Showing 36001 words to 39000 words out of 117873 words

Chapter 13 - Masarautar Mu 1 to 4 Complete

wutsilniya na tabbatar cikin Hashimu ne a jiki na.
To dama haka ake samun cikin kamar kiftawar ido? Kamar azal?
Fadin tashin hankalin da na samu kaina abu ne da bazai fadu ba, nayi kuka nayi kuka har na ji babu dadi. A karshe dole na dangana, ina ji ina gani na haifewa Hashimu 'ya.
Tunda na samu kaina na ce saidai ya sake ni ko in kai karar sa. Shikuma a lokacin ba abinda yake so a duniya irin rayuwar jaririyar sa, na fice mai a ka, sabida duk iya kyautatawar da namiji zai yiwa mace a duniya domin ta so shi yayimin, amma na kasa kallon shi da kauna komai kankantar ta. Ba don komai ba sai don abinda yayi wa mahaifi na, da hanyar da ya bi ya samu aure na.
Sai yace "mu yi jinga, na yarda zan sake ki, amma bayan kin shayar min da yarinyar nan na tsayin shekara daya kacal, ni kuma zan sawwaka miki kije duk inda kike son zuwa".
Da wannan yarjejeniyar na yarda na shayar da Sa'adatu na tsayin shekara daya. A ranar da ta cika shekara daya ya cika alkawarin sa ya sake ni saki daya. Yace ga gida nan ya mallaka mini albarkacin haihuwar Sa'adatu, ya san bani da kowa, ya san bani da inda zani, amma tunda haka na zabawa kaina shi ya bar min gidan, ya dauki 'yar sa yace kauye zai koma ya raine ta.
Wannan ba damuwa ta bace tunda na samu 'yancin kaina. Ba wadda zata san zafin kiyayyar namiji sai wadda aka yiwa irin auren da aka yi min. Auren dole is a challenge da ba duka mata ne zasu iya jure shi ba.
Kwana bakwai a tsakani na sayarwa da makocinmu gidan, na kulle kudi na sai tasha, na hau motar Maiduguri, don na kudurce a raina ni da Damaturu har duniya ta nade.
****
Aka sauke mu a tashar Bama, daga nan na rasa ina zan nufa. Ga yunwa ga gajiya. Haka na hau tafiya a gefen titi dauke da kullin kaya na. Tunani yayi min yawa har bansan na hau bisa titi ba, a yayin da zungureriyar motar ta shararo a guje, duk kokarin da direban yayi bai yi nasarar kauce min ba sai da ya kwashe ni ya watsar bisa titi.
Jini kuwa ya balle ko ta ina, baka jin komai sai salatin mutane. Sauran motocin dake biye dasu in convoy duk suka dakata a gefen titi. Fadawa suka fito bisa umarni suka ciccibe ni suka saka a mota sai asibiti.
Ban samu kai na ba sai bayan awanni uku. Na farka na ganni a wani hamshakin asibiti. Likitoci farar fata fal a kaina, ga karin ruwa ga karin jini, juyawar nan da zan yi sai na yi tozali da wani babarbaren mutum ma'abocin zati da kamala, mai yawan murmushi, yasha nadin rawanin da ya tabbatar min yana da alaqa da babbar sarauta. Baza'a kira shi tsoho ba, amma kuma ba yaro bane ko kusa. A bayan sa Fadawa ne guda biyu a tsaye sai muzurai suke. Ya fara da bani hakuri, sannan ya gaya min an dauko shi ne daga Airport zasu wuce garin su direbansa yayi duk kokarin da zai yi ya kauce min Allah ya rubuta sai sun kade ni. Ya tambaye ni sunana na gaya masa. Ya ce in bada kwatancen gidan mu aje azo dasu sabida na samu karaya a kafa da hannu bazai yiwu a sallame ni a yau ba.
