Showing 66001 words to 69000 words out of 117873 words
kun koma tare matsayin miji da mata yanzu babu laifi.
To yau ma tana jin su suna maganar kabakin abincin da za a shirya wa su Yaa Maira ita da kuyangin ta wadanda a nan za su ci abincin dare, bata dai ji hakikanin me zai kawo su ba amma taji ana maganar abinci na gani na fada zaayi yayan Askirama gabadayan su, da gudu ta kara murza key din kofar ta duk da dama a kulle ta ke. Kada ma wani ya shigo in da take. A bar ta ta ji da damuwar ta ita kadai tunda babu mai taya ta bakin cikin kaddarar da ta same ta. Karewa ma kowa harkar gaban sa yake yi, dan tausayin ta da Fulani ke ji a farko ta zubar. Abinci wannan Saade ta daina cinsa sai fruits kawai ta ke sha a firjinta, sai ko fresh milk din oldenburger gora-gora idan yunwa ta matsa mata.
Yau kwanaki biyu kenan rabon da ta sa Fulani a idonta. Wayarta ta kashe ta don ta san dole Saidu zai kira ta, ba ta san da wanne baki za ta fara masa bayanin ita matar aure ba ce yanzu, ta san babu kyau mace ta dinga muamala da wani kuma. Ta ce ita matar Uncle Yarima ce ma ai yanzu ai abun kunya ne bayan ta gama yi masa homar Yayan ta ne. Saidu-Saidun ta hakika zata yi kewar sa. Babban tsoron nata shi ne kada Yarima ya kira ta a waya.
Tuna sunansa kadai fadar mata da gaba yake yi. Duk wata kyakkyawar alaka da ke tsakaninsu a baya daga yanzu ta yanke ta. Karatun ma in dai ba hostel zaa maida ita ba ta hakura ta yafe shi har abada. Tana nan kusa da uwarta da kanwarta, a rayuwa wannan shi ne babban kwanciyar hankalinta wato ta gan ta tsakanin Fulani da Zarah.
Bayan ita ma Zaran ko za ta wuni tana buga mata kofa ba za ta bude ba sai Fulani ta zo ta kore ta a wurin.
Wajejen karfe takwas suka fara shigowa mazansu da matansu iyalin Mai Askira. Yaa Maira ce karshen shigowa har da bawan Allah Ashgar wanda bai san me ake yi ba shi dai an kira shi kuma ya zo.
Babban falon saukar bakin Fulani na musamman aka bude musu, kuyangin Fulani sai shige da fice suke suna shirya abinci na alfarma. Sai hirarrakinsu ke tashi cikin kasaita da taushin murya kamar ba magana ke tashi a falon ba sabida yadda suke yin ta cikin nutsuwa da salama. Sassan Fulani Bilkisu ya game da kamshin turaruka na alfarma, wannan na wane wannan. Ya kuma cakude da na wuta irin nasu na barebarin usli, ga sanyi da rabar iya kwandishan na ratsa su.
Ba jimawa Fulanin Askirama ta shigo cikin falon, as usual cikin kwalliya ta alfarma, ta fi kowacce iya tsara kwalliya cikin matan Mai Askira kamar yadda duk ta fi su kuruciya da daukar ido. Da faraa sosai wadda ta fiddo hakoran Makkanta na danyen gold guda biyu ta ke musu barka da zuwa. Ta dubi Mairam-Murjanatu cikin jin dadi ta ce,
Har da mutanen Istanbul? Lallai kuna ji da wannan yar kanwa taku, ga shi ta shige daki ta rufe balle ku gaisa.
Ya Maira ta ce, Kyale Saadatu kin ji? Kunya ce irin ta Baggara, me ake da amaryar da babu kunya? We really appreciate, muna nan tare har abada ai.
Mairam Murjanatu ta muskuta cikin lallausar royal chair three seater da take zaune a kai, ta ce,
Shin wane shiri ki ka yi Fulani game da biki ki gaya mana mu ji?
Fulani ta yi dan murmushi ta ce, Ban shirya komai ba. Na bar muku wuka da nama, ku ne Yayyenta kuma surukanta. Ni ina gefe yar kallo ce.
Yaa Maira ta ce, To madallah da wannan girma da anka ba mu, mu kuma za mu shirya mashahurin biki na alada, wanda za a dade baa manta a masarautar nan ba. Za mu huce na auren farko da ba mu samu yi ba.
Daga nan Fulani ta yi umarni a zo a yi serving dinsu abinci.
