Showing 93001 words to 96000 words out of 117873 words
kawai ya daura zuwa gwiwoyinsa, ta hango wani ingarman physique chestna manyan maza wanda ya sanya ta ba shiri ta sunkuyar da kanta.
Lokaci guda jikinta ya dauki rawa da makyarkyata lokacin da Yareema ya tako zuwa gabanta.
Kamshin bathrobb din da ya yi amfani da shi na desire dunhill ya bakunci hancinta. Saadatu Hashim, tayi saurin sunkuyar da kan ta cikin neman taimakon Allah ganin irin kallon da Yarima ke mata. Kallo ne mai aika sakon kiran miji zuwa ga matar sa. Ya kira sunanta da wata siga da bai taba kiran ta da ita ba wanda hakan ya sa ta dago ido a hankali ta dube shi, idanun ta na ragaita, ya kama dukkan hannayenta ya mikar da ita tsaye, hannayensa sarke cikin nata.
Ya ce, Saadatu hakurina ya gaza, na yi alkawarin da ba zan iya saukewa ba, Im so sorry Saadatu. Na daga kafar iya yadda zan iya, kuma na tabbatar kin samu tsarki, ki yarda ba zan cutar da ke ba, kuma ba zan hana ki karatunki ba, sannan zan bi hanyar da ba za ki samu ciki yanzu ba.
Ki yi hakuri Saadatu, hakkina nake so na aure a daren yau ba sai gobe ba Saadatu, I promised you it will only be sweet, not hurting akwai barazanar da nake fuskanta wadda tasa dole zan tabbatar da aurena a yau.
Saadatu ta soma kuka, Yaya Yareema ni ban shirya ba, na karanta a biology (reproduction) yana faruwa ne sanadin haka in na zo haihuwa mutuwa zan yi. Im only 19 years.
Daga yadda jikin Yareema ke kyarma ta tabbatar yau ba ta da maceci sai Allah. Kalaman fatar bakin ta sun yi kadan su sa Yarima fasa abinda yayi niyya.
Cikin wata sassanyar murya ya ce, Saadatu hakuri za ki yi, ni ma ban shirya hakan a yau ba, amma ba zan bari a raba ni da ke ba, dole in tabbatar da ke matsayin matata a daren yau.
Iyayenmu har shekaru sha hudu ana musu aure, kuma suna haihuwa lafiya tambayi Fulani shekararta nawa sanda ta haife ki.. and he began from there... with very hot and irresistible kisses..Saadatu roko ta ke tana magiya, amma kamar tana kara zuga Yareema Sageer ne.
To ka bari in ci abinci?
Ta fada cikin ragaitacciyar murya jikin ta na kara karkarwa. Kafin kukan ya kwace mata gabadaya.
Ya soma warware mata laffayar idanunsa ko buduwa ba sa yi, Abinci? Abinci fa ki ka ce Saadatu? Im sorry ki ba ni only two hours in ba haka ba zan cutu Saadatu.
Da ta ga ba sarki sai Allah, sai ta mika lamarinta ga Allah. Hawaye na bilbila, in wuya ta yi wuya ta kira sunan Fulani, yau har Hanne da Raheema sun sha kira da neman taimako daga bakin Saade. So it was with every woman. Cikin awanni biyun da Yareema Sageer ya ambata, ya mayar da Saade cikakkiyar matarsa, wadda ko mutuwa ya yi sai ta yi masa idda.
Bayan samun nutsuwarsa bai juya mata baya ba, rungume ta ya yi with utmost devotion and affection wanda baki ba zai iya fassarawa ba. Tunda yake biye-biyen matansa, farare, jajaye da bakake, da aure da ya yi na shekara da shekaru bai taba zama sexually satisfied irin yau ba. Rayuwarsa daga ranar ya tabbatar ta juya zuwa anotherdirection, zuwa sabuwar rayuwa wadda babu sauran sabon Allah a cikinta.
Saade na kuka, Yareema na lallashi, ta rantse cikin daren nan sai ya maida ita Askira, bazata kuma zuwa gidan sa ba, ashe haka auren yake bata sani ba? Kuma ya rasa da wa zai yi sai ita kanwar sa da aka bashi amana don kawai ita ba Askirama ne ya haife ta ba? Kuma ta rantse sai ta gayawa Fulani komai. Wani abun in ta fada dariya Sageer yake amma a cikinsa, yadda ta ke a fusace din nan daren yau za ta iya kai duka, tunda cizo da yakushi ya sha su har ya gode Allah.