"Bani da uwa bani da uba, bani da 'yan uwa, nikadai ce. Ban da kowa, kuma bani da inda zani". Na bashi amsa cikin kuka na zafin ciwo. Maimartaba Sarki Yusufu mai Askira, ya dade yana kallo na kafin ya ce
"Kin yarda ki bini masarautar Askira cikin amana in zame miki uwa da uba sannan MIJI abokin rayuwa?"
Haka naji furucin sa tamkar cikin mafarki, na kasa yarda da abinda kunnuwa na suka jiye min, na kasa amincewa ido na biyu it was just in a dream..... (and that was how I became a QUEEN) wannan ne silar zamowata Sarauniyar amaryar sarkin Askira, wanda daga kallo na farko na ji ya kwantamin a rai, da wani irin exceptional feelings..., wata irin kwantacciyar soyayya da kauna, da ban taba ji a rayuwa ta ba.
Komai ka ga ya faru da bawa to dama can rubutacce ne a lauhul-mahfuz, na yarda rabon Sa'adatu ne ya sabbaba aure na da mahaifin ta, ban taba jin son sa ba, domin soyayya ta Allah ce. Shi yake kimsa ta a zuciyar bayin sa. Haka itama kiyayya. Amma a ganina da ba ta hanyar da Hashimu ya bi ya aure ni ba kenan zan iya hakurin cigaba da zama da shi ko don maraici na dacrashin gata na.
Bayan na gama iddah a gidan Liman inda aka yi min masauki, Limamin Askira shi ya zama waliyyi na, Wazirin gari Ibrahim ya zama waliyyin Sarki Yusufu suka daura mana aure, auren da ya jawo cece-kuce mai yawa a masarautar Askira domin Sarki Yusufu bai taba auren diyar talaka ba balle mara asali mara dangi. Duka matansa 'ya'yan sarakuna ne daga masarautu daban-daban na jihar Borno. Gorin kishiyoyi da damuwar rashin dangi dana shiga shi yasa maimartaba maida hankali ya binciko min dangin mahaifana, wadanda suka zo kasar Nigeria tare, ta hanyar su ne aka bi aka cimma sauran a Chadi duk da cewa da yawa sun watsu cikin duniya wasu kuma sun murmutu. Kusan mutum biyar aka samu masu alaqar jini da iyaye na a kasar Chadi. Sannan ne na samu kaina daga gorin rashin asali dana dangi daga wajen kishiyoyi na. Aka maida gorin kan ('yar talakawa).
Rayuwar gidan sarauta rayuwa ce mai wahala, musamman ga ni da ban ta so cikin sarauta ba, na sha wahala ba 'yar kadan ba a hannun Ya Gumsu, ita Ya Kirjinoma bata da matsala sosai, ita kuwa Hibbani sai munafurci da tsugudidi da daukar zance. Sa'a ta guda daya ce; matsanancin son da miji na ke yi mun, wanda yayi maganin kowacce damuwa da kowanne kalubale dake cikin babban gidan sarautar Askira.
Sarki Yusufu bai kyale ni haka ba cikakken ilmin addini dana boko ba, malama ya dauka mai digiri take zuwa har gida tana koyar dani karatu da rubutu na zamani, sannan ya daukar min malamar karatun addini, don haka daidai gwargwado inada sani a duka fannonin har fiye da kishiyoyi na wadanda girman kai ya hana su zama daukar karatu wurin kowa. A cewar su wanda suka yo a gidan iyayen su ya ishe su.
A haka nayi haihuwa har biyar 'ya'yan basa sati a duniya suke komawa.
A cewar maimartaba alhakin SA'ADEN dana baro a lokacin da tafi bukatata ne, ko hakan ne ko ba hakan bane a halin yanzu na yarda na amince akwai hakkin Sa'ade a kaina, wanda ya zama dole in nemi yafiyar ta, ban taba ganin yarinya mai hakuri da son mahaifiya irin Sa'adatu ba.
