Showing 48001 words to 51000 words out of 117873 words
ba son sani nake ba" ta fada, her voice trembling. Kai gabadaya tsokar zuciyar ta ma rawa take sabida closeness din dake tsakanin su da kamshin Paco Rabbanne da yake hargitsa ta.
A hankali ya ja da baya yana murmushi yace "ki ce ma Fulani, ai mutum baya cutar da abinda yake so ya zama nasa gabadaya. Ta bar ki kiyi hira da Yayanki. Fi-amanallah, har zuwa lokacin da zai dau ajiyar da ya bata".
Bata gane zaurancen sa ba amma ta ce "toh" da sauri don ta samu ya bar ta haka, tayi jinyar sababbin abubuwan da ke ziyartar ta, a zuciya, ruhi da gangar jiki gabadaya.
"Gobe zamu fara karatu ni da ke, physiology will never fail you again. Na bar ki lafiya".
Har ya fita bata san meyasa ta kasa dauke ido akan sa ba, al'amuran sa na yau masu ban mamaki ne data kasa gane inda yasa gaba.
A hankali tabi lafiyar gadon ta, ta lumshe ido tana tariyo maganganun Yarima Sageer daya bayan daya. In wani yace mata yana magana haka zata karyata. To me ya canza shi haka? Me ya kawo canjin? Sai dai kuma ga mamakin ta ta kasa kiran Fulani ta gaya mata abinda yace din duk da bata iya boye mata komai. Amma wannan karon sai ta ji ta kasa. Kamar tana jin kunya.... Kamar yadda barci ma ya gagare ta. Sai scenes din Uncle Yareema ke mata gifcin gizon makauniya.
****
Washegari da safe basu hadu ba, kowa ya kama gaban sa, cikin daren an tafka rigima tsakanin Yarima da maidakin sa Aisha-Sultana, yace tunda ta yaudareshi ta cire mahaifarta ba da sanin sa ba tasa a ranta ta bashi lasisin auren wadda zata haifa masa 'ya'ya.
Sultana ta dauki kalaman nasa a matsayin abinda ake kira 'shifcin gizo', watakila ya fada ne out of frustration na ta cire mahaifa, amma in ma mafarki yake na zai hada ta da wata diya mace a duniya su yi sharing din sa ya dade bai farka ba. Lokuta da dama in a buge take bata mayar masa da magana, tana bin shi da ido ne kawai. Wadanda basa ko buduwa sosai. To yau ma hakan ta bishi da rinannun idanun ta har ya shige turakar sa.
Zaune take akan irin kujerun sumintin nan na cikin makaranta karkashin wata bishiyar lemon tsami mai duhun ganyayyaki, fitowarta kenan daga lacca ta zauna tana kara nazarin abinda tayi jotting cikin littafinta. Sallama ta ji a kanta da wata lallausar murya kamar ba ta namiji ba, da sauri ta dago ta kalli wanda ke tsaye a kanta, kallo daya tayi masa ta gane shi, coursemate dinta ne amma bata san sunan shi ba. Ta amsa sallamar sa tare da maida kanta kan littafin ta, yaron ya cika kyau kamar aljani, da ganin sa ruwa biyu ne ko kuma bafillace. Cikin lallausar turancin sa ya ce "Ma'am, ki taimaka min da laccar da kika rubuta inyi photocopying, i missed alot from it" Sa'ade ta zumburo baki "bana bada aron littafi na" murmushi yayi ba tareda ya ji haushin abinda tace ba, kawai sai ya sa hannu ya dau littafin daga cinyarta ya juya ya soma tafiya.
Sa'ade ta mike da sauri ta bi bayan shi tana fadin "Malam...malam" "sunana Mr. Sa'id ba malam ba" "to ni ina ruwa na da sunan ka? Ka bani littafi na" yayi kamar bai ji ta ba, ya nufi wani shago da suke photocopying, Sa'ade bata yi kasa a gwiwa ba wajen binsa tana ta mita "haka kawai sai ka daukar mun abu ba izni babu yardata? Don baka san wanene Yayana a jami'ar nan ba wallahi sai na sa an baka carry-over" bai san sanda dariya ta kubuce masa ba data fiddo fararen hakoransa, yarinyar akwai wauta kamar diyar fari ga magana cikin shagwaba.
Ya hadiye dariyarsa ya mika wa mai hoton takarda littafin ya fada masa yayi masa photocopy sannan ya juyo ya dubeta da wani irin kallo. "A'a spill-over zaki sa a bani ba carry-over ba. Sa'adatu Hashim I loved to be your friend" zaro ido tayi na mamakin inda ya san sunan ta, sai ta tuna a jikin littafin ya gani, ta kyabe baki tace.
