Showing 72001 words to 75000 words out of 117873 words

Chapter 25 - Masarautar Mu 1 to 4 Complete

matar sa. Daga nan ku zarce BAR din ke da ita ku sha ku yi mankas ku dawo gida ina jiran ku. Na bar ki lafiya sai mun hadu a kauyen naku na Tsanyawa in kin gudu, amma ina rokonki don Allah in kin tashi gudun, ki fi ruwa gudu.
Ya zuba hannuwa cikin aljihu yana kara jifarta da killing smile dinsa wanda shi kadai ya iya abunsa, ya kuma san maanarsa.
Bai tsaya sauraron amsarta ba ya juya cikin sassarfa da takunsa na haiba da mulki ya bar falon. Ya bar Saadatu a tsaye kamar an kafe ta a wurin. Ta kai hannu ta shafo kasan lips dinta a hankali. Damshin yana nan. Haka kamshin mouth freshner din bakin sa yana nan. Shin abin da ya faru yanzun da gaske ne ko a mafarki ne? Ta yi kissing da mijin auren tafor the first time a rayuwar ta? Kuma ba kowa bane Uncle Yareema ne, guardian din ta na NTNU Dr. Sageer Yusuf Askira?
Ta fi karfin minti goma a tsaye, ta kasa maida nutsuwarta, ta kasa yardar wa kanta abin da ya faru ba mafarki bane, ta dauki everything as an illusion. Kafin ta ja matattun kafafunta ta zauna. Me wannan ke nufi tsakaninta da Yareema Sageer? Ba dai wannan shi ne rayuwar kusancin da ake nufi yanzu zasu yi tare har abada ba, maimakon tasu ta Guardian da step sister irin ta baya?
Koda take yarinya karama ta san me aure yake nufi a darasin biology. Kawai sai ta ji kuka ya kwace mata. Shikenan ita tata ta kare. Ta zauna a dandaryar kafet ta yi kukanta mai isarta. Kanta cikin cinyoyinta, kan ta har sarawa ya shiga yi.
Fanna da ke jiran fitowarta daga daya falon, ta ga fitar Yarima da sassarfa da jimawa, da ta ji shiru-shiru Saadatu ba ta fito ba, sai ta biyo bayanta ta same ta a zaune tsakiyar kilishin falon tana ta kuka.
A zuciyarta ta ce, Dole ki koka Saadatu, wannan mutumin ya fi karfinki ta koina. Da dai sun barshi da bayahudiyar matarshi ita kadai zata iya dashi, amma ina innocent yarinya irin Saade ina fitinannen Yariman Askira? Tun suna yara suke da labarin sa cikin gidan nan, wa ya san irin rayuwar da yake yi a Abujar?
Fanna ta tsugunna da gwiwa bibbiyu a gaban Saade, cikin lallashi da ladabi ta ce,
Ranki ya dade ki yi hakuri ki tashi mu koma daga ciki.
Tana so ta gaya wa Fanna damuwar ta. Don ta san ita kadai ce a yanzu zata saurareta har ta fahimce ta. Ko ta fada mata abin da Yarima ya yi a gare ta yanzun nan, da abin da ya ce da ita, amma sai ta ji ta kasa. Maganar ta yi mata nauyin da ba za ta iya furtata ga kowa ba koda kuwa Fulani ce.
Ta mike cikin mutuwar jiki, Fanna ta kama hannunta suka koma ciki.
Ta gaban Fulani da su Inna Laure da ke zaune suna raba kayan daFulani ta diddinka musu suka wuce zuwa dakin Saaden. Fulani ta daga kai ta dube su. Idanun Saade jawur da alama ta ci kuka ta koshi. Ko me aka yi mata kuma? Fulani ta fada a ran ta.
Suka wuce zuwa dakin Saade inda suka tadda Hanne tana gyara dinkunan Saaden da aka kawo daga wajen dinki. Fanna ta koma bayan shigar Saade daki.
Bisa gadonta ta haye ta ja duvet ta rufa har saman kanta. Ba ta son magana da kowa, don ko Hanne ba ta jin za ta iya gayawa abin da Yarima ya yi mata wanda ya kara tsoratata da auren.
Ita ma Hanne har ta gama abin da ta ke ta yi wa danta shirin kwanciya ba ta tambaye ta komai ba.
Fulani ta so ta kira ta don ta ji dalilin kukan da ta fahimci ta yi, wata zuciyar ta hane ta. Gara ta bar Saade ta koyi rike sirrin auren ta yanzu girma ya hau kanta. In dai ba matsala ce wadda ta zama dole su sani ba.