Mahaifiyar da ko sau daya bata taba kyautata mata ba!!!
Amma kullum ta zo gaba na sai annurin fuskarta ya canza. Walwalar ta ta karu.
Sai ta nuna kaunar da ta ke mun cikin fararen kwayan idanun ta.
Meye laifin ta akan tsakanina da mahaifin ta?
Bata san komai ba, bata san an yi ba. Don haka cikin mu'amalar mu ta Uwa da Da na amince akwai daukar hakki......

A hankali Fulani Bilkisu ta sake lumshe idanun ta. Ta bi kofar dakin Sa'ade da kallo, inda take jiyo karadin su ita da Zarah.
Ko in ta baiwa Sa'adatu labarin nan zata yi mata uzuri ta yafe mata?? Domin hakika ta cuzguna mata ba dan kadan ba.
Wannan tunanin ne ya sa ta mikewa tsaye, ta doshi dakin Sa'ade cikin sanyin jiki da mutuwar zuciya......
****

"Bude bakin.....haa...in sa miki choculate" ta ji Sa'ade na fadi a lokacin ta tura kofar dakin, ta same su bisa gado itada Zarah, har sun sake wanka sun sake kayan jikin su kasancewar akwai wasu kayan Zarah a dakin Sa'ade sabida yawan yi mata wanka data ke yi idan tazo hutu. Murmushi Fulani tayi ta karasa gare su ta zauna a gefen gadon. Sa'ade ta saki baki tana kallon ta don abu ne da bata taba gani ba; Fulani a zaune gefen gadonta tana mata murmushi irin na UWA....murmushin Fulani, da zama akan gadon ta ya dugunzuma zuciyar Sa'ade. Kullum ta shigo tana tsayawa ne daga bakin kofa ta fadi sakon da ya kawo ta ta juya. Yau kuwa kyakkyawar fuskarta a sake, dauke da murmushi mai taushi. Ta lura da kallon tsoron da Sa'ade ke mata sai ta kara kashe ta da lallausar murmushi.
"Ki daina dura mata chocolate baki ga hakobranta duk sun cinye da zuma ba?" "Tana so ne Fulani, kuma da ta fara fanfara duk ficewa zasuyi masu kyau su fito". Ta sake yin murmushi, "an gama makaranta sai aure ko? Ko baki da saurayi ne?" Nan da nan Sa'ade tayi kicin-kicin da fuska kamar Fulani ta aiko mata da sakon mutuwa. Kamar zata yi kuka tace a shagwabe "to ni ina nake zuwa balle inyi saurayin? Daga makaranta sai daki na, ko tsakar gidannnan ba bari na kike in je ba, sabida bakya so a gane ni 'yar ki ce. Kuma Alanguburo yayi min alkawarin tafiya Jami'a a Abuja idan na ci SSCE dina, ke kuma kina zancen aure".
Fulani ta dora hannayenta biyu akan kafadun Sa'ade duka biyun tana murmushi tace "karatu ai ba ya hana aure Sa'adatu. Sanda ina kamar ki haihuwata uku don dai basu rayu bane, kuma shi Alanguburo ai ra'ayin ki yake bi amma ni da shi duka mun fi so mu yi muki aure....." da sauri ta tare Fulani "to sai ku bari sai Allah ya kawo mijin, ni 'yar mitsitsiyata dani....." ta fada tana zumburo baki. Fulani tayi dariya ta dalle mata siririyar fatar bakin nata "zaki je makaranta kamar yadda kike so, amma bazamu bari ki zauna a hostel ba, saidai gidan Yarima, tunda shi malami ne a makarantar zai taimaka miki, sannan gidan sa cikin jami'ar yake, zaki samu saukin zirga-zirga".