"Allah ya sawake in yi abota da namiji, matan ma sun ishe ni kallo ne balle kai sungumemen kato?" Yayi dariya yace "ko sai na yi kamun kafa da Yayanki mai jami'a?" Wani kallo tayi masa na sannu sarkin tsautsayi, sannan ta juya tana cewa.
"In ka so ka kwada littafin ka cinye na bar maka".
Ta kama hanyar komawa hall.
Tana zama laccara na shigowa suka fara karatu, sai ga wanda ya kira kansa Mr. Sa'idu ya zo ya zauna a gefenta, a hankali ya ajiye mata littafin ta yana murmushi, a ranta tace sai shegen murmushi kamar gonar auduga, jan aji da class sai Uncle Yariman Askira, kafin yayi murmushi ma za'a dade. Amma shi wannan sai faman murmushi yake kamar mace. Wata zuciyar tace Sa'ade! Me kike cewa? Da sauri ta ce "ba abinda nace kenan ba, nufi na Uncle Yarima yafi kowa jan aji a duniya" ta kara ankara da kalar tunanin da take yi tayi saurin toshe bakin ta tare da dafe kanta tana fadin "Yaa Ilaahy! Na tuba ya Allah!" Bata san cewa a fili ta fada ba.
Kowa a ajin sai da ya juyo ya dube ta, kasancewar an yi tsit ne ana sauraron malamin. Tayi maza ta sunkuyar da kanta tana fadin meke damu na ne? Ni Sa'aden Tsanyawa? Ba komai bane sai tunanin Yarima Sageer Yusuf Askira. Wanda ya dusar da hasken sauran maza daga idanun ta, ya dasa wani dan kankanin tsiro a zuciyarta daga lokacin da bazata iya tantancewa ba.
Sa'id bai bar Sa'ade ba, tun daga ranar ya like mata, inda duk tasa kafa cikin NTNU nan yake mayar da tasa. Ba da sanin ta ba ma ya bi bayansu a mota itada Salis bayan sun tashi karatun ranar ya ga gidansu cikin quaters ne, nan ya tabbatar 'yar wani babban Dr. Din ce kamar yadda tayi masa barazana. Kodayake ta ce Yayanta. Tun tana basar da shi amma yawan hakurin sa da yawan murmushin sa yasa dole ta soma kula shi suke harkar karatun su tare. Dama tana neman abokin karatu kuma ajin nasu maza sunfi yawa, tsirarun matan dake ajin kabilu ne.
Tun ranar da Yarima yace zai fara koya mata karatu kuma tafiya ta kama shi zuwa Lagos (Lagos State University) zai halarci annual conference. Basu kara haduwa ba sai yau da ya dawo, kuma Uche ma ya dawo daga Osun, tayi masa ta'aziyar mahaifiyar sa ta shige dakin ta a ranta tana fadin "shikenan na huta da girkau, wahalar da ba'a ce min an gode".
Uche yana tsaye yana girki ta shigo kitchen din, ruwa take so ta sha, na firjin dakin ta duk sun kare. Ta bude firij din kitchen din tana fadin "Uche what are you cooking for your Oga?" Uche ya ce "Basmati Rice and salad nake yi masa, ban sani ba ko zai so" tace "kada kasa spices din can da kake using, kayi amfani da rosemary, coriander da oregano, basu da karfi, he really likes their aroma". Uche yayi godiya da gyaran data yi masa.
Ta bude firji babu ruwan gora sai wasu manyan kwalabe, an cire takardun jiki babu rubutun komai, Uche ya bata baya yana yankan albasa bai lura da abinda take ba, ta dauka tana juyawa a hannun ta sannan ta bincire murfin zata kai bakin ta. Sai ji tayi an yi wurgi da kwalbar daga hannun ta, ita kanta saura kadan ta fadi sabida yadda Yarima ya angije hannun ta da karfi.
Kwalbar ta fashe, ruwan ciki ya malala a kasa, wani ruwa mai wani irin tsami da hamami, Yarima bai tsaya ba ya finciki hannun ta suka bar kitchen din yana ce da Uche ya gyara wurin ya fitarda duka whisky daga firinjin ya zuba a bola.
Bai tsaya da ita koina ba sai a falo ya jefata jikin Aisha-Sultana, wadda ke zaune tana danna ipad din ta. Ta dago a fusace sai idon ta cikin na Yarima, yadda ta ga idanun sa kamar na mayunwacin zaki ya kada mata 'ya'yan hanji. Muryarsa har sarkewa take ya ce "Sultana! Ban hanaki shigomin da giya gida ba? Ko kin san saura kadan yarinyar nan ta sha giyar ki? Me kike so in cewa iyayenta da ace ta sha da suka damka min amanar ta? Kuma har a firinjin kichin sabida kin raina ni?"
