Showing 39001 words to 42000 words out of 117873 words

Chapter 14 - Masarautar Mu 1 to 4 Complete

kuma Maimartaba ya ce 'yar Fulani Bilkisu ce ta cikin ta, matar da duk fadin gidan su in ka dauke mahaifiyarsa ba wadda yake gani da mutunci kamar ta, ba wadda ke kula da al'amarin sa dana matar sa kamar ta. Anya zai iya wulakanta jinin ta? Babbar damuwarsa Sultana bazata taba amincewa ba musamman sabida yadda take shaye-shayen ta babu takura, ta dauka bai sani ba, amma kallon ta kawai yake, duk abinda take ciki ya sani, baya magana ne don ya san shima da nasa guntun kashin a katara.
Aka ce wai in ka ji ma'aurata masu ha'intar juna suna zaman lafiya to tabbata daya na ha'intar daya, babu yadda dayan zai yi ya hana, kada nashi asirin ya tonu. Wannan shine tsakanin Yarima Sageer da matar sa Aisha-Sultana.
****
Babu yadda zai yi, haka yasa neman admission din Sa'ade a gaba a washegari a matsayin first thing da ya shiga ofis ya zauna, takardun ta duk sun yi kyau. Ya tsurawa sunan ido.... SA'ADATU HASHIM ASKIRA. Hatta course din ma nasa ta dauka......Pure and Applied Chemistry. "Does she know me?" Ya tambayi kansa cikin mamaki. Salon karatun ma mai Askira ya ce ni zan koya mata???
Tsaki yayi ya ture takardun gefe ya janyo na wasu, a lokacin da Dr. Ziyad ya turo kofar ya shigo dauke da sallama a bakin sa. "Wata hot baby na samo yanzunnan daga zuwa na Millenium Park, akwai abubuwa, kayi maza ka gama mu bar ofis dinnan". Tsaki yayi ya ce "kai baka san halin da nake ciki ba, wata yarinya za'a kawomin riko daga gida, Allah ya sa ba spy mai martaba zai kawo min ba, ko wani ya kai gulmata ban sani ba, ka san a ko'ina yana da jama'a musamman nan Abuja" ya fada kyakkyawar fuskarsa dauke da damuwa tsantsa.
Dr. Ziyad yace "i don't think so. How old is she?" "JAMBITE ce fa" "whao!" Inji Dr. Ziyad. Kace sweet 16 za'a kawo mana kawai, yo meye abin damuwa banda mu dinga kwasar rabon mu kawai muna saya mata pizza muna cika mata aljihu? Gida na is very quite and secret ko Sultana bazata san muna kwasar gara ba".
Wata muguwar harara Yarima Sageer ya zabga masa, ya tsartar da miyau da sauri. "Allah ya sawwake Allah ya tsare ni, ni ba dan akuya bane, ina dai neman matan bisa titi amma ban da na mutunci balle wadda ta fito daga gidan mu, daga gidan mun ma daga hannun mahaifi na, 'yar matar mahaifi na mai yawan karamci a gareni. Allah ya kiyaye! Iskancin nawa mai limit ne, and i'm hoping watarana in bari gabadaya". Dr. Ziyad ya kyabe baki tareda mikewa tsaye yana dariya yace "kai din? Na yarda bazaka iya neman ta gidan ku ba, ko don kada asirin ka ya tonu, amma bazaka iya barin mata ba i swear ...." Yarima ya dauki mukullan dake bisa teburin sa ya jefe shi dasu, Dr. Ziyad ya dafe keya ya fice da gudu yana masa dariyar data kara masa takaici kan wanda yake ciki, na yarinyar da za'a turo masa babu gaira babu dalili.
Cikin sati daya ya gamawa Sa'ade duk shirye-shiryen ta, an dauke ta a NTNU a tsangayar da yake koyarwa (B. Sc Pure and Applied Chemistry). Ya aikawa Askirama admission letter din ta ta email. Abinda ke gabansa yanzu shine ta yadda zai tunkari Sulatana da maganar.
Amma abin mamaki da ya koma gida da yamma, ya tarar ta riga shi dawowa, ta shawo ta yi mankas tana kwance dai-dai a tsakiyar falo. Haka ya tsallake ta yana tsaki ya wuce dakin sa ya sunce ya shiga wanka. Yana fitowa ya shiga kitchen don neman abinda zai ci, ya bude firji, abin takaici babu komai sai Giya nau'i nau'i, yanzu Sultana ta daina shakkar ya san shaye-shayen ta, kai tsaye take komai don ta ga baya daga ido balle ya nuna ya san tana yi.
