Showing 57001 words to 60000 words out of 117873 words
ya riga ya bushe. Tiryan- tiryan ta gaya mata mafarkin da Askirama yayi akan ta da yadda ya roketa ta bashi aurenta....da kuma auren da aka daura dazu....."Shine fa Ya Gumsu ta zo tana wannan jidalin". Ita dai Fulani ta san Sa'ade na sauraron ta amma bata san lokacin da ta fado jikin ta yarab! Cikin hali na unconsciousness......kamar suma, kamar fita hayyaci, cikin biyun bata san wanne Sa'aden ta ke ciki ba. Sai ta rungumeta tana kuka abin tausayi ta rasa wane irin taimako ya kamata ta bata....
MASARAUTARMU!
Ba ta taba jin tausayin Saade da soyayyarta ba irin yau, yau din da ta tabbatar sun kusa rabuwa, rabuwa ba ta aje a dawo ba, aah rabuwa irin ta kowacce diya mace da iyayenta idan munzalin aure ya riske ta. Fulani ta rasa taimakon da za ta bai wa Saade da ke kwance a jikinta numfashinta na shirin barin gangar jikinta. Ta san Saade za ta razana in ta ji zancen nan, amma ba ta zaci har haka ba. Abin da ba ta sani ba shi ne, Saade ta san sirrin Yarima, ta san na matarsa Aisha-Sultana, tana kyamar dabiunsu na sabon Allah fiye da yadda ba a zato. Hakan kuma bai hana ta ganin wani irin girman Yareema Sageer ba, da kimarsa cikin idanunta, saboda iyakar kyautatawa a zamanta tare da su Yareemah ya yi mata.
Amma kalmar AURE a tsakaninsu, ai is underestimated. Wani abu ne da hankalinta da tunaninta ba zai dauka ba. Kullum kallon kanta ta ke yarinya karama tamkar Zarah. A aura mata Uncle Yareema ta kai shi ina? Matarshi ta sha giya ta yi mata shegen duka ko kuwa za ta iya manta kalmar zina' da Sultana ta ce yana yi? Duk da ba ta gama sanin mene ne ainihin maanar kalmar zina ba, amma ta fahimci wani abu ne mummuna, abin kyamata a addini da alada, kuma da shi za ta ke kallon Uncle Yareema in har ba ta samu tabbacin ya tuba ya bi Allah ba daga bakinsa.
Ba ta taba kawo wa ranta aure a nan kusa ba, karatu ta ke so, shi ne kuma burinta, sannan tana matukar jin dadin abunta, yau da ba Askirama ne da kansa ya yi mata wannan yankan kaunar ba, cewa za ta yi ba ya kaunarta don ba shi ya haife ta ba.
Amma ta sani, ta kuma amince kaunar da Mai Askira ke mata daga Allah ne. ba zai taba yin wani abu da niyyar cutar da ita ba, amma har abada zuciyarta ba za ta yi amanna da auren Uncle Yareema ba. Kamar yadda ba za ta iya karbarsa a matsayin miji ba. Ba gara mata auren Saidu ba in ma auren ya zama dole? Shi ne tsaran aurenta.
Fulani robar ruwan faro ta dauka ta yi ta shafa mata a fuska, wuya zuwa kirjinta. Ba ta fasa ba sai da ta ji Saade ta saki nannauyar ajiyar zuciya. Ta kara langwabewa a kafadar Fulani ba ta kara dagowa ba. Duk suka yi shiru cikin wannan yanayin, kowanne da abin da yake sakawa a zuciyarsa.
Zuwa can Saade ta yi magana a hankali.
Ni bana son Uncle Yareema Fulani, kamar yadda Mamanshi ba ta sonki. Ki ba wa Maimartaba hakuri, ba zan iya ba.
Ta soma wani irin kuka a hankali mai girgiza zuciyar mai sauraro, balle kuma zuciyar UWA! Sosai kukan na Saade yake motsa zuciyarta. Ta shafa kwantaccen gashin kan Saade da hannun damanta ta ce.
Saadatu, me zan yi in faranta miki? Ki fadi ko mene ne, amma ban da cewa ba za ki yi auren nan ba. Bakin alkalami ya riga ya bushe. Laifi kan laifi mun yi miki ni da Askirama, ina rokonki ki dubi Allah da darajar da Allah ya bai wa iyaye a kan yayansu, ki dubi karamcin mai Askira gare ki ki yi hakuri ki yi hakuri ki yi hakuri ki bar wa Allah komai.