Sultana tayi mici-mici da brownish idanunta, "cewa nake mun yi da kai sai ka daina shiga gidan Ziyad yin zina nima zan daina shan beer?"
Da sauri Yarima ya nunawa Sa'ade hanya yace ta bace a wurin kafin ya kifta idon sa. Ai kuwa kafin ya kifta din ta kai kofar dakin ta tana jin karar marin da ya kaiwa Sultana. Ta dafe kunci ta ce "you slapped me?" Bai tsaya a wurin ba ya danna kai dakin ta ya watso su duk daga firinjin ta, ya kwalawa Uche wani mahaukacin kira, ya fito da gudu daga kitchen yana amsawa, ya nuna masa dakin Sultana yace ya kwashe whisky ya je ya zubar gabadaya.
Yau Sa'ade ta ga tashin hankali don har dare ya tsala tana jiyo fadan Yarima da matar sa har tissue tasa ta toshe kunnuwan ta tana kuka, marin da ya yiwa Sultana ya daga mata hankali ba kadan ba, ita bata san giya bace kuma ba sha zata yi ba sunsunawa zata yi taji menene? Sai Allah ya kawo shi. Tana so ta kira Fulani ta gaya mata ta tuna abinda Fulani ta gaya mata wancan karon cewa maimartaba ya ji wayar su, har yace zai dau mataki akan Yarima. Ina ga in ya ji ana shan giya kamar ruwa a gidan sa? Wa'iyazu billah.
Ko isashshen barci bata samu ba yau, don haka washegari ko karin kumallo bata tsaya yi ba ta riga kowa ficewa a gidan ko Salis bata jira ba, duk nisan dake tsakanin gidan su da cikin makaranta ta gwammace ta taka a kasa data kara ganin fuskar Yarima mai zuwa yin zina ko matarsa mai shan giya kamar yadda suke cewa.
Sa'idu ya ganta duk a birkice, ya bata wuri ta zauna, "hi friendy, me ya sameki haka?" Kawai sai ta saka kuka tace "don Allah ka san inda ake shiga motar Askira?" Ya ce "ni ko sunan garin ban taba ji ba" ta sake rushewa da kuka, yayi-yayi ta gaya masa abinda aka yi mata ta ki, har malamin su ya shigo suka fara darasi, dole ta tsagaita da kukan ta bashi hankalin ta, don inda abinda ta ki jini a duniya to carryover ne.
Da wuri suka gama lacca yau, tace da Sa'idu gida zata koma, da in sun gama lacca da wuri maimakon su tafi gida lab suke zuwa suyi research da ya shafi karatun su, yace ina direban ta tace ba shi ya kawo ta ba da kafarta ta taho, kuma ta baro wayarta gida balle ta kira shi ta gaya masa inda take. Sa'idu yace "do me a favour to drop you at home, tunda naji kina zancen zuwa Askira bazan barki ki tafi ke kadai ba".
Ya dage da nacin sai ya kaita, ta san Sa'idu zuwa yanzu yaron kirki ne mai kokari da son taimakon ta, don haka ta amince ta shiga motar sa kirar civic suka karasa gida.
Sa'idu na yin parking daidai Yarima ya zura mukulli jikin motar sa zai bude, yayi mugun hadewa cikin danyar shaddah ruwan madara samfurin excelcior (London). Wadda ta sha aiki da zare ruwan kasa irin na sarauta. Gilashin idonsa ya zare a hankali don tabbatar da Sa'ade ce yake gani a motar wani ko wacece? Fasa bude motar yayi ya kafa musu manyan lumsassun idon sa har Sa'idu ya kashe motar Sa'ade ta bude ta fito tana masa godiya. Sa'idu ya so ya fito ya gaida Yayan Sa'ade amma yadda yaga fuskarsa kamar hadarin da ya nausa yayi gabas dole ya kama kansa, ya ja motar sa da gudu ya bar harabar gidan don kwarjinin Yarima da haibar sa da cikar kamalar sa kadai ya tabbatar masa ba karamin mutum bane, kada yaje ya gane shi ma wani abu ya samu karatun sa, duk da ya so ya fito ya gaisheshi ya gaya masa taimaka mata kawai yayi shi dan ajin su ne, amma ina! Tsoro ya hana shi. Makarantar ma bai koma ba ya gudu gidan su a unguwar Maitama.
