Showing 6001 words to 9000 words out of 117873 words

Chapter 3 - Masarautar Mu 1 to 4 Complete

suke mai nuna kauyancin su tifikal, zuwa can Baba Sale ya nisa ya ce.
"Sa'ade! Ko me kika ga ya faru da bawa haka Allah ya ga damar ya kasance a gare shi, idan mahaifiyar ki ta karbe ki shikenan, idan bata karbe ki ba, ni zan rike ki tare da Hanne a cikin iyali na har iyakar nawa numfashin".
Daga yadda yake magana zaka gane ya karaya, bai san girman masarautar da kasaitar ta ya kai haka ba! Bai san sarautar babba ce irin wannan ba! Ya dauka normal sarkin kauye ne irin wanda ya sani. Masarautar Askira kuwa tana cikin manyan masarutun jihar Borno masu tsohon tarihi da yalwar arziki wadanda ke sahu na biyu a jihar ta Borno bakidaya.
Sa'ade cikin rawar murya ta ce "Baba Sale ni dai mu koma Tsanyawa.... ko ta karbe ni bazan iya zama a gidan nan ba tsoro nake ji....wallahi bazan zauna ba". Baba Sale cikin lallashi ya ce "ki kwantar da hankalin ki Sa'ade, idan ta karbe kin shine babban gatan ki, kin ga ni na tsufa, ko zan rike ki na dan lokaci ne nima wa'adina zai cika, baki da kowa a Tsanyawa bayan ni da Innar Hanne, aure zai yi miki wuya don kuwa babu wanda ya san asalin iyayen ki".
Yana rufe baki suka ji ana "gyara kimtsi mai Askira......taka lafiya Giwan Askira.....". Sarki ya shigo falon shi kadai, dogarawan suka tsaya daga waje. Kujerar sa wadda ita kadai ce kujera a falon ya je ya zauna. Baba Sale ya fadi kamar zai yi sujjadah yadda ya ga ana yi ya kara gaida sarki, sarki yai masa murmushi ya amsa da wata irin hamshakiyar kamilalliyar murya. Ya mika hannu ya yafito Sa'ade,
"zo nan kusa gare ni diya ta".
Sa'ade ta rarrafa ta isa gaban shi, ya dora hannu a kanta ya ce "yaya sunanki?" Murya na rawa ta ce "Sa'ade!" Yayi murmushi ya ce "Sa'adatu dai ko? Sannu da zuwa Askira kin ji Sa'adatu?".
Sannan ya maida hankalin sa ga Baba Saleh yace ya bashi labarin rayuwar Sa'ade a hannun mahaifin ta tun daga sanda mahaifiyarta ta bar ta. Baba Sale ya gaya masa duk irin abinda ya sani cikin nutsuwa akan Sa'ade da Baban ta, da irin yadda yadda ya raine ta cikin tsananin kulawa, ya gaya masa malam Hashimu ya gaya masa ba don rayuwa da yake zaton ta kare masa ba bazai taba baiwa Bilkisu 'yar sa ba, sabida bai taba jin dadin zama da ita ba har auren shekara biyu ya shiga tsakanin su ya kare a shekaru biyu kacal.
Ya gaya masa wahalar da yarinyar ta sha a hannun matar uban ta, da yadda ta kare rayuwar ta a talle. Sarki Yusufu ya kara jan Sa'ade jikin sa yana tunani cikin ransa "anya Bilkisu ce da ya sani? Zata haifi Da ta tafi ba waiwaye shekaru goma sha biyu? Kuma bata taba gaya masa ba daidai da kuskure, ya san dai a bazawara ya aureta amma bai san komai ba bayan wannan akan auren nata na baya. Bata son zancen ko kadan. Shi kuma nan duniya sai ya samu zuciyar sa da matsananciyar kaunar Sa'ade, wadda tausayi da soyayyar uwar ta shine sila.
Ya tambayi Baba Sale asalin malam Hashimu, Baba Sale yace "kowa ya san Malam Hashimu bakon haure ne a Tsanyawa babu wanda ya san asalin sa, amma a sanda yake bashi wasiyyar kawo Sa'ade wajen Innar ta ya gaya masa shi dan asalin garin Damaturu ne.
Daidai lokacin da aka daga labulen falon, ta shigo cikin taku na kasaita, sanye cikin farar alkyabba da hular alkyabbar a kan ta. A kasan alkyabbar wani kasurgumin bakin leshi ne mai matukar nauyi. Doguwa sambaleliya, fara sol, kamar da ka taba ta jini zai yi tsartuwa. Fatar jikin ta a murje, ga tsayi ga zati, sannan ga kira ta matan Shuwa-Arab tattare da ita. Akwai barima ta danyen gold makale a gefen hancin ta. Manyan fararen idanun ta sun sha 'kohl' sai walainiya suke suna fidda wani sheki na musamman.
A hankali take taku har ta isa gefen mijin ta ta zauna. Kuyangin ta suka tsaya daga waje. Ta bi mutanen dake sunkuye a gabansa da kallon mamaki, don sun fi kama da normal talakawan gari, amma a falon ganawar sarki da iyalin sa? Kuma saboda su ne aka kirawo ta?
Idanunta suka kai ga birkitacciyar bakauyiyar yarinyar dake zaune gefen sarki, ya rike ta cikin jikin sa. Ta tsurawa yarinyar manyan idanun ta tana kallon ta, idanunta a hankali suke kara girma suna fidda mamaki da al'ajabi. Da gaske ne da aka ce duk inda uwa ta ga dan da ta haifa cikin kowanne hali sai jikin ta ya bata.
Babu wanda ya ce mata uffan tsakanin sarki da Baba Saleh, har saida ta dauke idon ta daga kan yarinyar ta sunkuyar. Wani abu yammmm! Na bin jikin ta. Tsigar jikin ta na tashi. Ta kifa fuskar ta cikin tafukanta, cikin zuciyar ta take fadin......
"dama na san ko bajima ko ba dade zata zo ne da kafafun ta, muddin ni na haife ta. Amma ban zaci a wadannan kananan shekarun ba, na dauka dai sai ta mallaki hankalin kanta zata kawo kanta".