Saade ta ce, Ta ya ya zan zauna da shi mahaifiyarshi ba ta sonki? Ni ma bana sonshi, matarsa ba ta sona. Komai na rayuwarsu daban yake da tawa. Fulani yadda ake shan ruwa a firji haka ake shan giya a gidan nan kuma kuma Ta kasa cewa ZINA don sai ta ji kalmar ta yi gundumemiya a bakinta ta alakanta ta da Uncle Yareema, saboda cikar kamalarsa da cikar zatinsa kadai yana hanawa ka alakanta shi da kowanne irin aibi
Kin taba jin kishiya ta so kishiya ne Saade? Don haka ki cire wa kanki damuwar wai Gumsu ba ta sona. Yanzu matsayin uwar miji ta ke a gare ki, ki yi duk iya yadda za ki iya wajen kyautata mata. Sauran lamarin sai ki bar wa Allah.
“But I dont love him Fulani, ina da saurayi na dan ajinmu da na ke so, sunansa Saidu
Ki san abin da za ki dinga fada, don ke matar aure ce yanzu. Mace kuma addini bai bata damar ta so kowa ba ko da kuwa da fatar baki ne sai mijin aurenta. Ki gaya min me ki ke so in yi miki in faranta miki ki saki ranki ki manta da komai? Ki sa a ranki babu wani bambanci tsakanin rayuwarki ta da da ta yanzu. As if normally makaranta za ki koma ki ci gaba da karatu, ni kuma zan tsaya in ga cewa Yareema bai hada ki gida daya da Aisha-Sultana ba, kin san yana jin maganata. Sannan zan roke shi ya daga miki kafa har ki kare karatu, in ba zai iya hakan ba ya kara mata ta uku.
Saade kamar ta fashe da kuka saboda ita yanzu ko sunan Yareema ba ta son ji. Ya shigo rayuwarta unexpectedly ya rusa ta. Duk burinta na yin karatu mai zurfi ba a yi shawara da ita ba an kakaba mata aurensa. Yariman da ta tabbata yana neman mata.
Laifin me ta yi wa Fulani da Askirama da zasu rasa wanda zasu aura mata sai Yarima Sageer?
Ta mike za ta bar dakin idon ta fal hawaye Fulani ta sake riko ta tana murmushi.
Ba ki gaya min me zan yi miki ba a matsayin gift dina na aurenki.
Saade ta ce, Fulani ni me ye nawa a ciki da har sai an ba ni gift? Ai ba'a nemi yardata ba kafin a daura don haka bana bukatar kowanne gift din ki
Fulani ta danne dariyarta duk wani tension da ta ke ciki shirmen Saade ya sa ya tafi, ta ce, matsayinki na babbar kanwar ango.
Saade ta kyabe baki ta ce, Yana da kannensa su Humaira yan gayu, ni in kina so ki faranta min kawai ki sa a kai ni Tsanyawa in ga Hanne da Innarta, Baba Saleh da Inna Laure.
Ta yi ficewarta zuwa nata dakin, ta bar Fulani cikin tunani.
Hakika ta yi kuskure da ba ta kara kai Saade Tsanyawa ba, wajen bayin Allahn da suka sada ta da ita. Da kuma matar babanta, duk da Saade ta ce ba zaman dadi suka yi ba, amma dai ai ta rike ta komai lalacewar riko a lokacin da ita ta yasar da ita. Ta kudire a ranta za ta faranta wa Saade da wannan kuma za ta nemo mata wan mahaifinta Kyari da yarsa Rahima kawarta duk da ba ta da tabbacin da gaske Rahima yar Kyari ce ko ko kamanni ne kawai da suna ya zo daya.
A take ta kira Askirama a waya kasancewar ba girkinta ba ne. Ta gaya masa tunanin da ta yi, ya ce shi kuma ba zai kai Saade gidan Yarima ba sai ya nemo Babagana Kyari, sai ya aika an dauko Baba Saleh da iyalinsa don ya tabbatar wa Ya Gumsu cewa, Saade da asalinta. Ba don ya sassauta kiyayyarta ga auren ko ga Saade ba, sai don ya cika farin cikin Bilkisu da yarta.
A koina Mai Askira yana da mutane, daga bayanin unguwar da Kyari ya zauna a Damaturu daga bakin Fulani ya bi ya dinga tracing labarin Babagana Kyari. Mutanen unguwar suka tabbatar masa Kyari da iyalinsa sun dade da barin Damaturu zuwa garin Maiduguri inda Babagana Kyari ke kasuwancinsa na fata, har gidansa na Maiduguri sai da aka binciko, inda makwabtansa suka tabbatar da cewa Kyari da iyalinsa suna kasar Italy kwata-kwata inda yake sanaar kai fatu.
