Showing 33001 words to 36000 words out of 117873 words

Chapter 12 - Masarautar Mu 1 to 4 Complete

gab da kammala karatun digiri akan kasuwanci, Suhail dan wajen Ya Kirjinoma da Ahmad kanin sa a dakin su.
An kai ruwa rana kafin Maimartaba ya yarjewa Yarima komawa Abuja da iyalin sa, don a tunanin sa da farko ya dawo Askira kenan don har ya fara shirin yi masa nadin sarautar Chiroma, amma sai Yarima ya zo da batun samun aikin sa da NTNU yana rokon Maimartaba alfarmar ya bar shi ya tafi, sai da Fulani Bilkisu ta sa baki sannan maimartaba ya amince don baya iya hanata kowacce alfarma ta nema, kuma Yarima ya zama dan gidan ta yanzu tun lokacin da Maimartaba ya damka mata amanar Sultana. Ya bar shi ya tafi da alkawarin duk bayan wata uku a gida zasu yi hutun kowanne karshen zangon karatu na jami'a.
Ranar wata Lahadi Yarima Sagir da maidakinsa Aisha-Sultana suka tattara suka koma Birnin tarayyah. Humaira da Naja'atu da sauran kannen sa maza ne suka yi masu rakiya, basu dawo ba sai da suka taya su suka shirya gidan su tsaf wanda Jami'ar NTNU ta baiwa Yareema Sagir cikin jerin gidajen malaman Jami'ar.
Jami'ar NTNU mallakar Turkawa ce (Turkish University) da suka bude a kasar Nigeria, suna biyan malamansu sosai a matsayin ta na (private international university) ko kusa ba daya take da jami'o'in Arewacin Nigeria ba wajen biyan malamai.
Haka gidajen malaman jami'ar dole tsarin su ya burge ka. Flat ne hawa daya mara girma sosai, dakuna ciki hudu, kitchen da bandaki a kowanne dakin barci, tafkeken falo da bangaren cin abinci (dining) sannan akwai garden daga bayan kowanne gida, daga gaban gidajen kuma balcony ne domin shan iska da yamma, akwai rumfar gargajiya (hut) a cikin gate din kowanne gida wadda aka zuba kujerun roba da gadon shan iska na Turkawa, gabadaya ginin daga na jami'ar har na gidajen malaman an dauko tsarinsa da sample dinsa daga Istanbul ne, duka gidajen iri daya ne sun kai guda 100 a cikin jami'ar.
Su Humaira suka dawo gida suna ta santin gidan Yayan su Yarima (Dr. Sagir Yusuf Askira) sunan da Jami'ar ta mayar masa, da alwashin zuwa hutu duk sanda suka samu hutu domin ba laifi Aisha - Sultana tana da kirki ga kowa nasa, daga auren zuwa yanzu ta saba da daukacin kannen Yarima na sauran dakunan matan sarki, banda 'yan dakin Ya Gumsu. Tun bata fahimta ba sabida rashin jin yaren hausa dana kanuri har zuwa yanzu ta fahimci Ya Gumsu bata yi na'am da ita a matsayin surukarta ba. Da suka je mata sallama ma zasu taho abuja ko kallon ta bata yi ba, haka tace da Yarima cikin fushi "tattara wannan danyen naman ku bar min sassa tun ranka bai baci ba".
Ba wai ta ji me Ya Gumsu ta ce bane amma ta fahimci ba maganar arziki bace duk da Yarima bai nuna komai akan kyakkyawar fuskarsa a lokacin da ta yi maganar ba, baya ga cewa da yayi da ita ta tashi su koma gida dare yayi.
Satin su guda itama ta fara neman aiki da (Insurance Brokers) kasancewar tattalin arziki ta karanta, Yarima ya samar masu kuku da mai gyaran gida duka kabilu, ba'a jima ba kuwa suka dauke ta, sai ya zamo daga shi har ita ba mazaunin gida, a lokacin ne Yarima yayi wani aboki dan kasar Turkey wanda yana cikin masu ruwa da tsaki na jami'ar sunan sa Dr. Ziyad, zasu yi shekaru daya kuma a tsangaya daya suke koyarwa. Tun haduwar Sageer da Dr. Ziyad abubuwa suka kara canzawa Yarima, domin Dr. Ziyad fitinanne ne na karshe kuma shi ba shi da mata, gidan sa babu nisa da gidan Yarima don haka lokuta da dama suna tare, suyi yawo cikin gari ko su debo 'yammata gidan Dr. Ziyad,
A haka suke rayuwar shi da Sultana kowa yana sha'anin gaban sa, don so suna son juna har gobe amma rashin albarkar uwa ya hana auren gamsar da kowannen su ba tareda sun san hakan ba.