Sarki Yusufu ya kama hannun Sa'ade ya sanya cikin nata. Expression na fuskarta kadai ya gaya masa duk abinda Baba Saleh ya fada gaskiya ne.
"Jeki ga mahaifiyar ki Sa'adatu, ki ji dumin jikin ta, kamar yadda kowanne da yake jin dumin jikin uwar sa".
Sa'ade ta kasa yin hakan, ganin yadda matar ta cire hannu daga fuskar ta ta bubbude mata ido, kamr tana gargadin ta da yin hakan. Ta dubi Baba Saleh da kakkausar murya tace.
"Kai dan aiken Hashimu! Ka koma ka gaya masa yadda Bilkisu bata taba son sa ba, haka bata son abinda ya fito daga jikin sa, bana bukatar 'yar sa ya cigaba da rikon abar sa shi kadai".
Sa'ade ta fashe da kuka, Baba Saleh kuma ya sunkuyar da kai. Sarki Yusufu ya daga ido cikin firgici ya dube ta, anya Bilkisun sa ce wannan? Wadda ko barorin ta bata dagawa murya tsakanin ta da kowa kyautayi ne da mutuntawa? Balle dan da ta haifa? Dan da kullum take adduar Allah ya bar mata ko guda daya?
"Ko da Hashimun ya mutu bazaki rike 'yar da kika haifa ba?"
Muryar sarki akwai fushi da fusata mai tsanani a cikin ta a lokacin da ya jefe ta da wannan kalami, mikewa tayi tana shirin barin falon ko kadan zuciyar ta bata russuna ba, "idan ya mutu yana da dan uwa a garin Damaturu, a kai ta can ya rike masa". Har ta kai bakin kofa sarki ya kira ta da kakkausar murya...
"FULANI BILKISU!"
Ta dakata, amma ba tare da ta juyo ba.
"Zo ki kama hannun 'yar ki ki tafi da ita sassan ki, ki bata duk kulawar da uwa zata baiwa danta, tana karkashin amana ta, zamana zata yi a gidannan daga nan har karshen rayuwar ta, a bisa kulawa da kiyayewa ta".
Yana fadin hakan ya mike tsaye, ya dubi Sa'ade da ke kuka wurjanjan, "daina kuka Sa'adatu, mahaifiyar ki ce bazata cutar da ke ba, dauki kayan ki ki bi bayan ta". Sa'ade ta share hawayen ta da bayan hannun ta, ita in aka ce wannan galleliyar matar mahaifiyar ta ce ma wani iri take ji, tsigar jikin ta har tashi take, tsoron ta take ji sosai, gata da manyan ido da wani irin kwarjini, ita gara ta bi Baba Sale su koma Tsanyawa, abinda ta fada cikin kuka kenan, amma Baba Saleh ya girgiza mata kai ya ce.
"Bi ta Sa'ade, kiyi mata biyayya a bisa dukkan umarnin ta, aljannar ki na tare da ita".