Sun dade suna tsare-tsare da shirye-shiryen yadda abubuwa za su gudana a junansu, bayan sun gama cin abinci. Fulani ba ta saka musu baki sai dai ta raka da eh ko aah.
Yaa Maira ta dubi kannenta su Murjanatu ta ce.
“Kamar yadda kuka riga kuka sani a aladar bikin gidan nan za mu fara da sakun lalle ranar laraba, alhamis za mu yi nakiya, jumaa wushe-wushe, ranar asabar ake daurin aure, to tunda an riga an daura ba shiri, to a ranar ne za mu yi kelatul (wanke kai da kitso na amarya), sannan mu yi Biji Ginata (ana shimfida tabarmi ne a ranar a ajiye amarya ana kida ana wakoki bayan an yi mata kwalliyar masarauta.
Ranar lahadi za mu yi kaulu na amarya da ango da safe (kaulu shi ne, zaa ajiye miyar yauki a gaban amarya bayan an mata kitso da kwalliya, Baaba za su goyo amarya (sisters din Maimartaba su ne Baaba) su kai ta wajen Kaulu, yan uwa da iyaye su dinga dibar wannan miyar yaukin suna shafa mata. Da daya da daya kowa zai zo yana shafa mata yana ajiye wa amarya kyauta, wasu har gold suke badawa, wasu iphone ko mota ya danganta da mukamin mutum a masarautar, wasu kuma kyautar kudade suke yi, kaulu kenan.
Da yammacin lahadi kuma za mu yi ‘dubdo’, wato wunin biki a gidan amarya bayan an kai ta ranar asabar da daddare (a wannan ranar yan uwa da iyaye za a wuni ana shige da fice a gidan amarya.
Ke kuma Fulanin Maimartaba ke ce da alhakin yin Miskero (abincin da ake kai wa gidan amarya ranar wunin) wanda jamaa da ke shiga da fita a gidan za su ci.
Sannan a satin bikin gabadaya har ila yau ke za ki dinga ciyar da amarya da ango abinci mai kyau. Har zuwa ranar da za a kai amarya, wato asabar.
Idan asabar ta zagayo kuma ana ‘tulur’, wato sati daya da kai amarya, ranar ne ke da kawayenki (Fulani Bilkisu) da yan uwan amarya za ku je gidan amarya, mu kuma za mu yi mata kwalliya, sai a saka mata muciya a hannu, a ranar za ta fara girki kenan, ana wakoki da raye-raye, a ci a sha, to daga nan biki ya kare.
Ranar asabar kuma za mu kawo lefe.
Fulani ta ce, Turkashi, wani aiki sai Amale, bikin Kanuri sai Askira! Allah ya sa muna da rabon gani.
Aka yi adduoi aka shafa, bayan mazan ma sun yi nasu tsare tsaren, sannan duk suka fara watsewa. Amma sai da daya daga cikin kannen Yarima da ake kira Houdda yar dakin Yakirjinoma ta je har kofar dakin Saade ta yi magana ta hudar kofar dakin tamkar mai yin waka cikin harshen Kanuri.
Ki gama boyon amarya, kin riga kin zo hannu, da sannu za mu yi miki kaulu, kelatul, biji ginata da tulur, sannan mu damka wa Yarima ke.
Murjanatu ta zuba mata duka a baya [dundu], ta ce, Houdda kar da ki tsoratata ta kara kunshewa a daki duk zafin nan da ake yi, in kika firgita masa amarya ke da shi ne, kin fi kowa sanin halin sa.
Saade da ke cikin daki duk tana jinsu ba ta san sanda ta fashe da kuka ba..
Da gaske dai ya tabbata an yi mata auren kenan, this is the reality da take ta kokawa da zuciyar ta wajen yarda da shi. Take yaudarar kanta da kanta da cewa mafarki ne. Iyalin Askirama bazasu bata lokacin su su zo har da na wata kasa ba idan ba gaskiya bane. [They are very serious people] a sanin data yi musu. Auren kuma ba da kowa ba sai UNCLE YAREEMA! Yariman da ta yi wa farin sani, uban dakinta mijin Aisha-Sultana. Yanzu ya tashi daga mijin Sultana ita kadai, ya koma mijinsu su biyu. Da wane karfin zuciya za ta iya karbar wannan sauyin rayuwar na bagatatan da ya zo mata rana daya?
Ta tura kanta karkashin filo tana ta kuka, wani irin kuka wanda tun lokacin da Fulani ta sanar da ita zancen auren ba ta yi shi ba sai yanzu. Yanzu data ji ana shirye-shiryen biki kain da nain daga kowanne bangare.
