Showing 78001 words to 81000 words out of 117873 words
gidan Saadatu suke yi da komai da ke cikinsa. Yayin da Saadatu ke ta kuka har zuwa lokacin, tun suna lallashinta har sun gaji sun kama hira sun koma yi mata dariya. Hanne ta ce,
Sai ki yi ai, dadi ne ya yi miki yawa. Ni mijin nake so ya gudu ya bar ni, ke Allah ya kashe Ya ba ki kina so ki yi butulci, kukan dadi ki ke yi, ki ci gaba Saade.
Raheema ta ce, Ni in ni ce na samu wannan gidan na Saa ai bude ido zan yi in sha kallon abuna mu more niimar da Allah ya ba mu.
Sai jin gyaran muryar Awaisu suka yi daga bakin kofa. Ya yi sallama suka amsa, sannan ya dan shigo ya dube su ya ce,
Me kuke jira ba ku kama gabanku ba?.
Hanne ta ce, Kudin sayen baki mana!.
Ya yi dariya don daga jin maganarta ya san yar kauye ce futuk, ya ce,
Ai ke ce sayen bakin amma fadi me ki ke so a ba ki ki fito ki bar Yarima da Sa'adatun sa?
Sai ga Yariman ya iso kofar dakin ya ce cikin kasaitarsa da muryar da ke gigita Saade har cikin kwanyarta. Ba jimawa kuwa jikin ta ya hau tsuma.
Awaisu please drop them at home, na gaji da yawa.
Awaisu ya ce, Sun ce kudin sayen baki suke jira.
Ya ce, ka ba su ko me suke so, amma ku kama gabanku dukkanku, har kai.
Ai kuwa Saade ta sake rushewa da kuka ta kama hannun Raheema ta kankame.
Yanzu tafiya za ku yi da gaske ku bar ni ni kadai Raheemah?
Yareema ya jiyo abinda Saade ta ce, da kukan da ta ke yi mai ratsa zuciya, zuciyar sa ta motsu, ba zai iya jure jin sautin kukanta ba, daga Awaisu har su Raheema ba su ankara da sanda ya shigo dakin ba, sai sunkuyawarsa da daukar Saadatu kacokam a hannayensa biyu kamar ya dauki karamin yaro, ya juya ya fice yana ce da su.
please....Mun sallame ku, mu kwana lafiya.
Saade wadda kanta ke rufe ruf cikin laffaya tana aikin kuka, bata gane me ke faruwa ba, har sai da Yareema ya soma hawa matattakala da ita a hannun sa,wadda zata sada su da turakar sa, sannan ne ta gane a hannun Uncle Yareema ta ke dungurugum, ta hanyar jin kamshin invictus paco rabbanne da taushin hannayen sa da ya mamaye ta. Ta kuma ji an raba ta da kasa kacokam. Kukan ya makale don kansa ta koma salati tana wutsil-wutsil da kafafunta. Su Raheema me za su yi ba dariya ba?
Yarima bai sake bi ta kansu ba ya bi matattakala da Saade a hannunsa zuwa upstairs dinsa.
Bai dire ta a koina ba sai a kan sofa. Yana ajiye ta tana zabura tana mikewa suka tsaya a tsaye kamar zakaru suna kallon-kallo, idanunta jazur wadanda suka sha kuka suka koshi. Idanunsa a lumshe, wadan suka jiku da soyayya. Ba ta ankara ba ta ga Dr. Sageer ya juya cikin tafiyar sa ta kasaita, ta dauka daya dakin zai shiga don rage manyan kayan dake jikin sa, don a sanin data yi masa bai iya zama da kaya masu nauyi na tsayin lokaci, ta samu damar da ita kuma zata fice ta koma kasa.
Maimakon hakan data yi hasashe, sai gani ta yi ya isa ga kofa ya murzawa dakin keydin dake jikin kofar, ya kuma zare mukullin ya jefa a aljihun gaban rigarsa.
Ya koma can jikin gado yana rage nauyin kayan alfarmar dake jikinsa, ya cire babbar rigar ya ajiye a gefe, sannan ya zauna a bakin gado ya dauki wayarsa yana daddannawa ya baiwa banza ajiyar ta. Har zuwa lokacin Saade na tsaye inda ya barta kamar mutum-mutuma. Ta kasa motsawa ko nan da can.
