, idan kuwa bai ce lokacin Auren Yarima yayi ba Mai Askira ba zai taba zancen auren nasa da kansa ba sabida kawaici irin nasa.
"Me kike ci na baka na zuba Fulani! Akwai abinda nake jira ne, zuwa wani dan lokaci da zai dawo gida bakidaya".
Nan da nan fuskar Ya Gumsu ta washe, wani farin ciki ya bayyana akan kyakkyawar fuskar ta. Ta gyara zama tace "Alanguburo sai a san daga masarautar da ya kamata a dauko masa mata tun yanzu, ni in son samu ne na fi son masaurautun wajen Borno, kamar Kano da Bauchi, su ne kawai zan ce masarautun su sun fi namu, kuma auratayyar mu da su zai karawa masaurautar Askira kima a sauran masarautu tsararrakin ta".
Sarki Yausufu sauraron ta yake absent-mindedly a daidai lokacin da wani bakon tunani ya bakunce shi. Ya Gumsu sai gani ta yi ya miki zuruf! Kamar an tsikare shi ya nufi hanyar waje. Sai kawai ta biyo shi don abu ne da bai taba yi ba fitowa a lokacin da ya riga ya shiga barci.
Sai gani tayi kai tsaye ya doshi sassan Yarima Sageer cikin takun shi na alfarma. Yana so ya tabbatar da idanun sa. Yarima lafiya yake zaune ko yau ma ya kama 'ya'yan mutane ya danne.
Dogarawan da ke gadin bangaren Yarima tuni suka wangale kofofin suna bawa Sarki da Ya Gumsu hanya, da suka doso dakin barcin Yarima sai maimartaba ya dauke karar sawunsa, sadaf-sadaf yake takawa yayin da Ya Gumsu tashin hankalin bata san me Yarima yake ciki ba ya dugunzuma zuciyar ta. Sarki na zuwa ya danna kai dakin da ya tabbatar yana ciki, sai ya same shi bisa darduma yana sallah.
Ya Gumsu na iya jin nannnauyar ajiyar zuciyar da Alanguburo ya sauke, ya yarda ko Yarima bai daina halin sa gabadaya ba akwai improvement kashi 70% cikin halayen sa na yanzu, wanda ya kara masa karfin gwiwa akan sabon tunanin da ya bakunce shi a daren yau ba tareda ya taba kimsawa zuciyar sa ba. Ya kudure kafin ya gabatar da kudirin sa ga kowa zai yi istikhara ya nemi zabin Allah.
Juyawa yayi ba tare da ya ce komai ba, itama Ya Gumsu ta bi bayan sa. Da sa'an maganarta ne cewa zata yi "a dai dinga kyautatawa dan adam zato". Da ba sa'an maganarta bane sai ta kumshe abarta a cikin ta tana kunkuni cikin ranta "haka kawai kamar shi kadai ne fitinannen da a gidannan". Ta manta cewa adadin soyayyar ka akan mutum, adadin damuwar ka gareshi. Sannan 'ya'ya ababen kiwo ne ga iyayen su wannan umarnin Ubangiji ne.
Mai Askira bai kwanta ba a ranar sai da ya gabatar da sallahr istikhara akan kudirin dake zuciyar sa. Ita kuma Ya Gumsu ta kwana zuciyarta kal, a kalla dai daga yau zai sassauta zargin Yarima a ransa.
****
Kwana biyu kenan Sa'ade da Fulani basu hadu ba, kowacce fushi ta ke da 'yar uwarta. A jiya Yarima ya kara shigowa kamar yadda yayi alkawari amma bai dade ba Ya Gumsu ta ishe shi da aiken kira dole yayi sallama da Fulani ya tafi. Yau dai Sa'ade ta yiwa kanta fada bata yi musu labe ko leke ba, amma tana jiyo tashin sautin muryar Yarima mai kauri da zurfi (husky) a lokacin da yake magana da Fulani. Ta fahimci ko ma wanene bakon nan mai matsayi ne sosai a gidannan, tunda har yake shiga ko'ina ba shamaki.
"Idan ka kara shiga unguwar ta Allah ya isa ban yafe maka ba!"
Ya Gumsu ta fada a zafafe tana numfarfashi, munafukar baiwar ta ta gaya mata abinci Bilkisu ke bashi yana ci wanda basu san me aka zuba a ciki ba.
