Showing 21001 words to 24000 words out of 117873 words

Chapter 8 - Masarautar Mu 1 to 4 Complete

Hausawa suka ce wai "Mai Da wawa ne", wannan kyautatawa da kauna ta Sa'ade ga Zarah a hankali yake hakurkurtar da zuciyar Fulani Bilkisu, daga mummunan kullacin Mal. Hashimu dake cikin ta, wanda ya hanata ganin farin Sa'ade har ta kaunace ta matsayin 'ya 100%.
A hankali ta soma rage fada, da tsawa da hantarar da take yawan yi mata, ta soma yi mata magana jefe-jefi cikin sanyin rai.
Satin ta uku a gida sai ga Raheema Kyari, wannan karon ba'a hanata shigowa ba, Kuyangar data rako ta sai ta hada ta da Fanna, ita kuma Fanna tace ta jira daga waje, ta nemo izni tukunna.
"Kawa kuma daga Maiduguri?"
Fulani ta fada cikin mamaki.
"Haka ne ranki ya dade, sannan ta tabbatar min ita aminiya ce ga Sa'adatu sannan ta san da zuwan ta".
Fulani ta hadiye fushin ta wanda tayi aniyar saukewa akan Sa'ade bayan tafiyar bakuwar, ta ce Fanna ta shigo mata da yarinyar.
Cikin sallama da shiga ta mutunci da kamala Raheemah ta shigo, tunda ta shigo Fulani ta kura mata ido. She looks so much like her father wanda ta yi wa farin sani. Mikewa tsaye tayi ba tareda ta san lokacin da ta yi hakan ba, hatta tsagin fuskarsa biyu-biyu dogaye gasu nan kwance a fuskar Raheema.
Da ta gaisheta da kyar tayi controlling razanar ta ta amsa,
"yaya sunanki?"
"Raheema Kyari Babagana"
"Kyari?!"
Ta fada da amon muryar da ya baiwa Raheema mamaki, "eh, sunan Babana kenan" "daga wane gari kike?" "Daga Maiduguri na zo, acan muke zaune, amma mu 'yan asalin Damaturu ne".
"Shikenan dangin ubanta sun biyo ta, a lokacin da na fara sanyata a raina".
Fulani ta ayyana a zuciyar ta, ta kuma kudiri aniyar kin gayawa Sa'ade kowacece Raheema a gareta.
"Shiga nan dakin, tana ciki"
Ta fada tare da nuna mata dakin, ta kuma tashi ta bar musu area din gabadaya zuwa turakar ta.
Sa'ade sai ganin Raheema ta yi ta shigo da sallama, zo ki ga gudu da murna wajen Sa'ade, saura kadan ta kada Raheema. Ita kuwa sai dariya take. Ta dauki Zarah dake tsakiyar gadon ta tana fadin "masha Allah, beautiful baby". Hira kamar ta kashe su. Fanna ta shigo wa da Raheema abinci na musamman suka ci tare cike da farin ciki.
Can da yamma Raheema ta ce "Sa'adatu ki zagaya da ni mana in ga masarautar taku in samu abun baiwa su Sarina labari". Sa'ade tayi dan jimm! Kafin tace "ni bana zuwa ko'ina, daga daki sai daki, Fulani bata bari na". "Amma meyasa?" Inji Raheema. Ta dan kyabe baki "i don't know. May be sabida kishiyoyin ta". Daga haka suka bar hirar.
Washegari Fulani ta sa aka yiwa Raheema sallama ta girma, aka maida ita har Maiduguri.
****
Ya Gumsu ta shiga turakar mai Askira cikin kwalliya ta kasaita a matsayin ta na mai girki ranar, abinci yake ci tana gefen sa tana masa firfita, cikin hila irin ta matan da suka san kan mazan su ta yi durkuso a gaban sarki, ta ce "Alanguburo (Allah ya kara yawan rai) Yarima na rokon alfarmar a bar shi ya zo gida, ko da na sati daya ne, shekaru goma kenan rabon sa da gida, yayi digiri yayi masta ya jima yana aiki har ya fara digiri na uku, yana cikin damuwar rashin sanin halin da 'yan uwan sa ke ciki, yayi alkawarin baza'a sake samun sa da laifi makamancin na baya ba".
Nan da nan wani kwantaccen bacin rai ya bayyana a fuskar sarki, ya dago idanun sa da suka kada ya dube ta, sai da hantar cikin ta ta kada. Ta yi azamar sunkuyar da kai amma a ranta zata jure komai in har zai bar dan ta ya zo gare ta, haka kawai ai ba shikadai ne fitinannen Da ba, fitinannun nawa ya haifa? Amma bai daukewa Ya Kirjinoma nata ba sai shi kadai bayan ba fin su fitinar yayi ba. Yana kusa da su ma suna masa fada ai zai fi gyarawa fiye da hannun aminin nasa.

