Showing 87001 words to 90000 words out of 117873 words
Ba su taba ganin GIYA a fili ba, amma kallo daya suka yi wa kwalaben da kuma yanayin da ta ke ciki suka gane komai. Ko da ma can suna da labari. Kunya! A wurin Yareema kamar ya ce da kasar ta tsage ya shige. Allah ya so shi yan rakiyar sun tsaya daga waje, yau da ya gama tozarta a rayuwarshi.
Maimartaba sai kawai ya juya ya ce da Fulani, Bana zama a inda ake saba wa Allah, sannan yata ma ba za ta zauna ba. Ku juya mu tafi.
Yareema ya sha gabansa yana roko.
Alaguburo, Allah Kawun jo na tuba, na bi Allah na bi ku. Zan dauki mataki a ba ni dama ta karshe. Nan shi ne gidan Saadatu sabida cikin makarantar su ne. Ita na riga na kama mata wani gidan a Maitama, kusa da wajen aikinta.
Maimartaba ya yi tsaki ya fice, amma Fulani ba ta fita ba. Ya ce da dogarawan da ke bakin kofa a nema masa hotel din da zai sauka gobe da asubah zai juya inda ya fito.
Fulani ta ce da Yarima wanda ya zauna ya dafe kansa da dukkan hannayensa.Bai taba wulakanta irin yau ba. (Don ma ba shi aka kama a gidan Dr. Ziyad ba ke nan!) Kunyar duniya kenan da tozarcinta kafin a je lahira. Me ye riba a kin bin umarnin Allah kowanne iri ne? Bai san ya zai yi da Sultana ba, ya yi fadan ya yi nasihar, ya yi barazanar duka a banza. Har duka ya yi duk da ba girman sa ba ne. Nadamar nashi laifuffukan suka kara lullube shi. Mai yiwuwa ta nan Allah yake kama shi kan nasa laifin. Don kuwa duk da halin ta yana son kayar sa. A fili yake fadin,
Astagfirullah! Astagfirullah!!.
Ya kuma alkawarta ma ransa daga wannan ranar duk wani sabon Allah ya bar shi. Sultana kuma zai dauki mataki na karshe a kanta.
Fulani ta dafa kafadarsa, Ka kwantar da hankalinka Yareema, zan ba shi magana. Amma tunda ya ce ba zai zauna ba, to da gaske ba zai zauna din ba. Ka yi hakuri ka tashi mu je ka nema mana masauki, ita Saa zata zauna tare dasu Fanna zan bashi hakuri.
Tuni Fanna ta janye Saadatu zuwa dakinta wadda ke rufe cikin alkyabba ba ta san a kan me ake cece-kuce ba. Yareema ya mike yana hararar Aisha-Sultana wadda ke sakar masa murmushi cikin maye.
“Darling you.you are back?
Bai ce mata komai ba ya bi bayan Fulani suka fita.
Hotel din TRANSCORP HILTON ya kai su, ya kama musu daki na musamman kwana daya.
Saadatu ba ta san su Fulani sun juya ba, ita da Fanna kawai aka bari a dakin, ta dauka tare da su za su kwana cikin gidan suna wani dakin ne. Fanna kuma sai dauke mata hankali ta ke da hira don kar ta gane abin da ake ciki.
Haka ki ka tsara dakinki ranki ya dade gwanin shaawa? In mun tafi gobe sai ki kara tsara komai na gidan yadda ki ke so tunda ke kadai za ki zauna a cikin sa. Na ji maigirmaYarima ya ce Uche ya hada kayan uwargida ya sa a mota. Ki kula da cikin mijinki ta fannin girki bana jinki, na san Yareema ya gama morewa.
Haka ta yi ta hilatarta da daddadar hira har Yareema ya je ya dawo daga kai su Askirama Hilton. Ya leko kadan ya ce da Fanna,
In kin gama direba yana jiranku a waje zai kai ku inda za ku kwana.
Fanna ta gurfana tana godiya hadi da kirarin da suke yi masa, sannan ta dau jakarta tare da cewa da Saadatu.
Sai mun zo suna.
Idon Saade ya yi rau-rau kiris ta ke jira ta fashe da kuka.
Ta ce, Fanna Fulani fa?
Au, ta ce a yi miki sallama sun tafi masauki ita da Askirama, gobe kafin mu wuce za ta leko ku yi sallama.