A yadda Yarima ya ganta ya san ba karamar rigima ta ke ji ba, sai motsi take da baki amma ta kasa magana. A yadda yake ji shikuma ya shirya wa kowacce irin rigima da za ta zo da ita, koda zasu babbaka kan su a dakin, tunda finally ya mallake ta shi ke da nasara cikin kudura da iradar Ubangiji, ba don ya isa ba, babu tsumi ba dabararsa. So duk wani protest da zai zo daga gareta zai iya shanye shi. Tunda iya wuya ita aka kwara. Matsalar sa daya sarautar sa bazata barshi ya iya lallashin mace ba, ko ya nuna weakness.
Ta ya ya zai yi wasa da wannan kyautar bazata mai daraja da mahaifinsa ya yi masa?
Bai kara bi ta kan Saade ba yana ta latsa wayarsa. Da Awaisu yake magana kasa-kasa, inda Awaisu ya tabbatar masa ya maida su Raheema wajen Fulani, ya kare da cewa,
Ka tausaya wa yarinyar mutane please Yareema. Ka rike ta amana. Ka san dai a cancanta baka cancanci auren ta ba Allah ne ya dube ka da rahmar sa. Dubi yadda ta ke ta kuka kamar ranta zai fita, wallahi ta matukar bani tausayi. Very young da aure.
Ya san Awaisu gaskiya ya fada. Amma a ki-fadi irin nasa. A kufule ya amsa.
Ina ruwanka da matar mutane da har ka kalle ta ka san kuka ta ke yi? Awaisu ka fita idona in rufe, ka fiya shiga sabgata da yawa, ko kukan jini ta ke bai shafe ka ba, tunda dai ba Asiya ba ce. Wannan maganar da kake yi ba hurumin ka bace. Awaisu sai dariya yake har Yarima ya kashe wayarsa.
Malama, in kin gama kukan ki yi mana light-off, zan kwanta.
Saadatu ta sake bare baki tana kuka da sauti kamar karamar yarinya, wane irin light-off ita da namiji a daki daya? Kukan nata sai ya koma bai wa Yarima dariya, amma da yake ba gwanin yinta ba ne, sai bai yi ba. Ga tension din da Ya Gumsu ta saka shi a ciki. Ga maganar Awaisu ta taba shi. Ya mike zuwa closet din jikin bango yana canzawa zuwa pajamas.
Ta gefen ido Saadatu ta sato kallonshi, ai kuwa riga yake kokarin sa wa ta hango ingarmanphysique chest din Yareema Sageer Yusuf Askira da manyan damatsansa wanda ke lullube cikin muscles da ba shiri ya sanya ta kauda idonta. Jikin ta ya hau tsuma. Ta kuma durkushe a kan kafafunta ta bude shafin sabon kuka wanda ya ratsa har cikin kwakwalwar Yareema Sageer.
Zuciyarsa ta karaya, ko kusa bai yi niyyar rarrashinta ba a yau, so yayi su yi duk irin rigimar da zasu yi ya nuna mata ba gudu ba ja da baya a auren su duk rashin son ta da auren. Auren su mutu-ka-raba ne. Amma kukan nata ya karya lagonsa, ya ji ba abin da yake so irin ya san hakikanin damuwarta a kan aurensa. In dai har za ta yi hakuri ta zauna da shi cikin kowane hali, shikuma zai yi duk abinda take so komai tsaurin sa.
Gefen gadon ya koma ya zauna, ya dunkule hannayensa cikin junansuya dora habar sa akan su, ya rasa abinda yake masa dadi. A yanzu ko bata furta ba ya gama gane Saade bata farin-ciki ko kadan da zamowar shi barin rayuwar ta. Wannan kukan data ke yi ya wuce na amarci, kuka ne mai nuna an zalince ta, an katse mata rayuwa. A hankali ya kira sunanta da wata irin lallausar murya da shi kansa yake tababar kasancewar tasa ce.
Saadatu!
Ba ta amsa ba, haka nan ba ta fasa kukanta ba, kukan da ke cin ran sa, sannan ba ta dago ta dube shi ba. Tana nan durkushe a inda ta ke kamar an kafe ta a wurin, nannade cikin jar sassalkar laffaya ta bare-barin usli. Yarima ya mike daga zaunen da yake a gefen gado, a hankali ya soma takawa zuwa gaban Saade, kafarsa na nitsewa cikin tattausar kilishin tsakiyar dakin.Pajamas ce ruwan toka kawai a jikin sa iya gwiwar sa samfurin Marks and Spencer, ya daure tsakiyar da igiyar ta.
Yana zuwa hanayenta da ta rufe fuska da su ya kama, ya tsuke su tsakiyar tafukan tausasan hannayen sa, ya bude fuskarta wadda ta yi kaca-kaca da hawaye ta yi jazur, da ka ganta a wannan lokacin za ka san BAGGARA ce. Kamar uwa da uba duka shuwa-arab suka haife ta.