Sarki Yusufu AbdulHakimu mai Askira, ya dubi uwargidan sa Ya Gumsu da idanun bacin rai kamar koyaushe ta sako zancen YARIMA SAGEER a gaban sa, idan da abunda ya ke bata masa rai a rayuwar sa to al'amarin Yarima Sageer ne, babban Da, kuma zakka a cikin 'ya'ya mazan da Allah ya bashi, yet mafi madaukakiyar soyayya a zuciyar sa.
Dama an ce wai fitinannun 'ya'ya sun fi shiga zuciyar iyaye. Kusan wannan magana haka take. Duk cikin 'ya'yan sa maza da mata ba wanda yake so irin Muhammad Sageer, sai kuma ya zamo mafi munin jarraba da Allah ya taba yi masa. Ubangiji yayi gaskiya da ya ce "ya'ya da dukiya fitina ne......".
"A takaice dai kina rokawa dan ki alfarmar ya dawo cikin gidan nan ya cigaba da turmushe 'ya'yan mutane, ya cigaba da wulakantani tare da tozartani a idanun Bayi na da hadimai na dake tsananin ganin girma na, ta hanyar turmushe musu 'ya'ya dake hidimta masa?".
Fulani ta runtse ido cikin jin zafin kalaman sa, "Alanguburo, wannan abu ne na kuruciya, kai kan ka da ka ga Yarima ka ga nutsuwa da hankali a tattare da shi, abinda yayi yana yaro ba zai taba maimaitashi cikin hankalin sa ba, balle da 'ya'yan bayi makaskanta a gare shi. Wallahi don an ki yarda da nine, amma Yarima makiya ne suke jifan sa a baya, ba yin kansa bane.
Kai shaida ne akan tsantsani da tsafta irin na Yarima, amma a ce ya rasa matan da zai bi sai 'ya'yan bayi, ai daga nan zaka gane akwai lauje cikin nadi a al'amarin sa.
Bayan haka kuma na dukufa da yi masa addu'a tun tafiyar sa, Allah kuma baya juya addu'ar Uwa, inada kyakkyawan yaqinin cewa ya daina, mu taru mu kyautata masa zato, mu bashi dama ya rayu cikin gidan su kamar kowanne Da cikin gidannan, idan aka sake samun sa da wani laifi makamancin wannan, na amince ayi masa duk hukuncin da ya kamata da shi".
Maganganunta ga dukkan alamu sun dan shigi Askirama. Ya dade cikin halin shiru, ya kasa cigaba da cin abincin sa. A karshe yace da Ya Gumsu wadda ke jiran amsar sa kamar ta shiga zuciyarsa taga abinda yake yankewa.
"Zan yi shawara da Waziri".
"Alanguburo (Allah ya kara maka yawan rai nagode matuka, kuma insha Allahu Waziri zai amince da abinda na zo da shi, don shima na tabbata yana son ganin Awaisu)".
"Ina bukatar kadaicewa". Ya ce da ita.
Ta mike cikin azama ta soma tattare akusan abincin dake gaban sa. "In ma kwana zaka yi kai kadai ka yi, ni dai a bar Da na ya dawo gida". Ya Gumsu ta fada cikin ranta, a fili kuwa dukawa ta yi a gaban sa tana fadin.
"Na bar ku lafiya gatan Askira".

Fitar ta ke da wuya ya kishingida ya lula cikin tunani. Tunani mai zurfi na shekarun da suka gabata.
****










SHEKARUN CAN BAYA
(A Masarautar Askira)
Lokacin da Ya Gumsu ta samu cikin babbar 'yar sa 'Yaa Maira' duk burin sa da dokin sa shine a haife masa Da namiji domin ya samu magaji, kamar yadda kowanne sarki ke burin samu. Amma sai aka haifi Ya Maira, ciki na biyu ma yayi ta fata da addu'ar samun da namiji, amma sai ta kara haihuwar diya mace. Dalilin sa kenan na kara auren Ya Kirjinoma a daidai lokacin domin yana ganin 'ya'ya mata kawai Ya Gumsu zata yi ta haifar masa.
Kamar Allah ya san cewa bai yi farin ciki da haihuwar Mairam Lubabatu ba, bata fi shekaru uku ba Allah ya karbi abinsa.
Ya Kirjinoman ma da ta tashi haihuwar ta ta fari, sai ta haifo masa Mairam Murjanatu. Wannan ya kara mayar da shi desperate ga son haihuwar da namiji. Ba ruwan sa da 'ya'yan sa mata, duk kulawar su da hidimar su da tarbiyyar su tana wuyan iyayen su mata. A kullum ya tuna wancan lokacin ya kan ce "wannan shine deadly mistake da ya taba yi a rayuwar sa". Ba shikadai ba, masu sarauta da yawa hakane tunanin su akan haihuwar fari, idanunsu rufewa yake ga son haihuwar da namiji ba tare da baiwa Allah zabi ba.