Na ji duk abinda kika ce Saadatu, na ji ni dan ne, amma na Saadatu da Aisha-Sultana kadai, na amshi laifina ki yi hakuri ki yafe min, rayuwar will not besmooth ba tare da wannan din ba, baki ji ba yanzu duk wani tension da ke kaina ya fita, duk wata damuwa ta gushe, babu komai a rai da zuciya ta sai SAADATOUH,and I want to use this mediumin gaya miki tun daga karkashin zuciya ta cewa;I love you very- very muchhh!.
Yadda ya furta kalaman na karshe har cikin ruhin Saade, ta ci gaba da kuka ba ta ce komai ba. Har ya je ya hada ruwa ya dawo ya dauke ta ya sanya a jacuzzi idanun Saade a rufe suke suna bulbular da hawaye.
Idan wannan ita ce rayuwar diya mace hakika ta jinjina wa mata. Duk wani taimako da ya kamata miji maabocin kulawa ya nuna wa matarsa, Yareema Sageer ya nuna wa Saade daren yau.
Abincin kuma da ya ce ta ci bayan sun kimtsa, cewa ta yi ba za ta ci ba, sanda ta ce zata ci ai bai saurare ta ba. Ya yi juyin duniya ta ki, sai kuka.
A haka suka kwana, washegari ko waya bai kunna ba, tunda ya yi wanka ya tafi falo ya barta a dakin, ya kunna talabijin domin ya gaji da lallashin. Ko yaron goye nan ya ga Saa ya barta wajen kukan banza.
SAADATU SAAR MATA!!!
Yareema Sageer ya fada a fili, yana tuno kalaman Mai Askira.
Za ta dauke kwadayinka a kan sauran mata tunda Bilkisu ce ta haife ta matan Baggara ne don manya aka halicce su.
Murmushi ya yi yana jin kaunar mahaifinsa na kara ratsa shi. Sai kawai ya dauki wayarsa a gefe ya kira Maimartaba.
Da kyar ya daga wayar tashi, sabida a ganinsa Sultana ta ci gaba da kafirci ne da sakacin Yareema. Ga shi an ce Da na kowa ne ba zai so ya sa shi sakinta ba. Amma Allah ya gani auren Aisha da Yareema ya fice masa a ka. Damuwarsa ita ce irin tarbiyyar da za a bai wa yaya idan Allah ya kawo.
Ciki-ciki Mai Askira ya amsa gaisuwar Yarima, shi kuma excitedly yake bayyana masa dalilin kiransa da ya yi
Godiya marar adadi da ba shi auren Saadatu, ya kuma yi alkawarin rike aurenta da daraja da amana har karshen rayuwarsa. A karshe ya dora da bada hakuri a kan Sultana, ya ce, ya dauki matakin kaurace mata har sai ta daina shan giya.
Idan ba za ta iya dainawa ba ya ce ta tafi garinsu. Wannan hukunci ya sanyaya ran Askirama har ya sanya musu albarka, ya kuma ce ya saya wa Saadatu waya mahaifiyarta na cikin kewarta, ga shi ta bar wayarta a nan dakinta na Unguwar Fulani Bilkisu.
Yareema ya ce, A nan inda muke ba za a samu waya ba, amma in mun koma Abujan zan saya mata.
Mai Askira ya ce cikin tsokana.
An bar kasar ke nan zuwa shahar asal (honeymoon)?
Yareema ya yi murmushi cikin jin kunya yana shafa kai, ya ce,
Aah Alanguburo muna cikin Nigeria. Na kawo ta ta ga dabbobi ne, a nan Yankari Game Reserve.
Askirama ya yi dariya, idan yana magana da Sageer mantawa yake shi Sarki ne. He so much love him, zai iya komai don ya faranta masa ko da kuwa kara masa wata mace ne bayan Saade in dai har zai nutsu ya tsaya a kan matansa na aure.
To a ga dabbobi da kyau. Ina gaida Giwayen Yankari.
Dariya Yareema ya yi, sannan suka yi sallama cike da begen juna.
Ya koma dakin, Saade na kwance har yanzu yadda ya barta abincin da aka kawo musu ko tabawa ba ta yi ba. Da ya duba sai ya ga bacci ne ya dauke ta, ga busasshen hawaye a fuskarta, ya tsugunna ya sumbaci goshinta, sannan ya hau kintsa kayansu da ya yi watsi da su a dakin daren jiya.
Jinya sosai har ta kwanaki uku cif! Yareema ya yi ba shiga ba fita, ko kofar falo ta ki fitowa sai a rana ta uku ne ta yarda ta ci abinci ta koshi, amma a tsayin kwana uku oldenburger fresh milk kawai ta ke sha a Yankari.