Daga bakin kofa ta ji ana sallama da wata irin murya cike da doki da zakuwa ga son ta bude. Muryar da ba za ta taba mantawa ba. Ko mutuwa ta yi ta dawo bazata kasa shaida muryar Hanne ba, Hannenta, Hannen Tsanyawa! Diyar Innar Hanne da Baba Saleh.
Ai ba ta san lokacin da ta isa ga kofa ta bude ta da sauri ba.
Hanne da Saade aka tsaya ana kallon-kallo, kafin su runtuma da gudu su rungume juna tsam tsam.
Cikin yan kallon sakanni da suka yi wa juna, kowacce ta karanto irin sauyin rayuwar da ke tare da yar uwarta. Bi maana, Hanne ta gano tarin sauyi na ci gaba da nasarar rayuwa a tare da Saadenta, domin inda a hanya ta ganta ba za ta gane ta ba, to dadin abun mahaifiyarta Fulani ce da kanta ta tabbatar mata Saade na cikin dakin nan a kwance, in ta yi magana ta ji ita ce za ta bude mata.
A yayin da Saade ta hango tarin nakasu da koma baya a rayuwar Hannenta, ta zama kamar mai shekaru arbain bayan ko ashirin ba su rufa ba. Ta yi baki; ta rame; ga goyon wani katon yaro a bayanta wanda da gani ka san ya wuce goyo domin har rinjayarta yake. Saade ta soma kokarin kwanto dan daga bayanta don Hanne ta ji dadin zama, suka karasa bakin gado suka zauna suna hawaye.
Ina Baba Saleh?
Abin da Saade ta fara tambayar Hanne kenan. Hanne ta idasa rushewa da kuka, ta ce,
Baba ya jima da rasuwa Saade. Baba ya dade a kushewar sa. Mu kuma ba mu san garin da ki ke ba da tuni mun zo, shekara da shekaru muna kewarki.
An yi min aure shekaru hudu baya da saurayinki Naziru, tunda na samu ciki ya gudu birni ya bar ni yau shekaru hudu ba mu kara jin labarinsa ba, kin ga dan da na haifa masa nan, Inna ta sa masa sunansa Naziru.
Jiya kawai muna alwala a gindin rijiya sai ga sako daga gidan Maigari wai mu zo an zo daukarmu za a kawo mu inda ki ke. Inna Laure ta ce ba zaa zo da mu ba, ita kadai zaa dauko, sai da direban ya ce an ce masa iyalin Baba Saleh da Inna Laure, sannan ta yarda aka taho da mu.
Saade ta rungume dan Hanne a jikinta tana tuno Naziru don kamar su daya, ta ce, Yanzu ina Innarmu da Inna Lauren?
Aka bude kofar dakin aka shigo, Fulani ce, sai tsofaffin guda biyu biye da ita. Duk sun tsufa sun yamutse a idon Saade. Tana kuka ta ke rungumarsu daya bayan daya, ta ce,
Inna, ku yafe min. Na dade ban neme ku ba, ajizanci ya tabbata gare ni, wallahi karatu ne ya sha kaina sam bana samun hutu.
Inna Laure da Innar Hanne suka rike ta suka zaunar a tsakiyarsu suna fadin, Babu komai Saade kin ji? Allah ne ya nufa sai yanzu za mu sake haduwa, komai kana da niyya sai Allah ya nufa.
Innar Hanne ta ce, Shi ma Babanku yana ta wakar zai dawo ya sake duba lafiyarki, sai cuta ta sarke shi, bai jima yana jinya ba mutuwa ta raba mu. Mu kuma ba mu san garin ba, mun dai san masarauta ce a Borno. Sai yau da ki ka sa aka tura har Tsanyawa aka dauko mu cikin mutunci a mota.
Ashe Saade aure ya zo? To Allah ya sa an yi ke nan, Ya ba ku zaman lafiya.
Saade kamar jira take sai ta rushe da kuka, ta ce, Innar Hanne ku roki Fulani, don Allah ta bai wa Maimartaba hakuri, bana son auren.
Inna Laure ta ce, Kul Saade! Aure sunnar Annabi ne, wanda ba ya son sunnar Manzon sallallahu alaihi wasallam hakika Manzon rahma ya ce ba ya tare da shi. Ni dai rokonki zan yi ki yafe mini, na ga babbar ishara a kanki, duk abin da na yi miki kin manta ki ka ce a je a dauko miki ni har Tsanyawa. Ta saka kuka sosai.