Itama tunda ta waye da rayuwar Abuja shikenan ta koma harkokin ta na baya, bata kara tuna wani abu wai shi musuluncin data karba ba, shaye-shaye take na fitar hankali, data gane inda ake sayar da giya a Abuja kuwa shikenan kakarta ta yanke saka. Ta san halin Yarima akan 'giya' don haka bata taba gigin shigowa da ita gidan ba, kullum ta taso aiki sai ta tsaya a Bar ta sha mai isar ta, ta yo guzurin kayan mayen ta kala-kala sannan zata dawo gida, tana riga shi dawowa sau tari domin Dr. Sagir yafi fixing laccar yamma ga daliban sa, tana shigowa kai tsaye dakin barcin ta take nufa ta zube a kasa ko a gado tayi ta barci, har sai ya dawo ya tasheta da kan sa ya ce ta yi sallah.
Wannan itace kalar rayuwar Yarima da matarsa Aisha Sultana a birnin tarayyah, Abuja. Rayuwar da kowanne ya zabawa kansa. A haka lokaci ya cigaba da mikawa. Abinda Yarima bai sani ba tun dawowarsu Abuja da sati daya, Aisha-Sultana ta je an juya mata mahaifa.
*****

BAYAN SHEKARA BIYU!
Yau ne daliban El-Kanemi College of Islamic Theology suka kammala rubuta final paper din su ta barin makarantar sakandire wato SSCE wadda ta kasance darasin addinin muslunci (islamic studies). Farin cikin dake zukatan su ba zai bayyanu ba, fuskar Sa'adatu Hashim tafi ta kowa yalwar far'a, ta yi dakacen wannan rana inama da Rahima Kyari! Sun yi hotuna na tarihi kala-kala da kawayen ta da abokan arziki da suka yi zaman aminci tare. Babban farin cikin SA'ADE shine Alanguburo yayi mata alkawarin karatu a jami'ar Turkawa dake Najeriya (Nigerian Turkish Nile University) muddin ta fiddo da 9 credits, kuma daga yadda ta rubuta kowacce paper tana da kyakkyawan zato akan kokarin ta.
Humaira ta gama makaranta shekaru biyu baya, yanzu haka tana jami'ar Maiduguri. Da suka iso gida yau ta yi abinda bata taba yi ba a tsayin rayuwar ta (without minding the consequence); a guje ta shiga sassan su tana kwalawa Fulani kira, Fulani bata san hawa ba bata san sauka ba tana tsaye tana yi wa little Zarah fada taji anyi wuf! Da ita an kankameta a tsakar dakin. Dama ga ta babu kiba ko kadan. Saura kadan ta sha kasa "I have finally graduated Fulani, i've really -really made it!".
Kokarin banbare Sa'ade take daga jikin ta kada wani ya shigo ya gansu a haka, yayin da Little Zarah ke ta kyalkyala dariya cike da murnan ganin Sa'aden, ta tafi itama ta rungume su, Sa'ade ta saki Fulani da ke ta banbamin fadan so take ta karya ta? Ta russuna ta dauki Zarah tana rada mata cikin kunnen ta "na taho miki da choculates mai dadi" Zarah ta ce "bazamu san wa Fulani ba tunda tana yi miki fada" a haka suka shige dakin Sa'aden wanda Fanna ta gyare tsaf. Ta sanya turaren wuta irin nasu. Don tana da masaniyar yau ne graduation din Sa'adatun.

Sa'adatu Hashim dalibar El-Kenemi, doguwa ce sosai, mai kirar jiki na bare-barin usli, wadanda suka hadu da shuwa suka haifeta, suka bata colour din fata mai kyau da daukar ido. Doguwa sambaleliya tamkar kirar matan Saliyon, a yanzu ne take cikin shekaru goma sha takwas komai nata ya kai ya kawo, cikakkiyar budurwa mai wani irin class na daukar hankali.
Duka wadannan Fulani Bilkisu ta nazarce su ne a lokacin da Sa'ade ta dauki Zarah suka bata baya zuwa dakin Sa'aden, ta bisu da kallo cike da kauna tana jin wata irin soyayyarsu su a zuciyar ta, a yanzu kam ta saduda, ta tabbata ta kuma haqqaqe tana son 'yar ta, kwatankwacin ko ma fiyecda yadda ta ke son Fatima-Zarah.
Ta koma cikin hamshakiyar kujerar falon ta ta zauna, ta lumshe idon ta a hankali, yayin da tunanin shekaru goma sha tara a baya na yadda ta samu 'yar, ya soma rewinding filla-filla a cikin kanta.....
****
















SHEKARU GOMA SHA TARA A BAYA!