Hannayenta da ya kama ya ja ta a hankali zuwa jikinsa daga tsayen da suke. Bata kai shi tsayi ba iyakacinta kirjin sa.Slowly yake rungume ta tightly, ta yadda kowacce gaba ta jikinsu sai da ta hadu da yar uwar ta.
Haduwar fatar jikin su wuri guda tamkar jan wutar lantarki ya haifar ga kowannen su. Da wata irin azama Saade ta soma kokarin janye jikinta daga na Yarima Sageer, saboda wani alamari ne da bai taba faruwa da ita ba (physical contact) da kowanne Da namiji, balle wanda ta ke wa ganin matsayin babban Yayanta.
Tsatstsauran rikon da Yarima ya yi mata ya sa ta kasa kwacewa, tun tana kokawar da mutsu-mutsun kwatar kanta har ta gaji tubus! Ta bari, hawayen fuskarta Yareema ya soma wiping da lips dinsa, wanda hakan ya jefa Saade cikin wani hali da ta kasa ganewa. Wani ignition ne tamkar electrical shocking ke yawo a cikin gangar jikinta a duk lokacin da lips din Yarima ya sauka a kan fatar fuskarta. Duk da haka kokari ta ke ta kwace jikinta amma bai bata damar hakan ba.
Kina so in cika ki Saadahtouh?
Muryar Yareema Sageer tamkar ba tashi ba. Ta zama very pale idan aka kwatanta ta da ta dazu da yake magana cikin izza da sarauta.
Kai ta daga, domin kwarai ta ke so ya cika tan ko ta shaki numfashi yadda ya kamata, sabida ba ta saba da hakan ba. The feeling is awesome, and their closeness is so intoxicating. (Kusancin ta da shi mai bugarwa ne). Kai za ta iya rantsewa babu namijin da ya taba rike mata hannu in this manner ta ji irin abinda ta ji yanzun tun tasowarta, don haka komai da Yarima yake yi a yau is so strange to her, zuciya da gangar jikin ta sun kasa karbar sa.
Maimakon ya cika ta kamar yadda take fata, sai ya kwantar da kai gabadaya a kafadun ta ya kanainaye cikin jikin ta. Har tsayuwa ta soma gagarar ta domin ya saki duka nauyin sa a jikin ta, amma yasa hannu daga bayan ta ya tare ta.
Yareema ya soma magana da murya mai kassara zuciyar diya mace, mai nuna karbar laifi da shirya repenting, zaka rantse ba shine Dr. Sageer din da ka sani a NTNU ba. Kuma Yariman Askira mai jiran gado. Mafi soyuwa a zuciyar Mai Askira.
“Na ji kuma na yarda da korafin ki na cewa an miki laifi an aura miki mai yin zina. Ba tare da an nemi yardar ki ba. Ba zan iya cewa kin yi karya ba. Sai dai kada ki manta su din iyayen mu ne bamu da kamar su, nima baa nemi yarda ta ba, da an nema da na gaya musu ban cancanci mallakar pure soul irin ki ba Saadah!.
Tunda bakin alkalami ya riga ya bushe ni da ke duka bamu da abin yi banda fuskantar reality na rayuwar da ke jiran mu a gaba, mu manta da ta baya. Ko me ki ke so zan miki Saadah, in har za ki amince ki zauna da ni. Duk sharuddan da za ki kafa min a zamanmu zan bi su, in dai za ki ci gaba da amsa sunan matar Sageer Askira.
Saadatu this is not the right time to discuss anything sensitive like this, dukkan mu hutu muke bukata, don haka so nake ki kwanta ki huta na gaji Saadahtouh, bikin Askira mai wahala ne, hutu kawai nake bukata yanzu, ke ma kin gaji da hidimar bukukuwan mu na aladah, ki yi hakuri da kukan nan haka mu kwanta mu yi barci. Mu bar wa gobe tattaunawar, komai dacinta zan saurare ki!
Na yi alkawarin canza komai na rayuwata zuwa mai kyau daga ranar dana mallake ki Sa'adah na yi alkawarin nan.
Ka bude min kofa in fita to.
Karo na farko da ta yi magana tun shigowarsu dakin. Domin kalamansa sun sanyaya mata zuciya.
Saadahtouh, ke matar aure ce yanzu, kuma macen arziki ba ta raba makwanci da mijinta sai bisa lalura.
Muryar Saade bata fita sosai sabida kukan da ta sha. Ta ce. Don Allah Uncle Yarima ka bar ni in koma wancan dakin, ni ba zan iya kwana daki daya da kai ba. Ta fadi da iyakar gaskiyarta.