Fuskar Sa'ade ta nuna ba haka ta so ba, campus life take sha'awa, ta ganta a jami'a tana rayuwa a cikin dalibai 'yan uwan ta, rayuwa ta 'yanci ba irin ta EL-KANEMI ba. Sa'ade ta ga cewa zuwa jami'ar ma da aka barta dama ce, domin babu wadda ta samu irin wannan alfarmar a 'ya'yan gidan, da sun gama sakandire Askirama ke aurar dasu, itama ya duba maraicin ta ne da kuma tunanin karatun shine gatan da zai yi mata a rayuwa ranar da baya doron kasa.
Ta tambayi Fulani ko wanene Yarima? Da ta ce a gidan sa zata zauna a Abuja? Fulani tayi mata bayani yadda zata gane cewa babban dan maimartaba ne a maza, shine Yarima mai jiran gado, Chiroman Askira, wanda ya dawo daga kasar Amsterdam shekarun baya yayi aure.
Sa'ade ta kwantar da ido tana kallon Fulani, ganin yau akwai rahma tattare da ita, watakila in tayi sa'a ta gaya mata abinda ta dade tana son ji daga gareta....an ce Dama tana zuwar wa dan adam sau dayane a rayuwa....watakila daga yau din bazata sake ganin murmushin mahaifiyar ta ba, bazata sake ganin ta cikin wannan maternal mood din ba...don haka ta tambayeta abinda ta dade yana cin ta a zucci....
"Don Allah Fulani me yasa ba kya so na? Me babana yayi miki kika tsane shi? Meyasa kike bakin cikin kasancewata diyar ki? Fulani ko don ni babana talaka ne shine dalilin da......." ta kasa karasawa sai kuka ya kufce mata, tana tuno bad memories na tun zuwanta hannun mahaifiyar ta.....
Ga dukkan madaukakin mamakin ta, sai jin hannun Fulani tayi ya zagayeta cikin runguma kyakkyawa, ".....Ban taba kin sa don yana talaka ba, hasalima ni a mai arzikin sa na san shi. Ban taba neman komai a hannun sa na rasa ba, ya ciyar da ni ya tufatar da ni a tsayin zamana da shi. Laifin sa gare ni daya ne....hanyar da ya bi ya aure ni.....". Tiryan-tiryan ta soma bata labarin ta, labarin da ya dauki hankalin Sa'ade har bata san lokacin da tace.
"Lallai Baba bai kyauta ba. Amma ki dubi Allah Fulani ki yafe masa albarkacin ni da nake tsakanin ku, da kuma kasancewar a halin yanzu ba ya duniyar".
Ta fada tana share hawaye. Fulani ta kara jawota jikin ta, ta sanya fuskarta cikin tafukanta "daga yau kin daina zargi na akan babanki? Kin daina ganin beke na a kan sa?" A hanakali Sa'ade ta gyada kai. Ta ce "to na yafe masa duniya da lahira, kema ki yafe mini deprivation dina a gareki da yadda na tafiyar da ke a zaman mu tare. Nayi kokari in tanqwara zuciyata na kasa....amma alhamdulillahi yanzu na samu sauki daga duk wani duhu da kullaci dake cikin raina".

Ranar sai ta zama ranar reunion ta soyayyar uwa da 'yar ta. Kusan kwanan zaune suka yi a dakin Sa'ade, tana bata labarin rayuwar data yi tare da mahaifin ta a garin Tsanyawa tun tana karama har girmanta, da rayuwar wahalar data yi a hannun inna Laure da kuma yadda mutuwar mahaifinta ta kasance, har zuwa yadda suka yi suka zo Askira ita da Baba Saleh.
Sai ga Fulani Bilkisu tana share hawaye, "nikuma na zo na yi shekaru shidda ina cuzguna miki, a matsayi na na mahaifiyar data haife ki. Bayan a lokacin ne ya kamata ki ji dadi kamar kowanne da a hannun uwarsa...don Allah Sa'adatu ki yafe mini".