Washegari duka gidan ya rikice da hayaniya ana shirye-shirye. Kowa da ke cikin masarautar nan ya ci wa bikin nan na Yarima buri da alwashi don huce haushin wanda ba a yi ba a aurensa na farko.
Maimartaba ya aika da goron gayyata zuwa dukkan masarautun Borno guda bakwai, (Bama, Borno, Dikwa, Gwoza, Shani, Uba sai kuma Askira wadanda su suka hadu suka bada Borno Empire. Hakan nan ya aika da sakon gayyata har fadar Shehun Borno don haka Mai Askira ba karamin shiri yake wa wannan auren ba.
Duk wani gyara da ake wa amare na kayan mata Fulani ba ta yi wa Saade, banda Su dilke su halawa da dukhan kafin a mata lalle, (mai gyaran jikin Fulani daga maiduguri ta zo ta mata gyaran jiki), a cewarta Saade yarinya ce sai nan gaba in ta kara shekaru koda zata bata kayan mata, duk da tana tantama idan Yarima zai daga kafar yadda ya alkawarta. Kodayake fa bai bata cikakkiyar amsa ba akan hakan in zata iya tunawa cewa yayi zai duba.
Ta yi ajiyar zuciya cike da tausayin Saade, ta san duk ranar data shiga hannun Yareema sai Allah. Tunda dan Askirama ne.

Ranar talata, wato ana i-gobe sakun lalle Saade ta fito wanka tana busar da lallausar gashin kanta da dryer don ta cire wa kanta damuwar Yareema ko aurensa yanzu, ta hada su su duka ta zuba a kwandon shara, ta sa a ranta ba inda za ta yarda a kai ta, ko dai a barta nan a gaban uwarta ya koma gidan sa shi kadai yayi ta auren, ko ta bi su Innar Hanne su koma Tsanyawa ta yi zamanta a gidan su Hanne. Karatun ta hakura ta yafe in dai sai ta amsa sunan matar Yareema Sageer. Ina ita ina zama da yar giya matsayin kishiya? Ta je bar din ta ta dawo ta rotsa mata kai? A hakan ma kowa yana zaman kan shi ya suka kare balle suna zaman auren sa su duka? Wannan shine tunanin Saade.