Mai Askira bai gushe da ci gaba da tracing Kyari ba har sai da wani abokinsa ya bada lambar wayarsa ta kasar Italy, kuma a daren shi da fulani suka yi zaman kiran Kyari Babagana inda suka yi magana a handsfree baki da baki shi da Bilkisu.
Ta cikin wayar Kyari yake kuka da ya ji mutuwar dan uwansa Hashimu, ya ce Ba yadda ban yi da shi ba ya dawo gida ya ki, wai tunda kin guje shi ba shi ba Damaturu. Na ce ya ba ni yar in rika, Hashimu ya ce mai raba shi da yarki sai mutuwa. Ashe kuwa ita din ce za ta raba su, daga baya na bi bayansa har Kano inda ku ka zauna ban tadda shi ba, aka ce bayan kun rabu ya koma wani kauye da yarshi, kauyen da har yau nake bincike Allah bai ba ni ikon sani ba.
Ina fatan yar tawa tana lafiya, kuma ya ya sunanta?
Fulani ta gaya masa sunanta Saadatu, sannan cikin jin kunya ta ce, Mai Askira ya daura mata aure jiya, da Dan wajensa Yareema Sageer.
Askirama ya karbi maganar da cewa, Ka yi hakuri na yi maka shisshigi, ya kamata a ce ni na fara nemo ka kafin daurin auren hikimar hakan ba ta zo min ba har sai da Fulani ta ankarar da ni. Ka yi hakuri, ka yi hakuri, na yi gaggawa ga sadakinta nan na damka wa Bilkisu na warawaran danyar gwal guda shida.
Alhaji Kyari Babagana ya yi murmushi, ya ce, Its a pleasure meeting you your Royal Highness the Emir of Askira. A yi min alfarmar kara sati daya kafin a yi bikin yata Saadatu, don ni da uwarta da yan uwanta mu samu halarta.
Da sauri Askirama ya ce, An yi wannan alfarmar, na sanya har sati biyu biki da tarewa, don bikin da ban yi a auren Yarima na farko ba shi zan yi a yanzu, tunda yanzu ne na san Yarima ya yi aure irin wanda hankalina ya kwanta da shi, kuma na yarda da shi. Matarshi ta farko daga Asia ya kawo ta.
Sun dade suna tsara abubuwa na yadda bikin Saadatu da Yarima Sageer zai kasance kafin su yi sallama.
Maimartaba ya dubi Fulani tana hamma, ya ce, me ya hada ki da Gumsun gari? An gaya min wasu maganganu marasa dadi wadanda ban yi zato daga gare ku ba.
Fulani ta tabbatar ba wanda zai kawo wannan gulmar sai Fulani Hibbani uwar tsugudidi, Allah kadai ya san iya abin da ta gaya masa. Ta yi kwafa sannan ta ce, Ni da idanuna ban ga Ya Gumsu ba, kusan watanni shidda kenan. Amma na ji an ce ta zo nemana ina barci. Bayan wannan ban san wani ba kuma.
Maimartaba ya jinjina kai, amma bai ce komai ba. Ya san Bilkisu ba za ta yi masa karya ba, amma maganganun da Hibbani ta gaya masa sun tayar masa da hankali. Cewa ta yi, Ya Gumsu da Bilkisu sun yi dambe a gaban bayinsu da kuyangi. Bai yi wa Gumsu maganar ba don tun artabunsu akan maganar auren rabonta da sake tako kafarta turakarsa.
Yanzu abin da ya sa a gaba shi ne, ta yadda zai fuskanci Yarima da maganar, ya hana Awaisu gaya masa, ya ce shi da bakinsa zai gaya masa ta hanyar da za ya fahimta.
Yarima bai san wainar da ake toyawa ba, domin bayan rabuwarsu da Awaisu a ranar Maiduguri ya tafi, akwai wani project da yake rubutawa zai yi bincike a UNIMAID, wanda zai dauke shi har tsayin kwanaki uku. Bincike ne da yake bukatar nutsuwa (applied research) a fanninsa don haka ya kashe wayarsa.
A daren ranar aka yi ta tura masa text na taya murna da fatan alkhairi ba tare da ya sani ba, don duk wayoyinsa ya kashe su. Ya tattara hankalinsa kan abin da yake yi, yana gidan saukar baki na jamiar Maiduguri.
Awaisu ne kadai ya san inda yake. Kwanansa biyu kawai sai ga Awaisu. Har masaukinsa ya je, Yarima zaune cikin tattausar kujerar leather ta falon masaukinsa yana kurbar lemun Don Simon a cikin tambulan, ya dubi Awaisu wanda bakinsa ke ta motsi yana yan mutsu-mutsu wadanda Yarima ya riga ya gama gane su. Akwai abin da ke faruwa wanda ba ya son gaya masa idan yana irin wannan mutsu-mutsun.