Wani mugun tsaki ya saki ya rufe firinjin da karfi, yanzu in yarinyar nan ta zo ta gani fa? Mai Askira yace rana ita yau za'a kawo ta tare da kayan ta su gyara mata daki.
Ji yayi yunwar da yake ji ta kama gaban ta, da sauri ya fito ya sa kafa ya shuri Sultana da karfi. Ta bude idanu jazur dasu, ta sauke su a kan shi, dama gasu tun asali kamar na mage (brown eyes). A fusace yace "ki tashi ki kwashe abubuwan da kika cika min firji dasu, we're having a guest from Askira, and she's going to stay with us for years, so mind yourself else.....duk abinda ya biyo baya ba ruwa na".
Sultana tayi mici-mici da ido "bakuwa? A gidannan? Daga Askira? To ban yarda ba" ya galla mata harara yana hango wani irin muni a tare da ita da bai taba gani ba wanda yake bayyana in ta sha giya "sai ki kira maimartaba ki gaya masa" ya jefa mata wayar hannun sa.
Har dare suna fafatawa, ta dage sai ya kira Babansa ya ce bata yarda ba, shi kuma yace ba tarbiyyar da aka yi musu kenan ba but she's free to call him herself.
"To ko dai aure suka yi maka shine za'a fake da karatu don nasan mamanka bata so na!"
Sultana ta fada cikin kuka. Shi don mamakin kalamanta ma dariya yayi, wai aure! Wa ya isa yayi masa aure ba da yardarsa ba? Besides, su gidan su ba'a auren dole. Sannan ya gama aure a rayuwar sa ba zai taba yin mata biyu ba duk da kasancewarsa basarake.
Tashi yayi ya dau motar sa ya bar gidan zuwa inda ya tabbatar za'a faranta masa rai, yau ranar kwata-kwata a birkice ta zo masa. He's upset, sannan wannan mahaukaciyar Sultanar ta kara masa bacin rai.
Ai kuwa ya samu Dr. Ziyad ya dauko musu baby din da ya gaya masa sun hadu a millenium park, nan ya manta da zancen Sa'ade da Maimartaba ya shantake acan har karfe daya na dare.
Sanda ya shigo gida ya tadda Sultana ta baje kwalabe sun fi biyar duk tayi emptying din su. Ta koma zukar marijiuana cikin tsumma, gashin kanta a birkice, gabadaya sai ta zame masa kamar motsatsiyar tsohuwa, ya dinga tambayar kansa tun farko me ya gani a tare da ita ya yarda ya daukota har kasar sa ya aureta???
Tsaki yayi ya tsallake ta ya wuce dakin sa. Wanka ya fara yi ya tsaftace kansa, yana jin wani abu na tsirga masa a zuci da gangar jiki, wanda yafi kama da jin kunyar Ubangiji. Wankan janabar da bata aure ba alhalin ga matar sunnar ya tsallake tana nata sabon Allahn. Wannan wace irin rayuwa ce???
Idanun sa a rufe ya hau gadon sa ya kwanta. Addu'a yake cikin ransa in yana da rabon dainawa kafin ya mutu, Allah yasa ya daina......!!!
****
Tunda Askirama da kansa ya shigo ya ce da Fulani gobe ne tafiyar Sa'ade gidan Yarima jikin ta yake a sanyaye, don bata san wane irin riko da karba Sultana zata yi mata ba, tunda ita ba jinin gidan bace, duk da su Humaira suna fadin bata da matsala.
Amma ga Sa'aden sai murna take, very enthusiastic ga tafiya makaranta, bata tunanin komai da ya danganci abinda zata ta tarar banda kasancewa dalibar Turkish University.
Don a daren Fulani ta zaunar da ita a gabanta. Don ta ga murnar tata har ta so ta yi yawa, tun azahar ta kammala daure kayanta tsaf. Kadan ta bari wadanda bata cika amfani dasu ba. Allah-Allah take garin Allah ya waye ta kama hanyar birnin tarayyah.
"Sa'adatu bani hankalin ki nan" inji Fulani.
Ta dago fararen idanun ta ta dubeta, wadanda a lokuta da dama suke wani irin sheki da walainiya (sparkling eyes) wanda shine babban sirrin kyawun Sa'adatun. Fulani tace.
"Na ga sai rawar kai kike, ki kama kan ki, gidan Yarima zaki je, sannan matarsa asali ba musulma bace, sannan ba bahaushiya bace, don haka dole ki kula da tarbiyyar kan ki da kan ki, ki maida hankali akan abinda ya kai ki kawai, ba ruwan ki da rayuwar su, ban da sa-ido, banda daukar zance, banda shiga shirgin da ba'a sanya ki ba.