Ciki na uku da Ya Gumsu ta samu kusan a tare suka sameshi itada Ya Kirjinoma. Ita ta haifi MUHAMMAD SAGHEER, Ya Kirjinoma ta haifi MUHAMMAD ASHGAR tsiran watanni biyu kacal ne a tsakanin su.
Ashgar sai ya zo da rashin lafiya ta Autism wadda aka fi sani da (autism spectrum disorder). Baya magana (in a meaningful way) tun yana karami saidai ya maimaita abinda aka fada masa sannan kamar kwakwalwarsa ba daidai take ba.
Wannan yasa sarki Yusufu ya dauki soyayyar duniya da tattali da kulawa ta duniya bakidaya ya dora akan lafiyayye Yarima Sageer, wanda hakan ya ruruta wutar mummunan kishi tsakanin Ya Kirjinoma da Ya Gumsu, ya kuma sa Ya Gumsu daukar girman kan duniya ta dorawa kanta, da jin tafi kowa, tunda kuwa ita ta haifarwa sarki Yarima. Koma waye zai biyo baya saidai ya zo a matsayin kanin sa ba Yayansa ba.
Soyayyar data sa tun yana yaro daga uwar har uban suka sangarta shi, basa iya kwabar sa, gata na duniya babu irin wanda basa gwada masa. Hakan bai hana shi yiwa Sageer addu'a ba a duk sallahr farillar sa kan Allah ya kare masa shi a duk inda ya shiga. Musamman da ya bayyana ga kowa cewa yaron fitinanne ne na kin karawa.
Ya addabi 'ya'yan jama'ar gari da mugunta da tsokana, baya zama cikin masarauta saidai cikin 'ya'yan talakawan gari, sune abokan sa abokan mu'amalar sa, don Sageer ya tare yaro a lungu ya targadashi ya fasa masa hanci babu gaira babu dalili ba wani abu bane sabo a wajen jama'ar gari, suna dauke ido ne sabida mutuncin mahaifin sa da farin jinin yaron. Yaro ne mai shiga rai matuka, sabida kwarjini da kyawun suffar da Allah ya bashi.
Yana girma fitinar sa na karuwa a ciki da wajen masarauta.
Kullum Sageer ya fita makaranta da yaron da zai targada ko ya fasawa hanci ba'a kuma isa a kawo kara ba sabida tsoron Ya Gumsu, saidai Awaisu ya gani ya zo ya fada a gida. Waziri ya aika a bada hakuri. Don ba'a bari ma Sarki ya ji. (Awaisu dan Waziri ne kuma sa'an Sageer don haka tare aka raine su), har ta kai ga Awaisu ya kwaso kayan sa duka ya dawo dakin Sageer kwatakwata, sai dai hali kowa nasa daban. Don kuwa Awaisu babu ruwan shi yaron kirki ne, amma duk inda Sageer yasa kafa nan zai mayar da tasa.
Darajar Sarki yasa jama'ar gari suka yi ta hakuri da Sageer tun yana yaro har ya shiga sakandire anan Askira. Kafin ya gama sakandire ne kuma yayi dan hankali ya daina taba 'ya'yan kowa, sabida yawan addua'ar Alanguburo akan sa. Har yake dan shigowa fada a zauna zaman fada tare da shi kamar yadda Sarki ke so ya dinga yi kullum amma ya ki. Lokacin da Sageer ya soma balaga, sai abubuwan gabadaya suka canza, 'yar nutsuwar da yake da ita tabi ruwa. Ya koma neman bayin sa mata.
Lokacin da wannan mummunan labari ya kai kunnnen sarki Yusufu mai Askira sai ya kira Wazirin sa cikin sirri.


"Na yanke shawarar in aura masa mata hudu a rana daya, ina ganin hakan ne kawai mafita ga al'amarin sa".
Waziri Ibrahim ya girgiza kai yana kallon maimartaba sarkin Askira cikin tausayi, ganin yadda ya zabge ya birkice a kwanaki uku kacal da samun wannan labari da yayi. Lallai 'ya'ya da dukiya fitina ne. Kamar yadda mulkin kansa fitina ne da rashin kwanciyar hankali ga bawa. Yace.
"Baza'a yi haka ba Askirama. Baza'a yi haka ba gatan Askira, aure ba laifi bane a shekaru goma sha tara amma karatu za'a kai shi, zamani ya canza, auren mata hudu a rana daya ba zai zamo solution ba, don kuwa zai hanashi maida kai ya yi karatu musamman idan ya soma tara iyali. Ka manta da komai ka kwantar da hankalin ka ka barshi yayi karatun da zai amfane shi muma watarana ya amfane mu. Zan hada shi da Awaisu zuwa duk inda zaka kai shi zan kuma san yadda zan yi Awaisu ya zame masa jagora a komai nasa. Mafi a'ala shine mu bisu da addua".
Ya sani duk duniya babu mai kaunarsa cikin 'yan uwan sa na jini irin Waziri Ibrahim, wanda ya kasance Da ga wan mahaifin sa marigayi sarki AbdulHakimu mai Askira. Bai taba bashi shawarar da in ya bi ta baya ganin mafita da yaqini a cikin ta.
Don haka yayi na'am da shawarar Waziri ba tareda shawara da Ya Gumsu ba.