“You better be comfortable, wannan mutsu-mutsun naka da magana
Dariya Awaisu ya yi ya ce, Me ya samu wayoyinka na kasa samunka? Shi ya sa fa na zo da kaina.
Tunda na zo ban kunna su ba, ina da muhimmin project a gabana, amma dama yanzu zan dan kunna in ji lafiyar Saadatu. Tunda muka zo ba mu kara haduwa ba, kuma ni nan da kwana uku zan koma Abuja, ina so in ji yaushe za ta koma sai in dawo in dauke ta.
Awaisu ya tsura masa ido yana son karantar wani abu game da shi a kan Saaden, bai fahimci komai ba, ban da seriousness irin na Sageer da wuya ka iya karantar abin da ke zuciyarshi.
Maimartaba ya ce, in zo mu taho ni da kai yanzun nan.
Cikin mamaki Yarima ya ce, Lafiya?
Sai dumbin alkhairi. In ji Awaisu, Amma a yammacin nan mu kama hanyar Askira is too late, ka yi hakuri ka kwana zuwa gobe, sai in tattara hankalina waje daya in kammala aikina a daren nan da safe mu kama hanya.
Awaisu ya ce, Zan bi shawararka ne only in ka amince za ka jinkirta kiran Saadatu har sai ka fara ganawa da Maimartaba ko in ce ka yi hakuri da kunna wayar zuwa goben after encounter dinku da Maimartaba
Kokari yake ya fahimci me Awaisu ke son boye masa ta hanyar kura masa ido, kuma sai kawai ya ji gabansa ya fadi.
Wani abu ne ya faru da ita? Ya tambaya in subdued (cikin karayar murya).
Awaisu ya gyara kwalar rigarshi yana murmushi, ya ce, Ita wa ke nan?
Ita Saadatun da ka ce kada in kira. Ya fada cikin daure fuska don ya kasa gane inda Awaisu ya dosa. Awaisu ya sake sakin murmushi, in dai wannan damuwar da ya gani kwance a kan fuskar Yarima a kan Saadatu ne, to insha Allahu komai zai zo wa Maimartaba da sauki, Yarima ba ya taba damuwa da lamarin wanda ba ya so, ko da kuwa ba so ne na soyayya ba, to akwai alamun shakuwa da aminci.
Babu abin da ya faru da ita, tana dakin uwarta. You better call your wife not Saadatu, bana tunanin tunda ka zo ka kira ta. A hakan ake mana ikirarin duk duniya ba wadda ake so sai ita. Ita ma ko za ka kira ta, to fa sai gobe, in ka fito daga turakar Maimartaba Ya fada yana dariya, tare da kwashe wayoyin Yarima guda uku da ke bisa center table din gabansa, ya zuba a aljihun jamfarsa. Ya zabi daki daya cikin 3 bedrooms din da ke falon ya shige yana ce da Yarima, Lemme take a shower, ko na samu saukin gajiya ta.
Yarima ya bi shi da kallo, ya kasa cewa komai, lamarin Awaisu sai shi. Sai ya dauki kan telephone ya yi dialling lambobin da yake bada umarnin a kawo masa abinci, ya yi wa Awaisu odar abin da zai ci. Daga haka ya maida hankalinsa kan macbook dinsa yana ci gaba da abin da ke gabansa. Sai dai kuma duk hankalinsa ya rabu biyu, jikinsa ya ba shi akwai muhimmin abin da ke faruwa a cikin gida da Awaisu ba ya son gaya masa, ya fi so ya ji kai tsaye daga bakin Maimartaba. Kuma da kyar in alamarin bai shafi Saadah ba, in ba haka ba don me Awaisu zai ce kada ya kira ta?
Yana aiki yana ta tunane-tunane, duk a kan Saadatu da alamarinta da ya yi wa zuciyarsa karan tsaye, ya hana shi sukuni ya kuma hana shi enjoying komai da yake yi sabida rashin ganinta cikin kwanakin nan, sai dai ya kudire a ransa suna isa Askira da ya ga Maimartaba zai je har unguwar Fulani Bilkisu don kawai ya ga Saadatu.
******
Suna kwance a bayan mota 4-matic mai dauke da rubutun ASKIRA EMIRATE, direba na ta sharara gudu don su isa Askira cikin lokaci, ta garin Damaturu suka bi, duk da ta fi nisa amma ta fi lafiya sabida insurgency da ya fara kafuwa a daidai lokacin a jihar Borno. Zuwa Askira ta Chibok bai yiwuwa dole sai an bi ta Damaturu.
Duk hirarrakin da Awaisu yake masa don ya dauke masa tunani ya ki kulawa, jikinsa ke ba