Wata siririyar muryar budurwa ta yi sallama daga bakin kofa, da yakeSaade ta bada baya ne tana fuskantar mudubi, amma jin wannan murya ba ta san lokacin da ta yi azamar juyowa ba, muryar sounds so familiar a kunnenta.
Murya ce da ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta manta mai ita ba. Tana tsaye jikin kofa, harde da hannayenta a kirji, yar gaye da ita kyakkyawa sai murmushi ta ke. Ta kara tsayi da haske, ta murje sumul fiye da sanin da Saade ta yi mata.
Idanun Saade suka bubbude gabadaya, ta saki dryer din hannunta kasa, kafin ta tafi da mugun gudu ta rungume RAHEEMAH.
Fulani ta shigo, a bayanta wata mata ce da akalla za ta girme ta. Kyakkyawa da ita, da ganinsu ka ga mazauna kasar sanyi, sai kannen Rahima su biyu Sarina da Jamila. Kallo daya Saade ta yi wa matar ta gane mahaifiyar Rahima ce sabida tsabar kamannin su, wadda Rahima kullum ke kira da “Mama”.
Ta saki Raheema ta tafi ga Mama za ta tsugunna, Mama ta yi saurin riko ta a jikinta, sannan ta rungume ta. Cewa ta ke,
Masha Allahu, yau ga ni ga Saar Raheema, Saadatu Saar Mata!
Ta kama su ita da Raheema ta rike a jikinta, Sarina da Jamila sai murmushi suke mata. Ta tafi gare su suka rungume juna don dai ita duk wani ahalin Raheema tana sonsa a kan dalilin da zuciyarta har yau ba ta sani ba.
Raheema shi ne ki ka gudu daga El-Kanemi babu ko sallama, babu notice? Na shiga damuwa Raheema, zaman makarantar ya fice min a ka saboda rashinki. Na dade kafin na saba da rashinki Raheema, nayi kewar ki yadda harshe na ba zai iya bayyanawa ba, don Allah kada ki sake tafiya ki barni Raheemah. Sai kuka.
Raheema tana share mata hawaye da tafukanta, ta ce, har yanzu kina nan da kukan wofin kin nan ko? Is o.k Saadatu. Im here now, da ni za a sha shagalin biki, ba zan tafi ba sai na raka ki dakinki.
Ni ma ba da son raina muka koma Italy ba, kuma ban samu damar dawowa El-Kanemi don in miki sallama ba. Ki yi hakuri.
Sannan ne suka zazzauna a kasa, iyayen na daga gefen gado suna kallon su withaffection.
Nan Fulani ta gaya wa Saade labarin da ya girgiza zuciyarta, cewa ita da Raheema yan uwa ne na jini, da mahaifinta da mahaifin Raheema uwarsu daya ubansu daya.
na dade da gane hakan ban dai gaya miki bane tuntuni, don in Baban Rahimah ya san ke ce ba zai bar ki hannu na ba.
Saade sai ta ji duk wata damuwar duniya ta yaye mata. Feeling din da mutum ke ji idan ya san cewa yana da dangi na jini kuma na halali. Lallai da ake cewa wani farin cikin ya fi gaban kuka, sai dariya.
Ta zama kamar wata karamar zararriya don murna. Ta rungume Raheema, ta saki ta rungume Sarina, ta saki ta kamo Jamila ta rasa inda za ta sa su don kauna, su kuma sai dariya suke mata, don sun riga ta jin labarin tun suna Italy.
Maimartaba ya kira Fulani a waya ya gaya mata ta sa a rako Saade da Rahima falon saukar bakinsa ta gaisa da Babanta, wato Alhaji Kyari Babagana. Tare da Fulani suka tafi har falon ganawa ta musamman da bakin Maimartaba Sarkin Askira.
Kallo daya ta yi mishi ta hango kamanninshi da mahaifin ta Malam Hashimu, saboda jini ba ya buya. Har kasan kafafunshi ta je ta zauna ta gaishe shi a ladabce. Shi kuma ban da kallonta da tasbihi ba abin da yake a fili, tamkar Bilkisu ta yi kaki ta tofar, ko kadan ba ta debo dan uwansa Hashimu ba ko da da kalar fata ne. Sai yanzu ya tuna kallon sanin da yayi mata a ganin sa na farko da ita a El-kanemi. Ashe fuskar Bilkisu ya hango cikin idanun ta.
Alhaji Kyari ya ce, Madallah da yata mai albarka, Allah ya sanya alkhairi da albarka cikin aurenki. Allah ya hada hankulanku, Ya bada zaman lafiya.
Ba ta iya ta amsa wannan adduar ba, saboda nauyin da ta yi mata a zuciya da kwakwalwa. Idan ta ce, ameen, Allah ya amsa adduar fa? Aurenta da Yarima ya zama tabbatacce ba mafarki ba kamar yadda ta ke kallonsa? Duk da Yareema Sageer ya tabbatar mata cewa, reality ne, ta hanyar da bata taba zato ba, kuma ba shi da alamun ja da baya daga hukuncin iyayensu?
Don haka ya rage nata ta cigaba da yaudarar kanta da kanta, da cewa mafarki ne.
Sun dade yana mata tambayoyi tana ba shi amsa a kan marigayi da rayuwarsu a Tsanyawa, karatun da ta ke yi a yanzu a NTNU da kuma burin ta na yanzu wato barin karatun ta zauna a gida.
Daga shi har Askirama suka hada baki wajen tambayarta,
Saboda mene za ki bar karatunki Saadatu?
Ko shi Yareeman ne ya ce ba ya so?
In ji Maimartaba, sounding worried da hukuncin Saaden, duk da ya san hakan mawuyaci ne a matsayin Yareema Sageer na malamin jamia cikakke ya ce ya hana matar sa karatu.
Saade ta bude baki a hankali kamar mai ciwon makogaro, ta ce,
Saboda na fi son in ci gaba da zama a Askira, bana son komawa Abuja Alanguburo.
Fulani ta ce, Babbar magana, mijinki yana wani gari ke kina wani gari, a dalilin me?
Maimartaba ya yi saurin cewa, Ya isa Fulani, Saadatu za ki zauna a gidan Yarima na Askira har ki kare hutunki? Inyaso daga baya sai mu raka ki Abuja da kanmu ni da Fulani ki koma makaranta, kin amince?
Askirama ya yi maganar cikin lallashina uba mai tsananin kulawa.
Kaunar da Mai Askira ke nuna mata da yawan alkhairinsa gare ta ya fi gaban ya yi hukunci ta ce, aah. Sauran zai kasance ne tsakaninta da Yarima, tunda shine bai ce shima baya son auren ba, yayi uwa ya yi makarbiya ya amshe auren, ita ta fada a ce ta yi rashin biyayya, da kyar in Fulani bata bubbuge mata baki in ta fada hakan a gaban Askirama ba, amma tsakaninta da Askirama babu jayayya.
A hankali ta gyada kai alamar ta amince, idonta kuma ya cicciko da kwalla. Amma ta yi kokarin maida su sabida Askirama. Ko yayan da ya haifa ba ta taba jin ya raka gidan miji ba ko ya je gidajen auren su. Amma ita ya ce shi da kansa zai kaita. What an honour! Wannan ba karamin girma ne da kulawa ya ba ta ba.