A firgice ya dago ya dubi Ya Gumsu. "Me yayi zafi haka Ya Gumsu?" Ta harareshi kamar idanun ta zasu fado, ai har gara ya likewa Hibbani akan Bilkisu, itace ta dauketa mutum take kuma bata girmanta na Gumsun gari, ba wannan mai yiwa kowa kallon bai isa ba, bayan bata aje musu komai ba sai katon kashi da 'yar da ita da babu duk daya.
"Ubanka ne yayi zafin, nace Ubanka ne yayi zafin Yarima!". Ba shiri ya sadda kansa, amma hakika ya firgita da kalamanta, ya kuma tabbatar kishin ta da Bilkisu ba dan kadan bane don sauran matan ma ai ya shiga unguwar su amma ko sau daya bata yi magana a kai ba.
"Allah ya huci zuciyar ku Ya Gumsu, in kun yi hakuri ni da ba mazauni ba tafiya zan yi babu mai sake gani na nan kusa". Ya juya ya fita ba tare da ya bi ta kan abincin data shirya masa ba.
Koda ya koma bangaren sa ransa a bace yake, baya son wannan halin na Ya Gumsu tun yana karami, balle yanzu da ya girma ya mallaki hankalin kansa. A ganin sa a matsayin ta na babba kuma Gumsun gari kamata yayi ta kama girman ta ta rungume kowa dake karkashin sarki, tunda shi ya dauko da kansa ya kawo ya hada cikin iyalin sa to tabbas yana so ne.
Ya samu sako daga jakadiyar sarki cewa maimartaba yana son ganin sa gobe kafin ya shiga fada.
Wanka ya shiga sannan ya fito ya sauya zuwa pajamas, Awaisu ya kira a waya yana daga tsaye jikin taga "kana ina ne?" Awaisu yace "gani nan tare da Ba'ana (mahaifiyar sa) tana min hira, amma yanzu zan taho, hirar tata dai duk guda daya ce tun isowar mu bata wuce ta aure, wai har matar ta zaba mini" murmushi Sageer yayi, ya ce "ai gara a taimakeka a lullube a kaiwa wata mai tsautsayin, in ba hakan ba a haka zaka tsufa baka taba morar kuruciyar ka ba". Awaisu ya ce "gara in tsufa a hakan dai, Allah ya gani ban taba 'yar kowa ba balle in na haifa a taba min tawa". Sageer ya san magana ya gaya masa don haka ya cillar da wayar bayan ya ce da Awaisu "don't show me your ugly face, sai na neme ka"..
Washegari bayan ya shirya cikin sababbin dinkunan da maimartaba ya aiko masa dasu, sai kamshin invictus ke tashi a dakin, ya fuskanci alqiblah ya sallaci sallahr Dhuha. Idan akwai wata dabi'a mafi kyau cikin dabi'un Yarima Sageer to sallahr farillah ce akan lokaci da kokarin yin nafilfili babu gajiyawa. Ba ya yin sallahr farillah kadai ba tareda ya hada ta da nafila ba. Sannan sallahr "Dhuha" bata wuce shi komin busyn da yake ciki.
Karfe tara daidai ya tasamma turakar mahaifin sa, inda duk ya gifta sai ya bar kamshin turaren sa Invictus (Paco Rabbanne). Inda duk bayi suka ci karo da shi sai sun fadi sun yi gaisuwa sun yi masa kirarin da suka saba yi masa, a haka cikin takunsa na kasaita da sassarfa har ya isa falon da sarki ke ganawar sirri da iyalin shi.
Tare da Ya Gumsu ya same shi yana karya kumallo, ta sha ado cikin koriyar laffayan matan Kanuri, bai taba ganin Ya Gumsu da wata suttura da ba laffaya ba, da alama yau maimartaba cikin nishadi yake, nishadin nasa baya rasa nasaba da kyakkyawan sauyin da ya gani a tare da Sageer tun zuwan sa, da kuma na kyakkyawan kudirin dake zuciyar sa. Yarima Sageer ya zube yana kwasar gaisuwa wajen iyayen sa, su kuma suna amsawa with so much affection wanda ya bayyana karara akan fuskokin su, maimartaba ya zuba masa ido cikin murmushi ya ce.
"Kamar ba Sageeru na ba, Sageer wanda ya tafi ya barni dan firit da shi kamar a bushe, wannan dake gabana ai babban mutum ne wanda ya kamata ace zuwa yanzu ya ajiye mata hudu da kwarkwarori a gefen sa".