Kafin ya zama sarki shi Ambasada ne na kasar Egypt, saida mahaifinsa Sarki Abdulhakim ya rasu ne aka dawo dashi gida aka bashi sarauta, don haka yana da kyakkyawar alaqa da ambasadan Egypt mai ci a lokacin kamar amini yake a gare shi, sannan yana da connections mai yawa da kasar ta Misra domin yayi sama da shekaru goma yana aikin jakada a cikin ta.
Don haka ya yanke shawarar kai shi kasar muslunci bai kai shi kasar turai ba don ya kara hankali, a Egypt din ma hannun Aminin sa Amb. Hassan Labaran ya damka shi bai yarda ya zauna a hostel ba. Amb. Hasan bai taba haihuwa ba shida matarsa Hajiya Laila, suka karbi amanar Sageer da Awaisu a gidan su wadanda aka samarwa gurbi a jami'ar Al. Azhar. Saidai ba fanni daya suke karanta ba.
Daga wannan lokacin ne kuma haihuwar 'ya'ya maza ta budewa Sarki Yusufu daga duka matan nashi biyu, a lokacin ne ya hadu da Hibbani ya aure ta, daga baya ya auri Bilkisu, haihuwar ta biyar suna mutuwa.
Amb. Hassan zazzafan da boko ne mai zafi da sanya ido akan iyalin sa, tashin farko ya gano dabi'ar da Sageer ya zo masa gida da ita ta shan sigari, kuma ba jimawa yayi fata-fata da ita, ya cigaba da dora shi a hanya ta hanyar tsawatarwa da jan sa a jiki, yana nuna masa illar smoking ga lafiyar sa ta dan adam. Wani abu da bai samu daga iyayen sa ba sabida kawaici na masu sarauta ga 'ya'yan su. Gara ma Maimartaba akan Ya Gumsu wadda babu wani kusanci ko kankani tsakanin ta da dan nata, bata san me yake ciki ba, bata taba bincikar halayyar sa ba, ita dai burin ta ya kasance cikin gata ya samu duk abinda yake so, ya girma ya gaje sarauta.
Cikin dan lokaci kankani Amb. Hassan ya canza da yawa daga baragurbin halayen Sageer sai abinda ba'a rasa ba. Shima Awaisu a nasa bangaren yana iya nasa kokarin wurin ganin Sageer ya canza munanan dabi'un sa zuwa na cikakken dalibin da ya san ciwon kansa.
A karshe Awaisu ya fahimci wani abu, zai iya nasarar raba Sageer da komai, amma ba zai iya raba shi da 'yammata ba.
Mahaukatan kudin da sarki ke turo masa don yayi hidimar karatu, da wadanda Amb. Ke basu lokaci-lokaci duk a hidimar 'yammatan sa yake karar dasu. Yana kuma da masaniyar cewa yana branching da 'yammata a hotel ba da sanin Amb. Hassan ba.
Al'amarin ya kara kazanta ne lokacin da aka yiwa Amb. Hassan sauyin kasa, daga Egypt zuwa Amsterdam akan aikin jakadancin sa. Suka tattara suka bar Egypt suka koma can. Inda suka fara karatun doctorate degree dinsu a fannin da kowanne yake a babbar jami'ar Amsterdam. Awaisu na karantar (Social Work) yayinda Sageer ke karantar (Pure and Applied Chemistry).
A duka wadannan shekarun bai kara ganin kowa nasa ba, wadanda aka haifa baya nan bai san su ba. Haka wadda aka aura a bayan sa wato Fulani Bilkisu. Bayan su akwai kwarkwarori da yawa. Sannan elder sisters dinsa biyu duk sunyi aure sun hayayyafa: Ya Maira da Mairam Murjanatu. Bayan su an haifi maza biyar, biyu Ya Gumsu, uku Ya Kirjinoma, sannan Hibbani na da Humaira da Najaatu. Bayan kammala M. Sc din su dukkan su sun samu aiki a kasar Amsterdam, Awaisu aikin asibiti yake yi yayin da Yarima Sageer ke aiki da wani mashahurin kamfanin sarrafa kayan abincin gongoni

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login