Ranar da ta dan soma walwala, Yareema bai yi kasa a gwiwa ba ya sake kalallame ta ya maimaita laifinsa.
Sai dai wannan karon ita kanta ta san da bambanci. So sweet, so gentle. Kafin su bar Yankari cikin kwanaki bakwai Saade an zama manyan mata. Ta iya dauke wa mijinta Yareema Sageer Yusuf Askira lalurar da mata hudu ba za su iya dauke masa ba. Sun dinke sun zama miji da mata na haqiqa mafiya kusanci da juna, maabota soyayyar da biro ya yi kadan ya bayyana ta.
Sai a na i-gobe za su tafi ne suka zaga wild life na cikin Yankari Resort, Saadatu ta ga dabbobi iri-iri a fili, wadanda sai a talabijin ta ke ganinsu. Ta baro Yankari with nostalgia, ta sanya zamanta na amarci na dan lokaci a Yankari cikin kundin tarihinta as the beginning of the beginning na kafuwar rayuwarta da maigidanta Yareema Sageer Yusuf Askira.
******
ABUJA
Sun dawo Abuja ranar lahadi da yamma. Saade ta saki baki tana kallon yadda aka canza komai na gidan da ROYAL ONE. Duk abin da ke cikin gidan zubin na sarauta ne, sarauta ta zamani mai tafiya da boko.
Ta karaso cikin main parlour tana latsa cushion din Royal Chairs din da suka yi wa dakin kawanya. Komai ya burge ta beyond her taste, beyond her expectation. Da Yareema ya ce za a yi refurbishing gidan ne shi ya sa suka tafi Yankari ba ta taba zaton gyaran zai kai kayatuwar haka ba. Once again, she simply fall in love with her humble abode (ta fada a matsananciyar soyayyar gidanta).
Tunanin me ya kamata ta fara gyarawa ta tsaya yi. First of all zata gyara zaman kujerun. Su kalli juna madadin yadda aka ajiye su. Ta daga kai tana kallon hoton kyakkyawa Fulani Bilkisu cikin alkyabba da aka kafa mata a bangon gabas maso kudu na falon, ta saki murmushi ita kadai murmushin farin ciki. Ta matsa a hankali zuwa ga hoton, ta kai hannu ta shafi fuskar Fulani a hankali tana murmushi, lebbanta suka furta,
Ina kewarki Fulani ba dan kadan ba.
Ba ta san Yareema ya shigo jaye da trollies dinsu ba, yana tsaye daga bayan ta, ya ce, Me ki ka ce?
Ta juya ta yi masa wani kallo na kasa-kasan ido, sannan ta zumburo dan bakinta gaba ta ce, Na ce ne Im missing her Prince, don Allah yaushe za mu je Askira?
Dariya ya yi tare da mika mata kwalin wayar da ya sayo a hanya yana fadin,
Ke da Askira sai na ga kina daga kafa da kyar, kina tafiya da kyar, sannan kina tashi da kyar.
Ya karaso ya kama hannayenta ya sanya mata kwalin wayar, ya ce,
Call your Mum, anytime.
Har da dan tsallenta don farin ciki, ta makale a gefen kafadun Dr. Sageer ta na fadin,
Na gode Prince.
Dakin barcin Sultana na da nan ya kai mata kayan. Ya ja hannunta suka shiga dakin. Saade sai da ta rike numfashinta sakamakon ganin irin dankara-dankaran Royal furnitures da Maimartaba ya zuba mata. Wanda sai yayan sa su Ya Maira kadai zai iya yi wa. Hawayen farin ciki suka zubo mata, ba ta san sanda ta juya ta rungume Yareema Sageer ba.
Ka taya ni godiya ga Alanguburo, Allah ya kara yawan rai, ya kara nisan kwana mai albarka. Ya gama yi min duk wani gata a rayuwa.
Yareema ya rike ta sosai a cikin hannayensa, sannan ya ba ta kyakkyawar sumba saman idanunta. Yace.
Nima ya gama min kowanne gata a rayuwa, tunda ya bani ke a lokaci mafi dacewa. When my heart was bewildered. Na kasa tunkarar ki in ce ina son ki, haka na kasa tunkarar kowa don ina ganin Im not good enough to have you.
Bansan ni da ke wa Askirama ya fi so ba.
