Showing 117001 words to 117873 words out of 117873 words
ta ji dadin yadda Ya Gumsu ta dage ta hana a baiwa Yarima concubones, ta san da watakila shikenan ta bar shakar numfashi daidai a duniyar subhanah.yammata hudu rus! Ga Yarima Sageer? Ai karshen ta a barrow zaa kwasheta zuwa asibitin masu dan karamin tabin hankali.
Shima Askirama jin baki ne irin nasa, don ya san ba abinda Yarima ya ki jini irin ace ya kara aure. Da an fadi hakan zai jawo ayar Allah ya ce sai zaku iya adalci, shikuma bai iya adalcin tsakanin Saadatu da wata diya mace, da muguwar rawa gwamma kin tashi. Shiyasa Askirama yake so ya dauki kwarkwarori duk adadin da yake so, amma wani zubin har zuciyar sa yana ganin Yarima ya hada da concubines zai kara fiddo da kimar sarautar sa.
A yanzu dai Yareema Sageer ya ce baya da bukata bai sani ba dai ko can gaba in ya fara tsufa.
Baby ya ci sunan Askirama YUSUF. Ana kiran sa Chiroma. Tsakanin Mai Askira daYa Gumsu ban san wa ya fi son jikokin nan ba. Ya Gumsu kullum ta dubi yaran sai ta kara nadama ta yi dana sanin ja da hukuncin Ubangiji, lalle ne ko rabon wadannan yaya biyar ya isa ya kayar da ita kwanan ta bai kare ba.
A halin yanzu ta fi kowa alfahari da auren Yarima da Saade ta kuma yardada abinda Askirama ke fadi cewa Saadatu diyar Bilkisu,rufin asiri ce, suttura ce ga dan su Yareema Sageer Yusuf Askira.
Masha Allahu laquwwata illa billah.
Nan na kawo karshen littafin MASARAUTARMU 3&4. Kurakuran dake ciki ku tayani rokon Allah ya yafe mini. Abin alfanun da ke ciki Allah ya hada mu a ladan nida ku bakidaya.
Sumayyah Abdulkadir
18/11|2021.
Ina mukualbishirda sabonlittafinamaisuna NA HUCE!Wanda zaizo a matsayingoronsabuwarshekarainsha Allah.
TUNA SUNAN SA;
NAHUCHE (DagaFushina)
NA HUCE..
LITTAFIN
SUMAYYAH ABDULKADIR
Hawayen da yake ta rikewa ne suka kwace masa, ya juya kadan ya dubi Rahinah wadda ke kallon bayansa a lokacin, suka kuma hada ido, ji ta yi zuciyar ta na son karyewa (rauni irin na diya mace na son mamayar ta) amma ta amince wannan shine decision mai kyau ga rayuwar ta.
Sai ta maida idanunta ta lumshe su a hankali. Tana sauke ajiyar zuciya.
Shi kuma ya sa kai ya fita daga dakin, babu ko waiwaye. Kamar yadda yake ji a ransa ba zai kara waiwayar RAHINAH OMAR a rayuwarsa ba. Ko da bayan cikar burin ta, na zama cikakkar otorhinolaryngologist.
****
Ta dauki hoton karamin kyakkyawan yaron mai kama da ubansa a komai tana kallo with so much adoration, hawaye na sauka a kan fararen kundukukin ta. Ta san yanzu ya girma, watakila aji hudu na firamare? Cikin kowanne hali dai ta san zai kula da shi. Damuwar ta ba a kan kulawar da yaron zai samu ba ne domin hakika tana da tabbacin HABIBUNAHUCHEzai kula da dansa har fiye da yadda yake kula da Hotels din sa. Damuwar ta akan yadda har gobe ta kasa kallon kowanne namiji da idanun sigaraure, kowa ya zo sai ta ga bai kai shi ba, ko farcen kafarsa bai kama ba, ko da kuwaya fi shi komai na rayuwa.
Duk da cewa ta san shi ne kawai a matsayin dalibin jami'ar Cologne ba'a matsayinsa na yanzun ba (mamallakin NAHUCHE HOTELS) amma tana bibiye da duk wani fadi-tashinsa na rayuwa tun daga ranar da ya raba ta da Dan su.
Dalilin bibiyar ne ba ta sani ba har yau, tunda ita ta ce bata son sa. Farin jini kam har bata san irin nata ba, manema ba irin wadanda Allah bai ba ta ba, kuma burin Dada shine ta yi aure tun kafin Allah ya dau ranta, amma har gobe ta kasa kallon kan sauran maza daga shi sai dan mutanen NAHUCHE. The one that took away her pride na diya mace. Wanda ta tabbatar zuwa yanzu ya manta da ita, a irin shuhurar da Allah ya yi masa cikin shekaru goma kacal da rabuwarsu.
Bata san hawaye take ba. Sai da ta ji dandanon gishiri a bakin ta. Hawayen da ta tabbatar ba za ta daina zubar da su ba har zuwa karshen rayuwarta. Idan har rayuwa ba ta koma yadda take a baya ba; with him aside.
"Auren Wucin Gadi".
"Auren kwanaki bakwai kacal". Wadanda abubuwan da suka wakana cikinsu sun fi tsayin na shekaru bakwai. Wanda ya samar da kaddarar Dan da ke a tsakani, Dan da silar zuwansa duniya ne ya yi connecting komai, ya hada zukata ya kuma raba su cikin kwanaki bakwai. Jami'ar Cologne din Jamus ita ce tushe, mafari, ginshiki na dukkan walagigin rayuwar da ta samu kanta.
-Takori