Saade sarkin kuka nan da nan ta fara. Ya tabbata kenan ta shigo kwaryar sauran mata. Aure yau ya raba ta da Fulani, rabuwa ta har abada sai dai a je ziyara.
Ta yi kuka, ta yi kuka bayan fitar Fanna da ta gaji ta shiga bayinta ta daura alwala, tana jin Yareema yana ta yi wa Uche fada da harshen turanci kamar Charles Dickens ya diro Nigeria, kan don me sanda ya bugo masa waya bai gaya msa Sultana tana falo drunkard ba? Uche ya rasa kalaman kare kansa sai cewa ya ke,
“Im very-sorry Sir..
Yana so ya yi masa bayanin cewa wanka yake yi a baskwata lokacin, kuma kafin ya harhada bayanin da zai masa akan harshen sa ya kashe waya, ya bi bayan kiran network ya hana shi samun sa, ko kumfar jikin sa bai tsaya wankewa ba yasa wando ya fito kawai sai ganin motocin su yayi har sun shigo harabar gidan amma Yarima bai bashi damar yin wannan dogon bayanin ba sabida yadda ransa ya yi mugun baci. Wata muguwar tsawa ya buga masa ya ce ya bace masa da gani.
Saade ta kyabe baki ta tada sallah. Ai gara da Askiraman ya gani da idonsa, watakila shi in ya hana ta ta daina, tunda mijin nata ba shi da fuss a kanta, har nema yake a rufa mata asiri.
Ba ta san ya ya suka kare ba shi da matarsa. Ta fito ta shiga kitchen don ta sama wa cikinta abin da za ta ci ba ta gansu a falo ba, ba ta ga kwalaben giya ba. Ta dan tsaya tana nazarin falon ta ji tashin motar Yareema, ta daga labule ta leka ta waje sai ta hango shi ya yi ribas ya nufi get zai fita, Sultana tana gefensa kanta a kwance jikin kujera. Tsaki ta yi cikin jin kishi, ta ce a ranta,
Da kyar in ba shi ya dauke ta ya sa ta a motar ba, don in ta sha ta yi tatil din nan ko yatsanta ba ta iya motsawa, da ma ta gama gane shi gwani ne wajen daukar matarsa a hannu.
Ta zubo abinci iya wanda za ta iya cinyewa da Uche ya girka yanzun nan, ta zauna a dining tana ci. Shiru-shiru har ta gama ta koma daki babu Yareema. Tun tana duba agogo har barci ya ci karfinta, ta kishingide a kan gadonta, gadon yammatancinta a NTNU. A yau ya rikide ya koma na gidan aure! Kudurar Ubangiji ta fi ga haka.
Duk da bacci ta ke, amma zuciyar ta cike ta ke da damuwa, Yarima ya manta da ita cikin gidan ne ko kuwa? Ya dau matarsa sun fice. Ba ita ta bude idanunta ba sai da masallacin gidajen Malamai na NTNU suka tada sallar asubahi.
Ko da ta tashin ma da Yareema a ranta ta tashi. Ta yi zaton ganinsa a gefenta yana barci ko sallah, don ta gane shi maabocin sallah ne a zaman su na Askira kwanaki bakwai tare, kuma ya gaya mata muddin suna tare ba su ba raba makwanci, tun tana jin nauyi da kunya har ta saba da hakan cikin kwanaki bakwai da suka yi tare matsayin maaurata. Itama in ba sa manne cikin duvet bata jin dadin barcin.
Amma ga mamakinta har zuwa lokacin Yareema bai dawo ba. Tana alwallah tana hawaye, hawayen da ba ta san dalilinsu ba.
*****
Har karfe sha biyun dare yana tare da Aisha-Sultana a sabon flat din da ya kama mata a Maitama, jira yake giya ta sake ta, ta wartsake sannan su yi magana. Tunda suka zo ta ke barci, maigadin da ya daukar mata shi ya fiddo duk kayan sanyawarta jaka-jaka daga bayan motar Yareema ya shiga da su ciki, wadanda ya sa Uche ya kwaso mata.