A wannan daren daga Raheema har Saade sai goshin asubahi suka kwanta. Labarin juna suke bai wa juna. Inda Raheema ita ma ta sanar da ita ta samu miji a Damaturu suna karatu tare a jamiar Heartfordshire, U.K. sunansa Usman Bello Jajere. (Jajere garin fulanin Damaturu ne suna da kyau farare ne kuma suna karatu sosai yan garuruwan Jajere da Kollere. Yan Jajere kan yiwa kan su kirari da Jajere garin jajaye in ka ga baki to bako ne), amma aure sai ta gama karatu, shi kuma ya dawo gida ya yi service.
Ba abin da Saade ta tuna a lokacin sai Saidu, da yanzu ita ma yaro dan makaranta kamarta za ta aura, ina ma ta bawa Saidu damar da yake nema tuntuni tana gwasale shi? Yanzu gashi girman kanta ya sa an dauki mijin wata an ba ta wanda a haihuwar kauyensu Tsanyawa ya haife ta. Allah kadai ya san irin farin cikin da Usman zai sa Raheema, ita kam yanzu sai dai ta je ta yi ta fama da yar giya
Wannan tunanin ya fiddo hawaye daga idon Saade, wanda Raheema ta nace sai ta ji dalilin saukarsu. Don bata ga dalili ba.
Saade ta tuna cewa, wannan Raheema ce, mai kaunarta da zuciya daya tun tana bakauyiyar ta, kuma yar uwar da ba ta da kamarta a yanzu. Babu wanda ya dace da sanin halin da zuciyar ta ke ciki a halin yanzu ya kuma fahimceta ya bata shawarar data dace kamar Rahimah.
Don haka Saade ta gyara zama, ta warwarewa Rahimah komai a kan rayuwarta gidan Yareema Sageer, da halin da matarsa ke ciki, irin kyautatawar da yake mata, girmansa da ta ke gani, har da labarin Said sai da ta bata. Amma ta rasa dalilin da ya sa ta kasa ce da Raheemah Aunty Sultana na yawan cewa Sageer yana neman mata. Maganar ta yi nauyi sosai a bakinta tunda ba ta taba gani da idonta ba, shaidar zina kuwa sai ka kwana a ciki in ba ka yi taka-tsan-tsan ba.
Ta gaya wa Raheema damuwarta shi ne ba ta taba jin wani abu a zuciyar ta a kan Yareema ba, bayan na kasancewarsa guardian dinta a Abuja. Ita a wurin ta Uncle Yarima Yayanta ne mai kula da alamuran karatun ta.
Rana daya ta ji labarin aurensu daga bakin Fulani bagatatan kamar saukar aradu, ita ta fi son in auren ne ma a aura mata Saidu ba za ta damu ba, shine tsaran auren ta daidai da rayuwar ta ta yar talaka. Amma ina zata kai YARIMAN ASKIRA???

Raheemah Kyari, ta yi wani irin lallausar murmushi. Ta kama hannayen Saade ta rike cikin nata.
“inda kowacce mace take kai mijin ta Saadatu! Ina ma ni ce ke Saade! Ki yarda ba tun yau ba cewa you are among the luckiest. Auren matured men shi ne aure, wadanda suka san ciwon kansu, ki rabu da samarin nan yan rawar kai ki kama mijinki da iyayen ki suka zaba miki kin ji? What is your own business da rayuwar matar sa?
Kuma tunda Fulani ta ce ya raba muku gida, kuma ya amince, ina ruwanki da matarsa? Wannan rayuwar su ce shi da ita bai shafe ki ba.”
Saade ta zumburo baki, Raheemah ba za ki gane ba. I have no feelings a kan Yareema Sageer, na dauka zaman auren sai da feelings din soyayya yake yiwuwa???
Raheema ta girgiza kai, ta ce, inji wa? Saadatu, ki gode wa Allah kawai, ki kuma hada da addua, ki roki Allah ya sanya miki soyayyar mijinki, kuma zabin iyayenki. Soyayya da kike ambato shirme ce, cike take da unbearable challenges, aure daban soyayya daban, sai kin yi auren soyayyar in gishiri ya sauka daga kan kaza za ki gane shayi ruwa ne.
Above all kin ce kina ganin girman Yareema, to magana ta kare. Along the way soyayyar za ta zo, irinki in ku ka tashi soyayyar ma mahaukaciya ku ke yi, kuma makauniya, tunda kin ce ba ki ga alamun

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login