Ta gaban sa Sa'ade ta zo ta wuce amma ga mamakin sa ko kallon sa bata yi ba ta wuce ciki. Mamaki ya kusan kayar da shi, bin bayan ta yayi cikin takunsa na kasaita. Tana saka kafa a dakinta ta turo kofar yasa hannu ya dafe kofar.
Sai ta sakar masa, ta juya ciki ta na kokarin sauke jakar dake goye a bayan ta wadda ta lamushe dukkan komatsanta harda laptop.
Muryar Yarima har tsakar kanta, babu alamun wasa ko kadan a tattare da shi. Zata iya rantsewa bata taba jin sa yayi magana da irin wannan muryar ba. So furious, angry and jeolous.....!
"Sa'adatu who is this boy?"
Bata san yaya aka yi ba, bata san wa ya kitsa mata ba, kawai sai ta samu bakin ta da cewa "saurayi na ne" bayan ita kanta bata gama sanin ma'anar kalmar saurayin ba. Kawai ta san ta tsani Uncle Yarima ne yanzu, tunda dukan matar sa yake yi, in ta sha giya ai shi ya bata dama. Idanunsa sun rikide sun juye zuwa wani yanayi da bazata iya fassarawa ba. "Look into my eyes...and tell me he's your boy friend" kokarin ja da baya take. Data rasa mafita, ga zuciyarta na wani irin azalzala da mixed feelings; haushi, tsana, da zazzafar soyayyah duka a lokaci daya, kawai sai ta saka kuka.
"Ni dai a maida ni Askira, wallahi na gama zaman gidan ku"
Yarima ya ja da baya sabida da karfi ta fasa kukan. "Da mu kayi miki mene?" Ya fada yana hararar ta, in wani yaji irin kukan da ta fasa tsammani zai yi wani abun yayi mata. Ba ta ce komai ba sai cigaba da kukanta. Da zata iya da ta ce dashi sabida dukkanku fasikai ne marasa tsoron Allah. Amma ta san ko giyar wake tasha bazata iya dubar tsabar idon Dr. Sageer ta gaya masa haka ba. Apart from all these she respects him so much.
Yana da wata irin kima a idanun ta da bata san yaushe ta samu matsugunni a zuciyarta ba.
Tafi danganta hakan da kulawar sa da kyautatawar sa gareta.
Yarima ya dubeta a fusace, ya rasa yanayin da yake ciki yau, amma ya tabbata bai taba ganin abinda ya bata masa rai a duniya irin Sa'adatu da saurayin ta a mota ba, yaga yadda hawaye ke gudu akan kundukukinta kai ka ce wani mugun abin aka yi mata. Ya nunata da dan yatsa ba tare da ya bari hawayen da take zubarwa sun yi tasiri akan sa ba
"Yau ta zama rana ta karshe da zai kuma tako min gida, ba shi kadai ba kowanne rubabben saurayin ki ma, in ba haka ba in gayawa Fulani da maimartaba su cireki a makarantar su yi miki aure tunda hakan kike so".
Sa'ade ta zaro ido abin dariya abin tausayi "Uncle Yarima wasa nake ba saurayi na bane ba, wallahi, dan ajin mu ne" ya juya ya fice bai saurareta ba, damuwar duniya Sa'adatu ta shigeta, ba abinda take tsoro, taki jini take kuma gudu a rayuwar ta irin AURE!
Saida yayi kwana uku bai kara kula ta ba, bai kara nemanta ba, he's really suffering a ruhi da zuciyar sa akan ganin Sa'ade da saurayi akan dalilin da bai sani ba. A haka su Sa'ade suka fara jarrabawar karshen zango babu shiri ko kankani tsakanin ta da Yayan nata Yarima.
Ranar da sukayi takardar karshe ta kira Fulani ta gaya mata, Fulani ta gayawa maimartaba, shikuma ya kira Yarima yace yasa direba ya kawo Sa'ade gida tayi hutu. Yarima yace dama shima zai shigo Askiran jibi, zai taho da ita da kansa.
Sa'adatu na kwance a gadon ta tana karanta mujallar turanci ta 'Thrills and Boom' taji knocking a kofar ta. Ta gyara kwanciyarta da dankwalin ta daya cire sannan tace "yes". Yarima ya sanyo kai a dakin, t/shirt ce a jikin sa fara kal an rubuta Marks&Spencer da bakin rubutu, sai bakin wandon jeans mai kauri. Hararar ta Yarima yayi sannan ya jingina da kofar, a hankali ya ce.
"Sabida na hanaki kula samari, shine kika daina gaishe ni ko?"
Sa'ade ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, amma sosai taji kunya, wai wa yace ma Uncle Yarima Sa'idu saurayin