Da ya kashe motarshi ya dauke ta a kafadunsa zuwa cikin apartment din, ya kwantar da ita bisa gado kasancewar ya yi order already an zuba komai na bukata a gidan. Haka ya zauna zaman jiranta ta wartsake, ya tashi ya yi alwala ya yi sallar isha, sannan ya zauna kiraye-kirayen waya, ya gabatar da dukkan uzurorinsa ta waya. Amma duk abin nan da yake Saadatu na makale cikin ransa. Allah-Allah yake Sultana ta farka su yi maganar da yake so su yi, ya tafi wajen Saadatu.
Sulatana ba ita ta farka ba sai karfe sha biyu na dare. Ta yi mika sannan ta hau bude idonta a hankali, sai ta ganta a bakon wuri. Ganin Sageer a gefe yana sallah, sai tsoronta ya ragu. Ta sani ko ma ina ne shi ya kawo ta kenan a lokacin da ta ke cikin maye.
Darling ina ne nan?
Ta tambaya tana hamma.
When did you get back? I missed you!.
Hararar ta ya yi, sannan ya dauke kansa. Can kuma ya dago ya dube ta cikin ido.
“My father saw you drunk!.
Sultana ta zaro ido, Oh dear! Me ya sa ba ka gaya min kun taho ba?
Ya galla mata harara, ya ce, sau nawa zan ce miki in kina son zamanmu ya dore sai kin bar shan giya?
Ta zumburo baki, sannan ta mike ta yi kan Sageer ya soma ja da baya ya kuma kira sunanta da karfi,
Sultana!
Ba ta fasa abin da ta ke ba, ta ce, Ai ni ma na gama magana, ranar da ka daina branching da yammatan bisa titi ni ma zan daina shan giya tell your Dad Im sorry.
Ya ce, Sultana na dade da bari, har na kara aure. Don Allah ki daina in ba haka ba rabuwarmu ita ce mafi alkhairi.
Sauran maganar makalewa ta yi a makoshinsa sakamakon cewa, Aisha Sultana ba ta ba shi damar karasawa ba. And then she seduce him. Da ma ya dade cikin kishirwa, sai ya kasa tankwabe tayinta da kaunar da ta ke kokarin nuna masa. Ga dukkan alamu ba ta ji cewa da ya yi ya kara aure ba, idan kuma ta jin, to ba ta fahimta ba.
Yareema Sageer bai tashi dawowa Sageer dinsa ba sai karfe hudu na sulusin dare.
Lokacin da kuma ba zai iya tafiya gida ba. Ya tuno Saadensa, da kadaicin da ya barta ciki ranarta ta farko a gidan mijinta. Amma a addinance bai aikata haramun ba sabida girkin Sultana ne, ya yi mata kwana bakwai dinta da addini ya bata babu kwange.
Ya duba agogo ya kuma dubi Sultana da ke ta sharar barci. Ta inganta masa daren jiya kamar ba gobe, iyaka iyawarta. Don dai ta mantar da shi laifinta amma duk da haka ya kasa mantawa, abu in ya hada da Maimartaba ba ya daukansa da sauki. Ya yi wanka ya tsarkake kansa ya dauro alwalla. Bai jima yana nafilfili ba ladani ya kira sallar asubah a masallacin da ke kusa da su sai ya ga bara kawai ya shiga masallacin tunda ba su da nisa daga can ya wuce gidan Saadatu, sai ya hukunta Sultana.
Ya hau dukan bayan Sultana ya ce ta tashi ta yi sallah shi zai wuce masallaci daga can ya wuce gida. Ta ce,
Wane gidan kuma? Na dauka mun yi parking zuwa nan ne?
Ya ce, Kin yi parking dai, amma mu muna can, ke da gani na sai ranar da ki ka bar GIYA Sultana.
Da haka ya fice tana ba shi hakuri, amma ko juyowa bai yi ba.
Ita ma ta yi shirin ofis ranta a bace. Ba abin da ta ke so a duniya irin Yareema Sageer. Shi kadai ne daidai da rayuwarta haka babu mai wahalar da ita a duniya irinsa. Amma me ya sa ya kasa gane cewa alcoholism is an addiction?
Tana tuki cikin hawaye har ta isa wajen aikinta da ke kan titin Aguiyi Ironsi.