Saade ta ce, Inna Laure, ni ba ki yi mini komai ba sai alheri, rike ni da ki ka yi tun ina karama shi ne babban alherinki gare ni, don haka ni komai ya wuce a wurina.
Daga nan hirar ta koma kan yadda auren Hanne da Naziru ya kasance, Innar Hanne ta ba ta labarin Naziru ya sha kuka bayan tafiyarta Askira, A karshe da ya tabbatar ba za ki dawo ba ya like wa Hanne, Baba Saleh ya cire ta daga makaranta ya ba shi aurenta cikin mutunci. Amma tunda Hanne ta samu ciki aka neme shi aka rasa a Tsanyawa sanadin kamuwar Babanku da hawan jini ke nan.
Hanne ta haihu a gida, ba ta jima da haihuwa ba Babanku ya cika, ni na yi ta dawainiya da su da sanaoin hannu iri-iri har kawo yau.
Fulani ta ce, tunda ya shekara hudu bai dawo ba kuna da damar kai kara kotun muslunchi a ba ta yancinta, ko ta samu ta yi wani auren. Shi kuma in da gangan ya gudu ya barta Allah zai saka mata, in kuma wani uzurin ne ya rike shi, Allah ya sada su da alkhairi. Zan yi magana da Maimartaba ya shige muku gaba Hanne ta samu yancinta.
Hanne ta ce, Burina kenan, ban san ina da wannan damar ba da tuni na yi amfani da ita. Ina matukar son in koma makaranta in raini Naziru shi ma in sa shi makaranta.
Fulani ta ce, Kada ki damu Hannatu, insha Allahu komai zai yi daidai bari mu kare bikin Saade.
Sai da suka raba dare suna hirar yaushe gamo, a dakin Saade duk suka sauka don saboda zuwansu ta manta da damuwar ta, ta cire wa ranta kunci, ta ware suna ta hira da Hannenta.
Washegari Fulani ta raka su suka yi gaisuwa wajen Askirama, ya ji mutuwar Baba Saleh sosai, Fulani kuma ta gaya masa maganar Hanne, Askirama ya ce zai shiga maganar bayan biki insha Allahu.
Tun zuwansu Hanne, Saade ta samu walwala, amma ta ki kunna wayarta. Tabbas da ta ga sakonnin Yarima Sageer har guda uku. Sako na farko ga abinda Yarima Sageer yace.
“Thank you for being the PRINCESS Im waiting for.Thank you for coming to my life when my heart is desperate to have you..(Madallah da zamowar ki GIMBIYAR dana ke jira tuntuni, madallah da zuwan ki cikin rayuwa ta a lokacin da zuciyata ta dimauce ga son mallakar ki).
- Sageer.
Na biyu kuma yace.
“Saadatu save a soul by picking my call(Saadatu ki cece ni ki daga kira na).
- Sageer.
Sakon Yarima na karshe ga Saade cikin harshen hausa ne, ga abinda Yareema ya rubuta ma Saade.
Kin ki bude waya saboda ni ko Saadahtouh? Bonono kenan rufe kofa da barawo. Bari in tuna miki wani abu guda daya da baki sani ba ko kika manta; daga rana irin ta yau mun zama abu guda,tare zamu kare rayuwar bakidayan ta,daga nan har gaban abada, ko makwanci bazamu kara rabawa ba sai bisa unvoidable reason..
Duka wannan bidirin da Yarima ke yi shikadai yake yin abinsa Saade bata san yana yi ba don kememe ta ki kunna wayar ta kamar ta san tashin hankalin dake jiran ta cikin ta daga zafafan kalaman sa [ba raba makwanci har karshen rayuwa].
Da ga karshe Yarima ya kasa hakuri, Saade ta kure dukkan hakurin sa, idan ba ganin ta yayi ba ba zai samu nutsuwar fuskantar bikin nan dake gaban su ba, ba zai koma nitatstsen Sagirun sa ba, matukar son ganin Saade yake anyhow ko jin muryar ta, don ya ga da fuskar da ta karbe shi matsayin miji ne ko akasin sa? Ko har yanzu kallon Uncle take masa?
Ya aiko a gaya wa Fulani ta yi ma Saadatu magana ta kunna wayar hannunta su yi magana, mai muhimmanci. Da Fulani ta sa Fanna ta gayawa Saade, sai Saade ta ce ma Fanna ta ce da Fulani ta kunna har sun yi maganar, bayan kuma ko taba wayar daga inda ta yi mata kyakkawar