Dariya ta yi ta zame daga cikin rikon sa, cikin jin dadin kalaman sa, aah Prince. Blood is thicker than water, ni ce ma yakamata in ce Im not good enough to haveyou, ni da ba yar kowa ba, ba yar sarau!. Yarima yayi saurin toshe mata baki da nasa in such a waythat hakan ya sa ta hadiye abinda ta yi niyyar fada cikin cikin ta, ya kuma kalubalance ta da cewa;
watarana ruwan yana fin jinin kauri Saadatu.
A daren ranar suna cin abinci yake cewa, Saadatu in na tafi na barki ke kadai a gidannan sai maaikata, babu matsala? Zan sake yin tafiya ta tsayin kwanaki uku.
Da sauri Saade ta sake cokalin hannun ta, damuwa ta bayyana karara a kan kyakkyawar fuskarta. A dan zaman da suka yi tare a Yankari game reserve ta saba da Yareema Sageer fiye da tsammani, ya shiga zuciyar ta fiye da kintace. Tace tana son shi ma bata baki ne and is not enough to express the feelings
Zuwa ina kuma Prince?
Muryarta ta nuna tsantsar damuwar data fada.Yareema Sageer ya kamo hannunta ya dunkule cikin nasa, suka zauna a tare a gefen katafaren gadon Saaden, ya sassauta murya cikin lallashi,
Its a promise ba zan wuce kwana ukun ba, zan kai Aisha-Sultana ganin gida ne.
Wani abu ya zo ya tokare a kirjin Saade, wanda a nata sanin yafi komai zafi a zuciyar diya mace, a hankali ta janye jiki daga gare shi,sannan cikin karayar murya ta ce,
A dawo lafiya!.
Yareema ya sanya fuskarta cikin tafukansa, yana kallon fararen kwayar idanunta, ga mamakinsa idanunta sun cika taf! Da kwallah, kada dai Saadatu ta fara kishinsa? Babban burinsa kenan ta so shi irin yadda shi yake sonta.
“Look at me Saadatu, na yi tafiya da ke mun yi kwanaki bakwai, ita ma tana da hakki a kaina, so ki yi hakuri in je in rakata, na yi miki alkawarin ba zan wuce.
A hargitseSaadatu ta mike.
Ka ji na ce wani abu ne Prince? Ko na ce Aunty Sultana ba ta da hakki a kanka? Ko me ye damuwata a ciki don ka dauki matarka kun tafi kun bar ni jiran gida?
Ta juya masa baya a kokarin ta na boye hawayen ta.
Yareema Sageer yana daga zaune yana kallonta ban da murmushi ba abin da yake yi. She never talked to him in this manner (cikin tsiwa). Saade ba ta ankara ba ta ji Dr. Sageer ya sure ta yana juyi da ita a tsakiyar dakin, kafin ya dire ta a tsakiyar gadon su ya koma samanta, ya dora mata dukkan nauyinsa gabadaya.
Say it againba ki da damuwa don na dauki matata mun tafi Korea, to su wadannan hawayen kuma na mene ne, ya ya sunansu? Zan so kwarai in san maanar su.
Saade ta runtse idonta hawayen na ci gaba da bulbula. Kamshin INVICTUS da ya riga ya kama Yareema ya soma hargitsa ta. Yana tada tsigogin jikin ta. A hankali Yareema ya soma kissing dinta from head to toe, lungu-lungu, sako-sako, kusfa-kusfa, kafin dan lokaci Saadatu ta fice a hayyacinta.
Abin da ya biyo baya mai nauyi da girma ne da ya shallake tunaninsu. It was kind of gentle romance da ya gudana da hobbasar Yareema shi kadai, yayin da Saade ta sakar masa komai, gangar jiki, zuciya da ruhi, sai yadda ya ga damar sarrafa ta.
Daren ya zamo cikin dararen tarihi a rayuwar amarcin ta, dare ne da daga Sageer har Saadatu, bazasu taba mantawa ba.
Washegari suka yi shirin shiga makaranta. Saade ta yi tsaf cikin doguwar rigar atamfar chiganvy kalar pusher pink, ta yi lullubi da mayafi kalar kayanta wanda ya ciza sosai. Kallo daya Dr. Sageer ya yi mata yana shigowa dakin nata yana daura agogon hannunsa na danyar zurfa samfurin (Gucci) na maza, ya girgiza kai ya ce,
Ai da sake. Ba ke ba fita da irin wadannan mayafan Saadatu, ko dai ki sa hijab ko ki koma gado ki nade ki kwanta.
Saadatu ba ta kula shi ba, don ba wai ta huce daga fushin tafiyar da ya ce zai yi da matarsa ba ne, duk da duniyar soyayyar da ya dauke ta ya luluka