Ya karya kan motar ya shiga gidan sa. Yayi horn maigadi ya taso da azama ya bude masa kofa, misalin karfe shidda na safe, yana shigar da hancin motar maadanin ta yana harhada kalaman da zai yi amfani da su wajen lallashin Saade bisa wannan babban laifi da yayi mata da bai san yadda zai yi ya wanke kansa ba.
******
MU KARASA A LITTAFI NA 4. KADA KU DAMU TARE SUKE. TAKU HAR ABADA; SUMAYYAH ABDULQADIR (TAKORI).
26|11|2021
NA HUCE..
LITTAFIN
SUMAYYAH ABDULKADIR
Hawayen da yake ta rikewa ne suka kwace masa, ya juya kadan ya dubi Rahinah wadda ke kallon bayansa a lokacin, suka kuma hada ido, ji ta yi zuciyar ta na son karyewa (rauni irin na diya mace na son mamayar ta) amma ta amince wannan shine decision mai kyau ga rayuwar ta.
Sai ta maida idanunta ta lumshe su a hankali. Tana sauke ajiyar zuciya.
Shi kuma ya sa kai ya fita daga dakin, babu ko waiwaye. Kamar yadda yake ji a ransa ba zai kara waiwayar RAHINAH OMAR a rayuwarsa ba. Ko da bayan cikar burin ta, na zama cikakkar otorhinolaryngologist.
****
Ta dauki hoton karamin kyakkyawan yaron mai kama da ubansa a komai tana kallo with so much adoration, hawaye na sauka a kan fararen kundukukin ta. Ta san yanzu ya girma, watakila aji hudu na firamare? Cikin kowanne hali dai ta san zai kula da shi. Damuwar ta ba a kan kulawar da yaron zai samu ba ne domin hakika tana da tabbacin HABIBUNAHUCHEzai kula da dansa har fiye da yadda yake kula da Hotels din sa. Damuwar ta akan yadda har gobe ta kasa kallon kowanne namiji da idanun sigaraure, kowa ya zo sai ta ga bai kai shi ba, ko farcen kafarsa bai kama ba, ko da kuwaya fi shi komai na rayuwa.
Duk da cewa ta san shi ne kawai a matsayin dalibin jami'ar Cologne ba'a matsayinsa na yanzun ba (mamallakin NAHUCHE HOTELS) amma tana bibiye da duk wani fadi-tashinsa na rayuwa tun daga ranar da ya raba ta da Dan su.
Dalilin bibiyar ne ba ta sani ba har yau, tunda ita ta ce bata son sa. Farin jini kam har bata san irin nata ba, manema ba irin wadanda Allah bai ba ta ba, kuma burin Dada shine ta yi aure tun kafin Allah ya dau ranta, amma har gobe ta kasa kallon kan sauran maza daga shi sai dan mutanen NAHUCHE. The one that took away her pride na diya mace. Wanda ta tabbatar zuwa yanzu ya manta da ita, a irin shuhurar da Allah ya yi masa cikin shekaru goma kacal da rabuwarsu.
Bata san hawaye take ba. Sai da ta ji dandanon gishiri a bakin ta. Hawayen da ta tabbatar ba za ta daina zubar da su ba har zuwa karshen rayuwarta. Idan har rayuwa ba ta koma yadda take a baya ba; with him aside.
"Auren Wucin Gadi".
"Auren kwanaki bakwai kacal". Wadanda abubuwan da suka wakana cikinsu sun fi tsayin na shekaru bakwai. Wanda ya samar da kaddarar Dan da ke a tsakani, Dan da silar zuwansa duniya ne ya yi connecting komai, ya hada zukata ya kuma raba su cikin kwanaki bakwai. Jami'ar Cologne din Jamus ita ce tushe, mafari, ginshiki na dukkan walagigin rayuwar da ta samu kanta.
-Takori
MASARAUTAR MU!
4.
SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI
SADAUKARWA
Ga 'yar uwar da muka rasa a TAKORITES. Allah ya jikan ki da rahma HASNA'U yasa aljannah ce makomar ki. Ya bamu guzurin tadda ke. Takorites bazamu taba mantawa da ke ba. Da zaman amincin da muka yi tare. Muna son ki Hasna.
JINJINA
Har kullum jinjinar taku ce dukkan members na TAKORI'S ONLINE FORUM whtspp, littafin MASARAUTAR MU jinjina ne a gare ku, nagode da kauna da kwarin gwiwa, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah.
GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a