Mu 'yan kabilar "Baggara" ne wadanda aka fi sani da "Shuwa-Arabs", asalin mu makiyaya ne masu yawo da dabbobin su a kasashen Africa, mun fito daga kasar Chadi wadda take daga yammacin Ifriqiyyah, yawanci zaki samu yan kabilar Baggara sun watsu a kasashe irin Sudan, Cameroon, Niger, Chad, Nigeria, da kuma Central African Republic.
Baggara musulmi ne na haqiqa masu rikon addini tun karni na goma sha uku, harshen mu shine "Chadian Arabic" wanda muke yin shi da shuwa-dialect, Allah ya zubawa Baggara kyawun surah na kirar jiki data fuska, da wata irin kalar fata mai sheki da kyau, wanda ya samo asali daga cakuduwar su da larabawan Sudan.
Mahaifina Malam Soumana ya baro kasar Chadi tare da mahaifiyata a lokacin tana da cikina tare da 'yan uwan su Baggara zuwa Nigeria inda suka yada zango a yankin Borno, daga baya suka koma Damaturu bayan an haifeni da shekaru hudu, inda mahaifina yake sana'ar kiwo, shanu yake kiwo da tumaki ya sayar a karshen kowacce shekara ya sayi wasu ya sake sabon kiwo. Mahaifiyata Roumana tunda ta haife ni bata sake haihuwa ba, inada shekaru biyar Allah yayi mata rasuwa.
Babana shi ya cigaba da raino na, yasa ni a makarantar firamare, daga baya jarin kiwon nasa duk ya balbalce, wani abokin sa ya yaudare shi ya saye su da zummar washegari zai kawo masa kudin gabadaya, cikin dare ya bar Damaturu da dabbobin gabadaya, wanda hakan yayi silar talaucewar mahaifi na, muka koma rayuwa cikin kaka-ni-kayi, abinda zamu ci kansa ba kullum muke samu ba, mahaifina ya koma yin dako a kasuwa duk don mu samu abinci baya ko zancen aure don tsoron matan borno wadanda ba kabilar sa ba. A haka na rayu hannun mahaifina cikin kwanciyar hankali don talaucin mu bai hana mana kwanciyar hankali ba, duk wata buga-buga da dan adam zai yi don ya samu abinci mahaifi na yayi ta har na gama makarantar firamare, inada shekaru goma sha uku watarana mahaifina ya zo da dabbobi masu yawa, ya dinga yi musu turke yana daure su daya bayan daya, na tambayeshi inda ya samo su sai ya ce ya karbe su ne yayiwa wani kiwon su zai dinga bashi ladan kiwo duk karshen wata. Sabida zai yi tafiya Kano ci-rani bashi da wanda zai dinga kula masa da su.
Watarana muka wayi gari dabbobinnan babu ko daya, an biyo dare an sace su.
Mahaifina ya shiga tsananin tashin hankali, domin mai dabbobi ya kusa zuwa gida, duk bayan wata uku yake zuwa, sabida tashin hankali mahaifina har kwanciya yayi ciwo don bai san bayanin da zai yiwa mai dabbobi ba.
Bansan yaya suka kare ba, illa a wani dare mahaifina yana kuka ya gayamin gobe zai daura min aure, bashi da abinda zai biya mai dabbobi, shikuma ya ce sai ya biya shi, ko ya bashi aure na madadin dabbobin sa.
Na rasa a wane yanayi na karbi wannan zance na mahaifina. "Auren biyan bashi" zai yi dani, sai kace ni din ba mutum bace mai darajah. Ban taba yiwa mahaifina musu ba amma wannan karon na ce a'ah, bazan auri mutumin da ban sani ba ban taba gani ba, sannan kuma tafiya zai yi dani can wajen ci-ranin sa ya rabani da mahaifina wanda shi kadai nake da shi a duniya.
Amma rashin yardar tawa bata kara komai ba, washegari mahaifina ya daura min aure. Bayan gama daurin auren yana kokarin shiga gida ya fadi, faduwar da ta zamo numfashin sa na karshe.
Kwana uku da rasuwar mahaifina makota sun tayani zaman makoki, kowa ya tausaya mun, na zama abun tausayi, hankalina ba ya kara tashi sai na tuna auren da mahaifina ya daura min. Na tsani auren na tsani mai dabbobin tunda bashi da zuciyar musulunci da ba zai iya yafewa mahaifina asarar data same shi ba, zai ce ayi masa biyan bashi dani sabida rashin sanin darajar dan adam.
Washegari sai ga mata uku sun zo wai sun zo tafiya da ni, daya tace sunan ta Yagana matar Yayan mijin nawa ce, sai matan abokinsa guda biyu. Ina kuka ina komai haka suka fidda ni daga gidan mu ko wanka babu, a gidan Yayan sa Malam Kyari aka bamu daki wai zuwa sati mai zuwa zamu wuce Kano inda yake ci-ranin sa.