"Na yafe miki Fulani ban taba rike ki ba, kullum ina gayawa raina ne kina da hujjar ki, haka kawai uwa bazata ki dan ta ba, Allah ya yafe mana bakidaya".
Tun daga ranar, mu'amalar Fulani Bilkisu da diyar ta Sa'ade ya canza, ta cire mata takunkumin fita, ta bata damar shiga ko'ina take so cikin masarauta, bata ki ba don gaskiya ta fito gaban kishiyoyin ta a yanzu cewa Sa'ade 'yar ta ce, tunda ta san ba shegiya bace da uban ta. Ta ja ta a jiki har fiye da kima, idan zata shirya abincin mai Askira kasancewar da kansu suke masa abinci sai ta kirata sun shiga kicin tare, tana yi tana mata bayanin yadda ake komai, anan Sa'ade ta koyi girkin sarauta iri-iri dana zamani, kasancewar Fulani Bilkisu kwararriyar kuku. Ta kuma dinga koyawa Sa'adatu tsaftar jiki data muhalli da amfani da turarukan Borno a jiki da tufafin ta.
Duk da ta bawa Sa'ade damar shiga koina cikin masarauta Sa'ade bata yawon, kullum tana sassan su ko dakin Fulani, ko kuma suna kicin suna girkin Askirama idan ita ce da girki. Hatta gashin kan Sa'ade Fulani da kanta ke zama ta gyara mata yanzu, gyara na masu kwarewa akan kula da gashi, wata irin shaquwa suke yi cikin 'yan watannin nan wadda basu taba yin ta a shekara shidda da suka yi tare ba, ta yadda har Fulani ta soma zullumin zuwan ranar tafiyar Sa'ade makaranta Abuja.
Maimartaba ya fi kowa jin dadin wannan sauyi da ya ke gani a tattare da Bilkisu da 'yar ta Sa'adatu, 'yar da yake jin kamar shi ya haifeta saboda son da yake wa mahaifiyar ta. Jin dadin hakan yasa ya hada musu tafiya umrah karshen wannan watan don dai su kara shaquwa da juna ba idon kowa tare dasu, amma dole tareda Fanna zasu tafi sabida kula da hidimar Fulani.
A saudiyyah ba abinda Fulani Bilkisu ke roko a wurin Ubangiji sai miji nagari ga Sa'adatun ta, wanda zai rike mata ita amana ya rike maraicin ta, wanda ba zai taba duban asalin ta ya wulakantata a kan sa ba. Wanda zai zame mata miji kuma uba sannan Yayan da bata da shi a kafatanin rayuwarta.
Ta kuma sakankance cewa an amshi rokon ta, don wannan shine ladabin addu'a. Ba son tafiyar Sa'ade jamia'ar Turkawa take ba, amma ta yarda da hujjojin Maimartaba, na cewa gara Sa'ade tayi karatu kafin Allah ya zaba mata mijin aure. Karatun zai zamo gata kuma majingina a agareta ranar da babu su.
Suna dawowa suka tarar da sakamakon su Sa'ade ya fito, Mai Askira da kansa ya kira Yarima ya gaya masa kowacece Sa'ade, gaskiyar ya gaya masa cewa 'yar Bilkisu ce. Ya damka masa komai na alhakin nemo mata makaranta da daura masa dukkan nauyin hidimar karatun ta. Ya kuma gaya masa a gidansa zata zauna ba a hostel ba. Wata irin zufa ce ta soma ketowa Yarima ko mu ce Chiroman Askira. A tsarin rayuwar su shi da matar sa, ko kuda basa so ya gifta a tsakanin su balle dan mutum ya zauna a cikin su.
An tarbiyyance su da rashin yin musu ga magabatan su, an raine su a bisa bin umarnin na gaba, balle Mai Askira gabadaya. Don haka amsar sa ita ce kawai "toh" amma a ransa ya ce kora da hali kawai zai sa yarinyar ta bar masa gidan sa. To amma

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login