Tsakanin ki da su yi na yi bari na bari. Ki dinga taimaka mata da girki da ayyukan gida tunda ita ma'aikaciya ce. Na hore ki da kama mutuncin kanki, ko ya kike da namiji kada ki yarda ki kebe da shi, Ko hannun ki namiji ya taba cikin shege zaki yi, kin ji na gaya miki?"
Sa'ade ta gyada kai cikin fahimta, sannan ta dan zaro ido ta ce "to ai gidan ba maza ko?" Fulani ta hana kan ta yin dariya sabida yadda muryar Sa'ade ta koma razana zallah. Tace "shi mai gidan ma ai namiji ne, kuma ba muharramin ki bane ba, don haka matsayin uba yake a gare ki, ki kama kan ki, ki rike mutuncin ki. Allah yayi miki albarka ya saka albarka a neman ilmin ki. Ga waya karama na saya miki duk halin da kike ciki ni zaki kira ki gaya min, ban yarda ki bawa kowa lambar ki ba".
Sa'ade ta gyada kai cikin murna a lokaci guda tana mika hannu don karbar karamar wayar siemens da Fulani ke mika mata. Kawai sai ta ji Fulani ta hada da hannun ta ta janyota jikin ta ta rungumeta...
"Ki yafe min Sa'adatu don Allah ki yafe mini..." "ni baki yi min komai ba Fulani, na yafe miki abinda na sani da wanda ban sani ba. Nima ki yafe mini!"
Sallamar tasu is very emotional da ta fiddo hawaye daga idanun kowaccen su.
Washegari daya daga cikin direbobin gidan karkashin rakiyar kuyangin Fulani Bilkisu mata guda biyu maimartaba yasa suka dauki Sa'ade zuwa Abuja a daya daga cikin motocin 'Askira Emirate'. Tun asussuba suka kama hanya basu isa Abuja ba sai karfe takwas na dare. Inda Allah ya taimake su shine sun yo guzurin abinci da abin sha wadatacce wanda har suka iso Abuja sallah ce kawai take tsayar dasu a gidajen mai na gefen hanya.
Suna fitowa daga mota Sa'ade tayi mika....ta ware ido tana kallon kyawawan gidajen estate din malamai na NTNU kamar kana kasar Istanbul. Ashe ba ginin masarauta kadai ne gini mai kyau ba, ginin Turkawa ma abu ne mai matukar kyau da daukar hankali.
Ita dai tunda take bata taba ganin kananan gidaje masu tsari da kyawun zubin wadannan ba, ko ya mutanen cikin gidan suke? Koda yake Fulani ta ce turawa ne, ai sai turawan.... "wannan gida wanke hannu ka taba". Sa'ade ta ce cikin ranta. Daidai lokacin da daya daga cikin kuyangin da suka zo tare ta yi mata magana ganin ta shagala a kallon gidan "ranki ya dade mu karasa daga ciki ko?"
Suka isa ga entrance na gidan suka hau danna kararrawa, suka yi har suka gaji ba'a bude ba, a lokacin Sultana na kwance a falo ta sha ta kai mata karo, tun misalin karfe 6 na yamma take kwance har a lokacin bata san inda kanta yake ba.
Allah ya kawo Uche (kukun gidan) zai shiga da cefane, kasancewar yana da mukullin gidan ta kofar kicin ta baya. "Hey! What do you want here?" Ya tambaye su. Aka rasa mai amsawa don 'yan rakiyar Sa'aden basa jin turanci, sai itace ta gayamasa daga Askira suke, sun zo wajen masu gidan ne. Ya tambayeta ko Dr. Sageer ya san da zuwan su? Ta ce "ya sani" a takaice, domin bata da tabbacin hakan, Allah-Allah take ta sanya hakarkarinta akan shimfida sabida gajiyar zaman mota data kwaso.
Wayar sa ya dauko ya kira wata lamba yayi magana cikin harshen turanci, ya kalle su, sannan ya maida wayar aljihun sa ya ce su biyo shi. Ta baya suka shiga ta kofar kitchen suka kurda zuwa falon gidan. Nan Sa'ade taga mace jajawur kwance magashiyyan a dandaryar tayals, gashin kanta ya baje ya rufe fuskarta, Uche bai ko dubi inda take ba ya bude wani daki yace su shiga nan ne dakin bakuwar. Sannan ya ce su bashi minti 15 zai kawo musu abinci. Kafinnan ga ruwa da lemo su sha.
Tsaruwar dakin ya burge Sa'ade, duk da bai kai dakin ta na Askira ba amma daki ne mai tsari irin na turawa babu tarkace sam a cikin sa. Gado ta fada tana ce da Fariha daya daga cikin 'yan rakiyar ta in an kawo abincin ta tashe ta tunda ita tana fashin sallah, in taci abinci sannan tayi wanka.