Ban ga mijin ba sai da daddare. Ya manyanta sosai, ga shi bakikkirin ga rashin kyawun gani, ni duk ba wannan ne damuwata ba yadda zan zauna daki daya da shi. Ga dakin ciki daya falle daya. Ya cire babbar rigar sa ya rataye ya jawo ledar da ya shigo da ita yana ta far'a yace "Amarya Bilkisu taho ki ci, ki kwantar da hankalin ki ni mai kaunar ki ne, na dade ina son ki, kuma na gayawa Babanki yace shi bazai aurawa kowa ke ba sabida baki da kowa a kasar nan, burin sa shine ku koma Chadi cikin dangin ku.
Nayi duk iya kokari na ba abinda ban bashi ba amma ya ki karba. Sabida haka ne na bashi ajiyar dabbobi na kuma biyo dare na kwashe abina don in samu hanyar mallakar ki. Gashi dabara ta tayi min amfani, saidai ban ji dadi ba da ya rasu ban nemi gafarar sa ba. Na so bayan auren mu in gaya masa cewa ni na kwashe dabbobin".
Na daga rinannun idanuna ina kallon mutumin nan da wata irin tsana...tsanar da ban taba yiwa wani dan adam a duniya ba, kawai sai na sa kuka mai cin rai. Ya kawo hannu wai zai lallashe ni na kai masa mahangurbar data sa dole ya ja da baya. Ya sake kokarin kamo ni na buga tsalle na bar dakin da gudu. A ranar a dakin Yagana na kwana.
A gabadaya kwana bakwai din da aka ce zamu yi a garin Damaturu ban kara yarda na shiga wancan dakin ba, nasiha da lallashin duniya matar Kyari ta yi da shi kanshi Yaya Kyarin, amma bana ce musu komai sai kuka. Tunanin makomar rayuwata nake da ba uwa, ba uba, babu dangi sannan bansan asali na ba, abinda na sani kawai shine daga Western Chad muke. Bayan wannan bansan komai akan iyayena da asalin su ba.
Sannan ga auren wannan azzalumin mutumin! Yo azzalumi mana! Wanda ya sanya mahaifina cikin kaka-ni-kayi don biyan bukatar zuciyar sa. Ya raba mu, rabuwa ta har abada. Don na tabbatar bakin cikin irin auren da yayi min ne ya sa ya fadi, faduwar da ta zamo ajalin sa.
Kwana bakwai ta cika, Yaya Kyari ya sameni shi da matarsa, ya fara da yimin nasiha da nuna min girman hakkin aure a wurin Ubangiji, sannan ya kuma tabbatar min kanin sa mutumin kirki ne zai kula dani, in kwantar da hankali na in bi shi, duk abinda yayi min wanda bai kwanta min ba yayi alkawarin tsaya mini, yace daga yau shi uba ne a gare ni ba suruki ba, in na yarda da hakan to in bi Hashimu mu tafi garin Kano.
Haka ina kuka ina komai muka shiga motar da zata kai mu Kano, ko fuskarsa ban yarda na kalla ba, don yadda na tsani Hashimu da za'a bani wuka ace kisa halal ne da na caka masa na huta. Duk wata kulawa da tarairaya yayi min a mota, komai ya gani sai ya saya mani duk da bana yarda in karba balle in ci. A haka muka iso Kano, daganan muka hau motar unguwar da yake zaune. Gidan karami ne sosai, sana'ar kayan gwari yake yi (kayan miya) a kasuwar 'yan Kaba, idan ya fita tun goma na safe sai magariba yake dawowa, kafin ya dawo kuwa na gama duka abinda zanyi na dau abinci na na shige daki na sanya sakata. Bana kara budewa sai washegari inna tabbata ya fita kasuwa.
Mun dauki watanni a haka, a wani dare da bazan iya tantancewa ba, cikin barci na ji kamar ana kokarin balla kofar daki na, kafin a yi haka na ganshi a kaina. Na soma kurma ihu ya toshe min baki ya sa igiya ba tausayi ba imani ya daure ni jikin karfen gado. A wannan bakin daren ne na samu cikin SA'ADATU. Kuma daga ranar bai kara kusantata ba, domin ya tausaya min azabar da ya gana mini. Washegari ba irin kyautatawar da Hashimu bai yi min ba, amma ba abinda hakan ya kara min banda tsanar sa.
Ban taba sanin alamun shigar ciki ba, sabida ban tashi tare da mace ba, koda naga cikin ma yana turowa ban taba kawowa a raina cikin bane, don bansan me ake a samu cikin ba. Balle in yi tunanin na samu. A haka ciki na yayi ta girma, sai da na soma jin motsi da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login