Murmushi mai kayatarwa Yarima yayi, wanda ba kasafai ya ke yin sa ba, ya sake sunkuyar da kansa. Sarki Yusufu ya dan tsura masa ido kafin ya kira sunan sa cikin sigar son ya bashi hankalin sa.
"Muhammad Sageer. Kafin mu yi kowacce magana ta aure ce kan gaba, yanzu babu abinda nasa a gaba banda burin auren ka. Duk wani kyakkyawan kudurin mu akan ka ya cika. Ina fatan zuwa yanzu ka samu nutsuwar da kake ganin zaka iya zama da iyali?"
Yarima ya muskuta cikin jin nauyi, kansa a kasa bai ce komi ba, aure baya gaban sa ko kadan, don a ganin sa yanzu ne yake cikin twentieth din sa, ya ke cin kuruciyar sa da duk irin macen da yake so, aure zai zamo tamkar takura ne da takunkumi a gare shi, amma what if Maimartaba zai yarda ya auri zabin ran sa, Rose? In ita ya aura bazata takura masa ba, zata bar shi ne yayi rayuwar sa yadda yake so.
Ya ga cewa wannan itace damar sa ta karshe da zai samu ya gabatar da zancen ta. Idan wannan damar ta wuce mawuyaci ne ta sake zuwa. Don haka ya tattaro dukkan courage din sa, ya ce. Ya gyara zama ya fuskanci Baban sa.
"Alanguburo (Allah ya kara maka yawan rai) akwai yarinyar da na yi wa alkawarin aure a can Amsterdam, kusan shekara guda muna tare".
Sarki Yusufu ya ji gwiwar sa ta yi sanyi, kuzarin jikin shi ya kare. Me yasa ya fara tambayar sa kafin ya fada masa na sa kyakkyawan kudurin akan sa? Yanzu duk abinda zai ce bayan wannan da Yarima ya fada zai zamo tamkar yayi imposing dinsa ne ga auren da baya so, tunda ya ce yana da zabin sa tuntuni, zai zama auren force....wanda baya cikin tsarin sa, bai taba yi wa 'ya'yan sa auren dole ba daga matan har mazan. Kenan dole a matsayin sa na Uba mai muhimmanta hakkin farin cikin 'ya'yan sa da ya rataya a wuyansa kuma shugaba mai adalci ya bawa Yarima dama ya auri zabin ransa. Kamar yadda nasa iyayen suka yi masa.
"Kana da damar auren zabin ranka Yarima, Allah yayi albarka".
Ya Gumsu ta tattare gira tace "haba Mai Askira? Haba Askirama? Haba gatan Askira? Yaya ba'a binciki gidan da ya nemo auren ba za'a amince masa da gaggawa haka???"
"Ko a ina ya nemo in dai yana son ta shike nan"
Yarima ji yayi kamar ya rungume Baban sa, saidai duk da haka yana cike da fargaba, shin mai Askira zai amince ya bashi goyon baya idan ya ji cewa Rose bayahudiya ce wadda bata da addini koda na kiristanci ne?
Ya Gumsu ta kasa hakuri, ta ce a kagare "sai ka fada mana su waye iyayen ta, 'yan wace masaruta ne? Sannan daga wace kabila ta fito?"
Jin Alanguburo bai ce komai ba ya fahimci shima yana son jin amsar.
Mu karasa a littafi na biyu. Tare suke.
Taku har abada: Takori






MASARAUTAR MU!






2



Littafin







SUMAYYAH ABDULKADIR



SADAUKARWA
Ga Bilkisu Askira, (Billie Askira), Maiduguri, sabida gudummuwar ki yayin rubuta wannan littafi.

JINJINA
Har kullum jinjinar taku ce dukkan members na TAKORI'S ONLINE FORUM whtspp, littafin MASARAUTAR MU jinjina ne a gare ku, nagode da kauna da kwarin gwiwa, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah. You are my source of inspiration.

GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba batare da iznina ba, tun daga radio, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne daga

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login