Ta dauki tsummokaranta tana waiwayen Baba Saleh, shikuma yana yi mata murmushi, tuni Fulani Bilkisu ta fice, kuyangin ta sun mara mata baya, sai da ta hada da gudu-gudu ta cimmasu, Sarki Yusufu yace da Baba Saleh za'azo a kai shi masauki ya huta har zuwa iya kwanakin da ya ke so, sannan zai sa a maida shi har Tsanyawa a motar gida, zai bada sallama a bashi, Allah ya kai shi gida lafiya, yana yi masa fatan hutu mai dadi cikin masarautar sa.
Baba Saleh ya zube yayi ta godiya, a take dogarawa suka kai shi masaukin bakin sarki, aka wadata shi da abinciccika da ababen sha na alfarma, sittiru da duk abinda zai bukata. Amma duk wannan bai dame shi ba, tunanin sa na ga halin da Sa'ade zata kasance a hannun mahaifiyar ta.
Wadda ta nuna a fili bata bukatar ta cikin rayuwar ta.
Bai san laifin da Malam Hashimu yayi mata ba, amma ya lura kiyayyarsa ce ta shafi 'yar sa.
Abu daya yake da yakini yake kuma dan kwantar masa da hankali idan ya tuna ita ta haifeta da gaske, duk kin ta da ita bazata cutar da ita ba, sai dai ta kasa nuna mata soyayya.
Yana tausayin Sa'ade sabida bata taba dandana kaunar UWA ba, bata taba jin dumin uwa ba, ga wahalar data sha hannun Laure, sannan yanzu ga ta ga uwar amma bata kaunar ta.
Zuciyar sa tayi maza ta ce masa "ba ita ce bata so ba uban ta ne bata so, da sannu in sun zauna tare Allah zai musanya zuciyar ta zuwa alkhairi akan 'yar ta"..
Da kyar ya samu ya runtsa a wannan dare sabida tunanin Sa'ade, hutun da aka ce ya zauna yayi ya ga bazai iya ba, washegari ya gayawa mai kula da shi ya gayawa maimartaba yau zai koma garin su. Sarki yasa aka yi masa goma ta arziki, aka cika masa bayan mota hilux, sannan ya damka mishi kyautar kudi da sittiru masu yawa.
Suka kama hanyar zuwa Tsanyawa a mota hilux zuciyar Baba Saleh cike da alhini na tausayin Sa'ade.
****






Sa'ade na bin kuyangin Fulani a baya, fada nan fada can har suka dangana da wani babban gini, kamar gida guda bangare guda haka, aka bude kofar Fulani ta sanya kafar ta kamar wata Dawisu sabida yadda take taku su kuma suna biye da ita, kyawu da kayatuwar ginin yasa Sa'ade sakin baki da hanci tana kallo, har tana tuntube saura kadan ta fadi.
Manyan faluka suka rika wucewa har suka tadda wanda daga shi kuyangin suke da shamaki, sai guda daya daga cikin su ce ta bi bayan Fulani, bata jima ba ta fito tace da Sa'ade wadda ta tsaya a inda ta ga kowa ya tsaya itama, ta biyo ta ta kai ta dakin da zata zauna.
Inda Fulanin ta shiga nan ta ga sun shiga, wani (english parlour) ne komai fari sol har labulaye da kujeru, kilishin falon ne kawai launin makuba shima da adon fari da baki a jiki, kofofi ne wajen guda hudu a falon bata san a wanne Fulani ke ciki ba, kuyangar ta bude daki daya suka shiga. Sa'ade ji tayi numfashin ta ya tsaya a wuyanta sabida kyawun dakin da tsaruwar sa, komai dake cikin dakin kalar blue and light pink ne, ga wani shimfidadden gado na sarauta (royal bed) da ya ji shimfidu na alfarma.
Kuyangar ta shiga bandaki ta hada mata ruwan wanka, tazo ta kama hannnun ta ta kaita har gaban kwamin wankan, ta nuna mata yadda ake amfani da komai don ba sai da bayani ba kallo daya za'ayi wa Sa'ade a fahimci bata taba alaqa da irin wannan muhallin ba a rayuwar ta. Ta kasa boye firgici da razanar data ke ciki.
Kuyangar tace zata cuda mata baya. Sa'ade ta zaro ido tace "bana so". Ta fita ta barta bayan ta tattare tsummokaran data tube ta hada da kullin kayan ta ta fita dasu ta zubar kamar yadda Fulani ta bata umarni.
Kafin Sa'ade ta fito ta ajiye mata dogayen riguna daidai tsayin ta guda biyu a gefen gado, sannan ta shigo mata da abinci lafiyayye kala kala akan tray. Ta zauna har ta fito daga wankan daure da tawul din data nuna mata sannan ta gaya mata nan ne dakin ta, ba koyaushe zata ga Fulani ba, in tana son ganin ta zata nemeta da kanta, ba'a yarda taje ko'ina bayan dakin nan ba, duk abinda take so ita kuyangar zata dinga shigowa tana yi mata, ta gaya mata cewa itace amintacciyar Fulani, kuma ita kadai ke shigowa wannan sashen, sunan ta "Fanna".
Sa'ade ta gyada mata kai alamar ta gane, sannan ta ce da ita "ga hijab nan da darduma kiyi sallah".
Bayan fitar Fanna Sa'ade zama tayi a bakin gadon a dofane tana ta kallon dakin, sai ta ji duk alatun dake cikin sa bai burgeta ba, ta ji duniya tayi mata kunci, kewar Baban ta mai son ta, ta zo ta lullube ta. Soyayyarsa ta fi mata duka wannan alatun da babu soyayya a cikin sa sai kiyayya zallah.
Amma duk da wannan damuwar dake cin ranta, ba abinda zuciyar ta ke hango mata sai fuskar Fulani Bilkisu ma'abociyar zati da kamala, da wani irin feelings mai fizgar zuciya tamkar maganadisu (maternal love). Wata irin soyayya da bata taba ji akan kowa a duniya ba bayan Babanta, wannan soyayyar har ta zarta wadda take ji akan Baban ta. Shine abinda ta ke ji akan Fulani Bilkisu!
Ta lumshe ido tana hasaso yadda ta zazzaro mata ido kada ta zo kusa da ita, a kuruciyar Sa'ade ba don komai bane sai don ita 'yar kauye ce. Tana kyankyamin ta ne kawai. Tasa a ranta daga yau kullum zata dinga wanka, don Fulani ta daina tsantsamin ta.
Ta mike ta sanya hijab ta tada birkitacciyar sallarta, wadda ko kadan ba daidai take yin ta ba, sannan babu wani karatun sallah na azo a gani, karewa ma "BA-SIM-MI'ARA" take karantawa a cikin sallahr.
Data idar da azahar da la'asar sai ta ja farantin abincin da Fanna ta ajiye mata, ta ci iya cinta kunnenta kamar ya gutsure don dadin naman tolo-tolo, data gama ta je ta wanke hannu ta dawo ta kwanta a gadon da tun dazu take son ta ji yaya yake? Wane irin laushi gareshi haka da tun dazu ya ke fizgar idanun ta? Wani barawon barci yazo yayi awon gaba da ita, sau biyu Fanna tana shigowa, ta fidda farantin ta kunna mata iyakwandishan wanda ni'imar ta ya kara armasa mata barcin.
****