Uche ya kawo musu abinci mai rai da motsi suka ci suka koshi, sannan Sa'ade ta fara yin wanka, ta shirya cikin kayan barci tabi lafiyar gado bayan ta kure iyakwandishan, sukuma kuyangin suka kwanta daga kasa. Ba wanda ya nemesu har washegari. Da asubah suka kama hanyar Maiduguri lokacin Sa'ade tayi sallah ta koma barci.
****
Sai karfe takwas na safe Sa'ade ta tashi, ta duba babu 'yan rakiyarta, sai ta tuna sun ce da asubah zasu kama hanya, tsaki tayi tana mitar shine ko su tashe ta su yi sallama.
Wanka ta fara yi, kafin ta ji cikin ta yana kiran chiroma, a gurguje ta shirya tana fadin bari in bi su kitchen din tunda sun manta da mutum a gidan.
Tana kokarin fita bayan ta murda kofar dakin taji ta yi karo da mutum....Wani irin sassanyar kamshi mai huda zuciya, coupled with his gait and geniusness, beautiful elegant face wadda babu far'a sam a cikin ta.
A kiyasce yadda ta kimanta shekarunsa zasu kai talatin da biyar zuwa da shidda. Alamu sun gama nuna ya gama samun duk wasu achievements na rayuwar dan adam. Kama daga ilmi na addini dana zamani, sannan ya zauna da kafafun sa ya gama kama kasa.
Da farko ta dauka Askirama ne a gabanta (mai martaba) sabida tsabar kamannin su, saidai data lura sosai sai ta fahimci wannan akwai tarin kuruciya da hasken boko a tare da shi, bi ma'ana yaro ne mai jini a jika, babu ko tsillin furfura a kwantaccen sajensa zuwa gashin kansa, wanda ya kwanta luf a gefen fuskarsa.
A duniya bata taba katari da mutum mai cikar kamala da kyawun suffa kamar sa ba, ga wani irin kwarjini da ya banbanta shi da sauran maza. Sarauta ta gama bayyana kanta a komai nasa. His lips are so luscious kamar ana basu extra kulawa, fatar jikin sa fresh kamar haifafen kasar Morocco. Sai ta ga kamar ta taba ganin sa, somewhere else da bazata iya tunawa ba.

Yadda ta saki ido, hanci da baki tana kallonsa shi ya fi komai bashi haushi, amma da yayi kokarin yin magana sai ya samu halshen sa da kasa motsawa. Suka dubi juna directly cikin ido yayin da wani gravity mai karfi ya fizgi ido da zuciyar kowannen su. Alal hakikah a rayuwar Dr. Sageer Yusuf Askira, bai taba ganin macen da ta tabo wani sashe na kololuwar zuciyar sa irin wannan da ke gaban sa ba. As professional as he is akan sha'anin mata, ya fada a zuciyar sa cikin 'yan dakikan da suke tsaye..... "ta mallaki komai da yake mafarki a diya mace". Amma kuma nan da nan mulkin sa da izzarsa ta Yariman Askira ta zo ta shafe komai, daga ganin yarinya baka san komai akan ta ba, sannan wadda ta fito daga gidan ku?
Tuni ya mallaki kansa, fuska a daure ya ce da ita "come for breakfast".
Ya juya ya fita, ba tareda ya kara wata kalma ba.
Komawa ta yi ta dauko mayafin ta ta yane kanta akan doguwar abayar dake jikinta ruwan hanta, da sallama ta shigo falon, can bisa dining ta hange su shida matar sa. Gaskiyar Fulani ashe...baturiya tsantsa. Ai kuwa sun dace duk da shi baki ne kamar Askirama. Sa'ade ta fada a zuciyar ta. Sultana ta daga ido tana kallon Sa'ade, kallo daya Yarima yayi mata ya maida kai ga cin abincin sa. A take ta ji wani irin kishi ya soke ta, wannan kyakkyawar yarinyar za'a dauko a ajiye mata a gida? Ai da sake wai an bawa mai kaza kai.
Ta dauke kai daga kallon Sa'ade ta mayar kan abincin ta. Har kasa ta tsugunnan tana gaishe su, daga matar har mijin babu wanda ya amsa mata. Wannan abu ya sosa mata rai. Daga bisani Yarima ya mike yana goge bakinsa da tissue. "If you finish meet me outside" ya ce da Sa'ade. Matar ta tambayeshi inda zai kai ta? Yace tare zasu dinga shiga makaranta. Har zata yi magana, sai kuma ta ja bakin ta tayi shiru, itama ta mike ta bi bayan sa.
Haka jiki ba kwari ta ja jiki zuwa tebir din cin abincin, ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login