Me ki ke tsoro? In kin kwana gado daya da mijin ki Malaiku ne za su yi ta sa miki albarka har garin Allah ya idasa wayewa, musamman if you act as my messeuse (idan kika zama mai min tausa) duk jikina ciwo yake mun saboda zirga-zirga da hayaniya. Please Saadah help me... Ya fada yana kara makalkale ta ta yadda suka dunkule wuri guda kamar curin alkaki, ba tare da Saade ta san yaushe hakan ta faru ba Saboda gabadaya muryar Dr. Sageer ta gama kashe duk wani kuzarinta. Ta saukar mata da wata irin kasala.
Ita ma ba ta san me ta ke tsoro a kwanansu daki guda bisa gado guda babut shes really-really afraid, wani abu ne STRANGE a gare ta, don bata taba ganin inda akai hakan ba. Duk da ta san a yanzu an daura musu aure amma zuciyar ta ta kasa karbar wannan sabon dingimemen sauyin da sauki.
Tana wannan tunanin mai matukar dagula zuciya, ba ta yi aune ba sannan bata tantance komai ba ta ji Uncle Sageer ya soma warware laffayar jikin ta tun daga sama cikin nutsuwa har ya sauketa kasa tsaf, ya saura daga ita sai underwear din dake jikin ta, kallo daya Dr. Sageer ya yiwa Saadatu cikin fararen under wear ya ji komai na duniya ya tsaya masa; including numfashin sa.
Daga hakan ya sunkuce ta ba tareda ya tsaya sake kallon ta ba, bai dire ta a koina ba sai a royal bed din su, ya ja wani lallausar duvet ya lullube su, tare da latsa makunnin lantarki daga nan inda ya ke kwance. Fitilu shudaye suka maye gurbin masu haske (dim light).
A dirowar jikin gadonsa ya bude ya fiddo turarensa Invictus (Paco Rabbanne) ya soma feshe su dukkan su, ya ce.
Bana son wadannan turarukan matan barebarin da aka gumbuda miki, daga yau kada ki sake shafa su, we will be using the same scent, wadannan sun cika karfi da yawa hawa min kai suke yi.
Daga yau za mu dinga using nawa tare (Paco Rabbanne), you can use it too ba shi da karfi.
Saade ta zumburo baki kamar yana ganinta, ai kuwa ya gani ta cikin dan hasken dim din wanda hakan ya sa shi yin abin da bai shirya ba. A hankali ya soma sumbatar Saade tun daga yatsar kafarta
At first hes doing it gentle kafin gabadaya ya koma hungrily, da gani za ka san abu ne da ya dade yana fatan kasancewar sa. Ya dauki Saadatu diyar Fulani Bilkisu ya kai ta wata kololuwar duniyar soyayya da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba.
A yadda Saade ta yi amanna ta mika wuya ko me Yarima ya nema a lokacin tabbas zai samu, domin ba ta san inda Yarima Sageer ya dauke ta ya kai ta ba. Amma sai me? Kalaman Ya Gumsu ne suka fado cikin kwakwalwarsa suka katse duk wani hanzari nasa.
Ban yarda ka taba yar Bilkisu ba, ban yarda ka hada shimfida da ita ba.
Sai kuma na Fulani Bilkisun
Ina neman alfarmar ka daga mata kafa har ta kare makaranta.
Yarima ya rasa inda zai sa kansa a wannan lokacin. Ji ya ke tamkar ransa zai bar gangar jikin sa. A hankali ya mirgina ya koma can karshen gado ya runtse idanunsa yana ambaton sunan Allah.
Saade na jin shi, amma ba ta san dalilin sa na janyewar ba. Da nutsuwa ta soma dawo mata sai ta ji wata matsananciyar kunya ta kama ta. What happened like this? Wannan wane irin abu ne mai tsauri da nauyi yake faruwa tsakaninta da Uncle Yarima haka?
Kanta ta tusa cikin pillow kamar ta roki gadon ya tsage ta shige. Tana jin saukar numfashin Yareema a hankali har daga baya ta gane ya yi barci. Ta yunkura da zummar ta nemi mukulli ta fice, amma sai ta ji caraf! Hannuwan Yarima sun maida ta kwanciyar, ya kuma sake mirginowa ya rungume ta sosai a jikinsa. Bai kuma kara attempting komai ba, tun tana fargabar faruwar wani abu makamancin na dazu har ta gane barcin sa ya yi nisa sosai.
Akai-akai Saade