Sai safah da marwa take a dakin barcinta, ta kasa barci, ta rasa abinda ke mata dadi. It's very unusual maimartaba ya shigo sassan matan sa. Amma yau sai kawai ta ganshi ya shigo har dakin barcin nata, ba zaton ta ba tsammani.

"Zuwa nayi ki gaya min abinda matsayi na bai kai na sani ba, wanda ya faru cikin rayuwar ki ta baya".

Ya fada yana mai zama a gefen hamshakin gadon ta.

Gabadaya ta zama upset, daga rana zuwa dare, fuskarta kamar jikakkiyar takarda, ta zama yellow, kasancewar ta jazur, damuwa kwance baro-baro, ga wani tsohon kwantaccen bacin rai da ya dawo mata sabo.
"Allah ya huci zuciyar ku, Allah ya huci zuciyar Askirama!".
(Askirama na nufin 'mai Askira' da harshen Kanuri).
Ta cigaba da fadin "Al'amarin bashi da muhimmancin da zaku san shi, shi yasa baku san shin ba. Sabida ban taba daukar sa da muhimmanci ba, ban kuma taba zaton wannan 'yar zata biyo ni ba, don nasan uban ta ko za'a dora masa wuka a makoshi, akan ya bani ita, ba zai taba bayarwa ba".
"Sai kuma mutuwa ta yanke muku dukkan kudirin ku ke da shi, akan baiwar Allah, wannan ya isa ya nuna muku cewa karfin kudura da irada naShi ne, bawa bai isa ya tsarawa kansa rayuwa ba, face abinda Ubangiji ya tsara masa".
Mai martaba ya fada mata a tsanake.
Ta sunkuyar da kanta, tana wasa da yatsun hannun ta, bata ce komai ba.
"Ki gaya mini duk abinda yakamata na sani akan yarinyar nan, tunda dai kin yarda sunnah ki kai kika haifeta, kada ki zama azzalumar Uwa, wallahi Allah bazai bar ki ba".
Fuskarta tayi jajawur kafin hawaye su cicciko idon ta.
"Ran ka ya dade bana son tuna labarin nan, bana so. Ba abun fade a cikin sa, me kake so ka ji? Yes, aure na yi na haife ta, amma ban taba son uban ta ba! Sau daya ya taba kwanciya da ni bisa fin karfi har na samu cikin ta. Kana so ka ji cewa Babana biyan bashi yayi wa ubanta da ni? Ya aura masa ni a matsayin filin sa da yake bin sa bashi?"
Maimartaba ya nuna abin bai bashi mamaki ba, a fuska da muryar sa babu komai, yace "to ita yarinya meye laifin ta? Bata zo duniyar ba lokacin,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login